Showing 105001 words to 108000 words out of 115099 words
Chapter 36 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
da nake ganin nayi.
Da mamaki nabi jakar ina kallon ikon Allah don nasan koda nai sallah babu shi a gurin.
Ga yar leda datace sakon su yar sokoto a gefen namu ledan daganin shi na kasan wajw ne bana kasan mu ba.
A hankali na mike na nufi gurin da nake jin kukan Nusaiba a dakin su Umma na samu Umma tana lalashin ta nake tambayan ts may yasa may tane?
Umma take cewa wai ta na barci taga ta tashi tana kuka haka a raina nasan aikin yaran boye ne sune sukai mata wani abin.
Amma ai idan da alkawari babu cutarwa a tsakanin mu dasu don may zasu saka min yarinya kuka.
Kamar a mafalki nake jin kukan yaro a back yard din mu sai lokacin na juya banga Aisha ba a makwancin ta nace ina Aisha ta tafi kuma da safen nan.
Fita nayi falo da sauri bata ciki kofan back yard din mu na nufa yana abude koda na leka tana tsugune tana wasa harda dariyan ta.
Nace ke Aisha da safen nan kike wasa ke kadai a cikin sanyi bakya gudun mura ya kama ki ne ?
Tace mummy kiga yaron nan maman shi ta dake shi wai ya taka Nusaiba bai sani ba tana barci.
Nace Allah sarki don Allah anty kiyi hakkuri tunda bai sani ba ya take ta harkan yara ne kawai.
Ina magana kamar ina ganin ta a lokavcin nace wa Aisha tashigo ta saka rigan sanyi a jikin ta don ban da ikon hana ta wasa naja mata matsala koni kaina.
Kitchen na shiga bayan nagama shirya Aisha cikin rigar sanyi tafice da gudun ta.
Abin karyawa na hada muna sai na gyara gidan ko ina tsab dashi harda back yard din duk da baiyi wani datti ba amma sai da nai mashi kwal na shiga nai wanka na shirya.
Suna falo a zaune na jawo jakar kayan tsaraban da aka kawo muna idon Umma akan kayan har na iso inda suke na fara bude jakkan.
Dogayen riguna ne irin na matan larabawa masu matukar tsada da kyau kala biyar, sai kayan yara kowani na daga size din su mun fahinci mai shi.
Na baban Abba mai matukar kyau da laushi irin kayan yan Pakistan din na ne yasamu har kalla uku.
Sai na Umma dogon riga itama ga atamfofi na waje manyan super dake cikin kayan desgn masu kyau letes.
Ban bude na su yar sokoto ba sai nakai masu zamu gani mamaki ne fal a zukatan kowan mu sai dai cikin karfin hali suke fadin mun gode Allah ya saka da alherin sa.
Mun gama gani na saka hijjab dina sai gidan su yar sokoto ina fita ne daga gidan Umma tace wanan alamarin haka kamar a mafalki ban taba sanin ana haka ba arayuwa da labarin hakan aka bani sai nace labari ne kawai ba gaskiya ba ne.
Yace Umma alamarin sai dai ayi shiru kawai don abin sai gaba yake mata ni yau din nan a cikin mamakin ikon Allah nake a gidan nan.
Nifa na rufe gida da kaina ban kuma ga wani bakon da yashigo gidan nan ba amma wai wanan abincin alfarman da ta dafa jiya koda gari zai waye ba abinci ba kula agurin dana barsu.
Da ace ba, a gaban idona ne haka ya faru ba koda rantsuwa ne zan iya yi nace ba gaskiya bane wanan zancen.
Ni kan ina isa na samay su a waje zaune kofan gidan anty hauwa suna hira muka gaisa dasu nai masu ban gajiyan aikin jiya.
Bamu kai ga karasa gaisuwan mu ba yar sokoto ke fadin jiya muna tajiran muji baki sun iso muzo mugaida su sai mukaji shiru.
Ledan hannuna na mika masu nace ga tsaraban ku sunce a baki ikon Allah harda tsaraba muka samu ashe sun zo din kuwa ?
Nace sun dawo jiya cikin dare wanan akace na baku suna kokarin bude ledan riguna ne dogaye masu laushi da kyau sai turare kwali biyu a ciki.
Murna sukayi sosai tare da nuna farin cikin su akan kaya cikin zakuwa Anty hauwa ke fadin wata mata ce tai muna wanan kyautan haka maman Abba ?
Anty mukaddarasiya ce abokiyar zamana da muke zama a gida daya sunyi tafiya shine suka dawo daga tafiya jiya.
Kallon kallo sukeyi wa junan su ga kayan sai wani irin kamshi ke tashi a cikin sa.
Wai ban gane ba maman Abba kina nufin cewa mutanen ki ne dama bakin naki da mukai wa aiki jiya na bata amsa a takaice da sune.
Mun shiga uku mun lalace don girman Allah da gaskiya kike zancen nan mama Abba ?
Nace ga zahiri kin gani ni nayi tafiya ne balle na samo maku wanan tsaraba mai tsada ko makka naje ina zan iya sayo maku wanan rigunan haka ?
Aiko boni yaci mu inji anty hauwa kada fa su san damu ?
Murmushi maganan ta yasani nace tun yaushe anty hauwa mutanen da muke zaune tare dasu koda yaushe.
Da firgice tafara dan dube duben gefen ta kamar tana neman wani abu da ya bace mata .
Nace ni a ina na samay su ba a nan din ba don dai ban dasu da farko anan muka hadu dasu.
Mun shiga uku wai da gaskiya kike fadi maman Abba nace to anty ina wasa dake anty wallahi gaskiya nake fada maki.
Don Allah kuke ganin mu bamu fanin ku kutaimaka muna kada ku taba mu mun kuma gode da sakon ku Allah ya saka maku da alheri.
Mun dayi hira dasu amma a tsorace suke sosai sai da na kwantar masu da hankali suka samu natsuwa.
****** ********* ******
Motoci ne har guda hudu dirka dirka dasu suka shigo easthe din mu su yar sokoto suna waje suna hira da maigidan ta suka bi motocin da kallo.
Maigidan ta ke cewa wa yan nan dagani daga wani gidan gwaunati suka fito don wanan motan bana kananan mutane bane.
Ba su tsaya ba sai a kofan gidan mu nan aka shiga bude motocin ana fitowa da sauri security ne ke wanan aikin.
Bayan wata mota daga ciki aka bude yayin da wata farar mace tafito daga cikin motar tana gyara lafayan dake jikin ta.
Sai da taima easthe din kallon kyawo tafara dan takawa zuwa matakalan hawa gidan na mu.
Yayin da wata mace yar sanda take nocking din kofan na mu duk su yar sokoto suna kallon su daga inda suke a zaune da mijin ta.
Ina falo zaune tare da Umma naji kwankwasa kofan namike ina fadin waye kuma ke nocking din kofan.
Bakin fuska nagani a daidai lokacin da nake kokarin bude kofan hakan yasa na gane munyi baki ke nan a gidan.
Cikin hausan yare yar sanda ke min magana muna neman hajiya maryam anan gidan take don Allah ?
Nace eh anan take sannun ku da zuwa tace ok ki fada mata her excerllency zata shigo gurin ta yanzu.
Nace ki fada mata excerllency ana mata sannu da zuwa ta dan kalle ni da mamaki kamar zatai magana sai kuma ta juya da sauri cikin zafin nama irin nasu na yan kaki.
Ko second ba ayi ba sai gasu sun shigo tare da yar sanda tana take mata baya.
Ba laifi don matar abin kallo ne sosai saboda kyauwon ta ta hadu sosai dagani kuma naira ya samu gurin zama.
Sannu da zuwa nai masu tare da nuna masu gurin zama don su zauna ba musu ta zauna yar sandan tana tsaye a bayan ta.
Tace maryam muke nema don Allah ko anan take da zama muna son magana da ita ne ?
Nace cikin murmushi hajiya kina magana da maryam ne yanzun haka a gaban ki.
Tace tare da dan kara min kallo to ikon Allah don Allah sorry fa na dauka zan ganki wata babban mace ce wallahi.
Nace ba damuwa ai rashin sani ne yakawo hakan don baki san ni ba ne ai.
Tariza ki bamu guri please ta umurci yar sandan da haka don tafice zatayi siri ke nan.
Yar sandar ta juya bayan ta sara mata ta fice daga gidan ba bata lokaci bisa umurnin da aka bata.
Matar ta juyo gare ni tace nasan baki sanni ba amma sako ne na kawo maki, , , kafin tace wani abu nace daga guri Adisatu ko ?
Kallon mamaki ne tai min tace ta fada maki zanzo ne dama ?
Nace ban ma da contact din ta kawai dai nagani ne ta turo ki ki min albishir da bukata ya biya ko ?
Sai kuma ke da kikazo da matsalan ki gamay da maigidan ki da baki gane komai akan shi yadda kike so ?
Tace subbahanallahi haka ne ikon Allah a ranta tace nako zo karshw a rayuwana ashe don bankada.
Nace amma hajiya ya kamata ki godewa Allah da baiwa da niiman dayai maki a rayuwan ki.
Kin fi kowa sanin kina samu sosai a gurin shi amma hakan bai maki ba hajiya?
Kada ki manta da nauyin alumman dake a kan shi shi kadai idan bai sauke wanan nauyin ba gobe lahira shi Allah zai tambaya shi kadai.
Kina ganin duk tarin dukiyan dake gaban ki bazasu isheki rayuwa har jikokin su samu a ciki ba ?
Zan cen dakin yusuf yakamata kizo min dashi kafin akawo maki shi kasan nan a daure ba wanan zancen ba.
Ku dinga tuna ranan gobe kiyama da Allah zai tsayar daku kan irin mulkin da kukaiwa alummanku .
Tace nagode maryam da wanan fadakarwan dakikai min nace ki gode ma Allah daya saka maki fahinta na.
Tace naji kin min zancen dana Yusuf ga maganan ki wanda zancen ya daure min kai sosai ban fahinta ba gaskiya ?
Zakicce min baki san halin da yake ciki ba acan inda kuka turashi karatu ko may ?
Wallahi ban sani ba maryam wani hali Abban baba yake ciki nace bazan fada maki ba amma idan da hali ki shirya kikai mai ziyara na bazata duk abinda idon ki ya gane maki zaki iya dawowa nan mu san abin yi.
Hankalin ta yai matukar tashi amma duk yadda taso na fada mata ban fada mata komai ba sai ta gano wa idon ta kafin musan abinyi akai.
Jakar hannun ta ta bude tafito min da kudi a daure masu yawa tace wanan sako ne daga gurin Adisatu tace na kawo maki don halin da take ciki ba dama tabaro Niger tazo Nigeria yanzu.
Na kalli kudin dake tare agabana masu matukar yawa nace da ita kudin sunyi yawa ki raba biyu ki mayar mata da sauran ace mata muna godiya gareta.
Allah ubangiji ya raba su lafiya yabamu mai albarka.
Tace ai bamu kyauta mu mayar wanan rabonki ne Allah ya tsaga daga gare ta don haka ki rike naki ne nima ganawa akara taciro daurin yan dubu har uku ta aje min saman table din falon.
Nace hajiya kudin nan sunyi yawa matuka da ku rage yawan su kawai albarkan aiki yafi yawan ladan shi ai.
Tace nasan da hakan amma na hango nasarori mai tarin yawa a zamana dake wanan ba komai bane idan har bukata zai biya ?
Nagode nace mata tare da fadin idan kin tafi ki fada ma Adisatu cewa ta dan rage yawan fita koda yaushe ta dan zauna har cikin ta yakai wata hudu tafara fita idan zata iya.
Insha Allahu zataji zan fada mata ai mun gode don Adisatu tana a cikin wani hali na tsangwaman yan uwan mijin ta sosai wallahi.
Zasu daina don zasu sota yanzun haka ma wasun su sun fara daina hattaran ta sosai.
Allah yasa hakan wallahi don tana matukar bani tausayi sosai irin yadda suke nuna mata banbanci a cikin su.
Insha Allahu har kakan nasu zakusha mamaki sosai akan ta bari cikun nan ya baiyyana kawai.
Ta dai ja bakin ta yi shiru sai idan angane shi kawai a jikin ta komai zai fara baiyyana.
Muna gamawa tai min sallama suka fice a gidan tausayi tai matukar bani sosai don dan ta yana cikin mugun rayuwa a kasan turai amma ita tana ganin yana can yana karatu ne.
Bata san cewa yana can yana hole rayuwan shi da irin makuddan kudin da suke tura mashi daga nan kasan.
Kudin nake kallo a gabana dole nai saurin kwashesu kada wani ya fado gidan yagane su a haka .
Ban dade da kaisu daki ba sai ga yar sokoto tashigo tana fadin maman Abba ashe baki mukayi haka yau masu fada aji na kasan.
Ai na taso nazo security suka tare ni a waje wai ba zan shigo ba ciki her excerllency tana ganawa dake.
Ki ce min abin har ya kai ga zuwan excerllencys gidan yanzu baki ga yadda suka taso min ba kamar zasu cinye ni danya gani dama da tsoron bindiga atare dani na juya da sauri nabar gurin kada su halakani ga banza.
Mun jima muna hiran wata makwabciyar mu Ibo da muka samu a cikin easthe din mu mai daukan kai bata gaida ko idan taga mutum.
Nace yanzu ke ina ruwan ki da ita bako addinin ku daya ba bakuma kabilan ku daya ba da ita.
Duk hiran da mukeyi sai yanzu hankalina yakawo kan bangus watau awarwaron da Adisatu ta taba bani a baya.
Bayan fitan ta gidan namike na nufi daki na bude gurin dana boye shi yana nan gurin a ajiye kamar yadda na boye shi.
Namayar daniyar zai kan shi kasuwa a auna min gram din shi don naji kudin shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BA NE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
3โฃ2โฃ
Hajiya tana barin gidan mu da komawan ta gida abu ya dinga damuwanta a zuciyar ta yadda zata gaskan ta zancen da na fada mata.
Amna wanan karamar yarinyar ne za,ace tabawa Adisatu magani kuma ya karbu anyi nasara akai .
Ta girgiza kanta tana cewa ina wanan ma ai shirmay ne kawai amma akwai dai kawai dai lokacin samu ne yayi mata.
Da dare bayan ta dawo gida tana kwance saman dofon kujera duk gaban jikin ta ciwo yake mata don dan tafiyan da tayi na ranan.
Maigidan nata ya shigo falon yana saye a cikin dogon riga ta maza irin na zama a gida da manya ke amfani dashi a gida.
Idanuwan shi a kan ta ya zauna a cikin murmushi yana fadin duk gajiyan tafiyan ne kamar wacce tai tafiya mai nisa haka ?
Tace bari kaidai his excerllancy tafiyan ne sai bayan nayi ta ne na raina kaina don wallahi baka ga yarinya karama da na samu ba agidan wai itace mai bada taimakon da ake fadi.
Wai may yasa mutane suka baci da karaya ne yanzu saboda son kudi kawai sai kaga murane wai harda yara kanana a cikin wanan harkan ta bada magani.
Don kawai ido ya rufe da son kudin kota halin kaka sai dai kowa yayi kudi a duniyan nan.
Kai in banda abinki ai kudi abin so ne ga kowa ko da kike cikin wanan daulan bakiki ki kara samun wasu kudin ba fiye da haka.
Yanzu fa jira kike na sa maki hannu ku fara shirin ku na wayar wa mata kai akan tsarin iyali wanda ba karamin kudi ne za, a kashe ba a hakan.
Tace kai gaba yallabai ta nan kuma ka biyo min watau kowa dai baki kudi ba ke nan ?
Yace ai na kanta take nema ko ba biyoki tayi ba har gida ke ce kika kai kanki gare ta ai.
Tace ni saboda Adisatu na tafi ba wai kaina nakai ba amma sai gashi kawai don hali irin na masu magani ta jefo min maganan Abba a bakin ta.
Da sauri ya dago yana kallon ta a cikun mamaki yace zancen Abba kuma tace may akai ?
Dariya tayi har da dan kyalkyatawa ta mike zaune tana fadin waini zata mayar doll don an fada mata kila ina da da Abba shine wai nayi saurin taimaka ma rayuwan shi don yana a cikin wani hali kafin akawo muna shi kasan nan a daure.
Subbahanallahi wa, iyazu billahi ita matar ce ta fadi haka akan Abba din a ina tasan Abba din wai ?
Kin taba sanin tane ke yake kokarin tambaya don kalamin bai mashi dadi ba don shine dan su namiji babba yanzu da suke gani.
Matar tace cikin rashin kulawa kaima kasan ai zamanin median din nan komai mutane suna dashi akan gidajen wasu don barnan sunan su kawai.
Yace look wanan maganan ba maganan wasa bane koda kuwa karya ne takeyi akai mu yakamata muyi duba sosai cikin al, amarin don mu fahinci gaskiyan zancen.
Amma ke sai naga a matsayinki na uwa a gareshi kuma kece aka fadawa wanan zancen sai naga kamar zancen bai damay ki ba ke ?
Tace haba yallabai urin burgan aikin nan ne fa