Showing 78001 words to 81000 words out of 115099 words

Chapter 27 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6652

mamaki sosai ashe maman Abba tana fama da jinnu ne haka masu karfi ban sani ba?
Jinnu kuma yaushe ta samay su haka nan dai ta shiga bata labarin abinda ya faru a gidan mutane damu.
Sai da anty hauwa ta kewaya don tsoro da fargaban da ya kamata a lokaci daya.
Nan dai suka shiga magana akai har yamma yai masu bayan magariba suka shigo gidan namu.
Ina ganin su tare nasan takai gulma ko sun zo su tabbatar da zancen ta.
Zaune nake a kasan ties gurin kafan umma muna kallo suka shigo gidan.
Mun gaisa muyi komai take tambayana yaya jikin nawa nace masu da sauki.
Ban yarda munyi zancen komai dasu ba akan zancen don nasan shine ya kawo su gidan.
Har suka gaji suna cewa su zasu tafi don dare ya somayi a lokacin nai masu sai da safe suka fice.
Ashe suns fita sukaga wata katuwar mage bakakirin da its ta kura masu ido.
Da sauri suka wuce ta a razane sai suka ga kamar magen tana bin su a bayan su aiko binsu take cikin tashin hankali suka ruga aguje kowa ta shige gidan ta hankali a tashe.
A cikin wanan daren ne shima baban Abba yai mafalkin ana mashi kashedin idan ya fara ya mayar damu gida zai hadu da tashin hankali a rayuwan shi da dama .
Yana falkawa ne kawai yaji yana ta wani irin sufa wanda kamar ba sanyi akeyi ba a lokacin.
Hankalin shi yai matukar tashi a lokaci daya yake sharan zufa tare da sauke ajiyan zuciya.
Falkawa nayi nagan shi a zaune yayi tagumi kawai yana faman tunane nima hankali a tashe na mike zaune ina tambayan shi ko may ke faruwa kuma ?
Nake cewa akan wanan zancen ne ko nima baban Abba abin ya fara damuna inaji wa kaina tsoron kada na jawo maka matsala a garin mutane .
Komawa na gida naga kamar shine abinda ya dace dani da yaran nan don gudun abinda kaje yadawo muna nan gaba.
Baiyi magana ba har lokacin da nai shiru yake ce min debo min ruwa nasha.
Namike zuwa falon don na dauko mai ruwan yasha kamar yadda ya bukata, abinda idona yaganan min a falon namu ne ya tayar min da hankalina.
Yara ne a zaune suna cin abinci wasu kuma suna kallon Tv wasu na karatu kai su nan dai birjit dasu kowa da abinda yakeyi.
Hakana na ratsa a tsakiyan su ba wanda ya kulani a cikin su har na bude fridge na dauko ruwa da nufin nakai mashi.
Sai naji wata murya na fadin kai maman su Abba din nan yanzun ma dan ruwan da zan sha idan nagama cin abinci shine kuma zata dauka ta tafi dashi.
Wata kyakyawan mace ce tafito daga kitchen hannunta dauke da wani plate mai kyau dashi taci kwalliya sosai tana cewa.
Kai Afir idan na sake jin kana wa babba rashin kunya sai na nayi
maganin ka a gidan nan.
Mayar da ruwan nayi na aje ina cewa yi hakkuri ban san ai naka bane .
Ina fadin haka na juya zuwa gurin fanfo na debi ruwa nakai mai yadan kurba yadago kai ya kalle ni yana cewa babu mai sanyi ne zafi nake ji sosai.
Nace kasha wanan kawai falon baida dadin zuwa yanzu yace kamar yaya ya mike zai fita daga dakin nai saurin rike shi ina cewa kada kafita baban Abba bamu kadai bane a gidan nan.
Masu gidan suna falo suna hutawa a yanzu da sauri yadawo ya zauna yana kallo na acikin mamaki.
Bamu kadai bane agidan kamar yaya na bude baki da zuman nai magana amma kuma na kasa yin hakan.
Sai wani irin zazzabi mai radadi yazo ya rufe ni a lokaci daya haka na shige a cikin bargo ina rawan sanyi dani.
A haka na kwana har gari yawaye gashi yana son fita amma kuma yana tsoron kalamina danai mashi na bamu kadai bane a gidan.
Kalamin yai matukar firgita shi sosai hankalin shi yai matukar tashi dole da safe yakaini asibiti aka dubani.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU[11/15, 11:15 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง




BAMU KADAI BA NE A, , , ,




๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
2โƒฃ5โƒฃ




Sosai naji jiki ranan don na saka abin da nagani araina don ba wai a mafalkine naga wanan abin ba.
Bayan mun dawo daga asibiti ne barci ya dauke ni misalin daya na rana nai mafalki da matar da nagani a mafalki tare da yaran nan a falo.
Ta shigo dakina inda nake kwance mu ka gaisa da ita take ce min yaya jiki na dan yunkura na amsa mata da sauki.
Tace kiyi hakkuri yar uwa ban san zaki fito ba a wanan lokacin dana boye mu daga ganin ki.
Kin san halin yaran yanzu bajin magana sukeyi ba gashi kuma dare ku shine rana a gurin mu.
Likacin da kuka kwanta kuke hutawa muma a lokacin muke samu muna rayuwan mu yadda ya dace.
Fitan dare idan ba dole ba bai da amfani ga dan adam don gudun yin gamo da ire, iren mu jinnu.
Yanzu ki karbi wanan ruwan kisha insha Allahu idanbkin tashi zaki daina jin komai akan mu.
Daga yau kuma daga ke har duk wani wanda ke gidan nan bazaku kara ganin mu ba har sai idan kece kikaso ganin mu da kanki.
Godiya nai mata na karbi ruwan nasha nashafa a fuskana kamar yadda tabukata nayi.
Ta mike tabar dakin tana min Allah ya sauwaka tafice daga dakin a lokacin na falka daga barci nima.
Fuskana da na shafe da ruwa naji alaman shi a fuskana na shafa naga kamar ba zufa bane nayi nan dai na dade a kwance sannu a hankali naji jikina yana sake min.
Idanuwa na na lumshe a hankali ina tuna mafalkin da nayi nace a raina nikan maryam nawa kaddaran ke nan kuma hurda da mutanen boye a muraran haka.
Nai adduan neman tsari ga Ubangijina na mike zaune falo nafito na samu su Umma zaune da Nusaiba suna kallo
Na samu guri na zauna Umma tana min sannu yaya jikin nace da sauki tace min abinci fa nace na koshi Umma.
Maryam tun safe fa bakici komai ba ki daure ki dan ci wani abu mana ko ?
Nace umma tea zan sha maimakon namike na hada tea din sai ma nakai kwance kawai a gurin.
Ina bin komai na falon da kallo yadda nagan su a daren jiya ne ya fado min araina komai ma yanzu na gidan tsoro yake bani.
Tunda nasan bamu kadai bane mallakin komai da muke dashi agidan ashe muna sharing ne tare da wayanda bamu gani.
Nace kuka ganin mu bamu ganin ku don Allah kuyi muna adalci akan zaman mu yan uwa musulmai.
Umma take tambayana dawa kike magana nace ba kowa Umma ido ta tsura min tana zargina.
Gani take kamar mutanen nawane zasu taso min sai cewa tayi dauko hantitin ki kusa maryam.
Nace babu komai Umma magana kawai nakeyi amma lafiyata kalau.
Gaba dayan mu yanzu munyi farin ciki da samun natsuwan baban su Abba yanzu a gida.
Don idan bai gurin aiki yana gida tare da mu cikin kulawan da ya dace duk magidanci yaba ma iyalinshi.
Haka yasa hankalin Hanna ya kara tashi gashi yanzu sai ta kira wayan shi fiye da sau goma bai daga wayan ta.
Ni dai zan iyacewa tun lokacin da na fara amfani da abinda matar baba na tsibiri tabani yake min wanan irin likewan idan nabi ta nashi koda rana ma zamu kasance a tare dashi.
Ya soma mantawa da zancen wata hanna can idan ba itace takira wayan shi ba.
Koda takira din bai dagawa sai dai yaja tsuki kawai yabar wayan har ya katse.
Idan ma ya dauka ba wani magana mai dadi da zataji daga gare shi karshe ce mata yayi please hanna live me alone for god sake is over now between me and you.
Wanan kalamin ne yai matukar tayar mata da hankalinta sosai take gani idan ta rabu dashi wazata samu da zai kashe mata kudi kamar shi haka.
Ta samu mahaifiyar ta da zancen uwar taita mata fada tana cewa duk yadda zatayi ta gyara tsakanin shi da ita tayi kokarin gyarawa gashi har sun fara shiga wani halin dan rasa shi sa da suka yi kwana biyu a tare da su.
Hanna a cikin damuwa take sosai ta tafi gidan wata yar garin su dake zaune a kaduna ta fada mata halin da take ciki yanzu.
Matar ta girmay ma hanna sosai ga shekaru take cewa ke dama baki shiryawa shiga bariki ba kika shigo ta hanna ?
Kina da kaman wanan guy din zaki bari har ya kufce a hannun ki yaushe zaki kara samun kamarsa kuma.
Nan dai take fada mata akwai gurin wa ni boka da zata kaita aikin shi kamar yanka yake da sun tafi komai zai koma daidai gareta.
Hanna taji dadi sosai sai dai kuma can take cewa gaskiya anty akwai dan matsala sosai wallahi.
Namau kuma hana ?
Matar ta tambaya cikin son jin ina matsalar take kuma ?
Hanna tace wallahi anty matar Aliyu muguwace matsafiyace ta gaske don yanzu haka ma idan nace maki tasan wanan maganan da mukeyi baza, ayi mussu ba.
Dariya sosai mata mai suna Rabeca tayi tace amma har kin bani kunya hanna yaushe zaki tsaya wani tsoron matar shi kuma ?
Ai kawai fito nafito zamuyi da ita komai tsafin ta bata kai wanan gurin da nake shirin kaiki ba ke dai kawai kisa ido ki gani yadda za, ayi da ga ita har mijin nata.
Nan dai suka aje magana washe gari zasu tafi gurin bokan nasu a can wani kauye a yankin jos.
Tunda safe suka shirya don su samu suje su dawo a ranan suka kama hanya.
A gaban boka bai bari sun fadi abinda ya kawo su ba shi da kan shi ya labarta masu komai dake gudana tace mai hakane.
Yan abubuwan su na bokaye yayi suna kallon shi daga shi sai dan bante a jikin shi.
Yadago kai da sauri bayan ya watsa wasu farin kudi a kasa ya fara dan girgiza kan shi kadan kadan.
Can ya dago da idanuwan shi da sukayi ja yana kallon su.
Yace da zakubi shawarana sai nace ku rabu da mijin matan nan gaba daya duk son da kukemai.
Don wanan matar banga kurwanta ba a nan shi dai mijin gashi nan amma kinga matar ba, a ganin ta.
Akwai wasu abu da suka tare ta wanda basu bari ma aganta balle ai mata wani aiki.
Matar tace boka a daiyi kokari a duba muna don idan ba, a kawar da ita ba ko munyi aiki a kan shi matar zata iya bata muna komai da mukayi.
Nan dai take kara mai bayani akan maryam yadda zai fahinta yace ba sai kin fada min ba ai duk wanda na duba banga shi ba acikin nan nasan akwai matsala sosai ga mai shi.
Sun matsa mai akan yai masu aiki akan maryam da mijin ta ba don yaso ba sai kwadayin kudin da sukace zasu zube mai yasa ya yarda zai masu aiki din.
Sunyi dashi kwana biyu zasu dawo karban aikin da yayi masu sukai mai sallama tare da bashi na cin goro.
Sun kamo hanya suka dawo gida cikin farin ciki da ganin nasara atare da aikin da za, ai masu.

****** ********* ******
Yanzu ban son fita ko ina haka ma baban Abba ya hanani fita zuwa ko ina don gudun kada na fita abubuwan kaina su tashi.
Tunda idan na gani sai na fada yar sokoto sun shiga gulma a easthe din mu a kaina.
Har magana ya dan fara dawowa a kunne na na lura dasu yanzu mun rage hurda da shakuwan da mukeyi a tsakanin mu dasu abaya.
Ban damu ba dama can sune masu biyo ni ai banice mai binsu ba duk da dai sun girmay ni sosai.
Maganan su bai sa sauran mutane sun yarda ba don haka suka koma jin kunya kuma don kansu ban san may suka gani ba suka dawo min kuma.
Ban yarda na sake jiki dasu ba kuma don ban son yawan surutun da sukeyi.
Duk yadda suka so mu fita tare bana yarda na fita dasu in ma har fitan ya kamani.
Hanna ta koma ta karbo sakon ta gurin boka yadda yai mata bayani akan ta tunkare ni yasa ta shirya sai gidan mu.
Muna zaune a falo gaba dayan mu ranan ba aiki duk muna gida har shi maigidan.
Jin an yi nocking din kofa yasa muka mayar da hankalin mu a kofan muna kallo shine ya mike zai fita ya duba nace zauna kaci abincin ka na duba nagani.
Na nufi kofan na bude tana tsaye sai yatsunar fuska takeyi tana cewa munzo zamu duba jikin mummy ne.
Har zata kada kafanta a cikin gidan cikin wani irin murya nake cewa dakata anan.
Kamar an daureta taja ta tsaya take yanayi ya sauya na nunata da yatsa ina cewa ki koma da abinda kika dauko ki fadawa bokanki daga kaina bazai sakewa wani sheri ba a duniya.
Na nunata da yatsa nace ke kuma kinyi ganganci zuwa muna gida da kikayi da mugun abu ku tafi can kaikayi ya koma kan mashekiyar ta.
Naja kofa na rufe na barsu nan tsaye a waje cikun mamakina mikewa yayi ya nufo inda nake cikin wata irin murya nake cewa kada ka tako gurin nan yanzu daidai inda ta taka na duka kamar mai cire wani abu sai ga hayaki na tashi a daidai gurin.
Wani irin atishawa ne yazo min nan na mike kwance yazo da sauri ya kamani.
Umma hankalinta yai matukar tashi take tambayan ko su waye suka zo muna da sheri haka har gida?
Yarasa may zai ce mata sai kamani da yayi zuwa kan kujera ya kwantar dani da sauri ta koma daki ya dauko hantitina ya na shaka min a hanci na.
Barci ne ya dauke ni hankalin shi yai matukar tashi sosai don abin ya dade bai tashi min ba.
Jikun su sai rawa yakeyi don a zahiri abinda idon su ya gane masu yai matukar daga masu hankali sosai.
Ga boka yace tabbas ranan dayace suyi amfani dashi idan basuyi ba akwai matsala ga tashin hankalin da suka samu a gidan wanda yai sanadin har faduwa sai da dayar matar tai tangarde a hannun ta.
Basu kwana ba suka koma gurin boka a cikin dare suka isa sun samu a gidan boka ana kuka wai yana tsaka ga aiki akaji ya kyallara ihu sai abin ya koma mai kamar hauka tuburun dashi.
A kauyen suka kwana ba yadda zasuyi suka aje mai kayan daya basu suka juyo tunda safe suka dawo kaduna.
Wasa wasa suka fara dan ciwo wanda sherin da sukayi ne ya juye ya koma akan su.
Dole mahaufiyar hanna tazo ta dauki yarta ta tafi da ita garin su cikin tashin hankali.
Azumi ya fara kowa yanzu ibada yakeyi sosai babu babba ba yaro a gurin neman falala ga ubangiji.
Na samu cinikin kayana sosai don har na hadawa bin yusuf mai kayana kudin shi cif na kulle a guri daya.
Ga sauran kayan da suka rage a gurina duk a matsayin riba wanda idan zan sayar dasu zasukai kimani dubu dari uku da dan kai sama.
Wayan hajiya Aisha ne yazo gare ni take cewa sunan shigowa tana son ta kawo min kayan azumi kada naga kamar ta manta danine bata kasan ne yasa mukaji ta shiru.
Nace babu komai mama ai shiru alaman lafiya ne ga bawa.
Munyi waya da ita da kamar kwana biyu masu sayen kaya sunzo muna tsaka da ciniki tashigo gidan da yaran ta mata.
Mun gaisa dasu a cikin mutunci tana tambayana yarana nake cewa sun tafi islamiya karatu.
Daya daga cikin ditantana idon ta yakai ga kayan dake a zube take cewa taga kayan yaran na mika mata dayan tace na miko mata bedshirt tagani.
Sai naji yarinyar nata wace zata girmay min tace ikon Allah mummy kinga kayan da nagani a hongkong nai nema ban samu ba a lokacin.
Itama mai bedshirt abinda ta fada ke nan bedshirt suka zaba har kalla goma suka sa na buga masu kudin shi cif suka miko min kudina a take.
Maman tace dama suna ziyara ne don samun falalan watan azumi tace suzo gurina mu gaisa dasu.
Nan ta zube min bandar din yan dubu har uku a kan table tace ga abin shan ruwa nan sai bayan azumi tana son yin magana dani idan Allah yakai mu.
Zasu tafi taba Umma dubu hamsi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login