Showing 36001 words to 39000 words out of 115099 words

Chapter 13 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6640

kwalawa kira tazo yace ta shafa mai a kafan shi tana shafawa tana fadin sannu malam.
Nima dake gefe daya sannu nake mashi yana amsawa da kyat dagani yana jin jikin shi sosai gaskiya.
Muna nan zaune Baba yana zufa dayar matar ma tashigo muna tare dasu sai zufa yake can ya nisa yace ikon Allah naji matukar saukin kafan nan yau wallahi.
Sai da naga ya samu natsuwa nake cewa Baba naga sakon turare sai dai ban san kudin su bane.
Yai murmushi yace dubu ashirin zaki bayae na dago da mamaki ina kallin shi na sa hannu a jakkata zan dauko kudin yace min bani zaki ba ba ki aikawa wata boyar Allah a garin ku mai marayu tafini bukatan su kice na bata sadaka.
Yai min bayanin matar nace nagane ta baba ai nasan har mijin nata ma da ya rasu.
Nai sallama dasu nafito matan tai min rakiya sai lokacin take ce min baki daiyi amfani da abinda na baki ba ko ?
Tace kiyi kokari kiyi amfani dashi zai maki amfani ga matsalan ki da maigidan ki don wanan karuwan da yake tare da ita abokiyar shedancin shi ba banza tabar shi ba.
Nai matukar mamaki da tasan abinda Baban Abba ke aikatawa a lokacin.
Nadawo kasuwa na,sari kayana na dawo gida a gajiye kamai nai wani tafiya mai nisa dani.
Haka nakan ji kullun idan na tafi gurin su baba malam din sai na dawo a gajiye dani duk jikina ya mutu.
Masu sayen kaya sunzo har gida sun sayi kayan daga ranan na fara samun costamars masu sayen kayana a cikin mutunci su zube min kudi na.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUπŸ‘©β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦


BA MU KADAI BANE A ,,,,


πŸ‘¨β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦ πŸ‘©β€πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§
1⃣2⃣


ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MUSULMAI INA MAI BAKU HAKKURIN JINA SHIRU DA KUKAYI KWANA BIYU NAYI RASHIN BABBAN YAYAN MU JIGON MU RILWANU IDRIS MAKAWA WANDA YA RASU RANAN ALHAMIS DA YAMMA,
YARASU YABAR MU DA YARA HUDU DA MATA DAYA DAFATAN ZAKU TAYA MU YI MASHI FATAN DACEWA DA RAHAMAN UBANGIN MU DASHI DA DUK MUSULMAI DA SUKA RASU TUN ZAMANI ANNABI ADAMU HAR ZUWA YAU UBANGIJI ALLAH YA KAI HASKE GA KABARIN SU IDAN NAMU YAZO MUMA MU CIKA DA KYAU DA IMANIN UBANGIJIN MU A ZUKATAN MU ALLAHUMA AMEEN ALLAH,,,,
WALAHI NAYI RASHI BABBA A RAYUWANA YAN UWA MUSULMAI,,,
😭😭😭😭😭😭






Abubuwa gaba daya sun rikice min a lokaci daya don yanzu takai Baban Abba ba ruwan shi da zance na dana yarana.
Hanna ta riga tai nisa a zuciyar shi don yanzu takai ko albashi shi ya kwasa itace zata ciyen fiye da rabi gurin bukatocin ta na yau da kullun.
Sauki na daya shine ya na sayo kayan abinci amma ba kamar yadda ya saba ba acan baya da yake sayo muna kalla kalla abubuwan bukatan mu.
Hakan da yake muna ba mu kadai ya shafa ba yin hakan ya shafi har da Umma dake zaune a kauye watau mahaifiyar shi.
Hakane ya sa,Umma din ta fara zargi a ranta cewa nice yamzu na shiga tsakanin ya da danta ina mai wayyo ina karbe mai kudin shi.
Wai da su ne nake business din da nakeyi i na mai wayo ina karbe may kudin ina turowa a gidan mu.
Anty Lami ta bugo min waya hankali a tashe tana sanar dani abinda Umma take fadi a makwabta har ya dawo kunnen yan uwana sukaji.
Shine ran su ya baci suke gani koda ma kudin shi ne nake juyawa dashi ai naci na ci din don idan anyi la,akari da irin wahalan da nasha a baya can na zaman hakkuri a gida tare da mahaifiyar shi.
Haka dai Umma take ta faman sake zamce a gari kamar a gaban ta ne ya bani kudin da take ikirari da nashi na ke ta saro kayan da nake sana,a dasu.
Nikan hankali na a kwance nake al,amurana ban damu da,wani watsar da mu da yayi ba a cikin garin mutane ba.
Don Allah ya rufa min a,siri ina sana,a a anan inda muke da kuma can gida da,ake juya min kudin sana,a ta.
Yanzu takai ba ruwan shi da zance na dana yara iyakar shi da mu ya shigo gida idan mun yi sa a ya kwana a gidan ke nan.
Tun sa,safe ba,zai tsaya ya karya ba zai ce zai tafi gurin aiki don yanzu aiki yayi masu yawa,a,sosai.
Wai suna fita zuwa operation a daji don ana,smogal din kaya ta barauniyar hanya sosai inji shi.
Komai a gidan Hanna yakeyi wacce ya mayar kamar mayar shi yanzu don komai yi mata yake yi.
Wani abu daya da ya kasa ganewa shine duk lokacin da ya dauki kudina da nake sana,a dashi yai wa hanna amfani dashi daga shi har ita sai sun shiga uku don sai sunyi wahala a rayuwan su amma ya kasa gane hakan shi.
Sa,an shi daya ba kullun ne yake daukan min kudina na ba sai zuwa lokaci mai tsawo haka yakan yi min dabara irin na maza yace na ranta mai zaiyi gyaran mota dashi ko zai turawa Umma a gida ne .
Amma da zaran ya samu yakan yi kokari ya mayar min da kudina da ya,ara sai kuma wani jikon again.
Yau ma kamar kullun haka yazo min da yake yana da bukatan kudi a gurina da dan sakin fuskan shi ya samay mu a falon zaune.
Ya dan yi wasa da Nusaiba dake shan nono a jikina wance nake batun yaye ta yanzu don ta isa yaye sai ga Aisha ta shigo falon da har taso taron shi yadda suka saba da daddy oyoyo sai kuma taja ta tsaya daga inda take tsaye take cewa sannu da dawowa Daddy yace yauwa ido ya kuke ya gida kuma.
Tace lafiya ta samu guri ta zauna can ya juya inda nake zaune hankalinana yana fa kallo yake cewa baza,a bani abinci bane yau.
Nace naga ko nai ma tayin a kawo sai kace a koshe kake yaushe rabon ka da abincin mu a gidan nan nagani.
Yace cikin murshi to yanzu dai na roka sai a bani naci ko ?
Na mike ba tare da nace mai komaiba na jero mai abinci a kayan abincin shi zuwa falo inda yake zaune.
Sai da yaci ya koshi yai nak dashi ya dan kai kishingide yana cewa, duk ya gaji har na shirya yara suka fita suka bar gidan zuwa islamiya don ya kasance asabarce ranan.
Kamar mai jiran su fita yayo cikina amma na kauce yai dan murmushi tare da cewa idan kuma ban yi magana ba ace ban damu da iyalina ba.
Ba tare da na juyo gare shi ba naci gaba da harkokina hannkali a kwance nake aiyu kana fuska ba walwala a cikin sa.
Can dai ya gama murmukusan shi ya mike zuwa bakin kofa kitchen idana ke aikina hankalina a kwance ya dafa bangon kofan yana fadin.
Maryam ina son ki ara min kudi kafin ai albashi don mota na tana son service sosai nai kamar banji may ya fada ba don dama nasan akwai abinda yake bukata a gurina da wanan sakin fuskan da ta shigo muna dashi yau.
Ya kara fadan da karfi bakiji bane may na fada kudi zaki ara min na gyara mota ta da ita nace maki.
Sai da naji shi gap dani yasa na dan juyo inda yake tsaye ina fadin kudi kamar nawa don gaskiya a,satin nan mai zuwa nake son zuwa na saro kaya da kudin dake a hannuna .
Yace bazasu dade ba zan mayar maki da su insha Allahu, nace nawa zan bada ?
Yake cewa koda zan samu dari zan so don gyaran yana da yawa sosai nake gani.
haka na juya batare da nai magana ba zuwa dakina inda na dauko wasu kudin da aka kawo min na kayan da akasaya na kirga na bashi kudin.
Inda bai kara minti goma ba a gidan ya juya ya bar gidan da sauri a cikin farin ciki yake.
Bai ko tsaya mamaki matsayin shi na mijina wanda ya kawo ni birni da kauye na ina nake samun kudi irin haka a lokaci daya duk
Sai da ya nufi gurin Hanna wace ta tayar mai da hankali a kan duk yadda zaiyi ya samo mata kudi don tana da bukatan da kudi.
Yasan idan bai samo kudin da ta bukata daga gare shi ba babu lafiya ke nan a zaman su gashi duk ta bi ta susuta shi yanzu shiga nan fita nan duk akan zaman bamza kawai da sukeyi.
Niko ba abinda ya damay ni da harkan su sai sana,ata nakeyi hankali kwamce inda mutane ke yaba kyaun kayana wanda ba kowane zai samay su ba idan ya,shiga kasuwa sari zan ma mutum kwatamce amma bazai gane shagon ba sai idan nice na shiga kasuwa da kaina na sayo wa mutum.
Kayana suna matukar samun karbuwa a gurin mutane don wasu har cewa sukeyi wai a waje nake sayo wa ina dai masu bat da sau ne kawai.
Dariya sukan bani idan sun fadi hakan har lakani suke min wai hajiyar Dubai don sun gane akwai wanda nake ba sakon kaya na a boye.

****** ********* ******
Shiru har ana batun sati biyu da karban kudin da yayi bai bani ba gashi na kula hankalin shi a tashe yake duk kwanakin nan.
Sai dai bai fada min damuwan shi ba nima ban tambaye shi ba tunda yanzu ba shawara yakeyi dani ba kamar baya da komai a tare muke abin mu gwanin ban sha,awa damu.
Abinda ban sani ba,shine ashe daga shi har hanna suna cikin tashin hankali kan kudina da ya karba ya bata.
Don ranan da ya kai mata kudin ta karbe su a wulakance ba bu godiya ko yabawa a tare da ita.
Sai da dare ta,shiya ta dauki kudin zuwa sayen abinda tai niyar sayowa nan tasha dan banzan mari a cikin Napep din da ta shiga ba tare da tasan wanda yake dukan ta ba sai da jikin ta yai rudu rudu aka watsar da ita a daji ba Napep ba dalilin shi haka ta dawo gida rijib da ita kuma ga kudin bata gan su ba sun bace daga hand bag din ta.
Da kyat ta samu ta dawo gida ta sha dukan tsiya a kan kudin shiko gogan yana barin gidan ta yaga kamar mutum ya gitta mai a gaban shi.
Yaja burki da karfi ya tsaya yafito babu kowa a furin ya sauke ajiyan zuciya ya koma mota yayi yayi ya tayar da motar shi amma motar taki tashi mai.
Haka ya karasa office din su a gajiye ya kira bakanike ya duba mai motar amma taki tashi.
Ba,a gane may ke damun motar ba anyi anyi motar haka kawai an kasa gane may ke damun ta.
Hankalin yashi ya kasu biyu ga hanna dake kwamce akan dukan da tasha bata san mai dukan ta ba sai warning din da taji an mata cewa gobe ta kara karban alhakin wasu ta kashe.
Ana haka aka bugo min waya cewa babana baida lafiya yana fama da ciwon ciki.
Hankalina ya daga gashi dan abinda ke guri na na riga da na,sari kaya dashi a lokacin.
Hakalina yai matukar tashi yadda nake samun labarin mahaifina yana jin jiki haka yasa na yanke shawara zuwa gurin baba malam na fada mashi na shirya tare da tsaraba da zan kai masu na shiga mota sai tafiya muke amma yau abin mamaki ko alaman garin dan kauyen su baba malam ban gani ba.
Har muka fara shiga kauyukan garin plauto jos haka yasa hankalina ya fara dagawa na jawo wayana dake cikin jakata naga time din da kashe a cikin mota a zaune.
Da sauri nace wa driver ya sauke ni a,wani dan kauye da muka kai.
Nan na sake tare mota na juyo na dawo kaduna lokacin har magariba ya soma yi nakawo gida a gajiye dani.
Na,samu su Anty hankalin su a tashe don sun dauka ko nabace ne ko an sace ni tunda ban taba yin haka ba.
Idan na fita ban kai karfe biyun rana a,waje na dawo gida daga inda na tafi.
Ranan ko girkin kwarai ban samu girkawa ba a gidan sai indomie na dafawa yaran sukaci kawai.
Da dare ma,bamuyi wani dogon hira ba karfe goma duk mun shiga barci dagani har yaran saboda gajiyan dana kwaso.
Can musalin karbi biyun dare na fara mafalki kamar an tashe ni sai ganin anty nan wace nake nema a rayuwana nayi.
Tace min tashi muyi magana dake ban musa ba na mike zaune tare da cewa Anty mukaddarasiya may yasa kika bace bayan kin taimaki rayuwana kin hadani da mutanen arziki yan uwan ki masu mutunci da karamci.
Wanda ta sanadin ki na zama wata abin alfahari a cikin yan uwana da abokan arziki.
Murmushi tayi tare da dafa kafada na take cewa kwantar da hankalin ko don ke daga cikin jinsin bil,adam ta daban ce ke kina da mutunci da halarci maryama.
Kin min abin da ban zataba daga cikin jinsin ku maryama shine ya hana na dauki duk wani matakin da naso dauka akanki a baya.
Wanan gidan da kuke a ciki gidan mune ni da mahafana da yan uwana da mijina.
Munyi tafiya ne zuwa kasan saudiya gurin bautan ubangijin mu bisa ga yadda sunna ta koyar da al,umman musulmai.
Amma kassh sai gashi an turo ni ni da yara muzo mu fara gyaran guri na sami kunzo ke da diyan ki da maigidan ki kun mamaye muna guri.
Duk da dai ba,yawa ne daku ba kamar mu don mu a gidan nan yanzun haka mukai mutum dari da dan kai don haka kinga mun fiku yawa ke nan.
Yanzu haka iyayyena suna gap da dawowa garin nan ban san idan sun dawo yadda zamu kasance da ku ba.
Sai dai baba malam yai wa mahaifina bayanin irin halin kirkin dake gare ki keda diyan ki.
Hakan yasa aka hana kowan mu da ya cuta maku don yarana ne suka cutawa yar ki a baya shine sanadiyan da har na kaiki gurin baba malam don idan bashi ba duk nahiyar nan babu wanda zai iya taimaka mata.
Ina son ki kwantar da hankali ki kada ki tayar da hankalin ki, don da yardan Allah babu abinda zai cutata maku a gidan nan idan har kinci gaba da tsare irin dokin da kike tsarewa wanda bamu son kina yi a gidan nan .
Kina da matukar kirki maryama don haka baza mu bari wani ya cutawa rayuwan ki.
Sai dai kada ki kara cewa zaki tsibiri don bazaki iya zuwa ba da kin san irin nisan shi da baki wahalal da rayuwan ki ba a dazun don zuwa can.
Kamar yadda Baba malam ya fada maki idan kina son ganin shi ki nasa a ranki cewa zaki tafi can don ba,a kasan nan bane har fa birnin sin tsibiri yake kawai dai mu yan yankin wanan jinsin na kasan kaduna ne muna zaune ne daku kawai a nan cikin namu yanayi.
Nadago kaina ina kalon ta da mamaki don a lokacin har ta mike tsaye daga zaunen da take a kusa dani.
Nace birnin sin fa kikace anty tace min kwarai maryama kin san mu ba iriku bane yan adam mu jinnu ne ba mutane bane.
Mikewa nayi tsaye da sauri na taka har gaban ta tace kina mamaki ne maryama ?
Kwarai kuwa mu ba mutane bane nace a da sauri kina nufin harda babana baba malam ba dan adam bane ?
Tace malam yai maki kama da dan adam ne maryama ?
Malam ba mutum bane kawai dai mun juya maki ne ta tsigar yan adam don kada ki rana da kamanin mu idan kin gani.
Amma ba zamu taba cuta maki ba sai dai ma mu taimaka maki don malam din yace min mahaifiyar ki tana da alaka sosai da su malam din wanda ni kaina na yarda da hakan.
Kodon barin da akayi kina shiga cikin mu batare da wanin mu ya iya cuta maki ba don haka ni dake mun zama yan uwa daga yau ki rike a ran ki hakan.
Maryama ban san irin son da kikewa malam ba haka wanda hakan har takai naga nawa mahaifin da yake yaya ga malam shima yana matukar son ki maryama.
Don ko yaushe idan muna magana dashi zai tambayi lafiyan ki dana yaranki yakuma jaddada min akan na kula dake kamar yadda nake kula da sauran yan uwana dake nan.
Kudin ki da mijin ki ya karba yakaiwa karuwan sa sunan nan a cikin jakar ki na sa an karbo maki su.
Sai kuma wanan maganin gashi ta dora min a saman mirror dake dakin tace baba malam yabani magani na kawo maki .
Yace na baki hakkuri bisa ga rashin ganin shi da baki samu yi dazun ba don yana aiki shiyasa bai sanda zuwan ki ba a bude maki hanyan ganin ki ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login