Showing 102001 words to 105000 words out of 115099 words
Chapter 35 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
Yace to ki fita daga jikin ta kuma har abada tace angama malam insha Allahu.
Daga haka tai wani dunkulewa guri daya tare da murdewa kamar cikin ta yana ciwo tana sake wani irin atishawa mai karifi da sauri nace wa uwar ta dake gefe tajaye tabasu hanya su wuce.
Sai gata ta mike kwance tana mayar da numfashi wani iri kamar zata shude ranta zasu taba ta nace su barta akwai saura.
Nace baku san hajjo ruwa ba ko ita wata aljannace da ke zama a cikin ruwa tana da matukar kyaun sura tana da gashi har bayan ta mai yawa.
Bata faye baiyyana ba sai tayi barna sosai a jikin mutum kafin agane cewa itace tare da mutum don ba kasafai take baiyana ba.
Acikin yan adam wanda duk tafitowa asuran ta mutun kan kasance kamar ya haukace don siffan ta akwai kyau akwai kuma ban tsoro sosai da ita.
( Don haka kalubali gare mu mata mu kula da kawunan mu akan abinda bamu gani kuma bamu san dasu ba a tare damu )
Ban dade ba bayan tafiyan ta na juya kan mahaifinsu nace Malam Iliyasu kana wa iyalinka sakaci kaida matarka.
Gashi kai mutum ne mara rigima amma hakan yasa har kake sakacin kyale iyalinka gurin yin yadda sukaga dama ga rayuwan su.
Kai kanka kana da sakaci gurin saurin amincewa dana tare da kai.
Aikin ka ba na saurin aminta bane gama yanzu da wani nauyin zai kara karuwa a kan ka.
Sai dai don Allah kamar yadda kake sa tausayi ga dukiyan bayin Allah ayi kokarin ganin a kara tausayawa wanda baida laifi gurin neman nakansa.
Aiku yana da matukar hatsari sosai shiyasa akasarin ku suke karewa a nakashe don yawan yasin din damasu haki ke ja maku.
Duk da wasu mutanen suna da laifi gurin shigo maku da haramttatun kayan da ba, a son amfani dashi to amma adinga dubaiyya da yakamata.
Duk wanda aka hada da Allah baiyi ba sai ubangiji ya jarabe shi da cuta mai tsanani a rayuwan shi idan kunne yaji jiki ya tsira ni zan koma na barku lafiya.
Daga haka na dukar da kaina kasa sai wani irin atishawa mai karfi adaidai lokacin da Amina itama ta mike zaune ta dan dube duben gefenta ganin ta da tayi a kasa zube.
Nan dai suka fara muna sannu Umma ce ta mike tashiga kitchen sai gata da roba dauke a hannun ta ta dauko goran ruwa takawo min.
Nawanke fuska na nasha nace mika hannu da sauri Aliyu ya dauko min hantiti na na shaka sai na sauke wani numfashi da karfi nabi lafiyan kujeran dake kusa dani na yadda kaina a sama.
Ikin Allah hajiya kinji magana kamar ta almara yanzu mu ina muka san da aanan bayani badon Allah yai sanadin haduwan mu da mutanen nan ba.
Da haka uwata zatai ta zama da mugun abu ajikin ta basun mafarin sa ba mu.
Dama na dade ina hasashen cewa suke bata maganin da muke mata da anfara magani sai abu ya lalace kamar an tayar dashi ne.
Umma takada baki tace ai mafi yawan matsalan nan mune ke jawa kan mu to abinda baka gani kuma bakasan dasu ba.
Gashi dai dole kuma ayi rayuwan ba fasawa za, ayi ba tunda mata muke.
Oga yace amma hajuya sai ayi ahi a cikin kima tunda kinji abinda suka fadi mai kazantar ma ba barinta zasu yi ba.
Sun dauki lokaci tare damu har yake tambaya ina aikine umma tace a, a sana, a nakeyi.
Yace ikon Allah banyi karatu mai zurfi bane Aliyu yace mai ina da NCE danayi tun kafin muyi aure.
Yace gaskiya dole a duba kuma ya kamata na koma makaranta ai hakana tunda ma ina da takarda na.
Umma tace kuma Alhaji ayi hakan yace shi karatun yana da amfanine ba wai sai lalai mace tayi aiki ba don kinga tana sana, a akwai inda karatun zai taimaka mata ne ai.
Munyi sallama dasu suka fice suna godiya muka rakasu har gurin motar su hajiya tace na bata nombana tana bukata.
Bayan kwana biyu ta bugo min waya tana cewa wallahi sunga haske sosai yanzu akan yarsu don duk halaiyarta na da yanzu ta daina.
Nace hajiya sai a fake dokokin da suka aza maku akanta don samun lafiyan ta tace insha Allahu.
Tace tana bukatan watarana na kawo masu ziyara naga mazaunin su suma nace zan fadawa maigidan idan ya yarda.
Har zan katse kiran takecewa dani wai ba ance kina sana, a ba nacs eh hakanane hajiya.
Tace why not ki hada kudi akwai kayan da akai Options din su daga gurin su maigida zaki samu sosai a garesu.
Nace mama idan nai haka ban sabawa Allah ba kuwa ?
Dariya magana na yabata tace tayaya zaki sabawa Allah ba saye kikayi ba aiba cin hanci aka baki ba.
Idan ma baki saye ba wasu ne zasu saya kuma su sayar dashi da kudi mai yawa.
Nace to zan duba nagani idan sayen ba matsala muka kashe wayan tabarni ina nazari a raina.
Assalamu Alaikum yan uwa dafatan munyi jumma lafiya.
Ina mai baku hakkuri don yanzu bazaku dinga jini ba kamar kullun saboda yau insha Allahu zan fara novel dina na kudi mai so tana iya yin register don jin labarin sadaukar da rayuwa ga jajartun mata masu imani a zukatan su.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
BA MU KADAI BANE A, , ,
๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
3โฃ1โฃ
.
Ni kadai nake ta faman nazarin zancen da mukayi da hajiya Binta a raina na kasa kuma fitar da zancen a cikin zuciyana.
Saboda ina ganin kudin dake gareni ina zai isheni sayen kayan contener dungurun gun.
Gashi kuma ko baban Abba na kasa fadawa wanan maganan sai cina yake a raina saboda ina gudun yai min masifa akai.
Don abune wanda ya shafi bangaren aikin shi sosai bazan so na ja matsala ga inda yake samu ba.
Sannu a hankali na fara koyon mota wanda yar sokoto ce ke koya min tukin wani lokaci kuma baban Abba da kan shi zai fita dani ya koya min.
Yau sati daya cif da case din mu da diyar Ogan su Baban Abba da keda lalurar aljanne a kanta da mukai artabu wanda hajjo ruwa take zama a jikin ta na tsawon shekaru.
Kitchen nake ina aiki da safe yayin da wayana dake aje a falo yake ta faman ringing shikadai.
Sai da kiran ya kusa tsinkewa ne na iso gurin da sauri na daga wayan.
Bakuwar Nomba ce ake kirana dashi daga kasan waje nombar yanuna min daga kasan Chaina ne.
Nace a fili ina daukan wayan chaina kuma ina dagawa murya ce na mace ke magana dani a layin tana fadin.
Yau maryama dama na kiraki ne na fada maki yau zamu dawo da dare insha Allahu don haka nasan sai cikin dare zamu iso gari don jirgin yamma zamu biyo.
Ina son ki gyara gida ki muna abinci don kin san yaran ki suna matukar son cin girkin ki.
Mamaki ne fal a zuciyana don ban san dawa nake magana ba a lokacin gashi dai maishi tana min magana akan tasan ni kuma a tare muke.
Don Allah maryam duk da ban sanki da kazanta ba ina son ki gyara ko ina don ba dadi kai tafiya na tsawon lokaci kadawo ka samu gida ba tsabta haka baida dadi ga macen kwarai.
Lokacin da nake ni kadai a gida bana tafiya ban tsabtace gidana ba yanzu ko kin sa damu da kune a gidan.
Gabana ya fadi take Mukkadarasiyatu ta fado min a rai na nace kardai ace da ita nake wayan nan kenan.
Watau shirun da naji bana mafalkinta kwana biyu tayi tafiya ke nan basu gidan ?
Muryan tane yadawo dani daga tunanen dana keyi tana cewa nagode sai mun iso zuwa dare insha Allahu.
Nace kamar nafahinta Allah ya kawo ku lafiya Allah ya tsare hanya yasa ku samay mu lafiya ta amsa da Amin yar uwa mai albarka nagode nagode.
Ina kashe wayan nakai zaune guri daya hankalina a tashe na dafe gefen huskana da hannu na daya ina fadi a raina.
Yau ni na shiga ukku ni maryama abin nawa ba wani sauki sai kara ci gaba da al, amarin yakeyi ma yanzu.
Yau har takai ina waya da mutanen boye kai tsaye ba wani shamaki ko dar a tare da ni.
Na jima a gurin na mike ina fadi a fili zama ai bai ganni ba ni maryam ko banza kyaun alkawari cikawa.
Daki na koma da saurina na shiga shiri ina dakin ne ina faman tunane mutumiyata yar sokoto ta fado min a rai nace ita zan laluba naji a raina don munfi balain shakuwa sosai da ita.
Ban kaiga idar da abinda nakeyi bane naji wayan nawa yana ringing da sauri na fito zuwa falon na dauka a zatona ko itace ta kara kira na sai naga ba ita bace a layin.
Baban Abba ne yake kirana da sauri na daga kiran nashi da sallama muryan shi a cikin yanayin farin ciki yake magana.
Maryam lalai ke yar halas ce wallahi wai kin san may har na kasa bari na dawo gida nai maki albishi nace a, a cikin girgiza kai kaman yana a gabana.
Yace wallahi yanzu takarda ya samu Oga an mayar dashi controler na costom baki daya na Nigeria.
Nima murna nayi sosai nace masha Allahu kai ashe abin farin ciki ya samay mu baki daya yace wallahi maryam.
Yace waiko kin san jiya fa yai min magana a kanki yace yana son ki fadada kasuwancin ki zasu taimaka maki a baki daga cikin kayan da akai Option dinsu ki sara ke ma ki samu.
Amma wai na tambaye ki wani kike bukata daga cikin kayan sai na manta zancen faduwan Aisha yasa na manta da komai ban fada maki ba.
Mun dan dauki lokaci a wayan muna magana dashi yana min bayanin yadda abin yake yadai ce na bari sai ya dawo gida zai karasa yi min bayanin komai.
Har zamu kashe na marairaice nace dama yanzu nake son kiranka don Allah zan dan fita na shiga kasuwa ne.
Yace may kuma zaki sawo maryam kin san fa kudi ya kamata yanzu ki hada wanda zakiyi business don kin kusa zama big hajiya.
Nace ba kaya zan saro ba kayan abinci nake son sayowa kawai.
Da mamaki yace kayan abinci har yaushe na sayo komai a gidan nace ba wanan ba baban Abba baki zanyi shiyasa nake son sayowa.
Dan shiru yayi yana mamakina yace baki daga ina kuma maryam nace daga waje .
Ikon Allah yace to adawo lafiya ai zaki iya fara driving da kanki ko sai ki fita da motar ki ?
Nace tare da yar sokoto zamu fita yace hakan yana da kyau sosai sai kun dawo.
Ban san Umma tafito ba tana tsaye take cewa baki zakiyi yau gidan maryam ?
Najuya ina murmushi nace eh Umma yau masu gidan zasu dawo daga tafiya shine zan girka masu abinci.
Masu gida ta tambaya cikin mamaki ?
Ban bata wani dogon amsa ba don nasan ba ganewa zatayi bana dai ce eh afili kawai.
Nai mata sai na dawo ina sauri sai gidan yar sokoto nai mata bayani kasuwa zata rakani mu sayo kayan abinci zanyi baki ne.
Bata bata lokaci ba muka fice daga easthe din mu sai kasuwa tafini sanin kayan fita kunya don haka itace ta dinga zaba nawa biyane kawai.
Mun dawo gida a gajiye da kayan mu niki niki har cooler manya guda biyu na fita kunyan baki saida na sayo muna.
Mun dan huta yar sokoto ta leka gidan ta bata dauki lokaci ba tadawo tare da anty hauwa muka fara aiki sosai.
Abinci mukayi naji da gani kamar zamu tari wani gwauna sai yamma lis muka gama komai mun zuba a cikin manyan kuloli na alfarma sai kuma na shiga aikin gyara guri.
Na sayo kayan kamshi masu kyau da kamshi har sabbin labule saida na saka ko ina gidan ya koma neat dashi.
Sai tambaya suke wai wasu irin bakine zasu zo haka maman Abba wana gyara haka kamar shugaban kasa zaizo.
Amsa daya nake basu shine baku sannu ba amma sunan tafe munyi waya dasu.
Baban Abba yana shigowa gidan yaga yadda guri ya juye mai gwanin ban sha, awa ga kulolin tap da abinci masu dadi anjera na abinci sai plates kusan ashirin da dan kai ajere abin sha ba adadi.
Yake cewa rangas yau wasu irin bakine haka zamuyi maryam amsa dana ba Umma nabashi shima.
Masu gida ya tambaya da mamaki nace mashi eh kai kawai ya kada min batare da yai wani magana ba don ya fahinci da mutane na nake nufi.
To amma ta yaya zasuyi suci wanan abincin dana girka haka agidan yace zamu gani ai yau gamu gasu.
Har dare su yar sokoto ana lekowa ko zasu ga bakin sunzo su lakaci arziki amma shiru sai hiran mukeyi.
Takasa kannewa tace amma dai bakin sun fasa zuwa ne ko aiko da wanan aikin da mukasha ko basu zo ba da sun biya mu wahalan mu.
Nace sai dare zasu iso don jirgin dare ne zai sauke su sukace komai dare zasu zo ai.
Karfe tara da rabi na tura yara suka kwanta har Umma ranan nace da ita don Allah ina son a kwanta da wuri don akwai baki a gidan.
Kallon mara hankaline suka fara yi min don abina ya zarce na mai hankali.
Goma da rabi gaba dayan mu sai wani irin mugun barci muke ji kowa ya shiga shirin kwanciya ba baki na babu dalilin su na gyara ko ina na falon tas baban Abba shine ya kashe wuta ko ina ya kulle gida don ni barci nakeji sosai saboda aikin da muka sha da rana duk nagaji.
Can cikin dare kamar a mafalki nake jin hayaniyan mutane kamar gidan duk ya cika da suratan mutane amma kuma na kasa tashi kamar an daure ni sai na fara jin motsin plates ana cin abinci ga kamshi dadi ya gauraye gidan.
Da safe baban Abba da ya rufe gida yana min dariyan keta a ranshi na babu wanda zai zo nayi barnan abinci saboda haukana.
Ai zaiga yadda zanyi da wanan tulin abincin dana girka haka mai uban yawa, ya kulla a ranshi sai yai min sheri sosai da safe.
Sai dai may yasan dai shine ya rufe gidan da hannun shi kuma anan yabar komai dana girka amma yana fitowa zuwa sallah sai yaga wayau babu kulolin babu dalin su a falon.
Juyawa yayi zuwa kitchen do yaga kona fito da dare na kwashe su ne sai ya samu gasu aje anci komai naciki ga gorunan drinks nan ansha an aje su a gefe daya.
Ikon Allah yace yaushe yai barci haka har baki suka shigo gidan bai sani ba har akai wanan didiman duk yana barci.
Kai amma dai ba mutane kadan bane sukai wanan hidimar haka mai yawa ikon Allah.
Ko da yadawo daga sallah ina zaune saman salaya na ina addua yashigo yana zama yake cewa maryam ashe bakin naki sunzo ne daren jiya ban sani ba ina barci ?
Nace ai na fada ma daga tafiya zasu dawo sun iso ke nan ashe ya juyo da mamaki yana kallo na yake cewa ke baki masan sun iso ba ke nan nace barci nayi mai nauyi wallahi amma dai sai naji kamar a mafalki sun shigo da dare.
Allah ya kyauta yace ya koma ya kwanta don ranan sati ne ba aiki nima haka yasa a inda nake zaune nakai kwance saman sallaya na.
Sai barci ina cikin barci nagan ta wai tashigo tana murmushi a fuskan ta ta zauna a bakin mirro na tana ce min yaya bayan rabo?
Na amsa da lafiya lau anty yaya hanya yaya yan uwa tace alhamdullahi mun ma zo dasu baba sunzo suga gida su koma don yafi gane ma zaman su can yanzu.
Nace Allah sarki ashe hardasu baba akazo tace eh ai yana godiyan girkin da akai masu sosai naji matukar dadi maryam yadda kika karama mu nagode hakika ke yar uwace tagari abin alfahari ga wanda ya samay ki.
Halinki na alheri yasa nake kara son al,amarinki a raina Allah yai muna jagora ga alamarorin mu nace amin anty.
Ta mike tana cewa ga tsaraban ki nan dana yara sai dai naga makwabtan ki sun tayaki aiki ga nasu sakon nan a dan karamin leda kiyi min godiya a furin su.
Nace mun gode Anty Allah ya bamu hakkurin zama a tsakanin mu daku tace tama bamu sai dai ya kara muna maryama.
Zamu dauki lokaci mai dan tsawo da iyayyen mu gidan nan kafin su koma koda yake ma ba wai zama zasuyi ba na dindindin don zasu dan zagaya dangin mu a cikin kasan nan da fatan zamu samu halarci a gurin ki sai kin kara jina yaran ki suna gaida ke sunji dadin girki ki wallahi.
Daga haka tafice daga dakin ban dauki lokaci mai tsawo ba kukan Nusaiba ya tayar dani naje na mike ne nai karo da wanan jakar kayan data kawo min a mafalkin