Showing 12001 words to 15000 words out of 115099 words

Chapter 5 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6630

sakon ya zo gidan da kayan miya fresh one su tomatoes tattasai albasa dasu cabbage da sauran abubuwa girki dai.
Nakai kitchen nai ma komai muhalin shi yadda ya dace ayi a kitchen sai zuwa rana na samu nai wanka nai sallah.
Yaran na son fita waje na hana su na kulle gidan damu a ciki ba wani hayani ya sosai don mutane a gurin jefi jefine ake ganin su.
Sai da na idar da sallah ne muka fito daga wajen gidan muna kallon uguwan.
Nan naga yadda fasalin gurin yake dakyau na lular tsakanin gidan mu da gidan dake da mutane akwai gidaje biyu da suke empty ba kowa a cikin su sai namu can kuma zaka hango wasu suma daga nesa haka tsarin gurin yake a can ma gaban mu akwai wasu mutanen a wani gida don na hango mota a kofan gidan.
Nan muka dan sha iska zaune a gaban gidan zuwa dan wani lokaci muka koma daga cikin gidan na fara kokarin gyara kayan miyan da zan muna girkin dare.
Sai da nai sallah la,asar na dora girki ina jin yaran suna ta wasan su a falon gidan niko ina daga ciki ina aikina a cikin natsuwa.
Har na gama mukai wanka na gyara ko ina a falon bai dawo ba sai zuwa biyar da rabi kusan shidda naji ana kwankwasa kofan dakin na nufi gurin na bude kofan.
Shine a tsaye yana cikin uniform din shi kayan sun balain yi mashu kyau yana tsaye da leda a hannun ahannun shi nai mashi sannu da zuwa tare da karban ledan hannun shi.
A tare muka juya muka shiga gidan dashi yaran dake zaune suka sheko suna mashi oyoyo ya daga su sama daya bayan daya.
Nusaiba dake saman kujera tana wasa da ganin shi take wasan bakin ta don tasan uban ta sosai.
Sai da ya dan zauna suka taba shirmay da yaran yamike ya shiga wanka yayi yafito cikin jallabiya a jikin shi.
Sallah ya jamu mukayi a gidan sanan bayan mun idar ya,mayar ga,hankalin shi ga,tv yana kallon labaran duniyan da,akeyi.
Saida mukai sallah ishau ne yabar gurin na kawo mashi abincin shi yafara ci nisaiba tazo gurin shi.
Yana ci yana bata nace tafa ci abinci kwadai ne kawai irin nata yace da ta koshi aibazata karba taci.
Nan muka zauna ana hiran abinda aka gani a hanya da zamu zo jiya daga gida.
Yace yau na tafi school din da nake son sa yaran nan sunce zuwa Monday sai azo dasu su gan su.
Naji dadi sosai a raina yarana zasu fara makaran ta abirni kamar yadda muke gani sunayi.
Na zauna ina tunanen idan suma suka fara zuwa makaranta haka zan zauna ni kadai a cikin wanan gidan ga unguwa kamar daji.
Naji muryan shi yana fadin badai har kin fara tunanen gida ba ko ?
Nace a,a tunanen dai yaran nan nakeyi da zasu shiga cikin bakin fuska da basu sani ba.
Yace ke da kikai karatu kin san su ne ba a hankali ake sabawa da mutane ba.
Kada fa ki sakawa yara damuwa suje su kasa zama suyi karatu kuma.
Aisha tace nikan baba akaini makaran ta ina so wallahi bazan ki yin karatu ba idan an kai mu.
Abba dai ba mai yawan surutu bane kamar yar uwar shi hankalin shi yana can akan tv yana kallo abinshi.
Yace akwai wani abinda kuke bukatane kuma a,sayo maku na gida nace ba komai sai dai yan bahohin aiki nake so kanana da yan manya don wanki saboda wanki da bucket bai da dadi wallahi.
Bai min magana ba yaci gaba da kalon shi abinshi na mike zuwa kitchen na wanke kayan da yaci abinci na gyara gurin na dawo falo.
Na samu yaran har sunyi barci a lokacin nace yau ga shirmay har kunyi barci ko yanzun karfe nawa?
Yace suna da sauran gajiya ne a jikin su shiyasa sukai barci nace a gida fa suna kai dare sosai basuyi barci ba suna hira da umma ko kallo.
Yace sai na samu kudi zan dan duba masu kayan sawa wanan duk subar sa su anan sun tsufa da yawa.
Nace daya ke nan da agida muke ina zamu ga tsufan wanan kayan masu kyau haka.
Shiya tayani daukan yaran mukai su cikin dakin kwanan mu bayan nayi masu shimfida sun kwan ta.
Sai da na dawo falo na zauna nake cewa ashe uguwan nake ganin kaman ba mutane sosai cikin shi.
Yace sabon guri ne ba akai shekara da,dawowa ba bamufi gida ashirin ba dake da mutane ina gani kuma gidajen zasu kai guda hamsim.
Yace amma indai kaduna ne zakiga kwana biyu duk gurin ya cika da jama,a ai.
Washe gari da muka tashi ma nai sauri hada mai komai yadda ya dace yafita ya bar mu ranan bai dawo da wuri ba sai bayan sallah magariba.
Rashin shi a gida ya sa muka koma jigum jigum saida ya dawi aka dan fara hira da hayaniya a gidan.
Cikin dare har muna,shirin kwanciyane aka kirashi a,waya wai yazo zasu tafi operation an ji cewa,wasu zasu shigo da kayan sumugal wani kauye.
Ya mike yana fadin yes,sir gani nan zuwa kallon shi nayi da mamaki yace shi zai fita don zasu tafi gurin wani aiki ne .
Cikin daren nan baban Abba yana shiri yake cewa ai haka aikin kaki ya gada dama ba kuna can kuna fanin kaman mutum yana nab yana jin dadi bane kawai.
Yashirya yake ce min sai ki taso ki rufe gida idan na tafi don nasan ni sai da safe zan dawo gida ke nan tunda aikin dare zamu fita yanzu.
Gabana ya fadi tsoro ya kamani nace a raina yauko anayin ta dani da yaran nan kawai zamu kwana a gidan nan ke nan.
Binshi nayi a baya har zuwa kofan falon sai daya dan kai kofan zai fita ya juyo yana cewa ki kashe komai fa na,wuta idan zaki kwanta nace toh
Yana fita na kargamay gidan da bisimilah don indai adduoi ne mun san gwargwado tin muna yara a gidan mu kasan cewan babana malami.
Na juya na koma ciki na jashe wutan falon dana daki na shige cikin yarana muka kwanta abin mu.
Ban falka ba sai can cikin dare naji kamar an tayar dani ne daga barji ni ban yi barci ba kuma na kasa tashi na yi koda nafila ne.
Haka kawai naji tsoro ya kamani sai faman jero adduoi nake har dai barci ya zo ya sace ni ban sani ba.
Ko da na fito da safe na shi kitchen kayan da na wanke dare jiya sai na samu kamar anyi amfani dasu ga garin tuwon mu a bude ba kamar yadda na rufe shi ba kuma har a kasa ya dan zuba.
Naji mamakin ganin haka don dai nasan baya gani jiya babu wanda ya shiga kitchen din to wanene yai haka da kayan nan kuma ?
Har na dan fara sa abin a raina nace kai kilama dai nice nabarsu a haka na mata kawai sai na gyara komai naci gaba da aikina.
Sai rana yaya yadawo a gajiye tunda yai wanka ya kwanta bai falka ba sai bayan la,asar lis ya tashi ya dawo falo inda muke duk da ni ina kitchen ne aikin girkin dare.
Yace yau da dare zamu fita zuwa wani guri sai ki shirya da auri haka yasa nai duk wani abinda zan yi kafin magariba har wanka munyi mun shirya.
Cikin gari muka tafi gidan wani abokin aikin shi yana da mata shima da yara biyar matar ta tare mu sosai dakin ta muka zauna don mazan suna falo suna hira.
Muma dai muna ciki tana min hiran garin da yake bata sa,wuyan sabo ita sai da yaga dare ya soma ne ya kecewa mu fito mu tafi dare yayi .
Muna hanya ya tsaya damu wani shago na kayan yara da lashe lashe ya sai wa yaran kaya kusan kala biyu da kayan lashe lashe.
Mun iso gida ina matukar jin fitsari da sauri bayan na suke nusai ba na fada ban dakin mu don in kewa ya lokacin ne ma shi yake shigo ciki da wasu kaya.
Tau nidai a iya sanina mu kadai ne a cikin gidan nan amma sai dai gani nayi kamar yanzun wani ya gama wanka don har kamshi sabun da akai wanka dashi nakeji.
Ga ruwa nan yana dan diga gowa ga, soson wankan a hankali kasan cewa soson a rataye yake a saman window dakin.
Da mamaki nafito daga bayin inda suke zaune a falo yana barewa Nusai biscuit nake cewa akwai wanda ke cikin gidan nan ne bayan mu.
Kamar yaya kuma nace wanka naga anyi kuma da alama yanzun aka fito daga gurin wankan .
Dariya yayi yace wanka kuma ni ba wani wanda nabawa key din gidan nan balle kila ma ruwan shower ne yake dan digosa ya kike gani kamar wani ne yai wanka yanzun a ciki maganan don haka kawai na,share zancdn a raina n a ci gava da harkokina kawai.
Shima bai kara zancen ba yaci gaba da hiran shi da yara yadda na samay su sunayi da farko.






ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐ŸŒŸ: ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ ๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง

BA MU KADAI BANE,,
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ง ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ
6โƒฃ


Tun ina saka zancen a raina har nagaji na share zancen naci gaba da normal life dina tun lokacin kuma ban ba kara jin komai ba a gidan.
Sati yana kewayo wa yakai yaran makaran ta suka fara karatun su kamar ko wani yaro.
Naji matukar wanan sabon rayuwan da muka,shiga dani da yara,a gidan.
Don da ka gan mu kasan akwai canjin rayuwa matsalata data shine idan sun fita zaman kadaicin da nakeyi daga ni sai Nusaiba a cikin gida kawai.
Rana sun tafi makaranta shikuma ya tafi gurin aiki sai naji ana nocking din kofan falon mu.
Nafito don inga ko waye a wanan lokacin haka wata matace nagani tsaye a kofan gidan tayafa dan karamin gyale a kafadan ta.
Ban santa ba yasa nake mata kallon mamaki daga ina tai murmushi tace min ina kwana na amsa mata sai take cewa sorry fa kiyi hakkuri tunda kuka zo ban da lafiya ban samu shigowa na tare ku ba.
Nice makwaciyan ki ta nuna min gidan ta da hannu sai na fahinci gidan da akwai gida biyu da ba kowane a tsakanin mu.
Jin abinda tace yasa nai murmushi tare da ce mata Allah sarki shigo mana muka shiga tare ciki da ita.
Mun gaisa take ce min ance mu mutanen Niger state ne ko ?
Nace mata eh tace ita yar lokaja ne itama mijin ta aiki ya kawo shi kaduna yana aikin banki ne tana da yara hudu babban yana jss one sai mai bi mashi yana primary four yanzu kaunan shi tana primary two ita sai wanda ta yaye bai fara zuwa school ba.
Sunan ta Hauwa mijinta tana kiran shi baban mubarak.
Nan nima na dan fada mata nawa dan labarin irin yadda ta bani tace unguwar ba dadi shirun shi yai yawa kasancewan shi sabon guri ne.
Nan take ce min tana gani wancan gidan na gaba kamar kiristan ne su amma dai akwai mace da yara a gidan basu dade da dawowa ba suma kaman mu.
Mun dan yi hiran garin muka fito waje nan muka tsaya muna karewa gurin kallo muna magana nai mata alkawari nima zan shigo idan yara sun dawo daga makaranta.
Bayan mun rabu ne nadawo ciki naci gaba da aikin da nakeyi sai kallon da nakeyi jefi jefi.
Yaran suna dawowa ne tare da yaran Hauwa don maigidan hauwa yana riga Aliyu dawowa gida kullun don yanayin aikin su ba daya ba.
Wata rana su basu ma cikin gari sun tafi wani guri aiki yasa ya roki makwabcin namu ya taimaka mai da dauko yaran tunda makaran ta daya suke zuwa.
Muna zaman lafiya sosai da makwabciyata don na dauke ta a matsayin ya don ta girmay min sosai.
Saboda mu irin auren kauye ne kashiga makaranta da wuri ba nursery sai primary one ka gama da wuri daka gama secondary sai aure kuma sai saurin haihuwa.
Don yanzun haka ko agida akwai yan mate din mu ma dabasu yi aure ba sun tsaya karatu wasu kuma lokaci ne dai baiyi ba tukun.
Yaran sun dawo suna shigowa na saba masu da sun dawo su cire uniform sukai min can baya inda nake wanki zasu samu na fitar masu da kayan da zasu saka ajikin su.
Tun suna saka kayan Aisha ke cewa anty yau anbamu aiki home work kuma anti tace wanda baiyi ba gobe bulala ne zatai mai.
Nace to kici abinci kizo muyi homework din tare idan kin gama suna gamawa ne na zauna bayan na gama wanke masu uniform muka fara assignment din da ita.
Naji dadin yadda yaran ke iya kokarin su da irin karatun birni duk da ba turanci ne suke ji ba.
Yaran anty ne suka shigo gidan don alhamis ce basu zuwa islamiya ranan.
Nan suka zauna muna hira,suna tambayana labarin wai da zasu dawo daga school yau sunga biri a hanya .
Nake ce masu aikila na wanine sai fadila ke cewa baya cizo ne nai dariya nace yana cizo mana idan an tanlba shi amma bai cizon mai shi wanda yake dashi.
Tace wai Allah yasa dai bangani ba daya cije mu ko maman Abba nace idan kinje kusa dashi ba zai cije ki.
Tace shine fa yayan mu wai daddy mu ya tsaya mu kalla nace ai idan kin bashi banana bazai cijeki ba sai ku zama friend daga ranan.
Yariyar tace No no bazan iya bashi ba nan suka shiga mussu a tsakanin su wanan yace ni zanbashi wancan yace sai na jefa mai na gudu nabar gurin.
Ganin suna ta shirmayn su na,sulale nabar su suna ta hira akan biri yau zancen ke nan daya a bakin su tun dai Fadila dana fahinci bata taba ganin biri ba afili sai yau din.
Har nagama girkin dare na zuba masu sukaci muna hira sai ga maman su tabiyo su.
Nan muka gaisa da ita tace ku bakuga yamma yayi bane kuka zauna haka abinku har dare.
Nace yanzun nake batun turasu gida ai tace wallahi idan yamma yayi haka ban son suna fita waje don kinga gurin namu kamar daji yake mussan ma wanan gidajen da babu kowa a cikin su tsoro suke bani wallahi don wani lokaci sai makiji kamar akwai mutane cikin shi da dare tun ma wanan naku kafin maigidan ki ya dawo ciki zaki dinga jin wallahi kamar akwai mutane a cikin sa.
Sai ka natsu zakaga ba kowa kawai dai imagination ne mutum ke yi aini dawowan ku ba karamin dadi naji ba wallahi.
Ina Allah Allah akawo mai mata mu zama mu biyu a kusa dama don zaman kadaicin yai min yaw nace ai zama shiru baida dadi wallahi.
Nace da zasu tafi fadila ko na kawo maki birinki ne kije dashi da sauri yarinyar ta boye bayan mamanta cikin jin tsoro.
Uwar tace ai wanan matsoraciya ce sosai bata fa fita nan da kofa idan dare yayi sai shegen tsoron tsiya gareta ga jan magana da son hira.
Nace cikin murmushi ainaga alama yau Birin nan ya tsayawa Fadila a rai ko an manta sai ta jefo zancen birin ita.
Uwar tace muje nidai kadai ki soma kiyi min mafalkin shi nai maki dukan tsiya wallahi ko.
Sun tafi munyi saida safe dasu na juya muka koma ciki ni da yarana na kwashe kayan abincin da sukaci na shige dashi kitchen na wanke su kafin ai magariba.
Bayan na idar da sallah ina zaune kiran wayan baban Abba yashigo min dama tunanen shi nakeyi ya dade bai dawoba yau duk da wani lokaci sai magariba yake shigowa gidan.
Na dauki wayan da sallama tare da gaishe shi da aiki yake tambayan yaran nace gasu yanzun Aisha take tambayan ka ai.
Nan yace na bata wayan ta dauka suna ta hira da baban wanda tambayanta karatun su yakeyi.
Abba dake gefe zaune bai damu ba don yasaba hankalin uban yafi karkata ga Aisha basu faye shiri da Abba din ba sosai.
Nan dai suka hira yace tabashi Abban basuyi wani dadewa dashi ba yaron ya miko min wayan.
Yace kin gane ne maryam ki rufe gida don yau bazan dawo ba zamu fita operation din dare don akwai wasu kaya da muka samu labarin za,a shigo dasu ta barauniyar hanya.
Don haka ku kwanta abinku ina ganin ni sai dai gobe idan Allah ya kaimu ke nan lafiya.
Nace to Allah ya tsare ya kare muna ku lafiya yace Amin ina Nusaiba nace gata kwance tayi barci ko tundazun da nai mata wanka yace to ashafa min kan ta ko ?
Bayan mun gama wayan ne naji raina ya baci don in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login