Showing 66001 words to 69000 words out of 115099 words
Chapter 23 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
ce min zaki kara jina da yardan Allah amma don Allah ina son nai maki wani tambaya idan bazaki damu ba.
Ba matsala mama kiyi tambayan ki don Allah nace koke mutumiyar wani gari ?
Nai murmushi nace ni mutumiyar Niger state ne mama tace ikon Allah zamane yakawoku garin nan ko aiki.
Nace aikine yakawo maigidana garin nan shi ma,aikacin custum ne na kasa, shine muka zonan din tare dashi.
Tace yanzun na gamsu dake maryama kin san duniya abin tsoro ne sosai yanzu dole nayi bincike sosai akan ki don gudun kada wani ya turo ki gareni cikin rashin sani a yaudare ni.
Don hakan yasha faruwa dani sai ka yarda da mutum yazo ya yaudare ka daga baya kuma haka yasa nake jin tsoron hurda da mutane yanzu.
Amma kinga yanzu na gamsu na dai fahinci ke alheri ce a rayuwana maryam
Don kafin kizo na dade ina mafalki dake duk dare idan na kwanta zan dinga jin sunan ki a mafalki na ana fada min cewa kece zaki kawo min maganin warakana.
Da farko har ina daukan zancen zancd ne na mafalki kawai, amma daga baya danaga abin yai yawa sai na fara tunane akai.
Kwasan ranan da zaki zone nai mafalki da nai bakuwa maryam sunan ta zato zo min da warakana.
Ba karamin jin jiki nayi a gidan nan ba watarana ma sai naji dama na mutu na huta da wahalan duniyan nan kawai.
Nace mama mutuwa dace ne ga rahamar ubangiji don haka bawa ya roki Allah sauki akan al, amuranshi shine mafita kawai.
Tace hakane wallahi ina yawan kai kokena ga ubangiji kin ga Allah ya karba min.
Ta saka hannun ta a cikin hand bag din ta tana cewa Aisha da tashigo dakin baby zonan ki karba a saya maki alawa kinji.
Aisha tazo gareta tana cewa yaya sunan ki yan mata ?
Sai Aishan take ce mata Aisha Aliyu Auna.
Kai kice ke takwaratace ashe ?
Ikon Allah to karbi mummy ta saya maku alawa keda yan uwanki kinji ki yi kokari a school kinji kada kiyi ragganci ba, asan Aisha da tsoro ba.
Aisha tace na gode mummy abin yaba hajiya sha,awa yarinya karama ta san anbata abu tayi godiya haka.
Murmushi nayi daga inda nake zaune ina jin yadda hajiya take yaba mai sunan su.
Kudi ne sabbi rapper yan dubu daya mike dasu har guda biyu.
Nace kai mama kudin nan sunyi yawa wallahi da dai ki rage su please.
Tace haba maryam don baki san ko nawa na kashe akan jikin nan nawa ba ko .?
Na kashe kudi masu yawa ga banza banyi nasara ba don dan wanan dana baki aiba komai bane don ban iya biyan ki abinda kikai min arayuwana.
Sana dinki nake gani insha Allahu sauki ya samu a gareni da yardan ubangiji.
Nace dama haka rayuwa yake ciwo daban magani daban sai an wahala kafin asamu nasara akai.
Tana mikewa tana gyara tsayuwan glass din ta Aliyu ya shigo gidan ranshi abace.
Tun daya shawo kwanan mu ya hango wani katuwar motar jeep tsaye a kofan gidan shi yake mamaki kowake da wanan motan haka ?
Don iya sanin shi bai san wani ba aduk fadin garin nan da zai mallaki motar miliyoyin kudi har yazo gurin shi.
Har ya fito idon shi yana akan motar yana kiyasta yawan kudin wanan lafiyayyen motan daya gani fake kofan gidan.
Sun dai gaisa da bashir a waje amma bai mashi magana ba yashigo gidan.
Lokacin ya samu hajiya tana shirin ficewa daga gidan ganin shi yasa hajiya dakatawa daga tafiyan da zatayi.
Tace ko wanan ne surikin nawa ko ?
Tace mai barka dai yaya aiki yaya iyali ya amsa adan darare don rashin sanin ko ita din wacce.
Tace to ni zan tafi sai anjima ke nan nagode ko Aisha Allah yabamu Alheri.
Tana fita daga gidan yakai idon shi kan kudin da Aisha take mika min a hannun ta.
Cikin wani murya yake cewa maryam wacece wanan matar dana gani yanzu tafita.
Nace nima ban san ta ba kawai dai Allah ne ya hadani da ita har tazo gidan nan amma nima ban sani ba wallahi.
Sai dai naji ance kamar matar tsohon shugaban kasan nan ce ita.
May yakawota gurinki yanzu kuma ina kika santa ma wai ?
Nace sako tazo na bata kuma na bata abinta ta tafi sakon may naji ya jefo min tambayan abazata.
Nace magani ne irin na maganan mata kawai tazo na bata kuma nabata ta tafi.
Kallon sunkin kudin dake aje a gabana yakeyi yana kada kafan shi har lokacin
Kudin nan fa nace yara taba kyauta tace,
Yace mu gani nawane kudin kamar fa duk yan dubu dubu ne nace ban duba kalan su ba don basu gabana yanzu.
Mikewa yayi yatako har gabana ya dauki kudin ya bude wrappers din dubu dubu guda biyu a ciki.
Yace what kyautan dubu dari biyu kai tsaye haka ikon Allah.
Nace wanan bakomai bane a gurin su don Allah ya hore masu shi basu hasaran bawa nabaya dasu.
Kallona yake a cikin mamaki Ummace da tai magana yasa zancen ya katse bai samu furta komai ba again.
Nake cewa Umma may kike so ne na karasa da kyat zuwa inda take don duk jikina yai nauyi sosai a lokacin kamar nai wani aiki mai nauyi.
Ruwa take so na debo mata ruwa na kafa mata tasha tace Allah yai maki albarka.
Amin umma nace har na zauna take cewa kuma tana son ta kewaya bandaki.
Namike nakaita ta kewaya tafito duk yana zaune yana kallon mu duk abinda mukeyi da ita.
Haka yasa ya dan nisa kadan tare da dan bubuga kafan shi a kasa don yaga irin faman da nake da mahaifiyar shi abin yai yawa sosai cikin ma wai ta samu sauki ke nan.
Yace cikin dan sauke ajiyan zuciya amma yanzu naga kaman jikin na umma akwai sauki sosai don gashi har naji kaman tana magana ko ?
Gashi kuma tana dan takawa da kafan ta a hankali dai sauki na shigowa ke nan.
Har yanzu maganin hawan jinin ne kukeyi ko may ?
Nace ba hauwan jini bane ke damun ta ciwo dai ne don maganin hawan jinin ai halakata ya so yayi.
Sai dana canza mata da na gargajiya gurin dana taba karbawa Nusaiba ta samu lafiya can na karbo mata shine mukaga wanan saukin haka.
Maganin hausa kukeyi aka samu wanan saukin haka ke nan ?
Nace shi mukeyi da yardan Allah kuma zata samu lafiya takoma daidai da ita.
Allah yasa yace tare da mikewa tsaye yana fadin shi zai fita ke nan ko akwai abinci yunwa yake ji.
Kai Umma ta girgiza don takaici ni dai na mike na kawo mai abincin shi ya fara ci ga nama zuku zuku a ciki ya zauna yaci sosai can yace wai naman may ye haka kuka samu mai dadi ?
Nace naman baunane aka bani nai miya dashi da sauri naga ya mike tsaye yace what naman bauna a ina kika samu naman bauna haka?
Nace kaidai ba kaci ba may ye na tambaya kuma haka kaman wanda yaci naman mugun dabba.
Look ina kika samu nama nace maki please ?
Nace anbani ne a wani tsibiri danaje karbowa Umma magani.
Yace what ?
Sai naga ya fara kakaro amai kamar mai son amaye hanjin cikin shi lokaci daya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/11, 12:10 AM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BANE A, , , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
2โฃ2โฃ
Ya shiga damuwa don yasan tabbas akwai bakon al,mari ga zancen na a yanzu.
Fita yayi daga gidan bayan ya gama kare karen aman shi a back yard yafito zuwa waje.
Wayan shi dake a aljihu shi yaciro ya kira layin mahaifina wanda yake gani shi ya dace ya fara fadawa wanan zancen.
Sun gaisa da babana tare da tambayan jikin shi shima baba tambayan jikin Umma yayi da aikin shi.
Ya amsa alhamdullahi ba duk muna lafiya Umma ta samu sauki sosai don yanzu har tana tafiya tana magana.
Alhamdullahi inji baba din yace,
Aliyu yace baba dama nakiraka ne na fada ma wani magana akan maryam.
Subbahanallahi inji baba din yace maryam kuma may samay ta kuma ?
Aliyu yace baba a gaskiya maryam yanzu gaba daya ta canza wani bakon al, amari ne nake gani a gareta.
Ga mamakin Aliyu din sai yaji baba yace na jinnu ko ?
Yace a sanyaye haka ne baba.
Yace gaskiya maryam tana tare da jinnu kuma masu karfi ne a tare da ita sai dai bama su cutawa bane.
Dama kasan matsalan mahaifiyar ta ke nan shine yanzu suka koma kan yar ta.
Kada ka damu da wanan don nayi iya yina akan hakan amma babu abin da zan iya akai dole mu barta da abinta don musulmai suma kamar mu.
Al,amarin maryam da jinnun nan yai nisa Aliyu matsala daya ne ka kaucewa shiga harkan ta ta baya don kada su dauki fansa akan ka.
Saboda duk wanda ya shiga harkan maryam a shirye suke da su dau fansa akan mayshi.
Saboda son da sukewa mahaifiyan tane ya shafe ta har suke mata wanan irin son haka.
Amma gaskiya al, amarin maryam nima yafi karfi na don maryam tasan abinda ni dakai da ma wani bai sani ba a yanzu.
Kallo daya zataiwa mutum ta gane matsalan da mutum yake ciki kaga ashe al, amarin nata yayi nisa ke nan.
Nisawa Aliyu yayi yace to yanzu baba yaya za, ayi ke nan ko haka zamu sa mata ido muna kallon ta.
Murmushi baba na yayi yace Aliyu ka kwantar da hankalin ka akan al, amarin nan don abin yai mata nisa sosai.
Kuma zuwan ku gidan nan na kaduna ne abin ya karu a kan ta don a gidan kuna tare dasu duk inda ma kake tunanen zaku yanzu a tare dasu kuke.
Duk gidan da kake gani akwai su sai dai mu bamu sani ne sunfi mu yawa a duniya don su basu mutuwa.
Muko kaga muna ragewa don muna mutuwa kuma bamu da shekaru kamar su.
Maryam tare take da babban malamin jinnu wanda kowa ya sani da Alhaji malam
Sunan shi sulaimana malami kamar shehi ko waliyi a cikin su yai taimako ne shi a duk inda yaga musulmi yana a cikin halin bukatan taimako.
A sana diyar yar shi maryam ta hadu dashi wanda har yakai sun bude mata ido tana ganin su ko yaushe har tana zuwa biranen su ziyaran su.
Ziyaran su baba ita maryam din ?
Babana yace ita din kuwa duk sanda taso zuwa garesu suna bude mata ido zuwa tsibirin su dake kasan sin amma rayuwan su tankar anan ida kuke sukeyin shi don su a gurin su ba komai bane hakan.
Shiru Aliyu yayi yana sauraren babana a cikin tashin hankali da ke mai bayani akai na.
Su kai sallama da baba ya kashe wayan cikin tashin hankali yana mamaki yaushe ne wanan al, amari ya fara wa maryam haka har yai nisa bai sani ba.
Cikin damuwa yake sosai haka yaja kafar shi yafita yabar gidan cikin damuwa yana ta faman sake sake a ran shi.
Ji yake kawai ya nemi wani gida mu bar wanan tunda shine keda matsala.
****** ********* ******
Har yamma yana batun yi ban shiga gidan mai jego ba kamar yadda nai masu alkawari gashi sai faman jiran shigowa na sukeyi a gidan
Ganin banzo ba yasa suka biyo ni har gida gurin na sun samay ni akwance cikin mutuwan jiki kan abubuwan da suka faru dani don ba sabawa da hakan jikina yayi ba.
Yanzu mama Abba haka mukayi dake bayan kin san muna da appointment dake zaki share mu gidan maijego muna jiran ki.
Mu dai fito muna da kayan mugani idan irin wanda nake dasu ne nabar maki kayan ki.
Don ke san sokoto mune iyakan kayan mata ba a gwada muna kaya sai dai mu gwadawa wasu.
Ni dai sai murmushi nakeyi kawai na mike zuwa dakin yara inda na aje kayan tun lokacin da nazo dasu gidan.
Nake cewa dasu su shigo don Umma tana zaune a falon kuma ina jin kunya da nauyi tasan abinda mukeyi.
Nan muka zube na fara fitar masu ina masu bayani akan komai suna gamsuwa.
Yar sokoto take cewa gaskiya ita bata taba ganin wanan kayan ba tanayi tana dan danawa wai ita tasan kan su.
Sosai sukai min ciniki don sun sai kayan yadda ya kamata su saya duk da ban cika masu kudi ba sosai.
Sun fita na koma na kwanta abina don ina jin jiki na sosai a lokacin.
Sai dai kafin subar gidan mu har yar sokoto tafara wani hamma tana mika na ce yaya dai mutumiyar sokoto takecewa ai ba magana kawai wanan kayan naki maman Abba akwai caji wallahi.
Anty hauwa ta kara rudewa akansu sai dariya mukewa yar sokoto suka fice.
Waahegari yara na tafiya makaran ta sai ga anty hauwa a gidan mu cikin hausan tana yare take ce min.
Maman Abba zozozonan mu zauna yanzu kina da wanan kayan haka kika barni ina kashe kudi na a banza kan wasu.
Nan dai take bani labarin yadda suka kwashe da mijin ta a daren jiya.
A raina nace masu maza ke nan nikan rabona da nawa mijin ma aina manta rana.
Sai dai naga jiya ya kwana a gida yana ta faman juyi yana tsuki ban bi ta kanshi ba don nima ina fama da kaina.
Ganin na samu sauki washegari na shirya zuwa sarin kaya don na samu naci kasuwa gurin masu shigowa suna easthe din mu jibi.
Na shirya sai kasuwa shagon bedshirt na nufa na samay shi zaune shagon ya karade da sautin kira,a na Sudes.
Shima kanshi mai shagon sai ka dauka ko wani balarabd ne shi ga gemen shi mai tsawo kamar balarabe cikin kamun kai.
Yana ganina yadan saki murmushi yana cewa maman Nusaiba yaya kwana biyu ?
Yanzu bakya son zuwa da Nusaiba ta girma ko tayi wayo?
Nace tana gida na barta da yan uwanta a gida ne yace aiko basu gida akwai mutane a gidan ku don babu ku kadai bane a gidan.
Yace kina zaune tare da mutanen kirki masu halin alheri a tare dake.
Azatona ko su anty hauwa yake nufi nace hakane fa suna da kirki da dadin zama.
Yace lokacin da yake mikewa tsaye kwanaki mata suke fada min kin shigo gida sai dai kin samay mu da baki a gidan.
Nace hakane nima ban san da zancen haihuwan ba dana tafi da shiri na ai ranan sai kawai na samu gidan da baki a cike.
Yace sai dai kiyi hakkuri don na tambaya ko dai ba wanda ya razanaki ake ce min kin samu kulawa daga gurin Fati,a
Kin san bukin mu ba irin naku bane don mu mutane ne daga nahiya daban daban suke zuwa muna kowa da halinshi kuma.
Ba, abinda ya samay ni nace mai a gaiyar min dasu idan ya tafi gida.
Bedshirt ne masu kyau ya fitar min dasu a gabana yana cewa wanan kayan masu kyaune yan bugun chaina ne kingan su nan .
Saboda ke na ajesu don zaki samu alheri sosai akan su da yar da Allah.
Nace anya zan iya saran su duka kuwa sai dai na saya daidai kudina kawai iya inda ya tsaya.
Yace haba malama maryam damu dake yanzu mun zama daya kina zama a gida daya da yan uwana akan may bazamu taimaka maki ba.
Nace abarshi kawai zan dai dauki iya kudina inayi ina juya kayan don kyawon su.
Na koma fannin kayan yara ina dan dubawa a hankali muryan shi naji yana fadin .
Ki zabi wanda kike so sai na aje maki don kinga Azumi ya kusa lokacin cinikin su yayi .
Zan kuma dauki lokaci mai tsawo bana nan don bani azumi kin san a kasar na ina zuwa ibada ni da iyalina.
Ina zaba yana ce min hada da wanan wancan ma zai dauko gareki har na tara kaya masu yawa ban farga ba.
Na fita zuwa shagon turare na sai iya kudina da sauran tarkacen da nake bukata a kasuwan wanda nasan zasuyi sauri shiga gun mutane.
Nadawo gida niki niki da kaya mai taxi ya dora min kan step ya tafi bayan na biya shi.
Na dan zauna falo na huta har abinci sai da naci na dan sarara na mike zuwa dakina don na aje handbag dina.
Sai may ?
Kayan yaran dana zaba a kasuwa nace a je min idan na samu kudi