Showing 60001 words to 63000 words out of 115099 words

Chapter 21 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6643

a cike yake waccan dayan abokiyar zaman tamu ta haihune ake buki a gidan yau.
Daga kaina nayi ina kallon matan dake gidan ikon Allah sai nake ganin kowacen su a cikin irin hallitatanta da Allah yai mata nai suuu kamar zan fadi kasa.
Matar ta tareni da sauri tana fadin kinga zoki tafi gidan malam kada ki makara don yau gidan namu bamu kadai bane kuma ko a cikin mu yau ba jinsi daya bane a gurin kada asamu mugu ya cuta maki.
Da sauri taja hannuna zuwa hanyar fita daga gidan nan ma muka sake gaduwa da wasu gungun matan kaman dabbobi yanayin su kahonne a tsakiyan kawunan su gwanin ban tsoro dasu.
Mukai sallama nabar gidan da sauri inayi ina waige kudun kada wata daga cikin su ta biyoni a baya.
Gidan baba malam na nufa hankali a tashe nai sallama na shiga gidan nan na samu mutanen gidan suna cin abinci suna min sannu da zuwa.
Muka gaisa dasu amutunci sai sannu da hanya suks min babban matar malam tace yau Allah ya taimakeki da matan gidan bukin nan sun maki illla don wasunsu basu da tausayi ko kadan.
Yanzu Kafiya take sanar damu zuwanki gidan a cikin rudanin abin da kika sama agidan.
Maryam ke mai arzikice da sa, a a rayuwan ki ko da yaushe don badon Allah yana tare dake ba ai da wa yancan shedanun don ba sallah sukeyi ba da sai sun cuta ma rayuwan ki kona yar ki a garin nan.
Baban ki yana daga ciki yana jiran ki don tun dazu yasan da zuwan ki garin agurin shine ma muka samu labarin kina hanya tun dazun .
Amaryan tace wai amma kunsha hanya ga rana bari na baki ruwa da abinci ki danci ko.
Ikon Allah yau sai na tsinci kaina da tsoron su haka kawai nace a, a nagode.
Murmushi tayi tace haba maryam ko da ace zamu cutawa wani dan adam aikema kin san banda ke ko don ke diyar malam ne kin zama diya a gurin mu.
Murmushi karfin hali nayi don duk a rude nake iina dana sanin kafewan da nayi nazuwa garesu yau, nasa hannu ga jakar dana nazo masu da tsaraba acikin sa.
Turare ne sai sabule masu tsada da clean kowa guda daguda nakawo masu.
Takarba da murna da farin ciki tana min addua wanda duk na neman tsarine daga Allah.
Uwargidan malam tace ke kan wai baki gajiyane da halin alheri maryama ?
Nai murmushi nace mama ku iyayyena ne fada nake alfahari dasu a duniya don kun min riko da nuna min ku uwaye kuke agareni banda uwan da zanje gurin ta naji dadi na fata mata damuwana sai agurin ku.
Kuma ku bani shawaran daya dace sai nan gurin ku.
Ashe mai zasa da yagaji da kyautatawa iyayyen shi a duniya idan har yin hakan zai faranta maku rayuwan ku.
Idonane yakawo hawaye a lokacin da nake wanan magana don tuna cewa banda mahaifiya ko yar uwan, uwa, wace zan iya kai damuwana a gareta ta share min hawayena ga bani shawaran daya dace a rayuwana kamar su a yanzu.
Kuka ne yaci karfi acikin kukan ne nake fadin mama bazan iya guje maku ba don zaman mu yan jinsi daban daban ni daku duk da na san yin haka hatsarine a rayuwana.
Amma kun nuna min kaunan da yasa nakejin kun zama iyayye a gare ni wanda duk duniyan nan yanzu banda ku da mahaifina banda wani makusancin dayafi ku a gareni.
Kewan ku da damuwan makomata idan narasa ku a tare dani yana ci min zuciya don ban san yadda zan kasance ba daga baya idan har kuka barni.
Haba maryama ai mu bazamu barki ba sai dai ke ki barmu ma don mu kin sn ba mutuwa mukeyi kamar ku ba.
Muryan malam ne naji akaina wanda yasani dago kai a hankali na dube inda naji muryan.
Yana tsaye cikin fararen kaya tun daga takalman shi tufafin shi har rawanin shi da sandan shi ta carbin shi duk farare ne.
Zan iya cewa wanan ne karo na farko dana taba ganin malam din a tsaye kuma gani na sahihi da ban taba tantance kamannin shi ba kamar na yai din.
Fari ne dogo kyakyawan balarabe dashi ga saje fari da yai kwance lub a fuskan shi gwanin ban sha, awa.
Ko ba, a fada ba kaga lumana da malanta kwance karara a tare dashi.
Maryam ya ta kada ki bata fuskan ki da kuka don ke yar muce Allah da annabinshi kawai yasan hikimar hadaki damu a duniyan nan.
Yan adam nawa suke shiga a rayuwan mu amma baifi su gan mu sau daya ba idan ma har zasu ganmu din cikin wanan kama.
Amma ke gashi Allah ya hore maki mu kina ganin mu kina zuwa gare mu a duk lokacin da bukatan hakan ya taso gare ki.
Yau din ma ban so zuwan ki garin nan ba don garin namu yau ba dadi ko mu da muke yan jinsin su taka tsatsan muke da irin bakin mu don su bakake ne ba imani suka faye ba a rayuwan su duk da musulmai ne su ma amma suna da halin da kyaman dan adam tare dasu.
Gabana ne naji ya kara faduwa karo na barkatai amma kuma sai naji yana fadin ganin da naiyi kin dade a tsaye kan kin nace sai kinzo gare mu yasa nasa a bude maki ido kiga motar nahiyar mu har ki samu zuwa.
Idan ba haka ba ko kwana dubu zakiyi a gurin nan ai bazaki taba samun motan da zai kawo ki wanan nahiyar ba diyata.
Kai na na dago a hankali na dan kalleshi nace nagode baba.
Yace kici abinci ki huta kizo muyi maganan da ya kawo ki don yar kima tana jin yunwa gashi kuma ta wahala sosai a cikin rana kafin ku samu motan zuwa nan din.
Abincine lafiyayye aka kawo min sai dai duk tsoro da fargaba ne ya cika min zuciya ta.
Gudun su fahince ni duk danasan su san komai yasa na bude abincin tare da jawo Nusaiba a jikina na fara bata abincin a hankali.
Amaryan malam take ce min bazakici ba ke kina fa tare da yuwan ajikin ki ga damuwan da kike dashi na mijin ki da mahaifiyar shi.
Da sauri na dago kaina ina kallon ta don dai naga ban fada masu ko may yakawo ni ba gare su.
Tace kin bani mamaki dana baki abinda zakiyi amfani dashi irin namata amma kikaki yin amfani dashi da farko na zaci ko rashin yarda ne dani yakawo hakan amma daga baya sai na fahinci abin ne ke bai damay kiba a rayuwan ki.
Da ace kin gwada amfani dashi da a duniyan nan babu wata macen da zata iya shige maki a gaban ki komai hatsabibancin ta kuwa.
Mazanjen ku shedanune maryam ma don abune mawuyaci asamu namijin da ya tsaya mu, amula da matar shi na sunna kawai a yanzu tundai mutane irin na alkaryan ku dabasu dauki zina da wani muhinmanci ba a rayuwan su.
Yau zan kara baki wani don wancan na farko na dauki abina ganin baki amfani dashi ba .
Sai lokacin na tuna na nemay shi ranan ina son bawa anty hauwa da ta tambayeni ko nai ajiyan kayan mata na nemay shi kasa da sama banganshi ba a gidana.
Sai nai tsanmanin ko na jefar dashine ban sani ba kona sakashi wani gurin nai mai mugun boyo ne.
Wanan abinci akwai dadi da test sosai ban san lokacin da na kusa cinye shi ba sai naji tana cewa akaro maku naman ko naman baunace Maryama kike ci kin san ku yanzu yan adam baku samun irin wa yan nan namun dajin a garuruwan ku kamar mutanen da suka gabata don namun dajin sun boye daga gare ku.
Murmushi nayi nace na koshi mama na gode nace wani irin dabbane bauna kuma mama ?
Kaman a mafalki naganni a cikin wani daji mai yawan dabbobi ga garke wasu namun daji masu girma siffan su kamar na shanaye dana sani sai dai su bakake ne.
Sai kuma naganni zaune a ida nake da farko tace min kin taba ganin su a rayuwan ki na girgiza kaina tare da fadin a, a.
Nan dai na gama cin abincin tana min bayani akan dabbobi wanda wasu nasan sunan su wasu kuma ban sani ba sai a bakin ta na tabajin su.
Nan dai tabani wasu abubuwan masu amfani ga mace tare da jaddamin nai amfani dasu kuma zata bani wasu da zan dinga sayarwa ga mata yan uwa na idan ina da bukatan yin sanan an su don itama shine sanan ta, nace ashe kuma kuna amfani da wanan abubuwan tai murmushi take cewa haba muma ba maurata bane kamar ku ?
Duk rayuwan da kukeyi munayin shi maryama dan banbancin rayuwa atsakanin mu daku kadan ne ai.
Don akwai abubuwan daku yan adam zakuyi wanda mu bazamu iyayin shi ba don kunfimu hikima da fasaha da taurin kai.
Mun dauki lokaci muna hira tare da ita tabani kayan masu yawa tace nagwada idan sun karbu zata dinga bani cikin saukin farashi.
Ina gamawa da ita na shiga gurin baba malam na samay shi a zaune yana karatu rike da littafi a hannun shi.
Jin sallama na yasa ya dago daga abinda yakeyi yana dan murmushi a fuskan shi cikin kulawa.
Zubuwa nayi kasa ina gaida shi ya tare ni da fadin shiyasa muke cewa ku yan adam akwaiku da taurin kai a rayuwan ku.
Na fada maki cewa idan kina son ganina basai kin wahal da kanki ba da zuwa dakin bukaci ganina zaki ganni ai maryama.
Nace baba ina son zuwa gida ne naga su mama da sauran yan uwa, yace madalla maryama da irin son da kike muna.
Nasan yanzu kinzo ne kan mahaifuyar maigidan ki dakike jinya ko ?
Nace hakane baba.
Yace ai ba aiki kowa bane sai mukkadarasiya da yaran ta sune suke mata wanan aikin kan abinda tai maki suka ji haushi.
Kuma sunyi hakan ne don tasan muhin mancin ki a gareta wanda yanzun ta sani tasan komai kuma.
Munyi magana da ita danaga kin shiga damuwa tace min akwai abinda take son matar ta fahinta ne akan ki.
Sai dai kuna mata magani daban ciwo kuma daban wanda maganin da kuke bata na asibiti yanzu shine yakara kawo cigaban wani ciwon a gareta.
Maryama naga jikin mahaifinki ya samu sauki sosai malam yana da mutunci ban san dalilin da yasa mutanen gidan shi da suke zaune shekara da shekaru suka cuta mai haka ba.
Koda yake halinku ne na yaran zamani insha Allahi kuma bazasu kara cuta mashi ba bashi ba kowa ma na tare dashi.
Yanzun dai ki karbi wanan kiyiwa surukarki amfani dashi kin dai manta na taba baki maganin waraka na wasu cututuka abaya da kin mata amfani dashi da ya wadatar daku ai dazata samu sauki sosai.
Nakarba ina godiya zan bar dakin yace maryama akwai wani taimako danake son ki min akan wasu, mata da nake son ki taimakawa wanda hanya ne nake son nai maki ga hakan.
Bazaki gane ba sai nan gaba nace baba wani taimako kakeso a gurina.
Yace karbi wanan akwai wani gida a unguwar GRA wanda yafi ko wani kyau da girma a unguwar don haka ki kaiwa matar da ake kira da suna Aisha wanan maganin sha zatayi ta shafa ta kuma dinga alwala kafin ta kwanta barci.
Sai dayan uguwar dake a malali zaki samu gida mai hawa uku daga barin daman ki ma launin shudi da yawan furanin idan kinje kice hajiya Umma kike son gani idan kin samu ganin matar sai ki bata wanan sakon tasamu ruwan massalaci ta hada dashi tana sha tana shafawa akafan dake damun ta insha Allahu zata warke itama.
Kice mata mitumin da tagani ranan jumma, a a garin makka matarshi tana shafa mai ruwa a fuska ta tsaya tana kallon su shi ya aikoki gurin ta yace agaida ita.
Zancen dan ta kuma ta kwantar da hankalinta nan da sati uku zai dawo gida da yardan ubangiji.
Sai dai idan ya dawo kada taimai fada akasi aka samu ga rashin dawowan shi da baiyi ba na tsawon lokaci idan kikai min wanan taimakon dana bukata a gare ki ya wadatar min da komai a gare ki maryama.
Nace amma baba kasan halin mutanen mu nayau zasu yarda dani kuwa har su karbi sakon nan.
Yace ai ko wacen su tasan da zuwanki maryama sun sanki kece dai baki sansu ba kawai.
Ita Aisha ki fada mata nace ta idan da hali ta canza duk yan aikin gidan ta gaba dayan su har maigadin ta haka shine saukin ta.
Nace insha Allahu baba zanyi kamar yadda ka umurce ni dayi yace kada ki damu idan kinje komai ma da zaki fada zaki ganshi a zahiri kuma zaki aiwatar da shi.
Yace zancen mijin ki kuma komai zaizo karshe da yardan Allah kada ki damu da komai akai.
Nai godiya nafito mukai sallama da su ni dai nasan nakai zauren da zai fitar dani daga gidan baba malam din.
Amma bayan haka ban karasanin yaya akayi ba kuma sai ganina nayi zaune tare da kayana dake gefena aje a falon mu.
Firgigit dani ina cewa hasbbunallahu wa,ni,imal wakeel.
Tabbas a falona nake zaune ba a wani guri ba na daban don na kara tabbatarwa yasa na mike da sauri na nufi dakin da Umma take kwance tana ciki a kwance idon ta biyu sai dai duk ta bata jikin ta da kashi da fitsari.
Nace Umma kin yi lalurane ashe bana nan da sauri na fita na debo ruwa nafara gyara gurin na tsabtace ta da kyau na kawo kamshi na saka a dakin da gidan.
Abinci na fara bata wanda dama na riga dana dafa shi ko kafin nafita sai data gama na kada maganin da baba yabani na fara bata.
Tasha na shafe mata jiki dashi sannan nadawo da ita falo tare da kware labulen dakin don iska ya shiga sosai a dakin.
Nan dai na shiga yin yan aiyukan da ya dace nayi nagama nai sallah nan barci mai nauyi yai gaba dani.
Najima ina barci a gurin sai mafalkaiyyan abinda ya faru dani nakeyi ba abinda ya firgitana har na falka daidai lokacin da yaran ke shigowa sun dawo daga makaranta.
Ba komai nagani ba sai matan da nagani a gidan buki dana shiga cikin wani irin hallita suna min wani irin kallo da tsoratani sai ga mari ta mika min wani leda wai abin buki ne da ban karba ba ta kawo min.
Ina tashi kuwa idon yai tozali da ledan data bani a gefena wanda yake tap da kayan buki alkaki ne mai shegen kyau da nama sai nakiya mai kyau dashi.
Ga yara sun zagane ni suna fadin sun dawo amma ni sai zufa ne ke karyo min a fuskana daduk illahirin jikina.
Kafin na farga har yaran sun fara cin kayan bukin da suka gani suna fadin wai amma akwai dadi mama.
Da sauri nakai idona gare su naga abinda sukeyi naikaiwa Aisha wacce nasan itace tafara daukan shi duka akai.
Naji ance min akull kika kara dukan ta zamu hadu kina nufin yan uwa na zasu cuta maki ne ko may wai?
Babu kowa kuma babu wanda kejin may aka fada min yadda naga su ko a jikin su haka yasa nasha jinin jikina.
Ina kallo yaran naci ba halin na hanasu ci sai Abba ke ce min naci naji zakin dake akwai ga kayan.
Na dan gutsura kadan a bakina nace gaskiya akwai dadi sosai don ban taba cin alkaki mai dadi ba irin wanan din ba a rayuwana sai wanan na gabana.
Ranan nidai har na kwanta ban kara saka komai a cikina ba sai ji nake kawai a koshe nake tun abincin da naci a gidan baba malam din ga jikina sai ciwo yake min kamar nayi wani aiki mai yawa nake jin kaina.
Hakama yaran kayan bukin da sukaci ya saka su basu jin cin komai ranan haka muka bar abincin dana dafa nan ya kwana sai da safe na zubar dashi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BAMU KADAI BANE A, , ,


๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ


2โƒฃ1โƒฃ




ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DAFATAN MUN WAYI GARI LAFIYA ALLAH YABAMU WUNI MAI ALBARKA.
MASU SON NOVELS DINA ZAKU IYA REGISTER GA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO RECHARGE CARD NA 400
ZAKU IYA NEMANA A WANNAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257
NAGODE DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN SAI NAJI KU, , ,




Alhamdullahi don tunda na kai sakon nan sai nake jin kaina shakat kamar an sauke min wani nauyi babba a kaina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login