Showing 21001 words to 24000 words out of 115099 words
Chapter 8 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
sai dai bata dakin a lokacin shima Abba ya falka nace a,a ina kuma Indo ta shiga ne wai na bude bandaki bata ciki.
Nafito falo sai lokacin naga kofan back yard a bude can na nufa ina kiran ta amma ta shagala da wasa ita kadai.
Ina lekawa tana magana ita kadai har da dariyan ta tana nuna wani abu kamar mai dariya da wani.
Na dan dade tsaye ina kallon ta bata san ma ina yi ba har tana nuna yatsa tana dariya tana fadin la bagashi can ba gashi gashi gashi hannuta daya a cikin bakin ta dayan ta rike buta dashi sai surutu take tana dariya irin na yara.
Tsawa na daka mata sai ta zabura nace ke Aisha wani shirmay ne kikeyi ke kaidai haka a gurin nan tun dazu mazaki bar gurin nan.
Sai naji tace mama wallahi nafi yaron nan iya alwala kallon mamaki ne mata nace yaro wani yaro kuma?
Sai naga ta kalli inda bango yake tai shiru tana dariya nace maza ki bar gurin nan har na juya zan dawo falo sai naji ta sa dariya tana cewa bagashi ba hakka ake wanke fuska tana kallon sai saitin katanga inda bango yake na kara daka mata tsawa sai da ta kadu nace oyya taso mu shige daga ciki.
Ina mai bin ko ina da kallo amma babu komai a gurin na tasa ta gaba sai na dauka shirmay ne kawai na yara take min .
Tun wanan lokaci take zare jiki gurin ya zama mata gurin wasan yaran nan zata taita gwalanci irin nata na yara sai na kwalla mata kira ko in bubugi kanta tashigo daga ciki gurin yan uwan ta.
Anjima kadan kuma bai hana ta mike ta sace jiki ta koma gurin wasa wasa ta hada kayan wasa irin na yara can zata zauna tai ta faman surutu ita kadai tana jera kaya tana yan dariya.
Abin ya fara kaimin ko ina wallahi haka yasa na tura su gida Anty nace suje suyi wasa da yaran ta a can.
Baban su bai dawo ba sai da yai kwana uku ya dawo muna falo zaune muna hira yai nocking na bude kofa tsaye yake cikin kayan kakin shi.
Na dan saki murmushi nace sannu da,dawowa yace yawa barka da gida yaran najin muryan shi sukayo kanshi suna mashi oyoyo.
Harda Nusaiba da bata iya magana ba tana koyon tafiya a lokacin ta nufishi ya cabe ta.
Nan ya zauna falo dasu suka shiga shirmay su ya na gurin na kawo mai abinci ya ci sai gashi yau Aisha may matukar son daddy ta gashi ya dawo amma bata tsaya ta kan shi ba tana can ta sulale ta koma back yard gurin wasan ta.
Sai da Baban ya shiga wanka ne na farga ai bata falon nace ina Aisha Abba yace umhumm.
Namike a hasale Nusaiba na a hannu na tana shan nono na nuf bayan na samay ta kace kacekace ta baza kayan wasa irin na yara tana ta faman suraitai ita kadai.
Rankwashi nakai mata tare da shuri da kayan na,watsar dasu ban san cewa hakan babban kuskurena bane kafan da nai amfani dashi ne naji yakoma min kamar turumi ban iya daga shi sai kuka takeyi tana waigen gurin dakyat nake iya daga kafana na tasa ta gaba muka shigo falo tana tsala inhu hankalin ta yana kan kayan wasan ta dana watsar can gurin kwata inda ruwa kebi.
Zan shiga falo ne naji Nusaiba dake hannuna ta tsala wani irin ihu daga hannu na kan ta ya koma baya kamar anja mata suman kan ta.
Nace subbahanallahi na kama yarinyar ina dube dube babu komai sai ihu take yi a razane.
Jin kukan su yai yawa baban da ya fito wanka yana daure da towel yafito falon yana cewa kai kai wai yaya hakane may nene wai haka please.
Nace bugunta nayi bata da gurin wasa yanzu sai backyard din can ta mayar dashi kamar dakin ta wallahi.
Shine na watsar da kayan wai shine takewa kuka yace toke maryam inbanda abinki ana hana yaro wasa ne ?
Nace haba duk fadin falon nan bai isheta ba sai ta tafi baya inda babu kowa in wani abu ya samay ta fa acan?
Wani kallo ya,watso min yace may zai samay ta kuma acan din ke ti shiru kinji princess kyale mummy yau bakin halinta ya tashi ne ga Nusaiba ita kuma sai faman ihu takeyi a hannu na.
Ya juya gurinta bayan Aisha ta zauna a saman kujera tai dan shiru amma idon ta yana kofan back yard din yace ita kuma wanan may takewa kuka hakane wai ?
Nace ban sani ba ban san may ya firgitata ba gani nayi kawai ta tsala ihu haka kawai yace tsoron dukan da kikai wa Aisha ne mana yasa ta kuka ya juya yashige ciki.
Da kyat na samu tai shiru ta kama nono sai dai kuma a take naji jikinta yai zafi radau ga kafata dake ta min zogi kamar bargona zai tsage daga ciki wani irin azaban ciwo ke damuna a lokacin.
Yafito ya zauna falon remote ya dauka yana canza chanel ya kawar da inda nakai na kira,an Abba da dama tashan ya ishe shi ba dama ya canza don na hana ya sauke ajiyan zuciya.
Nace Baban Abba jikin Nusaiba fa yai mugun zafi sosai ya ce may kuma ya samay ta ba yanzun take wasan ta ba nace kila kukan da tayi ne ya saka mata zafin jiki.
Dan tsuki yaja yataso daga inda yake yazo inda muke zaune yakai hannun shi saman wuyan yarinyan.
Wani irin mugun zafi yaji jikin nata yayi yace wai wai ashe sosai ne haka zafin.
Tana da sauran magani ne ki bata nace wallahi wanda ka sawo muna ranan na nemi ledan gaba daya na rasa inda yake.
Tsuki yaja yace bari na fita na samo mata magani yace yaran suzo ya fita dasu Abba yace yana kallon tom and jerry ba zai tafi ba.
Suka fice shi da Aisha din jin kafana ya matsa min nace ya sheka ya fadawa Baban shi a sayo min maganin ciwon kafa ko na jiki.
Na shimfide yarinyar na kama massage din kafan nawa da hannu ina bisimillah in tofa in kai daga sama zuwa kasan kafa in yarfar magani ne sosai na ciwar wata haka Baban mu yake muna a gida idan bamu da lafiya.
Sai ko Allah da ikon shi naji kafan ya tsagaita min kamar an zare min allura a jiki naji.
Na gyarawa yarinyar kwanciyar ta namike don kafan nawa ya lafa zuwa wanke kayan uniform din shi daya dawo dashi yanzu ya cire.
Abin mamaki wai kayan wasan da na,watsar naga an kwashe daga gurin kwata an mayar inda suke da farko.
Na dade tsaye ina kallo na jjuya falo cikin mamaki nace Abba yanzun Aisha duk dukan dane mata kan backyard din nan sai da takoma gurin ashe ?
Yadan juyo duk da hankalin shi naga tv yace yana kada yatsan shi no no mama Aisha bata tafi can ba tun dazun tana ana zaune tare da ni.
Da mamaki na juya zan nufi gurin kayan wasa sai naji kamar murya cikin hasala ance kada ki soma ki taba masu kayan wasan su shine fa arzikin yaro kada ki watsar da arzikin yarki.
Cak naja na tsaya ina dan waige waige babu kowa a gurin gashi sha biyu saura a lokacin.
A,uzu bikalamatil lahi tamatt min sheri minhalak.
La ilaha illah antta subbahanaka inni kuntu minal zalimin.
Kamar ance min humm naji na juya ban taba kayan bs don warning din da akai min.
Cikin karfin hali ban bar gurin ba na wanke kayan na shanya duk zuciyata cike da tsoro tab.
Sun dawo sayen maganin na bata maganin tasha sai kuma amai ya biyo baya haka na wuni da ita ba lafiya Aisha kuma ta sulace ga uwar rana amma ta koma gurin wasan ta ta hada zufa tai sharkaf amma bai sa ta fita daga gurin ba.
Ganin na ba Nusaiba magani jikin bai sake ba nai shara dauko dan karamin cup nai addua aciki na bata tashs na shafe ta dashi.
****** ********* ******
Da yamma sai ga Anty sun shigo da sabuwar makwabciyar mu suka gaisa da baban Abba dake falo kwance nan suke ce min sun biyo min ne muje mu gaida yaron nan john da aka dawo dashi asibiti.
Na fada mashi yace sai mun dawo nan nabar Nusaiba tare dashi da take barci.
Mun shiga mun samu yaron kwance saman dogon kujera sai dai yana ganin mu yai zubur ya mike kamar yai mamakin shigowan mu kowa na gaida shi yana amsawa amma ni ina gaidashi sai ya mike yabar falon.
Mafalkin da nayi dashi ne ya fado min a rai nace wata sabuwa kuma may haka yake nufi kuma ?
Muna nan zaune maman su tana muna hiran abinda ya samay shi ne take cewa.
Tana barci taji ya kwalla ihu tana bude ido taga yaron kamar an shake shi a bango wuya ya kare idanuwan shi sun firfito waje tace kai bari naga tashin hankali.
Exactly yadda nagani a mafalki haka ta zaiyana muna ya faru da yaron duk sai nasha jinin jikina na kama bakina nai gum ban fadawa kowa komai.
Mun dawo nashiga gida su kuma suka suce nasu gidajen suna magana akan zancen unguwar.
Wasa wasa jikin Nusaiba yaki dadi haka muka kwana da ita ba dadi washe gari tunda safe muka kaita asibiti ganin likita.
Sai gashi an bamu gado wai bata da jini a jikin ta haka na dole na zauna asibitin shi ya koma gida ya dauko muna abin bukata tare da nemo jinin da za,a kara mata.
A gidan Anty ya bar yaran yace don Allah su zauna gurin ta ya rufe gida ya dawo asibiti gurin mu.
Nan muka wuni dashi sai yamma akasa mata jinin shi da aka diba aka kara mata sai da,dare sosai ya dawo gida ganin jikin yarinyar yai dan sauki.
Yana falo zaune ya hada tea yana sha yaran suna gidan Anty can zasu kwana gurin ta.
Motsi yaji kamar an bude kofa ya dan tsaya ya saurara can yaji kamar kofan ban daki ne aka buga a lokacin.
Mikewa yayi ya duba babu kowa a gurin saiya dawo ya zauna can yaji motsi ana diban ruwa a roban ruwan mu dake baya kamar yadda ranan naji.
Gaban shine ya fadi ya mike ya nufi gurin a hankali sai baiga kowa ba ya rufo kofan ya dawo ya kwanta saman dogon kujera.
Yana ci gaba da kallon film din da akeyi a tv sai yaji alaman wanka akeyi sosai yake jin ana wanka ana watsa ruwa kashe tv yayi yana saurare tabbas mostin ana wanka yake ji ya nufi ban dakin yaga gurin a rube kamar yadda ya jawo shi a baya.
Ya dawo ya kwanta saman dogon kujera bai dade ba barci ya dauke shi a gurin .
Can cikin barci yaga wata mace fara da,suma har kasa yana jan kasa yatsunta zara zara dasu tana tsaye a kan shi ga yaran ta duk cikin fararaen kaya sun kai kusan su goma tana tsaye saman kanshi sun zagaye shi tace.
Bawan Allah katashi ka bamu guri kun tare muna guri kwanciya kun hana mu shakat damu da gidan mu kunzo kun damay mu matar ta duko kamar zatai mai kiss yai zubur ya falka tare da dan ihu.
Ya juya ko ina babu kowa a falon sai shi kadai take ya hada wani uban zufa lokaci daya tsam ya mike tare da daukan gilon shi da yazo dashi ya shige daki ya rufe.
Jikin shi sai kaduwa yakeyi yace may haka ke nufi ne wai kenan maganan maryam gaskiya ne koko itama dai mafalki takeyi take ganin haka ?
Haka dai ya kwana gidan a,wahalce sai gabanin asuba ya samu yai barci sai motsi yakeji a cikin gidan.
Yana tashi da safe ya shirya sai ga anty Hauwa ta turo akawo mai breakfast tace namu da zaikai muna ta hada idan ya tashi wucewa yazo ya dauke su zasu su duba mu suma ita da makwabciyar mu.
Yagama yai wanka ya shirya ya biya ya dauko su sukazo asibitin tare dasu.
Sun samu Nusaiba tana barci ya dade a kanta tsaye yana kallonta yai muna sallama yace zai tafi ya leko office sai ya dawo.
Yace ko ya tsaya ya mayar dasu gida ne suka ce a,a zasu dan tsaya sai two zasu koma gida don yara na makaranta kuma yau akwai lesson basu dawowa da wuri sai four.
Nan muka zauna dasu sai hira suke zuba min kan maman Stephen da yaran ta bakuwar mu akwai surutu take cewa ita fa yaron tsoro yake bata idan ta kalleshi takanji tsikan jikin ta na tashi mata.
Mukai mata dariya nace kai wanan dan yaron Anty kawai dai don suna arnane kike ganin haka kila.
Tace ita uwar ma wallahi kanta wani kala take kallon ta aini da muka,shiga bakiga na matsu mu taso ba.
Sai muka saka mata dariya gaba dayan mu yadda ta zage tana aibanta matar mutane nasan halin yan sokoto da kyamar marasa sallah tun farko don su ko agaban su zasu ke arniya ta fa ko shi kafira ta bata sallah ai.
Sai zuwa wani lokaci sukace su zasu koma nace wa Anty Hauwa don Allah ta kula da Aisha nan nake fada mata abinda nake ciki da ita a gidan.
Makwabciyar mu yar sokoto yadda muke kiranta tace ke ke mutu wallah inji baki taba kayan ba nace ai danaji haka ban taba ba.
Tace ai duk yadda yaro yatara kayan wasan shi kibar shi sunan wallahi don ance yadda yaro ka tara kayan wasa haka yake tara arzkikin shi.
Idan kuma uwa ta zubar ta zubarwa dan ta da arzikine na nace oho shiya tace kada ki zubar da arzikin yar ki ashe?
Yar sokoto tace ni walleh kun ma bani tsoro wallahi Anty Hauwa tace to ai gidan ku da kuke ciki kafin ku koma wani lokaci cikin dare sai kiji kamar a,kunna wuta har kida ake sakawa wallahi.
Tace lokacin da muka dawo ba mutane da yawa gidan nan naku yana da ban tsoro sosai.
Tace yadda naji ance ai unguwar wai tsohuwar makabarta ce aka murje shi bayan yai shekara arbain akai quarters din gurin.
Yar sokoto tace aiko wallahi yau kun kashe ni wallahi kila ban kwana gidan nan muka sa dariya nace ina zaki kwana tace ai gara na dawo saman titi na kwanta da naga sanan mugun abin.
Nace ai addu,a takobin mumuni ne nidai nasan insha,Allahu ina masune a gidan mu to musulmaine don naji suna karatun kur,ani.
Tace na rabaki wallah inda wa yan nan na suka ganin mu bamu ganin su kinga ana zaman arziki a haka.
Dariya muka kara saka mata yadda take hausanta tsakani da Allah ita bata ga abin dariya ba aciki.
Mukai sallama suka tafi suka barni lokacin jikin Nusaiba ya kara tashi sosai tana ta kuka na rasa inda zan saka kaina gashi ni kadai ne a asibitin garin motane ban san kowa ba kuma ban ma iya ko kai kaina gida a lokacin don ban san ko ina ba.
Muna cikin haka sai ga Baban Abba ya shigo tin daga nesa yake kallon yadda nake fama da yarinyar ya iso yana cewa yaya ne may yafaru ne wai kuma?
Nake fada mai tana barci shine kuma ta tashi haka yanzun tana fitina yace bari yaga nurse yai masu complain.
Sai gashi ya dawo da nurse ta dan dubata tace ai lokacin aluran ta ma yayi abata magani sai ai mata allura dayani.
Haka yasa ta dan samu ta koma barcin ta ta daina fita yana gurin mu har dare yace zai koma gida nai mashi sai da safe ya tafi.
Zance yau abinda yaji gidan yafi na jiya don yana kwance falo barci ya dan dauke shi tv yana aiki aka danne shi ya kasa koda motsawa sai da yaita addua yasamu aka sake shi ya mike ya hada zufa sharkaf dashi.
A zuciyar shi yace yanzun kan na tabbatar da maganan maryam tana fadi ina ganin laifinta ashe da gaskiyan ta dole ne yasan abinyi tun wuri tun ba,a samu matsala ba.
Cikin dare ma bamuyi barci da dadi da Nusaiba ba washe gari da yazo yaje gun likita sai ga likitan yashigo round nan ya dubata yace ikon Allah.
Ai dole tayi kuka ba jini a jikin ta kamar ma ba,a kara mata ba da farko hankalin mu ya tashi yace sai an nemo wani jinin dole.
Nan uban yafita zuwa neman inda zai samo jini gamu a garin mutane na kira babana na fada mai yace nai ta addua Allah zai kawo mata sauki.
Na kira Umma ita ma na fada mata hankalin ta ya,tashi tace maryam kin ga abinda nake fada maki ko?
Yanzu da anan kuke ai za,a samu jinin kara mata ba sai an wahala,ba wanan wani irin ciwo ne ace ana karawa mutum jini yana zukewa.
Tai min Allah yakawo sauki muka kashe wayan muna nan zaune sai gashi da abokan aikin shi mutum uku za,a auna jinin su a gani ko zaiyi wa yarinyar akara mata.
Munyi sa,a ansamu jinin wanda yai