Showing 30001 words to 33000 words out of 115099 words
Chapter 11 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
๐ฉโ๐ฉโ๐ง
1โฃ1โฃ
Sosai mafalkin da nayi da malam baba da kamshin shi da nake ji ya tsaya min a zuciyana.
Gashi kamar an daure min bakina don na kasa fadawa kowa irin halin da nake ciki har shi mai gidan nawa ma ban fada mai ba.
Wani sabon yanayi da Baban Abba ya canza min yanzu yazo min da wani sabon sallo wanda ke nuna min rashin damuwar shi da mu.
Daga ni har yaran yanzu bai damu da damuwar mu ba hatta Aisha da,suke dasawa dashi ba ruwan da ita sam ya daina yawan damuwa da al,amarin mu kamar baya.
Da farko na dauka ko wani laifi ne nai mashi amma iya tunane na ni banga abinda nai mashi ba gaskiya.
Ko da yadawo ne yaran sukaje gun su yanzu zaice kada ku damay ni please ku barni na huta don Allah.
Tun abin yana damuna har nakai ga mashi magana ranan da ya dawo muna taron shi ya fada saman kujera a gajiye dashi.
Aisha tazo kamar yadda ta saba idan ya dawo tana ta faman bashi labari makaranta.
Wani tsawa ya daka mata yace for god sake Aisha ki barni na huta haka don Allah ba dama mutum ya dawo ya huta ku ishe shi da surutun tsiya kawai.
Take wani yaro ya kama kanshi da shi suka fita batun shi yarinyar bata barshi ba sai jefi jefi yake bata amsa.
Yafita yaje sallah ya dawo abinci kawai yaci ya koma daga cikin daki yana waya a cikin fara,a da nishadi.
A haka na shigo dakin na samay shi yana wayan shi cikin nishadi kamar bashi ba na gani a falon a daure yan mintinan da suka wuce.
Ni dai na dauki abinda zan dauka na koma falon gurin yarana mukaci gaba da abinda mukeyi dasu.
Haka muka kwana ko kallon gurin da nake baiyi ba har takai tsawon sati muna cikin wanan halin na rashi kula da mu da bai yi kamar farko
Idan yadawo kaga fara,an shi sai idan yana waya wanda da farko ma idan ya dawo gida kusan kashe wayan shi yakeyi.
Amma yanzu ko wani lokaci zaka ganshi da waya makale yanayi yana dariya cikin shauki .
Da naga abin yai yawa rana bayan yara sunyi barci nake cewa Baban Abba wai halan dai mun maka wani laifi ne ?
Nace idan ma laifi mukai maka don Allah dai kayi hakkuri da mu kaine uwar mu kaine uban mu a garin nan bamu san kowa sai Allah sai kai.
Zanci gaba yace for god sake maryam ki kyale ni please ban son yawan damuwan nan naki please ?
Kallon mamaki nai mashi nace to Allah ya kyauta ni dai har nai barci yana kan wayanshi wanda na fahinci da mace ce yake wayan a lokacin.
Ganin haka yasa na fita batun shi na kawo ido na,saka mai kawai duk da abin yana yawan damu na to amma yaya zanyi.
Kwaliya, girki, gyaran gida ladabi da biyayya babu wanda ban mashi amma ya dauko min wanan halin daga sama.
Ranan da zaman hakan ya ishe ni na,shirya naje gurin Anty hauwa na samay ta akan zancen sana,an da nake son yi na bedshet.
Nan tai ta,duba min ta yi seaching din shagon da ake sayar da kayan muka,aje ranan da zamu tafi shagon da ita.
Wanan kudin dai sune na dauko muka tafi muka sara kaya zanuwan gado da su takalma masu kyau sosai na hado har da kayan yara.
****** ********* ******
Yarinyar da yake waya,da ita ashe wata budurwan shi ce tun zuwan shi garin a unguwar da yafara zama kafin ya kwaso mu suke tare.
Kuma har yai mata alkawarin cewa zai aureta da yardan Allah sai bayan ya zo da mune ya canza unguwa abin nasu yai sanyi sosai.
Yanzun kuma ta nemo shi suka sake dinkewa da ita ba dare ba rana yana gurin ta ko suna makale a waya matan KD ke nan.
Yau kudi take so a gurin shi wai tana da buki don haka rake son ya bata kudi don yasaba sake mata kudi ana karya.
Gashi kwana biyu basu tafi operation ba yara ina ne zai samo kudi ya bata sai wanan kudin da maryam tai mai magana ya fado mashi a rai kawai don haka yana dawowa da dare yake cewa.
Bayan yaga kaya birjit a saman kujeran falo na zube su a gurin yake cewa maryam dauko min wanan kudin da kika nuna min a kwanaki.
Gabana ne ya fadi sai dai na dake a fili nace wasu kudi fa ke nan ?
Yace cikin daure fuska kudin da nace ki aje a gurin ki har nai nazari a kan su mana.
Nace kudin kan maisu ta karbi abin ta yau din nan yace kudin waye nace kudi anty hauwa ce mana.
Kallona yake a cikin mamaki sai lokacin hankalin shi ya kai ga tarin kayan dake falon yace wanan kayan waye haka kuma ?
Nakara cewa nata ne tasaro tabani nima nayi sana,a dasu zan tura gida ne akaiwa anty Lami.
Kamar zaiyi magana sai yai shiru na lura ya shiga tashin hankali a lokacin can wayan shi tai kara ya dauka.
Ya manta yasa handfree babu ko sallama take cewa yaya kabarni ina jiran kudin tun dazu ga kowa yasayo anko ni ban saye ba dubu hamsim ne fa kawai nace ka bani fa ?
Kunya yaji amma sai ya basar ya mayar da,wayan silent yana cewa ki saurare ni mana Nadiya banace zan baki ba.
Sai lokacin na gane abinda yake nufi da kudin dana kasosu yau a kasuwa.
Duk da raina ya baci ban mashi magana ba na dake kawai kamar banji may yake a,waya ba.
Sai da ya kashe wayan kunyane ya kamashi yace Aisha yau ba labarin makaranta ne.
Yarinyar da dama zaman shiru ya ishe su a lokacin ta shiga bashi labarin game din da sukayi tazo na biyu gurin gudu.
Kamar ban san sunayi ba na fita batun shi nan yake ta faman kamay kamay da yaran yanayi yana kallon fuskana.
Ranan duk cikin kamay kamay da yakeyi fa,wayan shi yarinyar tana ta faman kira amma daga karshe sai ya kashe wayan kawai.
Bayan yaran sunyi barci ne shi da kanshi ya kwashe su yakai daki ya kwantar dasu.
Nagama komai nashige abina na kwanta tunda yanzun haka ya saba muna dashi.
Can na fara barci naji shi a gefe na yana lalube na a hankali na bude idanuwa na nake cewa yau kuma ban yi laifin bane?
Murmushi kawai naji yayi yana kokarin jawo ni jikin shi kawai duk yadda yaso haka na kyale shi har yayi abinda zaiyi ya kyale ni.
Da safe na gama komai da zai fita yake cewa wai na shirya idan ya dawo zamu fita zuwa cikin gari gaba daya da yaran.
Tun fitan su ranan ban yi komai ba sai faman tunane nakeyi akan maganan matar da naji jiya a wayan shi.
Ana nufin cewa mace baban Abba yake nufin zai ba kudi har dubu hamsim gani ni matar shi ko goma bai taba bani ba a rayuwana.
Na sani ba zan hana shi aure ba idan ya tashi kuma bazan mashi magana komai ba a yanzu balle ya dauka ina kishi ne akai.
Yanzun badon Allah ya taimake ni ba yaya zanyi idan ta karbe kudin nan ni banci ba sai dai yaba wata yar iska can a waje ta cinye su a banza kawai.
Kai maza Allah dai ya kyauta kawai ina zaku kai alhakin matan ku ne wai da wanan irin cin amanan haka ?
Jifa yadda yazo min a daure wai na kawo kudin nan da tace na aje a baya kamar kudin shi ne fa ?
Haka na gaji na mike na fara parking din kayan a wani katon jakar ghana most go don na daure su guri daya yadda za,aji dadin tafiya min dasu wani abu bai samay su ba a hanya.
A karshe dai na yanke shawaran na koma gurin Baba malam nakai mai ziyar don na gaida su.
Baima dawo gidan ba yadda yace sai yamma ya shigo gidan kuma a gajiye babu batun fita ke nan.
Ina zaune na kurawa tv indo wanda a zahiri ba kallon nakeyi ba don ko antambaye ni may akeyi bazan iya fadi ba a lokacin.
Yafito cikin shigar kananan kaya sai faman kamshi turare ke tashi a jikin shi.
Yana daura agogo a hannun shi yake cewa ni zan fita sai na dawo nai mamaki yadda yau zai fita da dare haka abinda bai saba yi ba.
Sai da yakai kofa yake cewa wai may ye babu shi a gidan na amfanin safe ya sayo ?
Nace ban duba ba ban san ko mayye babu ba don ban saba fadin babu ba ya kalle ni kamar zaiyi magana sai kuma ya kyale yafita kawai.
Bai dawo ba har munyi barci sai can cikin dare naji tana ta faman nocking da kyata na tashi na bude maigidan ya shigo.
Ban tsaya tambayan shi abinci ba na juya nashige abina na kwanta shima yana gama shirin shi ya kwanta sai safe.
Washe gari kamar yadda na saba idan na dora wa yara breakfast na dawo nai sallah na zauna na dan yi azkar haka ma da magariba nakan yi hakan.
Yau ma ina gamawa na mike tare da ninke abin sallah na nufi kitchen na samu shimkafan da na,dora har ya tsane ko na mayar da miya saman wuta na dumama masu shi da kyau.
Yafito a cikin shirin shi lokacin ina gyaran falo nan ya zauna yana breakfast sai da ya kusa gamawa nake cewa yau ina son zani unguwa nazaci zaice wani abu amma sai cewa yayi a dawo lafiya kawai.
Bayan na gama shirina ne na kulle gidan na fita zuwa gidan baba malam da nai niya don na fada mai halin da muke ciki da baban Abba din yanzu saboda ya zama min kamar uba a guri na yanzu.
Sai dai may har na karaci tsayi gurin dana saba tsayi babu motar garin ba,alaman shi zafin rana ya isheni haka najuyo na,dawo gida ban samu zuwa ba inda nai niyar zuwa din.
Zaman da nayi a cikin rana yasa min kasala bayan munci abinci da Nusaiba na kwanta don na bata nono sai barci ya kwashe ni a gurin.
Can a cikin barci nane nai mafalki gani zaune da matan makam harda tsaraban da na dauka nakai masu gashi wai ina basu suna min godiya.
Na tafi gurin malam muka gaisa kamar yadda muka saba idan naje yake ce min kin manta cewa na fada maki cewa idan zakizo gurina ki kiyasta a ranki zaki ganni gashi kunje kun shawo rana dake da yar ki a banza haka.
Maryama baki gudun yarki ta kamu da wani cuta na daban kuma bayan Allah ya bata lafiya yanzu.
Yace yarona ne yagan ki kina jiran mota ya shigo gari dazun shine yake fada min yaganki kuma yasan nan gurina zaki zo.
Nace Baba kayi hakkuri na manta ne dama sai ya tare ni yace dama zaki kawo min karan mijin ki ne ko?
Yace mazan ku haka suke don haka kiyi hakkuri koda kince zaki tayar da hankalin ki a halin yanzu yai nisa baya jin kira da sannu zai gane gaskiya da kan shi.
Yace naga kin saro kaya ai a shagon yaro nane na fada mashi idan kinzo ya raga maki yadda kema zaki samu sai dai duk abinda zakiyi kada ki cika riba a kayan ki don riba bai da kyau kin sani.
Ya kawo wani dan karamin turare ya bani yace wanan kyautane na tafi umurah cikin satin na na dawo daga can.
Nai mai sallama nafito a daidai lokacin na falka daga barci sai dai idona a bude amma kamshin falon malam nakeji a falon namu a lokacin waras na bude idanuwa na still har lokacin kamshin bai bari ba.
Na dade a gurin ina kokarin tuna mafalkin da nayi da malam da iyalishi ina mamaki a raina kawai.
Yaron da zaikai min sako wanda Anty hauwa taiwa magana yazo ya karbi kayan za,a kawo kwantagora nabashi nomban wanda za,akaiwa kayan a gurin shi anty zata zo ta karba.
Har yara suka dawo daga school suka samay duk jikina kasalane ya damay ni ban iya yin komai ba a,wunin ranan kamar yadda na saba yi idan ina ni kadai.
Ummumm mama falon nan yau yana wani irin kamahin dadi inji Abba Aisha tace nima naji kamshi sosai wallahi mama.
Nace kai kun faye surutu bana hanaku idan kunji abu kuyi magana ba ashe.
Har kwana biyu falon mu yana kanshin irin ta falon malam duk wanda ta shigo sai yai maganan kamshin dadin da yaji.
Anty Lami da mukai waya take ce min Maryam.ina kika saro kaya haka masu kyau duk wanda yagani sai ya yaba kyawon kayan don kamar bana kasan nan bane wallahi.
Tace har an wawashe su ai don an taba kyaun kayan nan da sati biyu zan turo maki da kudin ki sai ki kara turo muna da wasu don akwai masu so sosai wallahi.
Naji wani irin dadi a raina nace a fili ALLAH na gode ma na goma Malam Baba hakika kai ubane na gari a gare ni.
Nakuma godewa wanan matar Allah daka hadani da ita mata mai karamci da mutunci ko ina zan kara ganin ta in mata godiya in kuma fada mata alherin da taimin tazama min wani babban baiwa.
Nace koda ban san inda zan ganki ba nagode ina maki fatan alheri a duk inda kike kema .
Sai naji kamar murmushi a bayana bandamu in waiga ba don nasan babu kowa a gurin shirmay ne kawai da zolayar kunne ke rudina.
Kamar yadda anty tace min bayan sati biyun takara ruro min da kudina tare da riba nakara zuwa wanan shagon na saro kayan na kara tura masu shi.
Washegari sai ga wayanta wai har kayan sun kare ko nace ikon Allah anty ashe abin zai karbu haka ne sosai.
Har lokacin baban Abba baida lokacin mu sai harkan gaban shi kawai yakeyi ba wani shakku a tare dashi.
Nima ban sakawa raina abinda yakeyi ba don bai rage mu da komai ba a gidan na bukatan mu.
Naga idan ma na saka a,raina,wahala kawai zanyi a raina nice da damuwa don shi ba abinda ya damay shi.
Ranan zanyi wanki sai na tuna da clean din da ke a cikin jakata nace bari na dauko shi nayi amfani dashi.
Sai dai babu komai a cikin jakan nawa sai wani kwalin turaren saudiya kawai nagani a ciki nai ta tunanen ko ina na samo shi amma na kasa tunawa.
Na mayar na aje ainda na ganshi da farko na bude wani clean naci gaba da aiki na dashi.
Ina wanki ne kyatan baba malam ya fado min a rai na turaren da ya bani a cikin mafalki.
Da sauri na koma dakin na ciro kwalin tabbas shine din bawai mantuwa nayi ba wanda aka bani a cikin mafalki din.
Mamaki ne ya kamani nace may hakan wai take nufi ne ana nufin daga cikin mafalki baba malam yabani kyauta kuma na ganshi a zahiri.
Gaskiya akwai magana indai bada aljannu nake hurda ba ban sani ba sai kuma wata zuciya take ce min kai haba kin fasan manyan malamai da rafanai suke hurda kamar waliyyai suke kila haka yasa yace idan kina son ganin shi ki saka a ranki zaki ganshi din.
Tunda malam baba yakai babban malami dubi fa yadda Allah yabashi bauwan tara yara yana koya masu kuma duk shi kadai ke basu wanan ilimin haka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:55 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BAMU KADAI BA NE A,,
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
1โฃ2โฃ
Alhamdullahi zance yanzu don sana,ata cikin wata biyu har ban san yadda zanyi musalin ci gaban da na samu ba akai.
Yanzu ya kai har kitchen equipment nake turawa gida duk a gurin wanan costumer din nawa nake sarin su.
Ya hadani da wani dan uwan shi yace ya dinga bani sarin kayan mata dogayen riguna masu kyau yakuma raga min naji yana cewa dashi kai mata sauki yar gidan malam SULAIMAN ne na tsibiri.
Sai lokacin na tuna da malam naji ina son ganin shi kodon alherin da nake samu a kan shi yanzu yaci naje na godewa malam hakana.
Sayayya nayi sosai na shirya sai gurin shiga mota ina rike da Nusaiba da yanzu tana tafiyanta da kafa tayi lafiya sosai ga,wani irin kiba da tayi kamar itace kadai ake kiwo a gidan.
Naje bus stop na tsaya sai ko ga mota yazo na shiga ban tsaya ko ina ba sai tsibiri.
Nashiga gurin matan nan