Showing 90001 words to 93000 words out of 115099 words
Chapter 31 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
tare da ita.
Alhaji sada ai ni wanan yarinyar yanzu ban ma san irin alherin da zan saka mata dashi ba a wanan duniyan.
Nan dai sukai ta farinciki da jin dadi a tsakanin su har suka watse acikin farin ciki kowa ya hari nashi tsabgan cikin jin dadin junan su.
****** ********* ******
Sati dana fadawa Asabe ya cika tun da safe anty lami ta karasa gidan Asabe din cikin masifan son karban kudin ta a gurin ta.
Amma sai bakar magana da cacan baki ne yabiyo baya har tana ikirarin taga uban da zai kwatar mata kudin ta a garurin ta.
Tabar gidan rai a bace takirani a cikin masifa take fada min yadda sukayi da Asaben nake bata hakkuri nace ta koma gida kada ta damu da zancen ta.
Aiko tai cikina da masifa ban san yaya akayi ba na daka mata wani irin tsawa sai da ta kadu cikin mamaki take kallon wayan kamar nice a fili take kallona.
Haka kawai taji zuciyar ta ya aminta da magana na tace don Allah maryam kiyi hakkuri zan bar zancen kamar yadda kikace din.
Ai ba, ai wasu awanni ba taji ana kwada sallama a kofa akece mata gidan Asabe ne ya kama da wuta kurmus komai na gidan ya kone amma ga kudin ta an samu wasu kudi a gidan gurin kashe wuta anji tana fadin kudin lami ne akai mata abinta.
Mamakine sosai yakama anty Lami tace ita Asaben ne take fadin haka yan sakon sukace ai ta zare ne ta koma kamar mahaukaciya da ita sai sambatu kawai takeyi.
Asabe dai bata tsira da komai ba a gidan ta har ginan gidan saida ya ruguje gabaki daya haka ta tashi ba komai.
Ga kuma kudin da da bakin ta take rokon mutane akaiwa Lami kudi kudin Lami ne.
Sai ga anty Lami ta bugo waya muna zaune take labarta muna yadda akayi kuma wai an rasa ta ina wuta ya shigo gidan don a lokacin ma babu wutan nepar a gari.
Nace kudin ki dai sun dawo gare ki ko tace eh nace barta kawai kadan ta gani gobe ma ta kara in halinta ne .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
2โฃ8โฃ
Gobaran Asabe duk yabi gari kowa da abinda yake fadi akan zancen gobaran gidan ta da ba, a san dalilin faruwan shi ba.
Sai dai ta koma karba ta tabu saboda irin yadda take faman sake magana ita kadai tawa kanta tujara .
Lami kudin ki dai nace bani basuwa, yanzun kuma gashi na baki kuddin ki ga kuma kaya min ajiye a gida kamar kullun.
Lami dake da Abbas sai na ga wanda ya isa ya kwatar maku kudinku a hannu cikin fadin garin nan.
Ganin ta soma haka yasa aka kamata akadaure ta cikin daki a gidan iyayyen ta duk da suma ba damuwa tayi da al,amarin su ba a matsayin su na iyayyen ta ba a baya.
Amma babu yadda zasuyi ance naka sai naka ranan wuya kuma sai naka shine kawai zai tsaya akan ka.
Haka suka fara shiga fita a kanta don nema mata lafiya gurin wani malamin suka tafi sai bayan yayi abin da zaiyi ne yake masu bayani abinda ke faruwa.
Yace daukan magana tayi shine ya koma mata ta taba wanda sukafi karfinta ne yasa wanan iftilain ya sauka mata.
Aka dan fara kus kus ana fadi ba, a tambaye kan fitinan ta da anty lami da sukayi na kudi.
Haka dai zance yai ta yawo kowa da abinda yake fadi akan zancen duk da basu san komai ba .
Sun yanke shawara tunda basu samun gani na kamata yayi su aika mace don zasu tafi gano masu gaskiya yadda abin yake.
Hajiya saratu wata abokiyar sana, an su kuma yar siyasa ce aminiyar su, suka turo gurin na tafe da abin arziki.
Kyauta ce ta ban mamaki sukai min wanda ban taba zaton samun shi ba a rayuwana suka aiko min dashi.
Ya kasan ce ranan Jumma, a ne, Muna zaune ni da Umma muna kallo a falo bayan mu kare sallah
Maigidan da yara sun tafi cikin gari mota ya tsaya a kofan gidan mu wanda yanzu har makwabta sun saba da zuwan bakin motoci dake yi na manyan mutane a kofan gidan mu.
Wanda da farko idan sun gani suke shiga gulma ko a ina na samo manyan mutane haka nake hurda dasu.
Hamshakiyar matar ta shigo gidan cikin tafiyan kasaita irin ta manyan mata sai faman raraban ido take yi sako da lungu na gidan namu.
Mun tare ta a cikin mutunci tare da girmamata wanda dama haka rayuwan ta yake bukata ita a dinga mutanta ko yaushe.
Ta zauna kamar mai kyankyami gidan namu sai bayan ta zauna dakyau take cewa gun malama maryam nazo don Allah.
Umma tace to sannu da zuwa ta dubi umma da kyau tana tuhumar ko itace maryam din da tazo gurin ta.
Amma sai taji Umma tana cewa ga tanan zaune a gaban ki itace maryam din ai.
Wani kallon mamaki ne tai nmmin na jinki yafi ganin ki tafurta a fili karamar yarinyace ashe ke da wanan baiwan.
Tace damaan turo ni ne zuwa gare ki ko zaki iya tunawa da mutanen da kika taimaka sati biyu da ya wuce ?
Shiru nayi ina nazarin ko wa take nufi ya aiko ta zuwa gare ni bata fada ba kuma ban fahinta ba sai dana lura cewa so take ta gwada ni taga abinda suka fada mata akaina.
Hannu na na hada guri daya nadan fara murzawa a hankali sai ko na fara hamma Umma dake gefe tafara magana irin na manya tana cewa.
Ikon Allah sannun ku da zuwa ashe kuma kuna tafe a yanzu sannuku, sannuku da hanya.
Aisha ce ko Rukaiya ko babban yaya nace Umma kuna lafiya yaya jama, an ku ?
Ta amsa cikin jin dadi da Alhamdullahi sannu da zuwa matar dai da yake goggan yar duniya ce ta saba da ganin irin haka.
Sai wani kallo take min kamar bata yarda da abinda take gani ba, zahiri.
Umma take ce anzo gurin bakuwar mu ko sai nace Umma mukkadarasiya ce take magana nazo ne na bada sako na koma don ina akan tafiya ne.
Hajiya dama baki tsaya kina wanan ba don ke yar soko ce zancen ki akan naki kayan da kike kokarin aikawa hakan bazai yi ba agare ki don kayan ki duk haramtatune dake da malka da kika ba sakon duk kasan saudiya zasu kama ku idan har kinyi yunkuri tura ta dasu cikin satin nan.
May yasa kuke son yin kudi ko ta halin kaka dukiya bakomai bane sai tarin wahala a duniya da lahira amma ke kin kuke da wanan harkan bayan kin san ba alheri bane.
Yaran mutane da kike turawa a kasa mai tsarki da kasashen turawa da zaki daina wanan harka da zaifiye maki alheri ki fada harkakin na tsiya dakike yi da farko don sabuwar gwaunatin da za, a kafa idan kin matsa zaki samu shiga sosai don zasu dama dake.
Kallo na take a cikin mamaki nace hajiya kina ganin sakon da Alhaji sada ya baki na kudi da mahaukaciya ki kawo min kamar sun min yawa ko ?
Kada ki soma taba kayan daba naki ba musan man irin wanan don zaki iya samun matsala babba a rayuwan ki.
Yarda da son ki gano masu gaskiyan al, amari yasa suka turo ki nan don su tantance daga gare ki.
Amma kuma ga shedan yana son rudinki ki aika wani abinda ba daidai ba akan sakon.
Jikin ta yai sanyi sosai nace idan kin koma ki fada mai duk ritsi nan da jumma, a ya tabbatar da ya canza akalar maboyar dukiyan shi don daga cikin ku yan kasuwa kuma na tare dashi suna mai zagon kasa idan yaji walillahi hamdu.
Ki shirya zuwa Abuja ranan laraba ranan samu ki shiga da ahabiyu akwai alherin da zai samay ki kan abinda kika dade kina nema acan.
Nabarki lafiya zan koma dama nazo ne na walwale maki tuhumar dakike yi akan abinda idon ki ya nuna maki.
Ajiyan zuciya ta sauke a hankali tana cewa ai min afuwa kusan dan adam da kwankwato amma yanzu na sheda komai da idona yadda ya kamata.
Kuma ina fatan za, ai min afuwa sai don Allah ina neman alfarma ataimaka min kan kayan da akace bazasu shiga ba don su samu shiga don Allah.
Nace sam haram kaya basu shiga ba don akwai haram acikin sa idan zaki iya ki tura su kasan turai zaifi maki alheri sosai.
Take cewa ban taba aikawa can ba nace ki gwada kada kiji komai amma kuma wanan ba sana, an alheri bace duk kayan da zai iya kawar wa mutum da hankalin sa.
Atishawan da nayi yasa Umma fadin ta tafi ai shike nan da zaki fake abinda ta fada zaifi maki alheri don ita wanan da kike gani yar kaidace da kannetane sukazo za ku iya fahinta amma ita magana daya takeyi.
Kuma tunda kikaga tazo gun ki da kanta akwai matsala sosai don ita gaskiya bata faye zuwa ba sai idan abu ya baci zaki ganta ko ita ko Alhaji malam baban su.
Ikon Allah hajiyan tace tana fuskantar umma dake shaka min magani a hanci tana ce min sannu maryam.
Na dago ina cewa wai, tace sannu kinji balle sun dan kwana biyu basu taso maki ba.
Yanzu mama ita wanan abin nata tun tana karama ne take dasu haka ko yaya?
Umma tai murmushi tana cewa daga bayan nan dai ne bayan ma dawowanta garin nan Allah yakawo matasu haka.
Sabbin hawa ne ma ke nan za, ace hajiyan take tambayan umma da hakan cikin kallon fuskan umma din.
Umma tace tau sabbin ke nan za, ace amma gaskiya su abin nasu kamar gado ne don mahaifiyan ta ma haka tai ta fama dasu sosai a baya.
Ikon Allah abin akwai mamaki basai ka fadi laluran ka ba sai dai kawai kaji ana ma tonon sillar haka ai wanan ba gurin zuwan mugun kai bane don sai mutum yasha kunya wallahi.
Umma tace kin san musalaimane sosai kuma malamai ke tare da ita don haka nan kan ba gurin zuwa munafuki bane ko mugu idan ma yazo zai sha kunya don za, a fada mai komai kwata hilla.
Hannu ta saka cikin jakar ta tafito da daurin kudi masu yawa tare da dan makullin mota tana fadin ga sako inji Alhaji sada kan taimakon da akai mai yaji matukar dadin wanan abin donnkayan shi sun shigo mai lafiya ba tare da matsalan komai ba haka yasa yace akawo wanan a matsayin goro.
Umma tana kallon kudin tana fadin a, a a kai masha Allahu wasu idan an masu alheri a rayuwa sun sani sun san darajan alheri su saka da tukwaici mai tsuka haka ake so gaskiya.
Daga inda nake zaune kaina sadde a kasa na dago kai ina kallon Umma dake wanan maganan haka.
Nace Umma wanan abin baiyi yawa ba ashe taimako ne fa kada ya zama kuma hainci gare shi don an taimaka mai kuma ya zamanto na haince shi kinga haka baiyi ba .
Hajiyan cikin mushi take cewa kai diyata baki san ko waye Alhaji sada ba ko a kasan nan ?
Wanan shi ai bakomai bane a gurin shi don shi ko banza mutum ne mai sonyi alheri a rayuwan shi nasan ko wanan ma acikin shakkune yaba dasu.
Don haka karbi abinki Allah ne ya cisheki daga gareshi kuma idan baki karba ba sai yaga kamar kin raina ne.
Kudi ne sai kyautan mota ta hawa kawai yai maki yayiwa banza ma balle ke da kika taimaka mai haka.
Umma tace mota ikon Allah kyautan mota ga mutum hajiya tace ai idan kana da halin haka wanan bakomai bane gamasu shi.
Baki san irin nasaran daya samu bane wanda yace tun fara kasuwancin shi bai taba cin nasara irin haka ba.
Nan dai bayan sundan taba hira da Umma tamike tana fadin zata koma amma zata sake dawowa nan gaba don nata bukatan idan ta dawo daga Abujan.
Munyi sallama da ita ta tafi tabarmu a cikin mamaki da abin alherin da ta kawo muna gida.
Umma na shiga wanka na kira mahaifina don na sanar dashi wanan alherin dana samu ta silar wanan al, amarin nakaina.
Bayan mun gaisa dashi ne sai na fara kuka ina fada mai kamar haka.
Baba shi ke nan ni na zama mai bada taimako ga jama, a duk yadda muka gujewa hakan baba abin sai da yahau kaina.
Babana yace haba maryam may ye na kuka bazan tauye ki ba yadda na tauye mahaifiyar ki har abin ya zama sanadin rayuwan ta.
Don kin san kafi ne dasu idan an masu ba daidai ba sai su koma akan maishi.
Yace matsala dai daya shine kada ki kaucewa mahaliccinki da ibadan ki akan wanan abin.
Ki rikr darajanki na ya mace da Allah yai maki haka kuma ki rike darajan auren ki da kimar mijin ki.
Kin mayi arziki musulamaine kuma malamai a tare dake basu bari ki aikata wani abin ashaba a rayuwa.
Nace a hankali cikin sanyin murya hakane baba baba yanzu fa kyau tan kudi ne zai kai miliyan daya da mots aka kawo min.
Maryam kin kara samun kyautan mota kuma?
Allah shi yasan daidai ga bawan shi wanan tafiysn naku maryam a zahiri dai tafiyan ki ne kukayi bana mijin ki ba.
Don kece kikai gamu da alherin rayuwan ki a garin mutane don haka ki daina wanan kukan ki natsu ki san abinyi kafin ki makara da hakan.
Lokaci yayi da zaki fara gina kan ki da diyan har ma da yan uwanki idan kin kwantar da hankalin ki komai zaizo maki a cikin sauki ta yadda baki taba tsanmani ba.
Abinda nake boye maki tun kina yarinya maryam ina tsoron kada ki gado mahaifiyan ki da wanan abin don baki da gurin wasa tun kina karama sai gidin wanan iccen tsamiyan dake kofan gida.
Duk neman da za, ai maki acan za, a samay ki saida nayi kamar inayi na samu kika daina zama a gurin.
Wanda tun lokacin hasashe na yake a kanki kada dai ace kema kna da gadon wanan abubuwan tare dake.
Nagode ma Allah da yasa ina a raye wanan abin naki ya baiyyana a kan ki.
Insha Allahu bazasu taba barin ki tabe a hakana ba a rayuwan ki tunda na fahinci da alheri suke bibiyan rayuwan ki .
Mun dauki lokaci dashi yana kwantar min da hankali wanda hakan ya sa na samu natsuwa a tare dani har nakejin zan iya tunkaran baban Abba ga duk yadda zai fahinci wanan kyauntan da akai min.
Don ni dama ga nawa wautan shine kada ya zargeni akan wasu mazan waje ta wani fahinta na daban.
Ga mota a kofar gida an girke min ga tulin uban kudi a cikin gida da aka zube min sai faman tunane nake araina.
Anyya idan ana ban kudi irin haka rayuwana ba zai shiga wani hali ba kuwa don muddin idona ya bude da karban kudi masu yawa kan taimako to nan gaba bazan iya taimakawa mai karamin karfi.
Zancen hajiyane ya fado min a rai da take cewa wanan abinda na gani ba komai bane a gurin hamahakin mai kudin daya bani wanan kyautan haka.
Watau masu kudi suna nan a inda suke ke nan a kasan amma tallaka bawan Allah yake cikin wahalan rayuwa haka.
Sai bayan karfe shidda na yamma ya shigo gidan tun da ya karyo kofan gidan ya hango wanan dirkekiyar motar parke a kofan gidan yake cewa a ran shi.
Kai wanan kuma waye haka mutane basu dai bari mutum ya huta kowa ya dauko matsalan shi yakawo maka gida.
Su gare su wani sabon hanya kuma ya bude ke na ga jama, a haka duk wanda ke bukatan ban kada ya kwaso matsalan shi ya kawo kamar basu san Allah ba.
Haka ya shigo gidan fuska a daure yana zaton zai samu bakin nawa a falo zaune ne.
Ga mamakin shi babu kowa a cikin falo sai Umma dake zaune ta kura ma shirin yara da akeyi a tv ido.
Sina gaisawa da Umma yake faman raraban ido yaga bakuwar da ta shigo gidan amma babu kowa ga motsina daya ke ci a cikin kitchen ina daka kayan yaji da zanyi miyan dare dashi.
Umma ce take kwala min kira daga falon nazo gashi ya dawo lokacin nafito ina yarfe hannuns dana dauraye da ruwa ina mai sannu da zuwa ya amsa a dakile.
Na dauko mai abincin