Showing 48001 words to 51000 words out of 115099 words
Chapter 17 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
akwai mugu a ciki wanda ke yawan wahalal da ita shine yace sai idan zatayi bada magani zai kyale ta.
Ni kuma ina zan yarda da wanan a gida tunda sai an kauce ma irin wanan sana, an nasu.
Shine yakawo tunzuran zuciyar su har sukai mata illa ta rasu ta sanadiyan hakan.
Amma tana da na kwarai tare da ita lokacin da abin ya faru da ita wai basu tare da ita sun tafi ibada shine har wanan mugun ya samu kafan yi mata illa haka saida tai wata daya baci basha ba barci kafin ta rasu.
Anty lami tace kai gaskiya mama Amina ta wahala lokacin sosai wallahi ko.
Don ban son jin labarin wahalan da mamana tayi saboda abin yana matukar tayar min da hankali sosai nace ma anty lami anty muje na baki sakon ki.
Da mamaki take cewa sako kuma maryam dagawa ke nan nace daga anty na na kaduna mukkaddarasiyatu.
Mukkadarasiyatu kuma suna sai kace sunan aljannu maryama ?
Baba tace sunan su ne ai daji itace dai bata ganewa saboda tsigan da suke fito mata kawaine bata ganewa.
Kai kaji baba kuma ina maryam zata hadu da aljanna tai hurda da ita kawai dai mutane ne dake saka sunaye yanzu any how.
Ba karamin mamaki anty tayi ba dataga sakon tace maryama wanan zannuwan fa manyane super nace nima haka nagani anty don bata bani sakon tun can ba balle nai mata godiya tun can.
Anty bata damu data tambaye ni ta yaya aka bani sakon ba sai murna takeyi tana sakawa mai sakon albarka ni kuma ban fada mata komai ba sai dai nabar zancen kawai a raina.
Ga maganan da babana da yayi yanzu yana damuna a rai don hakka na kuddiri aniyar fada mashi komai don ya warware min matsalan daban sani ba.
Sai da mukai sallah la,asar ne na sulale jikina zuwa gurin shi na samay shi ya jingina baya ga bango yana karatu.
Ganina yasa ya sake fuskan shi yandan sauke littafin da yake karantawa na illimi dake a gannun shi.
Yace zaku komane maryama ?
Nakai zaune dakyau nace baba sai dan zuwa anjima dama dai nazo ne da wani magana dake damuna.
Yace taufa nace baba kasan na fada maka run farkon zuwan mu kaduna abin dana fuskanta.
Yace na sani nan na fara bashi labarin duk yadda abubuwa suka faru dani dakuma harkan sana, an danakeyi yanzu wanda nake ganin haske acikin sa sosai.
Nace baba shine nace bari n fada ma ko zaka fahinci wani abu acikun magana ta.
Yace cikin sauke ajiyan zuciya lalai maryama al, amarin ki abin dubawa ne sosai wallahi don haka ki bani yau zuwa jibi zan duba naga may nene matsalar taki ne hakan .
Zanyi kokari nayi aiki akan matsalan ki ko Allah zai nuna muna gasken al, amarin naki don mu san abinyi akai.
Kuma nagode da baki boye min halin da kike ciki ba kikakibarwa rayuwan ki matsalan ke daya har yai nisa.
Nai sallama dashi bayan mun dan kara tataunawa da baba akan zance zuwa karfe biyar na yamma na shirya muka bar gidan na koma gida don yanzu ban yarda yamma kuma tai min a waje tunda har naji abin da babana ya fada da ya samu rayuwan shi.
Mun samu Umma a gida tana jiran isowan mu a hasale wata makwabciyar mu ta zugata ta cika fam akaina ta dauki kudirin ranan sai tayi min tas akan cutar dan ta da nakeyi ina mashi wayau ina karbe mai kudi.
Wai mahaifinane yai min asirin da na samu kan dan ta har na rabata dashi yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BA MU KADAI BANE, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
1โฃ7โฃ
GA MASU NEMAN LAYIN WAYA NA ZAKU IYA KIRANA DA WANAN NOMBA DIN SAI DAI BAN DA LOKACIN TURA WANNAN NOVEL DIN DAGA FARKO PLEASE KAMAR YADDA WASU KE BUKATAN HAKAN, , ,
08036959257
INA DA SARAUTAR MATA DA ALOKACIN MUKE A KASA WANDA NA GAMA SU NA KUDI SU MAI SO YA BIYA YASHA KARATU DA KARUWA ACIKIN SA, , , ,
Muna shiga gida da sallama abakina tare da fadin umma sannu da gida mun samay ku lafiya ?
Sai ji nayi tace muna fukan banza muna fukan wofi da ban wuni lafiya ba zaki ganni ne ?
Dake da munafukin mahaifin ki mai maku tsubbu kuna cutan mazajen ku waiku diyan malami sai Allah ya tona maku asiri wallahi.
Ni dana yafi karfin sherin ku ke da mahaifin ki wallahi maryama don Allah bazai baku ikon yin yadda kuka ga dama ba akan shi insha Allahu.
Dama bayau ba nake jin cewa wai idan za, a kaiku aure sai an maku masan manta uwa kunci don miji ya manta da kowa nashi sai ku kadai.
Ni da kuke ganina wallahi nafi karfin sherin ku balle jini na.
Komai bazaki sakeyi wa Aliyu ba kai idan ma naga masa bata sure wallahi sai na raba auren ya auro min daidai ni wace zan iya juyata yadda naso.
Duk fadan da Umma takeyi ina jinta don karshe ma a gaban dakina ta dawo ta tsaya tare dafa bango don naji ta dakyau.
Nidai ban tanka mata ba don nasan rudin sgedan ne ke damun zuciyar ta yau ina zaune kawai a bakin gadona damuwa ya damay ni.
Taci gaba dacewa dama tun farkon tafiyan ku nasan kulli ne munafukin tsohon nan yayi.
Ya taso min nan da funtun nasihan shi don yaga zan wargaza mai shirinne ashe.
Ai gashi yau sherin shi ya bishi da yakewa diyan mutane akan nashi haka zai kare a lalacen nan wallahi.
Wanan magana da Umma tayi kan mahaifina shi ya bata min raina, ban san lokacin da nace wallahi Allah babana ba mugu bane kuma ba munafuki bane.
Kuma ciwo ai yana akan kowa wallahi don mu munyarda da Allah shine mai sakawa bawan shi cuta aduk lokacin da yaso.
Au zagina zakiyi maryam don na zagi munafukin ubanki in anyi magana yace wai shi na Allah ne.
Karya na fadi ba asiri kukai wa gadanga bane ya manta da kowa sai ke kawai da diyan ki.
Dubi tun zuwan ki garin nan yaran nan basu sake maida kayan da suka saka ba ajikin su sai sabbin kaya kuke sakawa kedasu.
Gaiyan tsiya kawai gaiyyan na anya tun faeko kamar na sani naso hanashi auren irin gidan ku amma yanace shi sai yayi yau gashi da rana tsaka da raina da ladiya na kuna batun rabani da dana macuta diyar azzalumi kawai.
Ta Allah bataku ba wallahi don sai na dawo da dana a hannuna yadda na saba na rabashi da sherin ku.
Na fitowaje nace Umma kina daukan wa kanki alhakine kawai wallahi kuma ni ki daina zagin mahaifina da baici ba shaba akan daki.
Wai ma wani danki kikewa wanan halakon haka badai dan naki macuci wanda bai san darajan iyalin shi ba wanda karuwai birni suka daukewa hankali akan kowa.
Don kawai ina hakkuri dashi ina kokarin boye sirin shi don ko banza uban diyanane.
Yadda kike ganin ya cuta maki muma haka ya kwashe mu yakai garin mutane ya watsar damu can don Allah ya rufa min asiri ban wulakanta ni da yaran yadda kuka so ganin mu ba kedashi.
Shine yanzu bakin cikin ki damu umma ?
Kaya kuma da kike cewa yara na sakawa na dauka alfaharinki ne hakan ai ba bakin cikin kin ki ba.
Ni idan mata uku zaki aurawa Aliyu ba abinda ya damu maryama don ga Allah na dogara baga danki ba Umma.
Kuma ki tambaye shi idan yabani Naira biyar din shi tunda muka taka garin kaduna dashi dasunan karuwana ko taimaka min sai wani abu.
Don haka ki daina zagar min ubana dake fama da kanshi may danki ya ke bashi balle zargi ya biyo baya kuma?
Umma tace wallahi koma may ye ai ba fadi zakuyi ba kuma sai kungani wallahi.
Nace muga Alheri idan bamu da amanan ki sai dai wanda yabimu da mugun nufi yagani ga rabon shi wallahi na yarana a lokacin duk sun gudo sun dawo gareni don basu son tashin hankali.
Sai cewa suke mama please live her alone don't fight with grandma please.
Au zagina ma kuke waiku ga diyan nasara ko to nasara yaci abu kazan uban shi ni da naga mungun park karshen jankune ke nan.
Ta juya a dusace zata shiga dakin ta cikin fada aiko kamar an wullo ta daga baya ji kakai kucaaa ta fadi kasa da karfi ta yanka wani irin ihu mai razana mutum.
Ban tsaya ta kan ta ba na dauki buta zuwa alwala abina na share ta kawai nan don tai marukar bani haushi da mamaki yau.
Yadda ta rufe idon ta tana zagina da mahaifina son zargi kawai da take muna kan abin duniya.
Bayan da zanzo sai dana kashe mata kudi yafi dubu hamsim amma duk bata gani ba ita.
Koda na fito na samu bata furin taja kafa zuwa daki nai alwalana na shige dakin na tare da yarana.
Sai da na idar da sallah na kira dan anty lami ga waya yazo ya sayo muna abinda zamuci nida yaran ranan .
Yaeon bai dade ba yazo na aike shi sai gashi da drinks snacks da nama na bashi dari biyar ya tafi yana murna.
Nan mukaci mukasha muka kwanta abin mu har na kwanta nafito na rufe gida abina na kulle kofana sai safe.
Yaron anty da yaje ne take fada mata cewa yana ganin ba lafiya gidan mu don yayi gaida Umma yau bata tanka mashi ba nima yangani raina a bace.
Haka yasa tunda safe sai gata gidan mu har lokacin da na fito nai sallah banji motsin umma ba ni kuma ban bi ta kanta ba da zan muna abin karyawa ne na dan tsaya daga kofa ina mata ina kwana ban damu da ta amsa min ba na wuce kitchen abina kai tsaye na dora girki na.
Sai bayan nagama tea ne na hada muna na zuba mata nata a jug naba Abba ya kai mata dakin ta.
Shine yadawo yake fada min wai grandma is sick today
Nasan bacin ran maganan jiyane kawai yake damunta a rai don haka ban tsaya bin ta kanta ba naci gaba da gyaran gida kawai.
Shigowan Anty lami da sasaafe haka gidan mu yasa naji wani irin a raina muka shiga daki muke gaisawa da ita.
Sai take tambayana ko may ke faruwa tsakani na da Umma ban boye mata komai ba na fada mata duk yadda mukayi da Umma jiya.
Tace an ma matan nan dama abinda suke fadi a gari ke nan akan mu tunda sunga muna zaman hakkuri a gidajen mu da mazajen mu.
Nan dai muka kara dan taba hira tana kara bani hakkuri take cewa ba anga Allah ya daukaka ki ba ai yanzi ki dinga jin zargi tako ina yana tashi akan ki sai kin toshe kunnuwan ki.
Don kowa da irin abinda zai fadi saboda haka duniya ta gada dama da anga Allah ya rufa ma asiri sai an samu sherin da aka lakakawa mutum.
. Da muka fito zata tafine ta tsaya daga kofan Umma tana gaida ita mukaji shiru bata amsa ba har ina cewa tazo kawai ta tafi da hannu.
Sai ta daga labule kofan a hankali salatin danaji ta saka ta fada dakin yasa na mara mata baya hankali a tashe .
Umma ce kwance cikin amai da zawo kace kace bata ko iya daga hanayen ta a lokacin.
Hakali a tashe muka taimaka mata da gyara mata jiki muka nufi asibiti da ita.
Nan aka bamu gado dole na shiga jiyar umma ba shiri nida yan uwan ta duk wani abinda za, a kashe nice mai bayarwa.
Nakira Baban Abba yafi a kirga karshe ma a gabanta tanajin yadda yake min fada a cikin waya wai yaya nake son yayi shi fa baida ko kudin da zai kawo shi gida yanzu idan taji sauki mu mayar da ita gida kawai acigaba dana gida a gani.
Naga lokacin da Umma ta lumshe idon ta nasan bakin ciki ne ya kumay ta a lokacin.
Kwanata biyar a asibiti aka sallamota gida sai dai bata da lafiya har lokacin sai dai likita yace baiga abinda ke mata ciwo ba shi.
Haka naita dawai niya da ita a gida amma ba wani sauki atare da ita saidai kawai ta daina amai da zawo sai dai ba baki kawai sai ido da take bin mutane dashi.
****** ********* ******
Zaune nake a gaban mahaifi na wanda zuwa yanzu ya samu sauki sosai na jikin shi.
Dan shiru ya biyo baya kafin yai gyaran murya yace maryama nayi duba sosai kan al, amarinki wanda sai dana dauki tsawon lokaci kafin na iya warware al, amarin naki.
Al, amari ne wanda ke cike da abin tsoro da al, ajabi acikin ga duk wanda yaji labarin ki.
Shin maryama ko kin san kin hurda da mutanen boye kuwa ?
Da sauri na dubi gefen da nake zaune kaikace ko akwai wani zaune a kusa dani a lokacin.
Baba yace maryam Allah yai maki gyadan dogo a rayuwan ki da ya hada ki da aljannun kirki a rayuwan ki.
Nace cikin wani murya na mamaki baba aljannu kuma yace kwarai kuwa maryama da jinnu kike hurda maryama.
Shiru mukayi daga ni har baba din babu wanda yai magana kowa da abinda zuciyar shi ke kiyarsta mai a lokacin.
Muryan babane ya katseni yana fadin ki kwantar da hankalin ki don munyi hira da baban naki sosai.
Mutumin kirkine don ko a cikin jinsin su daban yake malami ne yana da ilimi sosai mai tarin yawa yasan darajan bil, adam sosai.
Ya fada min dalilin taimakon ki da yakeyi wanda ba lalaine ni na fada maki ba don yanayi ne saboda Allah.
Ke kanki maryama kin sai mutunci a gare su sosai don irin alherin da kike masu yakawo yarda da kauna a tsakanin ki dasu.
Yanzun dai matsala daya ce shine idan kina son kanki da arziki duk dokikin daya fada maki kafin ki fara sana, a ki rike su don kariyan ki.
Sun fada maki abinda basu so a gidan Alhamdullahi don kin kiyayye komai wanda hakan ya kawo taimako a gare ki don rashin masu taurin kai.
Ko anan da kike yanzun haka a tare dasu kike don sunce bazasu bar ku ke da yan uwanki jinin Amina kuyi kunya ba sai idan ku kuka kauce wa dikokin su.
Ki daina wanka da rana tsaka ki ki kuma kaucewa yin girki da tsakiyar rana wanda kuma gaskiyane.
Mu da ba haka matan mu sukeyi ba yanzun ne mata suka lalace da kiuya son jiki zai sa mace sai rana yai tsakiya tace zata dora girki a gidan ta.
Wanda bamu kadai bane a gidajen mu ba sunfi mu yawan jinsi saboda su basu mutuwa kamar mu, haka yasa sukafi mu yawa.
Duk wanda yai niyar cuta maku sai ida karfin su ya kare gurin taimaka maku koda kuwa a cikin jinsin su ne.
Don su na tare dake junsi ne masu martaba a cikin jinsin jinnu .
Kinga ashe abin naki bana wasa bane ko ita uwar mijin ki ba komai ke wahalar da ita ba sai mutanen naki.
Don ta bata maki rai ahine sukuma suka taba ta don su nuna mata kuskuren yin haka.
Don haka ina mai rokon ki da ki daina fushi da mutane don kada kija wa mutane wahala.
Saboda dazaran an taba ki su ko sai inda karfin su ya kare akan mashi gurin daukan maki fansa.
Gidan ku yanzu lafiya bake ba har makwabtanki kuna a karkashin kulawan su ne akan ki duk suke wanan alherin haka.
Maryama kinyi arziki don kinyi taraiya da jinsin daba naki ba har birnin su kike ziyara ba tare da kin sani ba.
Amma don su dakatar dake da wahalan tafiyan da bakin mai nisa kikeyi ba yasa suka dakatar dake daga hakan.
Ta hayan nuna maki ko da suwa kike hurda amma sai dai kurciya bai barki kin fahinci komai ba akai.
Yanzu baba ashe ba mutanene nake zuwa gurin su ba dama ?
Ba mutane bane maryama da jinnu kike hurda ba yan adam yan uwan ki ba da kika sani.
Nashiga uku baba aiko na debowa kaina magana ke nan ban sani ba.
Yace hukuncin Allah ne hakan maryama ai bake kadaine irin wanan ifitilain ke fadawa ba akwai ire iren ki da yawa da haka ke faruwa dasu sosai kuma babu abinda ke faruwa sai alheri kawai ke samun su.
Don haka yadda suka rikeki amana ke ma kiyi kokarin rike su amana din sai dai