Showing 99001 words to 102000 words out of 115099 words

Chapter 34 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt

16 Dec 2024

6656

cewa a, a Nusaiba yau alawa aka samu najiki shiru ?
Yace Umma kin fito ai na dauka barci kike da bangan ki ba a falo ?
Tace ina ciki ina lazumi ne bayan na idar da sallah.
Sun gaisa hankalin shi yana ga yara da suka samu kulawan shi yau shidai Abba da ba sabawa yayi da halin shi ba dawo yayi inda nake ya manne min ajikina tare da mika min nashi wai na bude mai.
Bayan na bude mai yaron yamiko min wai na diba nima naci na girgiza mai kai kawai nace ci abinka abba nagode Allah yai maku albarka.
Jin haka yasa Aisha dawo da gudun ta inda nake itama tana miko min ta wai nasa mata albarka.
Nace sha abinki Aisha Allah yai maku albarka nima babana zai sayo min mai dadi wanda yafi naku.
Tana jin haka tace wallahi mummy sai kin sha kada babakin ya kawo maki naki ki hana min.
Na karba na dan gutsura kadan nace mata na gode nace wai amma akwai dadi shima Abba yana ganin haka yace sai nasha nashi dole na dan gutsura na mika mashi.
Muryan shi naji yama cewa Nusaiba ke kai wa mummy tasha naki kada ta hana maki na baban ta.
Sai taki don akwaita da shegen rowa Umma tace o bazaki bayar danaki ba ko to maryam kada ki bata naki idan an kawo maki ke ma.
Can naji Umma tana cewa dashi yaya zancen naku akwai nasara a cikin sa ko har yanzu ba aikai iyaka ba ?
Jin haka yasa na kasa kunne a gare shi don naji mai zaice gamay da zancen nasu.
Yace bari Umma ai alamarin wanan yanzu tsoro yake bani maryam anya kuwa nan gaba ko ruwa nasha a waje bazaki gane su ga hanji na ba kuwa ?
Umma tace ga tsiya abin ya koma mata maita ke nan kake nufi ko may ?
Yace abin nata ne akwai abin alajabi sosai a cikin sa wallahi nan dai ya kwashe duk abinda ya faru daya fita yake fada muna.
Nace ai Jibrin bazai dawo ba don kunya bai bari ya kara zama a cikin ku kuma.
Nace ina gani ma nan bada dadewa ba kamar za, a watsa kune fa.
Dasauri ya dago ya tsura min ido nace haka ne zai faru amma aiko ka tafi controler bazai bari ka tafi ba.
Yace waye controler kuma nace Ogan naku mana shine zai zama Control wani sati da yardan Allah.
Kaima sai nake ga kamar zaka samu dan sauyi sai dai matsalan takardunka ne zai kawo tsaiko kawai.
Mamaki yayi yace kai maryam na barki inda na ganki don ba maryam dina bace wanan gaskiya ya fadi a cikin zolaya.
Nan dai mukai ta hira akan irin aikin su na rashin imanin da basu dashi wanda yake jawo masu matsala a karshen rayuwan su wani sai kaga bai gamawa da duniya lafiya.
Umma tace shine fa dalilin da mahaifinki lokacin da ya samu aikin nan yake ce min da zai samu wani da yafi wanan aikin da yafi.
Nace baba ai ba karamin masani bane shima zaman kauye ne kawai ke cuta mai ba, a sanin ire iren su sunan da yawa.
Maryam ina kika san haka ni zan fada maki akan wanan mijin ki din da kike gani irin taimakon da malam yai muna aiba kadan bane har Allah yasa na samu yakai haka.
Sai dana hafa har tara suna macewa shine nan Allah ya bar min dataimakon Allah dana mahaifinnki .
Murmushi kawai nayi Aliyu ya mike ta shiga daga ciki bai dade da shiga ba naji muryan shi yana kirana daga ciki.
Ina shiga abin mamaki mutum da muke kamar baisan daraja na ba shine wai yau ya rugumoni zuwa jikin shi.
Nokewa nayi ina fadin maye haka kuma yau yace ke tsiyanki ke nan wallahi da an dan taba ki yanzu ki kawo wani zance.
Nidai Allah ma ya cece ni kada su rabani dake su ce maki kuma ina wari nan gaba.
Dariya maganan shi yabani nace kai wani sabon sheri ke nan kuma da zasu rabani dakai ai da tuni sun rabaka dani tun lokacin da kake kwana gurin hanna.
Yace kai akwaiki da tashin tashin may kuma ya kawo zance wata Hanna can ni nama manta yaushe rabona da ganin ta wallahi.
Nace idan ba ta ai akwai wasu sabbin don ba fasawa za, ayi ba tunda kasawa rayuwan ka irin hakan.
Yace da ke nan idan ma ina yi aida kin gani kun fada ni ai na rufawa kaina asiri da tonon sila da ake min bibiya akai.
Nace dadai yafi ma alheri da wanan mugun rayuwan na alfasha murmushi kawai yayi yace wai ke su mutanen naki sune suka dakatar dake ne fa haihuwa haka komay ?
Naga da can baki ma yayewa sai da ciki amma yanzu ga Nusaiba har tana batun shiga na ukku amma shiru ?
Dariya maganan shi yabani don yaushe rabo danaji wani dadadan kalami haka daga gare shi.
Maza ke nan ba kunya garesu ba su ko kadan idan idon su yarufe kai da banza daya idan ya bude kuma ace da kai akeyi.
Nace nidai gani ka kirani bakace komai ba sai wani zance kakeyi haihuwa nice zanba kaina ko Allah zai bani idan yaso ni da hakan ?
Aini na dauka ma baka damu ba wa yan nan sun isheka kawai da muka samu da kai ?
Kai kajiki da wani zance ina bahaushe dan musulmai zance zuria sun isheni nace a zasu isheka dani mana sai sabuwa tazo ta haifa ma wasu kuma.
Baiyi magana ba sai ma kamoni da yayi zuwa jikin shi ya shiga shafa na kamar yau ya fara sani na haka yasa na dakatar dashi nace.
Amma kasan yaran basuyi barci ba dai ko zasu iya shigo muna daki fa.
Yace bake kika saba masu da hakan ba ko ina nan zasu iya shigowa kai tsaye nace kadai fadi sai dai ban ki ba in Nusaiba amma bada sauran ba.
Sai da yagama abinda yakeyi ba kunya yabarbi da jin nauyin Umma yai wankan shi ya fita daga gidan kafin magariba.
Nan ya fice ya barni ina najin nauyi da kunyan Umma haka dai na tsarkake jikina na fito falo naci gaba da aiyuka na.
Sai bayan ishai ne muna zaune da yaran Umma tafito daga dakin su tana cewa maryam dama ina son nai maki magana.
Nace Umma ni tace eh maryam ba wani abubane dama zance dake ne don Allah kiyi ta hakkuri da mijinki Maryam shi kadai Allah ya barmin nake gani nake jin dadi sai kuma yaran nan da Allah ya baku nake kara jin dadi a rayuwana.
Maryam ko bayan raina banyar da Babana ya kara wani aure ba a rayuwan shi muddin kuna raye.
Don baki rage ni da komai ba aduniyan nan na fada mashi kin min abinda ko nice na haife ki ya tsaya nan hakana.
Don Allah maryam kiyi hakkuri da mijin ki duk wanan halinda yake na rudin duniya nasan zai daina insha Allahu.
Nace cikin murmushi Umma ai baban Abba yayana ne ni ban damu da abinda yake muna ba don kanshi yakewa don duk abinda yake min yana gani kamar yaran nan basu da wayyo wallahi sun san komai.
Don haka ni ban sa zancen shi a raina ba balle har abin ya damay ni a raina.
Harkan gabana ma kawai ya isheni yanzu ban zancen komai ni a raina.
Tace nasan da haka amma dai kiyi hakkuri maryam ki dinga saka shi a hanya koda ba zai yi amfani da maganan ki ba dole dai wata rana yayi da wani.
Nace insha Allahu Umma na gode bazaki taba samuna da abin asha ba a rayuwana ba.

****** ********* ******
Yau kwana uku da zancen gurin aikin su bayan yafita daga gida ranan kuma ba fita aiki can sai gashi ya shigo duk a gidimay yake.
Yana cewa maryam muna da baki fa ga Ogan nan zasu shigo da iyalin shi yanzu yake min waya.
Bai gama magana ba mukaji horn a kofan gida alaman sun iso ko ke nan yanuna don horn din da akayi a kofan mu.
Dadtijone kamili dashi daganin shi ba mai son hayaniya bane sosai don yanayin shi ya nuna tafe suke shi da matar shi da yaran su uku.
Mun gaisa dasu a cikin mutunci ban zauna saman kujera ba ina zube a kasan ties din falon.
Sunji dadin wanan girman dana basu sosai har cikin ran su yace wanan ce malaman ya tambaya ?
Aliyu da duk ya kasa zaune a kasa tsaye yau ga sugaba da kan shi a gidan shi saboda dalilina.
Yace itace sir ikon Allah yace tare da nuna yar shi dake a zaune wacce nake gani da alama ita ce babba a cikin su.
Ogan yace nai farin ciki haduwa da wanan family din a rayuwa na da fatan Allah yasa mu kasance da junan mu a cikin amana.
Yace diya ta nazo da iyalina gareku ne don na mika godiyana akan taimakon da Allah ya nufa kikai min.
Don badon Allah ya kado ki cikin alamarin ba da bamu san iya iyakar inda abin zai tsaya ba.
Murmushi nayi tare da dukar da kaina kasa cikin kunya yace na zone da kaina muyi maki godiya har gida abisa amin cewan maigidan ki don sai da yardan shi zan shigo har cikin iyalin shi.
Nan dai yake mika godiya ga taimakon da akai mashi shida sauran abokan aikin shi.
Hannu naji na dan fara murzawa a lokacin da yake maganan sai hamma ya biyo baya again.
Gurin da yarsu ke zaune na juya nace mama hajo tare ake dake ashe anan kika zauna kuma ?
Matar Ogan tai dariya tace ai ba sunan ta hajo ba Amina take.
Umma tace Umm, Umm kyale ta ba ita bace akwai abinda tagani tare da ita tunda kikaji sun fadi hakan.
Ikon Allah inji matar ta mayar da hankalinta a gare mu sosai daga ita har kowa dake falon.
Nace mama hajo uwar ruwa in babu ke babu ruwa inda ke ruwa ya gyaru.
Sai wacce suka kira da Amina din ta fara hamma ita ma sannu a hankali kamar yadda nayi zamowa tayi kasa kamar yadda nake zaune muna kallon junan mu.
Nace ba, asan ki da barna ba kamar Inna doguwa inna uwar manya, inna uwa maba da mama wanda baida uwa yazo ga Inna.
Tace hakane ni da ina banbancin mu kadan ne don ni bani zama jikin mai muni kuma bani zama ajikin kazami sai wanda ya amsa sunan shi gurin kyawo.
Kadai kai nayi nace hakane mama amma yau sai gaki gaban malam Alhaji musulmi mai aikin musulunci bani baiyana sai inda yadace.
Tace nasani malam nakuma yi mamaki ganin ka a cikin wanan karamin gidan.
Muryan mu duk ya canza daji kasan na larabawane ko wani jinsi na wata nahiyar.
Nace shi musulmi ko kin manta duk daya suke a gurin Allah mahaliccin mu ?
Ai damu da karami duk daya muke ga Allah don Allah ne kadai yasan wanda yafi wani a gare shi.
Tace hakane malam nace kin fadi gsskiya yanzu may kike nema a jikin wanan boyar Allah dakike wahalwa haka.
Wani irin gyatsa tayi mai karfi kamar wacce ta koshi tace malam Amina godiya tace ban son naga wani bil, adam ya rabe ta ko kadan.
Shiyasa ko yaushe nake nisanta ta da kowa sai wa yan nan marikan nata kawai kosu don suna matukar son tane na barsu da ita da tuni nagama dasu.
Nace amma kin san kin shiga hakki ko hakkin daba naki ba kina cutawa boyar Allah.
Tace na sani malam amma Amina tana da abubuwan da nake son hutawa a cikin sa.
Nace tun ysushe kike tare da ita tace malam tun tana yar shekara biyu da rabi.
Ina matukar son mace mai yawan gashi kasani kamar yadda nake baka da gashi har baya haka nake matukar sha,awan mace mai gashi sosai.
Iyayyen ta sun kasance masu gyara mata kai akoda yaushe suna barin kan asake yadda jama, a zasu gani su yaba wa kwalliyan ta.
Nikuma a irin gurin nake samu ina shigewa a jikin mace ya zama gurin hutawa na.
Ina matukar son yaron da ake barin kansa a sake ko yaushe wanda ake yawan gyarawa a ko wani lokaci.
Kai ba yaro ba ma koda babbace idan tana barin kan ta a bude zan shiga na yi yadda nake so a raina don nan ne gurin hutawa na.
Zan iya hana mace aure idan makinyi sa, a kinyi aure zan iya hanaki jin dadin duniya watau haihuwa.
Idan ma kina haihuwan zan iya hana diyan zama a duniya ta hanya fito maki ta wani siffa cikin mafalki na kashe yaron.
Subbahanallahi ke kuwa musulmace hajo ?
Tace malam aika sani ko ta gurin sunana dakaji hajon ni sunana hajjo ruwa.
Murmushi nayi nace nasani amma a ruwa aka sanki ba zama a jikin mutane ba irin haka.
Tace malam ke nan amma aikasan ni a gurin keta ko ?
Haka kawai idan naga mace mai yawan sake jikin ta zanji na shiga jikin ta na dinga cutawa rayuwan ta kawai.
Wani lokaci zamu jona dani da karuwa kasanta gurin keta itama sai mu dinga saka mace tana abubuwan shedana don a zage ta kawai.
Muna yawan yin hakane ga yan mata masu sha, awan sake tsiraicin su ga wasu mazaje da sunan kwalliya kawai.
Amma mace mai yawan ibada bamuga guri ba ma balle mu zauna da ita don kariyan da takewa jikin ta.
Abinda bamu so shine mace mai yawa saka lalle ajikin ta don bama son warin shi.
Warin lalai yana matukar cutawa jinnu sosai munyi arziki matan yanzu basu son amfani da lalai wanan ne yasa muke matukar samun sauki gurin shige masu.
Da ace suna saka lalle koda a yatsun hannuwan su ne baza mu samu kafan shiga jikin su ba haka.
Amma yanzu Allah kadai yasan yawan matan da muke zama a jikin su wanda su basu sani ba muna matukar cuta masu don sun bar suna mai karfi da aka umurce su dayi.
Wanan hakana ne amma da ku shige su aida kun sanar dasu gurin matsa masu su dinga yin abinda addini ya koya masu ba na nasara mai jan kunne ba.
Tace malam munyi kuskure anan gaskiya amma muna matukar jin dadin zaman ajikin su dan yazamo muna gurin hutun mu.
Nace yanzu naji wanan zaki bar jikin Aminatu ta samu ta sarara a rayuwan ta ko kuwa bazaki fita ba ?
Dukar da kai tayi kasa can ta dago tana hawaye tace malam idan kace nafita zan fita amma da sharadi.
Nace muna jinki sharadin may kike son saka mata kuma ?
Tace malam sai tayi alkawarin bazata dinga zama kanta a sake ba koda ko agida take.
Sai kuma idan zata fita ta tabbatar da jikin ta yana a rufe ko yaushe a cikin mutunci saboda mun saba zama a jikin ta mina jin dadin yadda take bamu mmasauki a jikin nata.
Idan ta daina zaku barta har abada kunyi alkawarin hakan tare da ku dake da yaran ki da sauran yan uwan ki ?
Tace malam munyi amma aisu bil, adam kamar sune suke kiran mu yanzu a jikin su don basu tsare rayulan su daga ire iren mu jinnu masu sha, awan su.
Shiya kaga matan su sunfi kowa samun wanan matsalar a rayuwan su don irin yadda suke kasan cewa a yanzu babu kimtsi sam a tare dasu yadda ya dace da dan musulmi.
Mama hajjo baki ganin wanan zamani ne yakawoo masu hakan ?
Maimakon kukan da takeyi sai ta koma dariya tace ai zamanin muke bi muna aiwatar da shirin mu gare su.
Malam wani lokaci fa har da kazama muna shiga don wanan doyin dake fita daga jikin su muna matukar jin dadin shi sosai.
Zakaga mace kazama ce amma muna tare da ita muna morewa don karuwan mu gare ta.
Yanzu ina son daga nan ki bar jikin boyar Allah nan har abada kada ki sake shiga jikin ta idan ba haka ba zan kona ki ko na daure ki.
Ta dukar da kanta kasa tace malam mun san zaka iya muna fiye da hakan ma don haka zamu barta har abada.
Ko yanzun ma da mun san nan za, a zo da ita da ban tsaya har ka ganni ba don ai an kaita gurin masu magani da dama amma sai mu shiga mu bata maganin ko mu halaka mai maganin gaba daya kowa ma ya huta.
Nace to ina son don Allah ku fita daga yau kubar jikin ta ba sai mun hadu da ku ba.
Tace an gama malam amma tai min wani abu daya a rayuwan ta don taci gaba da zama lafiya.
Shine duk ranan jumma, a ya kasance ta daan yi sadaka da abinda ya sauwaka a gareta.
Ba wai duk ranan jumma, a ba a, a idan dai ta samu halin yin haka zaifiye ma rayuwan ta alheri sosai.
Kasan yanzu biladam su watsar da taimako kansu kawai suka sani bayan kuma Allah ya hore ma wasu sun su abinda zasu iya bayawar ga mabukatan su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login