Showing 63001 words to 66000 words out of 115099 words
Chapter 22 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
lokacin.
Sai bayan kwana biyu na daina jin mutuwan jikin dake damuna wanda ban san dalilin yin sa ba lokacin.
Alhamdullahi don Umma kan har baki ta fara samu a lokacin sai dai sai mutum ya saurara sosai zaiji may take fadi.
Amma dai ko hakan ma mun godewa Allah matar da ke kwance sharkaf da ita yau da bin bango tana iya fita zuwa falo da kanta batare dana cicibeta ba kamar baya.
Matsala daya ke ci min raina a yanzu shine rashin dawowan gida da baban Abba baiyi sai yaga dama kuma koda ya dawo din ba lalai bane ya kulani nida hoto daya muke a gurin shi.
Duk yadda mutum ke tunanen hatsabibancin mace Hanna ta wuce gurin don tashiga tafita ta rabashi da kowa nashi a yanzu baya ganin kowa da daraja sai ita da yan uwanta da sauran tarkacen ta.
Ko nawane zai iya kashe mata shi batare da yaji wani darr ba akai amma mu a gida bai damu da damuwar mu ba ko kadan.
Kullun cikin ci da shan kaidin ta yake har ma da shafawa idan ya kwana a gurin ta.
Hakan ke kara dauke mai hankalin shi gare mu yadda take bukata gani koda yaushe.
Na gode ma Allah da bai saka min wahalan akai ba don ni harkan gabana kawai nasaka agabana.
Yau nagama abinda nakeyi nace bari na shiga gida makwabciyar mu yar adamawa da ta haihu nai barka.
Can na hade da su yar sokoto da anty hauwa aka zauna zaman hiran duniya.
Har akazo akan zancen kayan mata sai lokacin na tuna da wanda nake dashi.
Nace aiko ina dasu dana sarara kwanaki kuma suna da kyau duk matan dake gurin suka shiga tambayana don Allah mai kyaune maman Abba ?
Nace ku gwada ku gani zaku bani labari ai na dinga gidada abin kamar nasan amfanin shi ni.
Anty hauwa tace kai amma maman Abba ke muguwa ce yanzu kina da wanan kayan haka kikaki fada muna kika barmu muna sayen na banza a waje.
Nace ban dade da na fara sana, an ba shiyasa baki sani ba nan dai muka aje magana da yamma zamu hadu kowa yaganin.
Ina shiga gida na samu baban Abba da yai kwana uku bai gida ya shigo na samu ya shiga wanka.
Na zauna falo gurin Umma da Nusaiba da bata fara zuwa school ba suna kallo.
Nace Umma akawo abinci ko kai ta gyada min alaman a, a nace tau bari na dauko maki fruits kisha ko.
Namike zuwa gurin fridge na duka ke nan naji muryan shi yana fadin ina kika fito haka.
Sai da na dauko ledan fruits din na kalli inda yake tsaye ya rike labulen shiga inner room din mu.
Nace daga gidan yar adamawa nake ta haihu tun jiya ban samu shiga ba sai yau.
Yanzun abinda kikaga dama kikeyi gaban kanki ko don kin mayar dani mutumin banza ko ?
Ita Umma da kika fita kika bari agida ita kadai wakike son ya kulata idan tana bukatan wani abu.
Nace ikon Allah baban Abba akan Umma kan banda maraina gareta don baka san cinmu ba baja san shan mu ba haka kuma bakasan tashin mu ba.
Oho shiyasa kike bugun gaba don ban sani ba ko nace naga bai dace har ka fada min haka bane idan ni ban fada maka ba.
Yace nagane yanzu wuyan ki yayi kauri maryam kina ganin kamar ban iya rabuwa dake ne ko may ?
Da mamaki na dago kai ina kallon shi don jin furucin shi nace rabuwa kuma na yaushe kuma.
Ai sheda kawai ya rage ka gwadawa duniya na ka rabu damu ni banyi magana kan zubar damu da kayi a garin mutane ba sai kaine zakace wai zakai min wanan.
Ai dai duk abinda kakeyi Allah yana ganin ka tunda karuwan ka tafi mu daraja da kima a furin ka.
Nufoni yayi gadan gadan da nufin ya mareni ya daga hannun shi sai yaji hannun nashi yaki sauka ji yake kamar an rike hannun nashi daga baya.
Gani nayi ya juya baya kamar yana kallon wani abu sai dai babu kowa a gurin yayi yayi ya sauke hannun nashi amma ya kasa.
Sake shi nace rai a bace sai kawai hannun nashi ya sauka daga makalen da yake nace barashi ya buge barshi.
Take idanuwana suka sake laune sun rine sunyi jajajir dasu nace cikin wani murya da ba tawa ba yau daka mareni da ka kwana a lahira.
Kayi kuskuren daga hannuwan ka ka mari godiyar mu duk mutuncin da halarci da take maka tana maka bauta da mahaifiyar ja da ka watsar saboda karuwan ka hannan.
Hanan hanan hanan ko ?
Zaku gane kuren ku daga kai har ita idan baka fita harkan wanan karuwan taka ba.
Ka sani tana gab da kashe ka idan ta samu abinda take bukata daga gareka don ymunafukace bakai kadai take hulda dakai ba idan ka musa ka tafi gidan yanzun nan kaganan wa idon ka ko wacece hannan din.
Zata bada kai watarana nan bada dadewa ba yau kaje gurin ta karfe sha daya na dare zaka san ko wacece ita.
Ina fadin haka na zube gurin a somay a kasa Umma dake zaune a gefe duk abinda ke faruwa a gaban idon ta sai ta fasa ihu da kuka tana son tasowa zuwa gare ni sai dai jikin ta da nauyi bata iyawa.
Shi ya dauko ruwa da jan shi ya zuba min na sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi zubur namike ina mayar da numfashi a hankali tare da dan waige waige.
Ina ganina a kasa abinda ya faru na zuwa mari na da yayi ya fado min a rai.
Take na karasa mikewa zaune da kyau nakai tsaye kasa tafiya nayi na koma saman kujera na zauna.
Kaina jin shi nake kamar zai tsage min gida biyu don ciwon da yake min.
Wayana dake saman kujera ne yai kara shi ya dauki wayan a rikce yake a lokacin.
Muryan mace yaji kuma da bakuwar nomban da ba suna akakirani ya amsa da hello matar ta ce don Allah maryam nake nema please.
Maryam bata da lafiya mijin take magana matar tace idan ta falka ka fada mata matar tsohon shugaban kasa ce takirata tana son magana da ita please.
Layin ya mutu da mamaki ya furta a fili matar tsohon shugaban kasa maryam ?
A ina maryam ta san matan ko chairman balle matar shugaban kasa masu fada aji a kasan.
Mamakine sosai ya rufe shi a lokaci daya yana cewa a ran shi kai al,amarin maryam fa ya fara bani tsoro gaskiya.
Ga yadda ya kasance da ita a yanzu gaban shi yaga yadda ta juye takoma kamar namijin zaki.
Ga hannun shi da aka rike yana mai wani irin zugi kamar zai balle mai don zafi da ciyon da yake mai ga Umma dake kuka wiwi a gaban shi abin ya taru yai mai yawa a lokaci daya.
****** ********* ******
Hajiya Aisha dake zaune tana kallon yadda ake kwashe kujerun gidan ta tace tabbas yarinyar nan mutunce ke nan da gaskiya.
Tunda ga mijin ta har munyi magana dashi ya tabbatar min da tana kwance bata da lafiya.
Taso ta gaiyace ni zuwa dakin tane na duba mata idan ba sihiri a cikin sa sai ta bar kayan dakin nata dama duk ko ina na gidan.
Gashi yau har taji sauki ta fita zuwa gidan marayu kai ziyara kamar yadda takeyi acan baya.
Ta dade idan tana barci tana ganin fuskan wanan yarinyar ana fadin zata taimaka mata itace zata taimaka mata a dalilin tane kawai zata iya samun sauki.
Sai gashi Allah ya kawo mata maryam har gida da kan ta ta taimaka mata sai dai kuma yarinyar taki karban komai daga gareta ko abin gidan bata yarda ta taba komai ba.
Dole ne ta nemo gidan wanan yarinyar a duk inda take a cikin garin nan ko kasan nan yazama wajibi a gareta don tanemo yarinyar na don lafiyan ta dana yaran ta.
Mutunci da kamala da kuma tarbiyan da tagani ga yarinyar yasa taji son yarinyar ya shiga zuciyar ta farat daya a lokaci guda.
Wayan ta dauka takara kiran layin yarinyar har lokacin mmijin tane ya dauki wayan again.
Cikin kwantar da murya take cewa don Allah a wani unguwa kuke ne ina son na gantane please.
Bai tsaya tunanen komai ba ya fada mata uguwa da gida da yadda zata ce idan tazo gidan.
Ba bata lokaci ta shirya take cewa kanin ta da ta dauko yanzu ta aje shi a gidan ta don yanzu hajiya tsoron kowa take ji.
Bashir ka shirya mota zamu fita ni dakai ban son ka fadawa kowa fitan mu kasan yadda kayi ka kawar da kowa a get yanzu ganinan saukowa.
Asirtacen hanyan daba kowa yasan dashi a gidan ba tabi har tafice daga gidan su karimay basu sani ba.
Uguwar da zasu tafi ta fada mashi nan Allah yakawo su har gidan mu lafiya.
Baban Abba wanda yaki fita gidan don tsoro ga hannun shi dake ciwo yana son zuwa ya gaskanta zancen da yaji yanzu a bakina yanajin tsoro.
Haka ya daure don tabbatar da zargin shi ya nufi gidan hanna din bai tsaya sallama ba ya sakai dakin.
Suna kwance tsakiyan aikata masha,a da wanda take kira wai dan uwanta ne yasan mutumin farin sani don wani lokaci har tana sa sai ya taimakawa mutumin.
Ganin su a haka yasa shi rimtse idanuwan shi suka dago a firgice suna kallon shi juyawa yayi yabar dakin da sauri yafada motar shi yabar unguwar.
Ina kwance naji sallama a kofan falo da kyat na iya daga kaina ina kallon mai shigowa gidan.
Tana saye da bakin abaya ta yafa dan kwalin shi a kanta rataye da jakarta a hannun ta.
Umma dake zaune take gaiyawa jin yadda Umma ta amsa mata magana bai fita cikin daga hannu yasa ta fahinci umna din ba lafiya gareta ba.
Namike zaune da kyat ina gaida ita da mata sannu da zuwa lokacin ne kuma yarana suka taso daga makaranta suka shigo gidan.
Nace mama kece tafe shine baki kirani ba nazo kika taso tace na bugo waya ance baki da lafiya diyata shine na taso.
Nace ni lafiyata kalau ina dan murmushi a fuskana mamakine baiyyane a fuskan ta karara tace to yaya kuke nace lafiya kalau mama.
Mama kin dai ki koran mutanen gidan ki ko idan baki koresu ba sun kusa ganin bayan ki dake da dan ki Ahmed da zai dawo satin nan suyi shiri sosai akan shi don shine matsalan su dake, sauran diyan naki matane basu damu dasu ba sosai.
Ikon Allah inji hajiyan ke ko diyata duk a ina kika samu wanan labarin haka dan Allah nace nima ban sani ba na dai gani ne a tare dake kawai.
Ta gyara zama da mazaunin glass din idon ta da kyau tare da kura min ido sai wani hamma nakeyi kamar mai jin barci a lokacin.
Kafin tai magana nace mama Alhaji Ibrahim ya sha alwashin rabaki da komai naki a duniyan nan har rayuwanki dana diyan ki sai dai kuma da yardan Allah bazai taba cin nasara akanki ba don halin ki na alheri garesu .
Matsalan ki daya dasuke samun galaba akan ki shine sakaci da Ibadan ki da kuma saurin yarda da bokaye da malamai don dasu ake hada baki ana kara cutata maki.
Duk wanda kika gani a gidanki an riga da an saye shi da makuddan kudi masu yawa.
Aikin wasu sukeyi a gidan ki banaki ba kawai don sunfi ba da aminci ga wancan din dake biyan su fiye dake.
Kinga hajiya halira da itace ake kulla maki komai gashi kuma itace ta kusa dake sosai kin watsar da yan uwan haihuwan ki kin kama yan bariki ajikin ki.
Mama ki jawo yan uwanki ki saka ajikin ki zauna da abinki lafiya don sune naki naji.
Yan adam suna sakaci da zumunci a wanan zamani zumunci kuma ba abin wasa bane.
Idan kin bar gidan nan zaki shiga gida ki tabbatar da abinda hajiya harira ta kawo maki wata biyu da ya wuce antone wanan mugun abin a gidan ki don babu ke ba lafiya muddin wanan abin yana a tare dake a gidan ki.
Yanzun nan kisa Bashir ya shiga bayan ban dakin ki dai gurin da ruwa ke zuba zaiga katon dutse sai ya daga dutse duk abinda yagani ya dauke shi a kona akan ki da yaranki akai wanan sihiri wanda haka kawai zaki dinga jin haushin su kina hattaran su kiji baki son hulda dasu ko kadan.
Duk wanda yai maki aanan aiki nan da kwana biyu da kan shi zaizo neman gafaranki da bakin sa.
Abuna karshe yar uwarki halima dake lagos itace kawai nake son ki dan ja dabaya gareta ki rike sirinki a cikin ki don tana maki zagon kasa sosai a rayuwan ku.
Ni zan tafi lokacin kararu yayi idan kin tsare wanan abin dana fada maki da yardan ubangin ba abinda zai kara samun ki ki karbi wanan dake da yaranki kuyi wanka da hayaki kusha na barku lafiya.
Suuu natafi na koma saman kujera sai atishawa na fara sakewa mai karfi har sau uku na mike zubur ina dan waige waige Umma nagani zaune tana barci a saman kujera sai hajiya da ke zaune cikin damuwa ta kura min ido kawai tana faman yi min sannu.
Nace mama ni lafiyata kalau ba abinda ya samay ni fa kina min sannu haka.
Tace ai na sani amma sannu da kokari maryam nagode nagode kinji.
Kallon Mamaki nake mata don ban san may takewa wanan godiyan ba haka a gareni.
Wani atishawa na sakeyi again nace hajiya Aisha barka da zuwa tace yawa dawa nake magana kuma tace mukkadarasiya ce diyar Alhaji malam kike magana da ita.
Tace sannu dazuwa ko muryana sak ya koma kamar wata balarabiya dani nace yauwa hajiya.
Kin dai yi arziki mahaifina yasa hannu ga aikin ki amma ke ma baki da dama hajiya duk abinda ya faru dake kece sillar sa.
Zaki iya tuna baya lokacin da kika tafi wani kauyen kasan Ibo gurin wani hatsabibin boka keda kawarki Ajoke.
Wacce yau shekaran ta goma ke nan da mutuwa to tun wanan lokacin matsalarki ta fara.
A matsayinki na musulma da kika san Allah da Annabinsa kikaje gurin kafirai inda ake tsafi don kawai son duniya.
Ku bil,adam kuna da taurin kai sai ku sani ku take sani kamar yadda namu jinnu suke da taurin kai sosai idan an hadu da miyagun mu.
Wanan bokan ba kowa yasa akaiki furin shi ba sai makiyin ki dan uwan mijinki kuma abokin shi Ibrahim.
Sun hada baki da wanan matar data kaiki inda ya bata makudsan kudi masu yawa.
Da ace kin dogara ga Allah kin mika kukan ki gareshi da zakifi samun nasara da haske ga bukatun ki.
Da adam Allah zai mai falala yatsaya ga taimakon dan uwan shi musulmi, kina ziyaran asibitocin ku kina taimakawa marasa lafiya kina taimakon maraya ko dabbobi da zaki samu haske ga duk wani bukatan dakike dashi a gurin ubangiji.
Wanan godiyar tamu maryama boyar Allah ce da tana dashi zata taimakawa marasa galihu sosai a rayuwan ta sai dai kukukuku ta kada kai arziki bai zuwa gurin da bayi ke bukatan shi .
Hajiya tace don Allah wama kikace sunan ki tace sunana yana da wuya a gareku.
Hajiya tace yanzu idan ina tin wanan abubuwan dakika lissafo min kina ganin zan gyara tace dayafi maki alheri.
Waccan kawar ki Ajoke tuni aka gama da ita akan wani aiki da akaso tayi akan ku amma takiya.
Ku dinga sa tsoron Allah ga al, amarinku matan bani adam sun shaga da son duniya suna mantawa da komawan su ga mahaliccin su.
Macen bani adam zata bushe zuciyarta ta aikata ko maynene akan abokiyar zaman ta ko wani dan uwanta mutum wanda hakan ba daidai bane a garemu bisa ga koyarwa da manzo yai muna.
Akwai hanyoyi da dama da zaka kai ga nasarorin ka amma duk an watsar dasu ankoma ga hanyan shedan wanda dama shi gurin shine yaga ya halaka duk wani mumuni na Allah su kone a tare.
Nakima yana da sauki sosai gana wasu don ke neman zaman lafiya da maigidan ki da farin jini kikatafiyi bakice ai mashi wani mugun abin ba can.
Kuji tsoron Allah ga rayuwan ku akwai jinsin mi jinnu da aikin su halakar dakune kawai zuwa ga halaka duniya da lahiran ku ni zan barki don godiyar mu ta huta sai mun sake hadu wani lokaci.
Na sake wani atishawa mai karfin gaske har uku sai sannu Hajiyan take ta faman yi min duk umma tana ta sharan barcin ta ba aikomai akan idon ta ba.
Wanda nasan haka aikin sune kada taji sirin wasu ko taga halin dana tsinci kaina aciki a garin mutane.
Maryam na gode ni zan tafi sai kuma kin karajina ki min godiya gurin Alhaji malam.
Ban fahince taba na dai amsa mata da to mama insha Allahu zaiji take