Showing 3001 words to 6000 words out of 115099 words
Chapter 2 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
baban Abba a waje inji malam hassan makwabcin mu ke nan.
Komawa nayi zuwa bakin gado inda yake a kwance na dan taba kafan shi kadan.
Abinda yasa shi bude idon shi ke nan yana kallo na a hankali cikin yanayin mai jin barci a lokacin.
Nace wai baba hassan ne yake maka sallama a waje yanzun ya aiko yaro daga wajen.
Dakyat ya bude idon shi tare da dan jan guntun tsoki yana fadin kai yanzun mutane bazasu bari mutum ya hutu ba wallahi gashi duk a gajiye nake .
Dogon rigan jallabiyan shi dake gefe ya zura yafi gurin mai sallaman makwabcin mu ne dattijon kirki yana kula mu sosai kuma ya daukan yarana kaman jiko kin shi.
Murnan motar da ya gani a kofan gidane yazo yi mashi inda yai mashi fatan alheri da fatan a gama da,karfe lafiya.
Nan sauran makwabta suka samay su ana ta taya shi murnan samun karuwan da yayi na sayan mota.
Sai zuwa rana da mutane suka rage ne ya samu ya shigo gida wanka yayi ya zo ya shirya ya zauna ya karya.
Anan ne yakewa Umma magana kan yana son kwashe iyalin shi ya tafi damu can gurin aikin shi.
Nayi zaton Umma zatai farin ciki da jin haka amma tace mai yanzu kai kaga ya dace ka kwashi iyalinka sunan cikin kwanciyan hankali ka tafi dasu garin da,baka da kowa a cikin shi.
Murmushi yayi yace umma ai da ita kaduna ainihin sunan ta ke nan garin masaukin bakine tan arewa garin kazo na zo.
Zakiga akasarin mazauna garin duk baki ne dako ina na nahiyar arewancin Nigeria dama sauran kasashen africa don gari ne da yaci sunan shi na bariki a cikin kasan nan yanzu dai abuja ce kawai zata nunawa yan kaduna wayewa kawai.
Umma tace bakaji ba bariki fakace garin shege da shigiya ke nan ina tarbiya a gurin nan.
Dariya umma tabashi yace umma ai idan tarbiya addini kike bukata to kije kaduna don acan addini ya yanke cibinsa sosai.
Ni dai yanzu kabari sai nayi shawara don gaskiya ni hankalina bai kwanta da ka kwashi yaran zuwa har wata kasa ba inda ba kusa da gida ba.
Yace tau Umma sai dai gaskiya ni nagaji da zama ni kadai a gida hakana ina bukatan zama da iyali a kusa da ni don na samu gida yanzun idan su bazasu tafi ba sai na samu wata yar can na aura ke nan.
Dif naji kamar ruwa ya cinye ni a lokacin wani irin sakaiyya Umma da dan ta zasu yi min haka a daidai lokacin da nake ganin riban hakkuri na yazo min a rayuwa.
Don yanzun alama ya nuna yaya yana a cikin budi da samu daga gurin aikin shi.
Haka ya mike yafita zuwa cikin gari don ya gaisa da yan uwa da abokan arziki na gari.
Nima mikewa nayi ba tare da nai magana ba na fice daga dakin umma tare da kayan da yaci abincin shi.
Umma tabi ni da kallon tausayi don ta san indai hakkuri ne na yi shi a gidan nan akan komai yanzun kuma gashi yazo da wani magana mai wuyan sha,ani.
Idan har da zasu tafi ne ya barta da yaran zasu dan debe mata kewa ai kila amma kuma yace zai kwashe su gaba daya har yaran gaskiya zaman kadaicin zai mata yawa sosai.
Tasaba da hayaniyan su a gida suna debe mata kewan shi yanzun kuma yace zai kwashe su har zuwa wani kasa mai nisa haka.
Nikan yinin ranan duk abinda nakeyi tunane ne yai min yawa kan yadda umma ke kokarin jawo min komawa baya a gidan.
Ke nan fa idan yai auren bariki ni sai dai naci gaba da zaman hakkuri agidan ke nan don nasan halin mijina akan mata hankalin shi gaba daya zai koma ga sabuwar marar shi ke nan ni sai yadda akayi damu kuma.
May zan gane nasan bani gane komai daga gare shi kuma gashi ina na da matular son ace na bishi inda yake aiki tun farko ban dai da yadda zan yine kawai na hakkura na zauna a gida.
Ina ganin yadda anty na suwaiba keyi idan tazo daga minna yan uwa naji kamar su lashe ta daga ita har diyan ta don dan hausan su daya banbanta da namu da kuma shigan su daban yake dana yaran mu damuma kan mu iyayyen yaran sai kaga ta fito daban a cikin mu.
Sallaman wasu makwatan mune da muke abin arziki dasu sunzo yi muna murna da arzikin sayen motan da sukaji yayi.
Daga ciki har da kawata Lariya da tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe amma ta iya tasowa zuwa ganin abin arzikin da ya samay mu.
Dakin Umma suka fara shiga sukai mata murna da fatan samun ci gaban da yafi wanan watarana.
Suka fito muka shiga dakina nan muka fara gaisawa dasu suna min murna da samun sabuwar kishiya a cewan su.
Suwaiba tace ai karfe kishiya ce don tafi kai matar gida cin abin hannun maigida sosai.
Lariya dai tana gefe sai murmushi kawai takeyi a zancen mu nan nake fada masu labarin da yazo muna dashi na son tafiya da mu.
Amma kuma ga cikas din da Umma take son ta kawo muna ga tafiyan.
Sai a lokacin ne Lariya tai magana tace kai haba ita ko umma idan tai maku haka batai maki adalci ba gaskiya.
Duk hakkurin da kikeyi kuma yanzun samu yazo zata tace haka ai wanan ba so bane ni yanzu fa ba aikin gwaunati yake zuwa yi ba amma da zai ce zai tafi damu lagos din da yake zuwa gurin cirani aida nabishi tuni wallahi.
Nan dai kowa ke fadin maganan shi suke cewa gaskiya kada na yarda da zancen umma na gwada mata ina son bin mijina kawai.
Lariya tace a,a ta kyaleta ai tasan abinda ya dace itama ai mace ce kamar mu tasan abinda ya dace da ita.
Yanzun idan ta nuna mata rashin kunya ba umma ba har shi dan nata zai iya canza mata zaman su ya lalace ai ba abinda ya gagari Allah.
Don haka kikai kukan ki ga Allah ya haushe ki akan umma da dan nata don tunda kikaji ya fara maganan aure killa ya shiryawa hakan ne kawai.
Maganan lariya yai matukar tasiri a zuciyana sosai don haka na hau kan shi na zauna akan zan kai kukana ga Allah yai min jagora ga al,amarin.
Sun dan dade muna hira dasu suka fito zasu tafi sukaiwa umma sallama na raka su ina cewa wai lariya anya wanan cikin naki abin baizo ba kuwa sukai dariya sukace gata nan dai wallahi.
Bayan tafiyan su lariyane nai alawala na shiga sallah tun a lokacin na fara sallah ina kai kuka na ga Allah kan al,amarin.
Shiko Aliyu sai harkokin gaban shi kawai yake yi ya murje yayi kyau sosai dashi sai annuri yakeyi kawai yana bushashan shi hankali a kwance .
Niko ina cikin matukar damuwa a lokacin don nasaka zancen tafiyan nan a raina sosai.
Kwanan shi biyu zai tafi yake cewa yana sauraren shawaran da Umma ta yanke don idan yai wani dawowa sai batun tafiya kawai da mu zai rage umma tace mai taji.
Mukai sallama dashi ya tafi yana cikin farin ciki da jin dadi gashi ya murje yayi kyau duk macen da ta ganshi dole ne ta kyasa a kan shi.
Don Aliyu ba dai kyau ba da iya shiga ga ilimin zamani da ya ke dashi kaman shi yasawa kan shi brain.
****** ********* ******
Tafiyan Aliyu washegari muka tashi da tashin hankali a unguwar mu don Lariya ce gurin haihuwa haihuwan yazo mata da matsala aka kwashe ta zuwa asibiti.
Nan mayan uguwa suka kwashi jiki zuwa asibiti don diba matsalan ta a can .
Sunyi dafifi a kofan dakin haihuwa Laure na zaune a saman wani gawo lokacin da likita yazo da kan shi zai shiga dakin haihuwan ne sai faman gaidashi mutane ke yi.
Har ya dan zauda inda suke a zaune sai yadawo gurin tsofin ya tsaya can yai dan murmushi ya kalli inda laure take a zaune yace.
Mama aida kin tashi saman wanan gawon naki ko zata samu ta haife abinda ke cikin ta kafin ku karasa ta.
Yai matukar girgiza duk wanda yake gurin a zaune yadda ya likitan banufe yai tsaye akan su laure da wata kawar ta da,ba,a san tana maita ba.
Shi bai wuce ba su kuma basu daga ba kamar yadda ya bukaci su daga a saman gawon da suke zaune akai.
Ganin zai iya tona masu asuri yasa laure ta dan zauda kadan ta tura gawon baya ya fadi kasa baya table din da suke zaune sama, yana ganin haka yai murmushi ya shiga dakin theater sai ko ga kukan jariri ya kauraye dakin a lokaci guda.
Ga murna ga kallon mamaki gaba daya mutane sai mamakin su laure sukeyi ga kuma murnan haihuwan Lariya da tayi.
Likita ya kalli Lariya dake cikin wahala a lokacin yaji matukar tausayin ta ya kamashi don yasan is too late don sun riga da sun gama da ita ko lokaci kawai ake jira gare ta.
Abin tausayi ga yan uwa da abokan arziki sai murna sukeyi na ta haihu lafiya a lokacin.
Yafito yana share hawayen da ya dan zubo mashi a lokacin sai faman gaida shi mutane ke yi suna mashi sannu da kokari.
Fitan shi daga dakin bai kokai office din shi ba sukaji an saka salati Lariya rai yayi halin shi lokaci yayi.
Muna gida zaune wannan bakin labarin na,rasuwan Lariya kawata ya samay mu.
Hankalina yai matukar tashi, ranan munga tashin hankali don haka a ka dauko gawan Lariya zuwa gida cikin tashin hankali kafin wani lokaci labarin abinda su laure sukai wa lariya yabi gari ko ga jariri ana mata wanka sai faman tsala ihu yakeyi a gidan hankalin kowa a tashe.
Muna ji muna gani aka tafi da lariya gidan ta na gaskiya akabar mu da yaron ta kowa yazo gaisuwa yaga yaron sai hankalin shi ya tashi aita kuka.
Haka aka wuni a cikin uguwan mu a cikin tashin hankali kowa sai tunanen yadda tashi zata kasance mai yakeyi.
Bamu ga tashin hankali ba sai da dare duk gidan dake makwabtaka da gidan su lariya irin namu sai da muka wayi gari da abin al,ajabi.
Har dani da Umma bata bari nabar koda kyalen mu a waje da tukwane duk dare sai na tattara kayan aikin mu nakai kitchen na boye.
Amma ranan a can na kwaso su kofan gida a,watse haka mutane akai ta kwasan kayan su ana kaiwa juji ana watsar wa.
Mutuwan sai ta girgiza mutane don yadda yazo da abubuwan al,ajabi wasu sukace ranan ma wa yan da ke cikin gidan sunfi shiga tashin hankali sosai.
Don ga jariri na ta tsala ihu ga iska ya cika gidan kamar guguwa zai daga masu kwanon dakin su dan katfin shi.
Sai da safe kowa ke fadin abinda yaji a dare jiya a gidan nan suka samu anfito masu dakayan gidan an kai waje cikin juji an tara masu tsibi guda.
Hankalina yai matukar tashi ranan sosai don abin da,bamu taba gani bane ko ji.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ
BA MU KADAI BANE A GIDAJEN MU
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
3โฃ
A kaita zancen Laure gari nan takoma abin tsoro ga manya da yara yan uwan ta da,suka zama dolen ta kawai ke hurda da ita ko su a cikin dari dari suke hurda da ita.
Mun kan a gidan mu Umma a tsaye take a kan mu ba Laure ba shigowa a gidan mun don yai mata nisa amma dai nikan duk da abinda Umma take kirarin tana yi darr nake da,al,amarin laure tunda ta lashe min kawata har abada ta tafi ta bar mu.
Muna waya da Baban Abba sosai don yana yawan kiran mu yaji lafiyan mu ko yaushe.
Nan nake bashi labarin rasuwan Lariya da kuma sanadin mutuwan nata da,akace shine sila.
Dariya yayi yace kai ku dai mata wallahi baku gajiya da shirmay wallahi ba,a mutuwan Allah sai kun canfawa mutum kun bata mai gawan shi.
Nace nima abinda naji ana fadi ke nan na fada maka amma gaskiya akwai kamshin gaskiya a zancen.
Yace adduan ku take bukata kawai yanzu ita nata ai yakare kuma tayi kyakyawan tafiya tafarki maikyau hanyan haihu.
Har mun gama,waya banji yai muna zancen tafiyan mu gurin shi ba ni kuma ina jin nauyi na fito mashi da zance daga bakina matan hausawa ke nan akan kunyan bin hakkin su.
A bangaren Umma ba,wani zance ita ma koda ma naji ta tayar da zancen daga bakin ta babu shi.
Dalilin dayasa na yanke shawaran naje gidan mu da zancen ke nan naji shawaran da za,a bamu.
Na shirya da yara na duka mukaiwa Umma sallama muka tafi tana cewa gaba daya zaku tafi ba wanda zai zauna dani a gida.
Nace a raina ashe akwai aiki ke nan kuwa don umma da,wuya tabar mu da zancen tafiyan nan tamu.
Ko da yake ba komai take wa haka ba sai shakuwan da mukayi da itane kawai yake damun ta a zuciyar ta.
Mun fita ke nan daga gida sai ko mukai kicibis da Laure nikan banji kunya jaye yara a gefe ba muka wuce ta don Ance maye ko da ido yana daukan kurwa in yaso.
Bin mu tayi da kallo nace a raina kurwan mu kur muguwa li,ilafi kureshin .
A zaure muka samu mahaifina yana tila karatu kamar yadda ko yaushe mutum.yaje zai samay shi yanayi.
Ko kuma ka samay shi da jama,a masu zuwa gurin shi tambaya abubuwan rayuwa.
Yana ganin mu ya sake muna murmushi yana cewa ai mutanen Alangasa ne yau a gidan namu haka.
Nan muka zube muna mika gaisuwan mu a gare shi yake tambayan mu Umma nace tana nan lafiya kalau.
Yake cewa yaya shi wajen maigidan naki kuna jin labatin shi ko ?
Nace cikin kunya lafiya yake baba yace ai kwanaki yazo yake ce min yana son ya koma da ku can wajen shi.
Nace hakane Baba yace amma sai dai umma ce bata yarda ba da zancen har ya tafi ba tsayar da matsaya ba kan zancen.
Yace subbahanallahi ita kuma Ige mai yakaita wanan halin yau ba dadin ta bane ace ya kwashe ku inda yake ai shine kamalan shi da ita ma.
Yau har Allah yasa da kan shi yai magana zai tafi daku amma har zata kawo cikas ga maganan.
Kai mata dai mata ne wallahi bata gudun fadawan shi a cikin halaka da kamuwa da cututunkan zamani da sukai yawa.
Idan tai maku haka bata kyauta ba daga ke har maigidan naki zata shiga hakkin ku ne sosai.
Baba yake cewa Abba abokina ga shi kayi sa,a andama hura yanzu sai ka dauka kaje kusha ko.
Nace Baba kaifa idan suka shaye maka yace ai arzikin ke nan maryam mu godewa Allah da yasa har suka san mu yau ina Amina take cewa mahaifiyana nace hakane Baba yace su sha sai a sayo min wani a dama min.
Na mike ina cewa bari mu shiga gida na gaida su umma kasancewa mahaifiyan mu mu ta dade da rasuwa a gurin kishiyoyin ta muka tashi kuma sun muna riko mai kyau baka cewa basu ne suka haife mu ba.
Ga idona ya ciko da hawaye a lokacin fon tina min da mahaifita da Baba yai min a lokacin.
Don mu shidda ne mahaiyar mu tabari nice babba a dakin mu saran duk kanne na ne su mu mata mu biyu ne sauran duk maza ne su.
A yadda muka ji wai iskokaine suka saka mahaiyar mu a gaba wanda suka hanata lafiya har rai yai halin shi.
Ina shiga na samu amaryam baban mu tana daka wa je tsakar gida tana ganin mu take cewa a,a yau mutanen Alangasa ne a gidan namu.
Nai murmushi na shiga gaida ita nake gaisawa da yan uwa na yan mata dake zaune a tsakar gida suna cin tuwo a lokacin.
Dakin Inna muka wuce don an ce muna tana ciki muna shiga na samu yayata tazo diyar mama da tayar dani nan muka baje muka shiga gaisawa dasu nakawo dan tsaraban da na kawo masu na basu tashiga saka min albarka da fatan gamawa da duniya lafiya.
Ban dade da shiga ba itama Amaryan baban mu da muke kira innan sahura tashigo dakin gurin mu tana cewa.
Dada maryam sai mukaji labarin rasuwar kawar ki boyan Allah ashe haka abin yazo mata da akasi nace wallahi innan sahura.
Lariya boyan Allah ta tafi ta barmu anty lami dake zaune tace ba ance mayune wai makwaciyar ku suka kashe ta ba nace haka ake fadi wallahi anty aida kafin ita da dani tafara sharewa.