Showing 18001 words to 21000 words out of 115099 words

Chapter 7 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6666

dake da suminti kamar an nufi wani guri sai dai babu kowa a gurin har lokacin.
A hankali nabi filin da kallo banga kowa ba kuma roban yana a rufe yadda na barshi da farko.
Na sauke ajiyan zuciya na dawo falo na zauna tunanen wanan bakon al,amarin duk ya cika min zuciya na.
Firgigit nayi lokacin da naji ana buga kofan shigowa falon mu gashi lokacin sha biyun rana yayi nan tsoro ya kamani ina tunanen waye kuma a wanan lokacin haka.
Daukan Nusaiba dake barci nayi na saka a bayana na nufi kofan falon da ake ta bugawa.
Na bude a hankali ga unguwan namu yayi tsit bakajin komai sai sautin kukan tsuntsaye da kwari kawai.
Wata mace nagani tsaye a kofan tai min murmushi tace sorry na damay ki ko nice wance ke wancan gidan na gaban ki ta nuna min gidan dake can gaban mu wanda nakan ga jan mota a kofan gidan.
Tace sunana maman Stephen don Allah nazo ne ko kunyi ajiyan wake ki dan bani nawa ya kare na manta na fadawa daddy mu ya sayo muna.
Nace mata ayya bari na duba maki na barta nan tsaye bata shigo ba nima ban damu da nace mata tashigo din ba .
Na debo mata wake mai yawa a cikin wani dan blue roba na bata tace wiiii duk wanan mai yawa haka na gode fa nagode ina son nayi cooking ne kafin yan makaran ta su dawo.
Mukai sallama matar ta tafi na dawo tare da rufe falon gidan gurin girkina na nufa yau ba lesson yaran da wuri zasu dawo gida.
Karfe daya suka dawo gidan gida ya kaure da surutun su sai Abba ne ke ce min dana debo masu abinci mama ni fa kin san ban cin wake fa nace wallahi Abba na manta ne amma bari na dafa ma idomie idan zakaci lokaci daya na rana na dora tukunya a wuta yaran sun dan fita da Nusaiba takofan mu suna wasa.
Na fita na jika kayan uniform din da suka cire a roban da nake wanki dashi.
Koda na dawo sai samu nayi an kashe gas din an sauke tukunyan saman wuta.
Tsayawa nayi da mamaki ina kallo don dai ni nasan na dora ruwan dafa mai indomie din.
Na fita inda suke zaune suna wasan su nace waya shiga kitchen yanzu cikin ku ?
Kowa yace basu shigo cikin gida ba suna waje suna wasan su kuma basu ga kowa ya shiga ba.
Na juya na nufi kitchen din ina wasi wasi a raina towa ya sauke min tukunyan har da kashe gas kuma ?
Na dauko abin kuna gas din zan kuna naji ance kada ki kunna shi na fada maki kamar a hasale akai maganan.
Da sauri na juya don gani ko wacece take min magana babu kowa a kitchen din tso na aje tukunyan na fito kicin din na saka hijjab dina na dauki zanin goyon Nusaiba nafita inda yaran suke na karbi yarinyan hannun Aisha dake ta janjalanbo da ita don bata inmata ma sosai nace masu ina rufe gidan kuzo muje.
Gidan Anty muka nufa kamar kullun gurin gidajen nan biyu sai naji tsikan jikina yana tashi idan nazo gurin.
Gidan ta yana bude yaran ta duk suna ciki sina hayaniyan su mukai sallama na shiga nida yaran.
Tana dakin ta kwance taji muryan mu sai tafito falon su nan muka gaisa sai hayaniyan yaran suna fira a tsakanin wanda hiran wani film ne yaron ta sa,an Abba yana bashi labarin gilm din na yarane.
Tace maman Abba gaki kamar a firgice mana nagan ki tana mai kallon fuskana ido cikin ido.
Na sauke ajiyan zuciya nace wallahi anty akwai matsala gaskiya nan na fara koro mata abinda nake yawan ji a gidan namu ko yaushe.
Tace inkon Allah injin baki dora tukunyan ba nace ban dora ba shine ma nafito muka zo nan.
Tace lalai ba,a rasa jinnu a gidan amma kuma shi Baban Abba yaki ya fahince ki asan yadda za,a bullo wa matsalan kuma.
Tace wallahi muma hakane lokacin da muka dawo sai gidan ya kama juya muna idan da rana ne sai kiga gidan ya koma wani iri idan dare ne kuma sai a juya gidan ya koma part daban daban.
Nace ni yanzu hankalina ya daga gaskiya ya mayar damu gida kawai ko ya sake muna wani guri .
Tace gaskiya kan da matsala amma idan anyi sulhu dasu ai kila za,aci nasara su bar gurin kinga zan yi wa baban su Yasir magana yai wa maigidan ki magana ansan abin yi.
Tace balle yanzu fa rana tsaka ne ance lokaci suke al,amuran su idan ka taba su a wanan lokacin suna iya cutata maka.
Tace bari taba Abba din abinci yaci kada ya zauna da yunwa a cikin shi tace kindai yi arziki da baki kara dora tunkuyan ba da Allah yasan abinda zai faru da hakan.
Nan muka zauna har wani lokaci sai da rana yai sanyi da la,asar muka nufi gida na shirya yaran zuwa islamiya suka fice.
Hakana muka zauna yau dadi gobe madaci ina jin abubuwa barkatai a gidan.
Gashi baban Abba yai min fada sosai wai ina son in tayar mashi da hankali da nasan ban son zuwa na zauna lafiya may yasa na matsa mai cewa zanzo inda yake shiga ba nan yake fita ba nidai nai shiru ina mamakin halin shi.
Tun ranan ban kara mai magana ba kuma ba,a daina muna saddabaru ba a gidan.
Yau watan mu daya cur a gidan muna zaman mu dai hakana na maneji da rayuwa irin tayau.
Yace shi zasu fita operation zai kwana daya ko biyu a can komai da zamu bukata ya aje muna a gida kafin ya wuce nai mashi Allah ya tsare ya tafi yabar motar shi a gida.
Lafiya muka wuni da yara ba komai har dare hankalin mu a kwance muna kallon super story da akeyi a N T A .
Nan Aisha da Nusaiba su kai barci Abba da ni dake yan zirga zirgana ne kawai ke ido biyu shima dai nan barci ya dauke shi sai naga muyi kwanciyan mu a falon ma kawai mana.
Can na gama ina shirin kwantawa akan shimfidan da nayi sai ji nayi ance to ni Ummi ina zan kwanta ga wanan ya kwanta min a guri.
Dubawa nayi babu kowa a gidan sai naji ance zulkafalah kasan halin bani adam da son kai irin nasu sun tare muna ciki yanzun kuma nan din da muke kwanci kuma sunzo sun tare muna.
Cikin karfin halin da ban san zan iya ba nace ai baikai na son kai ba bari na kwashe su na baku gurin ku a zauna lafiya.
Muryan karamin yaro naji yana cewa dadai yafi sauki wallahi don ba yarda zanyi ba yau.
Kallon yaran dake barcin su nayi na rasa daga cikin su waye zan fara dauka zuwa,daki don gudun kar na barsu wani abu ya samay su.
Don haka na tayar da su gaba daya a lokaci daya na tasa su gaba muka shige daki cikin karfin hali na kara fitowa falon na kashe wuta tare da daukan abinda zan dauka nabar gurin.
Nai alwala nan nafara sallah ina neman tsari tare da bude kur,ani na har safe ba wani motsin dana sake ji.
Ban tashi jin tsoro ba sai da,asuba naji tsikan jikina yana tashi hankalina yai matukar tashi lokaci guda.
Har barci ya dan dauke ni dole na falka ne masu abin karyawa dana zuwa school da safe.
Ke nan ana nufi da wasu muke zaune a gidan ko may haka ke nufi bafa barci nayi ba balle ince mafalki ne nayi.
Idona biyu duk wanan abin ya faru kenan fa gaskiyane wanan al,amarin yafaru really.
Ga barci ina ji amma kuma tsoron kwanciya nakeyi hakana na zaune sai karatu nake fa Nusaiba da yanzu idan mu biyu ne a gida bata yarda na barta ita kadai ko kadan kamar wace ke ganin abin firgita a idon ta.
Wa ma zan fadawa wanan zancen ince ga abinda naji Anty ce kawai tasan halin da nake ciki a gidan.
Hayaniyan mutane naji daga waje shiya sani fitowa daga cikin gida na leka naga wasu ne sukazi zasu shiga dayan gidan dake a tsakanina da na su anty haka yasa naji dadi sosai a raina koba komai zan dan samu sauki a raina.
Fatana dai Allah yasa musulmai ne nafi son makwabtaka da musulma yar uwata ba irin su maman Stephen ba da ko yau she kida ke tashi daga gidan su.
Ina tuna haka dabara ya fado min a raina nace kawai na tsiri kai tashan da ake kira,a na dinga sake shi a gidan always tunda aljannu basu son karatun kur,ani.
Ina shiga ciki kuwa na lalubu tashan da ake kira,a alkur,ani maigirma ko yaushe.
Ina aikina ina bin karatun a hankali nima haka ya shagaltar dani na kara mantawa da damuwan da nake ciki.
Abin mamaki na daina bin karatun amma sai nake ji kamar wata murya mai zaki ba,a cikin tv ba ana bin karatun a hankali.
Saurarawa nayi haka din ne kuwa nace ya salam nashiga uku kuwa a gidan nan ashe har karatun ma bin shi akeyi .
Sai naji anyi shiru muryan da naji har yafi nawa da na mai karatun dadin ji sosai.
Ban kashe ba na barshi har rana yara suka dawo suna murna suna fada min sunga ana saka kaya a dayan gidan nan da babu kowa a cikin shi.
Na ce masu ai nima nagani muna ciki naji ana nocking din kofa ina daga ciki nake cewa Abba duba waye a kofa.
Yana bude kofan yaron da,ake kira Jonh ne a tsaye kofan dan maman Stephen da,roban da na ba uwar shi a hannun shi.
Yace ga roba inji mummy mu wai na kawo maki nace ma yaron ya shigo har ya saka kafan shi kamar zai shigo sautin kira,an da yaji yana tashi ne yasa shi saurin ja baya yace No bazan shiga ba ya juya da sauri ya,wuce yabar gurin.
Kallon mamaki nakewa yaron ban san may yakewa wanan wiki wikin ba da ido gashi har zai shigo ya juya da sauri yabar gidan.
Nikan ban kawo komai ba,a,rai na nashare zancen yaron naci gaba da tsabgan gabana.
Sai dare mun kwantane nai mafalki da yaron wai yana warning dina idan ya kara jin na saka kira,a a gidana sai ya kashe ni ya nuna min sani zundumaymay wuka a hannun shi.
gani nayi wani abu ya daga yaron sama ya rade shi ga bango yaron yana wani gurjin ihu.
Aiko a cikin barci na ke jin ihu har a fili daga gidan maman Stephen gashi dare ne tsoro ya kamani na zaci ko barayi ne suka shigo muna quarter din.
Shirmay na sai motan baban Abba dake tsaye kofan mu na tuna nace shike nan sun sace dan motan ke nan mun huta.
Ban yi barci ba ban kuma daina jin hayaniya ba a makwabtan mu abu ga yare sai ihun kuka da kiran juses takeyi.
Can naji kara mota aka fita daga unguwar ashe sune suka fita da motan daga uguwan zuwa asibiti da yaron.
Sai da safe tunda safe bakuwar makwabciyar mu da anty suke buga min gida na bude a gigice suke ce min ni jiya ana ihun neman taimako ban fito ba ?
Nai saurin kai idona ga motan mu tananan tsaye inda take suke fada min wai John dan maman Stephen ne ba lafiya ankwanta smdashi lafiya lafiya cikin barci akaji yayi ihu sai ganin kan shi da, wuyan shi kamar ya kare jini yana fitowa sai da aka kaishi asibiti.
Take mafalkin da nayi da yaron ya fado min a rai a zuciyata nace sabon matsala ke nan.
To may kuma wanan al,amarin yake nufi kuma sai dai naja bakina na tsuke ban fadawa kowa mafalkin da nayi dashi ba.
Don yanzun magana wuya gare shi ko banza suna iya fara zarga min wani camfi a kaina banji ba ban gani ba.
Tun safe aka dauke wuta a layin namu don haka zafi ya ishi mutane muka fito daga waje mu sha iska.
Dan zaman da kowa zafi ya ishe shi daga ciki ne yafito da yara ta,wajen gida a nashan iska hankalin kowa ya dauke.
Sabuwar makwabciyata mutumiyar sokoto ne mijin ta dan sanda ne suma dai aikine yakawo su yaran ta biyar ta dara mu yara ke nan.
Nan muka zauna muna hira da yaran ta da suka kwaso zuwa gurin mu suna wasa da sauran yara.
Mikewa nayi in shiga daga ciki in duba girkin mu dana dora a wuta na samu an kashe gas din again.
Naja na tsaya ina mamaki nace da karfi gaskiya ni wanan abin da ake min fa, ya fara isata wallahi mutum da gidan shi kuma a hana shi shakat wanan ai cin zalin ne in ma wani abune afito fili a fadawa mutum mana ya daina amma haka kawai don cin amana a saka mutum a gaba.
Ga mamaki na sai kawai naga gas din ya tashi yana aiki na tsaya ina kallo da mamaki.
Na juya zan koma naji ance min ku bamu gidan mu mana in baku san haka ?
Nima yanzu na iya nace inba tsoro ba maishi yafito fili mana nagan shi nima amma haka kawai za,a hanaka shakat may mukai maku ne wai salaman salaman muke da kowa.
Saida dare ina barci gashi ba wuta ga zafi nai mafalkin wata mata tsaye a kaina tana fadin kiyi hakkuri kin san halin yaran nan baji sukeyi ba yanzu.
Tana fadin haka tajuya lokacin na bude idanuwana sai ko naga gilmawa kamar mutum daga dakin da fararen kaya.
Zubur na tashi zaune har falo nake da yar toci na na haska ko ina babu komai a gidan na dawo daki sallah na tayar ina kai kukana ga Allah cikin damuwa da,wanan bakon al,amarin da ya samay ni a rayuwana kuma.
Gashi mubar gida da fitinan mayi mun shigo bariki kuma ga fitinan da yafi na mayu ya taso min wanan rayuwa da may yai kama rana zafi innuwa kuma kuna.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
BA MU KADAI BA NE
๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง
8โƒฃ


Washegari da da safe haka na fito jikina kamar an dadake ni yai min mugun nauyi sosai.
Da yake weekend ne ban tayar da yaran ba na barsu suyi dan barcin weekend su huta.
Duk suna can cikin bed room suna barcin su ni ce kawai a falke ina zaune ina dan tasbihi duk da idanuwa na,nauyin barci ne sosai ke cina.
Can kamar a mafalki naji shara daga back yard din mu da farko danaji sai na dauka daga gidan waccan sabuwar makwabciyar mu ne sautin sharan ke fitowa sai nai shiru ina,saurare sai ji bayi lalai lalai a cikin gidan ne kawai ake sharan nan.
Nace oh Allah ni maryamu ni kuma nawa kaddaran ke nan gogaiya da aljannu ko may ?
Ban daina jin abinda nake ji ba har lokacin ana ta faman motsi a gidan jefi jefi.
Sai tsawon wani lokaci na mike na fito daga bedroom har lokacin yaran barcin su sukeyi hankalin su a kwance ba abinda ya damu yaro nace a,raina da ace shekarun su yakai su san halin da muke ciki a gidan nasan ko runtsawa bazasu yi ba balle barci hakan ga.
Ina shiga kitchen komai yanan yadda na barshi ba,a taba min ba nace a raina Allah ka kare mu da kariysn ka ya Allah.
Na kunna gas tare da dora ruwan zafi don yau ba tea nake da muradin musha ba a gidan so nake mucen kalar abin karyawan mu.
Irish na debo na fara herewa a hankali daga inda nake a tsaye ne naji kamar gilmawan mutum a bayana.
Nai matukar razana na juya da sauri banga komai ba a gurin sauke ajiyan zuciya nayi bakina tunkan nafito daki dauke yake da ayyatul kursiyu har zuwa wanan lokacin da nake aikina.
Faten dankalin nai muna da ganyen alaiyahu yaji attarudu da albasa sai kamshi yake yi.
Na kusa gamawa ne Aisha ta fara tashi wanda nasan yunwane ya falkar da ita bakin kitchen din ta iso na dan juya na ganta nace a,a Indo an tashi tace eh mama.
Nace oya maza jekiyi alwala kizo kiyi sallah hankali ya dauke ga aikin da nakeyi ashe ba bathroom ta shiga ba can ta nufi backyard din da nake aiyukana ta dauki buta tafara alwala sai kuma ta hau wasa irin na yara ita kadai nake gani amma tana ta zuba surutu kamar wacce take wasa da wani yaro dan uwan ta a fili.
Sai da na fito na shiga daki bayan na gama kwashe abinci ne na dora ruwan wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login