Showing 42001 words to 45000 words out of 115099 words

Chapter 15 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6661

gama waya nake mashi magana akan tafiyan mu gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Nan yake fada dani wai ahi fa na matsa mai bayan ya fada min baida shiri akan tafiyan don haka idan zamuyi hakkuri har ya samu kudi wani karon mutafi muyi.
Nace haba baban Abba bayan kowa yasan cewa zamu shigo yanzun kuma nace masu na fasa tafiya gashi a nan duk munyi sallama da mutanen arzikina cewa zan tafi gida.
Yace to idan ke kin shirya ne sai ku tafi goben nace idan ka amince insha Allahu gobe tafiya ba fashi a gare mu da yardan Allah kuwa.
Na fice a dakin raina a bace watau dan kudin da zamuyi tafiya dashi na fahinci sune ya kashe wa hana din.
Gurin al, amarin mutuwan mahaifin ta shine yanzu yake min wani kamay kamay can dashi.
Ranan falo nai kwanciya na a kasa tare da yarana duk da tsoron falon da nakeji banji tsoro ba a raina don bacin rai da nake ciki.
Tun karfe hudu na tashi na hau shiri munyi wanka mun shirya ni da yara komai na adanashi wanda zai lalace na saka a fridge ko.
Bakwai mun shirya na samay shi daki nace mun shirya ko yace ke nan tafiyan zakuyi ba zaki tsaya kigani ko zan samu kudin ba ko?
Nace idan ka samu sai ka aiko muna dashi nikan zan tafi gida naga mahaifina yau ba fashi insha Allahu.
Ya mike yana cika yana batsewa ya saka rigan shi yace muje ya sauke mu a tasha ni da yaran.
Haka muka fito makwabta duk sunzo ganin tashin mu suna min adawo lafiya suna gaida mai jiki nace nagode muka kama hanya sai tasha ba wanda yaiwa wani magana a cikin mu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง


BAMU KADAI BANE, , , , ,


๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ


1โƒฃ5โƒฃ


Tafiya mukeyi muna ta bugun daji inda driver ke ta faman sharara gudu da mu a hanya muna cikin mota zaune hankalin mu a kwance sai faman tunane nakeyi a raina.
Babu aabinda na fara tunawa sai irin halin da zan zamu mahaifina a cikin sa indan muka isa gida.
Sai kuma tunanen yadda zamu samu Umma idan mun isa gashi baban Abba yana ta jaddada min cewa na tabbatar da cewa gida gurin Umma muka sauka idan mun tafi.
Sai kuma daga karshe na fada cikin tunanen sabon bakon, yanayin da na tsinci kaina a cikin shi na hurda bakin fuskan dake zo min da tsigar mutanen boye.
Tambayan kaina nayi shin mafalkina da mukkadarasiyyatu gaskiya ne koko just mafalkine irin wanda kowa ya saba yi as mafalki ya wuce.
Abu biyu ya tsaya min araina shine zancen maganin da baba malam yabata tabani sai kuma kayan tsaraban da tace zangani nakai wa anty lami da babana.
Yanzun ai ta haka zan gane idan mafalkina gaskiya ne don na kudiri aniyan zan ba babana wanan maganin na gwada na gani idan, zai yi aiki a kan shi.
Zancen tsaraban da ni dai banga komai ba kamar yadda tace har na gama shirya kayana na wuto ba wani alaman sakon da nagani.
Bamu isa gida ba sai ana sallah magariba muka sauka garin mu lokacin mutanen unguwan mu sun shiga sallah magariba.
Umma ma mun samay ta daki ta tana sallah don bata san da zuwan mu ba a ranan.
Nan aka shiga shigo muna da kayan mu manyan jakkuna ghana most go da sauran tarkacen kayan mu har jakka biyar da sauran abubuwan da nazo dasu don tsaraba dan amfanin mu nan gida.
Jin hayaniyar mutane yasa Umma ra sallamay sallah ta fito tagan mu muna shigowa driver da ya kawo mu dan kwantagora don daukan motar mukayi dagani sai yara har gida ya kawo mu mukai sallama ya juya abin shi ya tafi.
Nan umma ta shiga yi muna sannu da zuwa ta shiga dakin ta ta dauko key din dakina muka bude aka loda muna kayan mu cikin dakin.
Fada takeyi yanzu ashe kuna hanya ban sani ba balle ai maku dan abinda zakuci gashi dare yayi yanzu ina zan samo abinda zakuci.
Nace ba komai Umma akwai miya da mukazo dashi zasu ci bread dashi zai ishe su ai.
Umma kan sai murnan ganin yan jikokin ta takeyi don gaba daya taga sun girma sun yi kyau dasu sosai.
Sai da nai sallah na fito zuwa gurin Umma muka gaisa da ita tare da yaya bayan rabo.
Badai yabo ba fallasa a yadda naga fuskan Umma din da akwai wani manufa dauke a fuskan ta.
Tambaya ta jefo min cewa halan kun samu labarin rashin lafiyan malam ko ?
Nace eh an fada min wallahi Umma hankalina bai kwanta ba yadda nake jin labarin ciwon shi yasa na matsa muzo mu gane shi yafi.
Tace yanzu maryam dake da babana yadda kuka tafi kukai watsi damu haka kusan shekara biyu ake nema fa baku leko gida ba.
Shi shiru ke shiru haka yayi daidai ke nan irin wanan abin nake gudun faruwan shi tun da farko yasa na hana tafiyan naku.
Shiru nayi tana ta fada a yadda na fahinci fadan Umma laifina kawai take gani bana Baban Abba dan ta.
Na dai ce ayi hakkuri umma abubuwan ne sai a hankali wallahi amma yadda kike tunane ba hakana bane.
Yanzu ai dadade baiji baigani sai ke ke bidirin ki kawai da yan uwan ki komai nashi ya koma hannuki sai yadda kikayi dashi maryama.
Maryam ki tuna fa ke ma watarana uwace kamar ni baku gudun alhakina ya kama ku ne wai ?
Ace ina da da kamar babana amma abin duniya yana batun gagarana sai na je nema a makwabta.
Duk wanda na fadawa cewa yaron nan bai min sakon komai yanzu ba yarda da zance na za, ayi ba .
Sai aga kawai banda hakkurin ne na yana bani ban godiya ne kawai don na bata mashi suna.
Nace Umma kiyi hakkuri kona fada maki ba yarda zakiyi ba amma yanzu baban Abba al, amarin shi sai hakkuri kawai.
Haka zaki ce ai tunda ke ya rike maki kan maciji kina wasa da bindin sa badole ki fadi hakan ba tunda yana maki yadda kike so ke da yan uwan ki.
Ku daiyi hankali da alhakina wallahi don idan ya tashi kama ku ban san yadda zakuyi ba da rayuwan ku don kuma kun haifa ba baki nake maku ba ni gaskiya nake fada maku.
Yanzu dubi irin wanan shirgin kayan da kuka lodo saboda Allah amma ni dan abinda zaku tsakura ku turo min ya gagare ku.
Na dai gane Umma tana ganin duk abindake gare ni na mijina ne wanda ita batasan cewa babu ko kwandalan shi ba a cikin bida na ba.
Ban iya kwana ba nace zan tafi na duba jikin babana don ance kwanan nan jikin nashi sai a hankali sosai.
Umma tace na bari da safe na tafi mana nace Umma bari dai tunda nashigo nadan je naga halin da yake ciki tukun.
Ko Nusaiba ban dauka ba sai handbag dina na saka hijjab dina na fita na samu mashin na hau zuwa gidan mu.
Nan na samu dukka yan uwana suna gidan don jikin baba na ya tsanan ta sosai kwana biyun nan.
Yana cikin turakan shi sai nishi da kugi yake na ciwo na shigo da sallama na duk suka juyo suna fadin a, a maryam ashe kuna hanya tafe?
Na kutsa kai dakin tare da basu amsa da eh yanzun muka sauka wallahi shine nayo nan don hankalina yana ga baba wallahi.
Nan dai muka gaisa dasu tsatsaye na karasa har gaban baba inda yake kwamce ya dunkule sai nishi yakeyi.
Nace sannu baba yaya jikin naka baba yaya ka kara ji kuma da jikin ?
Ya bude udon shi da kyat ya dan dago kan shi yana kallona yace cikin halin ciwo maryama kin zone ?
Nace eh baba sannu yaya jikin naka ka kara
Ji kuma da sauki dai ko yace Alhamdullahi maryama da sauki kun shigo yaya maigidan naki da yara suna lafiya ko ?
Nakai zaune jiki na duk yayi sanyi nake cewa duk suna lafiya baba da yaran ne ma muka zo nan ai sai dai suna gida na barsu a gurin umma ne.
Nan dai kuma bai samu cewa komai ba ciwon ya taso ya dunkule guri daya yana nishi a cikin kugi kamar wani karamin yaro don wahala.
Hakan yasa nasan cewa ba karamin jin jiki baba yakeyi ba sosai saboda yadda na san shi da karfin hali a baya.
Duk na rude su dai sauran yan uwana sun saba ganin wanan halin da yake ciki sai sannu kawai suke mashi .
Tsananin rudewan da nayi yasa na manta da zancen wani maganin da nazo dashi daga gurin baba malam.
Sai da naji ana zancen wai an karbo magani a wani kauye a jika mai yasha ne abin ya fado min a rai.
Naji mama tace aiko dazun an jika mai yasha amma kamar bai sha ba wallahi sai dai idan za, a kara jika mai ne yasha din kawai.
Nan dai na yanke shawaran gabatar da wanda nazo dashi a gwada a gani ko Allah zai sa a dace.
Nace cikin sanyin murya mama akwai wani magani da wani babban malami can da ya dauke ni a matsayin diya ya bani na kawo wa baba ai amfani dashi.
Shiru naji sunyi ba wanda yai magana sai babban yayan mu ne yace to kawo a gwada bashi a gani nace amma yace idan za ai amfani dashi sai anyi alwala tukun za, a bashi dashi da wanda zai bashi din.
Sai maman Aina tace ai yiwa malam alwala a wanan halin da yake ciki haka ?
Yayan mu yace bari a gwada mai mana sai nima nayi na bashi mugani ko Allah zai sa a dace haka yadda suka ce din akayi akaiwa baba alwala tare da kma yayan mu yayi mai duk yadda nace ance ayi da maganin.
Muna tsaye gefe daya muna kallon yadda baban mu yake wahala bamu da yadda zamuyi gashi ya hana akaishi asibiti wai yafi son ya cika a dakin shi idan ma mutuwa zaiyi yayi a dakin shi kawai yafi mai.
Kamar minti goma da shan maganin sai ga zufa ya fara karyo mashi yana furta Alhamdullahi da bakin shi yace ya ji jikin ya fada mashi sosai.
Bai kara wasu mintina ba sai barci ya dauke shi mai nauyi haka yasa muka watse a dakin don mu barshi ya huta ya samu barci a lokacin.
Ganin dare ya soma nace zan tafi gida sai dai da safe idan Allah ya kai mu zamu shigo muka watse muna mai Allah ya nashi lafiya.
Koda na fito lokacin dare ya soma yi sosai har yan mashin sun dan rage a titi don haka mun jima gurin bamu samu abin hawa ba.
Sai can wani mai mashin yazo muka tsayar dashi na hau mukai sallama da yan uwa na don su da kafa zasu karasa gidan su don basu da nisa sosai da gidan.
Mun dayi nisa da gida naji mai mashin din yace yaya jikin baban naki da sauki dai ko ?
Cikin rashin damuwa nacd mai Alhamdullahi ya samu sauki sosai a zatona ko yasan ni ne nine dai bangane shi ba.
Mun dan kusa da gida naji ya sake cewa ki fada mai ya daina fitowa zuwa ban daki da karfe biyu ya dinga barin sai zuwa uku da rabi ko hudu zaifi sauki da kariya.
Nace kana gani fitan dare ne yajawo mashi matsala haka ko may yasa yake wahalan nan.
Bai bani amsa ba muka iso kofan gidan namu don haka na sauka ban tsaya ba bita kanshi na ciro kudi na bashi amma yace na barshi kawai yaja mashin din shi ya tafi sai lokaxin na tuna bai bani amsa ba ya tafi.
Dakin Umma na kwana ranan don dakina ba gyara ba zai kwantu ba a ciki hakana don haka muka kwana a dakin ta kawai
****** ********* ******
Washegari tunda safe na shirya sai gidan mu duk sakkon da nayi na samu yan uwana a gidan baba yana zaune a waje tsakar gida an mashi shimfida ya zauna ga kunu a gaban shi yana sha.
Yana ganina yace maryama ashe kunzo ne sannun ku da zuwa yaya hanya yaya bayan rabo ?
Nace Alhamdullahi baba yace ance kece kika kawo min magani daren jiya na sha na samu sauki haka ko ?
Kenan ana nufin duk maganan da mukayi daren jiya babana bai cikin hayacin shi ke nan komay ?
Nan dai muka dan shiga hira sama sama dashi duk da har yanzu yana jin zafin jikin nashi.
Nace baba malam yace na gaishe ka da jiki sosai ko da zan wuto ban samu ganin shi ba yana wani aiki shiyasa ma bamu tattauna ba dashi sosai akan ciwon ka dashi ba.
Yace maryama da alama dai kina ji da wanan baba malam din naki sosai gashi kuma da gani malami ne da yasan kan shi sosai.
Don wanan maganin da ya bani akwai kyau sosai wallahi don ban taba shan maganin da naji dadin shi irin wanan ba tunda na fara ciwon nan.
Gashi yau na samu barci sosai har sai da aka tayar dani sallah asuba.
Cikin jin dadi nace ai baba baba malam dattijon kirki ne sosai wallahi mutum ne mai mutunci da son jama, a wallahi ya dauke ni tankar yar shi daya haifa na cikin shi.
Sai dai kuma ina matukar mamaki yadda akayi yasan mama da ta rasu sosai har yace ne maka gaisuwan rasuwan ta.
Da mamaki baba yace min yasan Amina fa kikace mutumin ?
Nace cikin rashin damuwa kwarai kuwa baba yasanta sosai harda matsalan da ya samay ta sai da ya dan labarta min .
Baba yace ikon Allah a can kasan aka samu mutumin da yasan Amina wacce duk rayuwan ta anan tayi shi bata san kowa ba, a can .
Nace wallahi fa baba nima nai mamaki sanin hakan da yayi amma danaga babban malami ne shi sai ban kawo komai ba a raina.
Baba yace Allah ya kyauta to nace Amin baba sannu da jiki yace yauwa sanu maryama Allah yai maku albarka na amsa da Amin baba.
Sannu a hankali akaci gaba dayiwa babana maganin da na kawo mai shikuma Allah yana kara bashi lafiya sosai idan ka ganshi kasan yanzu ya samu sauki sosai a jikin shi.


Ranan da hanna ta dawo kd daga makokin mahaifin ta tace tunda bani gari a gidan mu zata kwana don dakin ta ba gyara sai washe gari zata tafi ta gyara dakin ts da gidan da take ciki.
Komai ya sayo masu na bukata wanda zasuci da wanda zasuyi amfani dashi da safe idan gari ya waye.
Karfe takwasa suka shiga gidan don lokacin kowa yana cikin gidan shi ba ganin su za, ayi ba.
Sunci sunsha suka yi wanka nan suka baje abinsu a falo suna kallo suna batun fara aikata masha , ansu.
Daga bayan shi yaji kamar an kwashe shi da wani irin mari a bayan shi sai da ya gigice don zafi ya rike kumcin sa da sauri.
Waige waige ya fara yi ko zaiga abinda yai mai wanan dukan haka da ba, a taba yi mai irin shi ba a rayuwan shi.
Da sauri ya ja baya ya fada saman kujeran da yake zaune akai dafe da gefen fuskan shi.
Take yaji jikin shi ba wani lakka a tare dashi sai wani bishi bishi yake gani a idanuwan shi na ya zube ya somay mata a falon.
Hankalin Hanna yai matukar tashi ta mike da sauri ta debo ruwa ta zuba mashi amma bai farfado ba lokacin.
Hankalin ta yai matukar tashi gashi daga shi sai ita a gidan ba kowa kowa yana cikin gidan shi gudu taso tayi amma sai kofan yaki budewa kuma.
Gurin shi ta koma yana kwance a somay ta fara kiran sunan shi cikin tashin hankali amma shiru kake ji ba magana.
Bulala taji an fara zana mata ana fadin gobe ki dawo gidan matan aure da niyar yin fatsikanci zaki kara fada sai da ta linkidu sosai ko ina jikin ta sai da shatin bulala yafito mata.
Tana tsala wani irin ihu da karfin Allah amma babu maijinta don an toshe kunnuwan kowa da zai iya jiwo ihunta lokacin.
Wani abu tagani mai wani irin tsawo ga hakora manya jikin shi da fuskan shi da jikin shi nan ta fadi ta somay itama.
Bata falka ba sai asuba sanyi asuba yasa suka farfado duk kan su babu mai iya taimakawa wani a cikin su don kowan su ya gala baita.
Da kyat ya iya mikewa ya nufi inda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login