Showing 1 words to 3000 words out of 115099 words
Chapter 1 - Bamu kadai ba ne book Complete by Zainab Makawa .txt
๏ปฟ[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI WANDA NA SABA MAWA DA WANDA BAN SABAMAWA, MASOYA NA NA GASKIYA DON KU NAI WANNAN DAN GUNTU LABARIN DON BAZAN MANTA DA KU BA HAR ABADA DON KUN NUNA MIN SO DA KAUNA .
WANAN LABARI ALMOST TRUE LIFE STORY NE DA FATAN ZAKU DAN FAHINCI MAI YAKE NUFI.
๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ BA MU KADAI BANE A GIDAJEN MU๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
Zaune take tana wanke wanke a farfajiyan tsakar gidan nasu inda yarta yar wata tara take zaune daga baran da tana wasa kasan cewan yaran ta biyu da suka dan tasa sun tafi islamiya.
Mama ce tafito daga nata dakin ta idon ta akan yar jikan ta dake zaune gefe tana wasa ita kadai.
A,a Nusaiba kece zaune haka ga yamma ya kusa maryam ina fada maki kullun da zaran almuru yayi ki dinga goya yaran nan bai da kyau barin yaro a zaune shi kaida haka.
Kiuya yai maku yawa yaran yanzu mu manyan mu ko yaushe suna fada muna mu kula da hakkin yaran mu don gujewa fadawa hannun shedanu.
Umma so nake na gama wanke kayan nan na zo na dauke ta Allah ya kyauta kawai mama tace tare da daukan yarinyar dake zaune saman suminti tana wasa irin na yara yan shekara daya sai faman gwalaci take irin na yara.
Daukan ta tayi suka koma cikin daki itako maryam hakane yasa ta jin dadin karasa aiyukan dake gaban ta kafin dare ya karaso mata.
Bayan wasu yan mintina sai ga sauran yaran biyu sun dawo Ahmed dan shekara hudu da rabi sai kaunan shi Amira yar shekara uku.
Suna dawowa gidan ya fara da baku bari ko dan fadan da suke a tsakanin su da yawan kawo kara mama kinga wani yai mun abu kaza ko.
Oya ki zauna kuci abinci nai maku wanka nan ta kawo masu tuwon masara da miyan kubewa danya yaji attarudu sai kamshin daddawa dake tashi a cikin shi.
Tsakar gida ta aje masu don kada su bata mata barandan da ta share dazun da yamma.
Don maryam mace mai tsaba da tsanda bata son kazan ta ko kadan a rayuwan ta.
Nan yaran suka zauna suna tacin abinci suna fada a tsakanin su daga inda uwar take tana aikin ta take tsawata masu.
Umma ce tafito tana fada tana goye da Nusaiba a bayan ta sai kuka takeyi tace kai kuyi ku daga daga gurin nan ku koma ciki almuru yayi sosai.
Maryam zo ki karbi yar nan ta damay ni da kuka tun dazun daga abin arziki zata saka min kuka na shegen kiuyan ta.
Kai Nusaiba don Allah ki bari na karasa wanke tukunyan nan mana.
Ni dai zoki karbeta ban iya kiuyan wannan yar taki mai shigen fitinan tsiya ita har yau bata saba da mutane ba uwar ta sai ubanta kawai ta sani.
Maryam tadata daure hannunta tana dan gogewa da zanin jikin ta takaraso gurin tana dariyan maganan Umma.
Ta karbi Nusaiba dake miko mata hannu daga bayan Umma da zata karbe umma takai mata dan duka a bayan ta.
Sallama akayi daga kofan shigowa gidan Laure mai ganye ce Umma tace innalillahi ni gaskiya ban san mai ke kawo wanan matar da magariban fari ba haka gidajen mutane.
Laure lafiya dai ko kika zo muna gida haka a lokacin da kowa ya ke kokarin natsa kan shi gida saboda yamma da yayi.
A,a Umma Aliyu zuwa nayi idan kuna da dan gishiri ku bani don nawa ya kare kuma yanzu nasan masu shago sun rufe suna shirin zuwa sallah.
Maryam don Alla debo mata gushiri ki bata inji Umma maryam ,ta juya da yarta a hannu ta nufi kitchen din su ta dauko gishiri a leda.
Tana mika wa laure na karba taji kan ta yai wani irin uban sarawa a lokaci guda da sauri ta daga kai ta kalli laure dake tsaye a kofan dakin Umma.
Idon laure akan yaran ta dake zaune a tsakar gida ganin haka Umma tai saurin gane may maryam ke nufi.
Da sauri ta wuce inda yaran suke zaune tana cewa oyaya kutashi muje na wanke maku hannu ku koma daki.
Nan tabar laure a tsaye tana kallon su, sai da ta dan numfasa tace to mama Ali ni zan koma na gode lokacin har an fara kiraye kirayen sallah ko.
Futan laure daga gidan duk maryam sai take jin jikin ta ba dadi a lokaci guda kanta yana wani irin sarawa.
Take jikin ta yai wani irin zafi radau dashi a dadafe ta samu tai sallah magariba ta samu guri ta kwan ta.
Jin maryam shiru yasa Umma lekowa don da zaran tagama sallah zata koma dakin Umma suyi kallo duk da dakin ta akwai kayan kallo a cikin shi.
Amma don su debewa Umna kewa a dakin ta suke zama ita da yara suna mata hira.
Samu Umma tayi maryam ta rufe cikin wani katon zanin gadon ta tana rawan sanyi don zazzabi yariga ya rufe mata jikin ta ko.
A,a maryam yaya haka kuma ikon Allah ina yanzun ne kike walwalan ki a tsakar gida kina aikin ki.
May ke damun kine maryam Umma take tambayan ta tare da daukan Nusaiba dake kuka.
Maryam ta bude baki da kyat tace Umma kaina jikina duk ban jin dadin shi wallahi.
Tana taba jikin maryam yadda yai zafi a lokaci daya yaba umma tsoro tace a,a maryam ashe ba abin wasa bane.
Take zuciyar ta tace mata laure a fili cewa tayi ina bako a gidan nan ba wallahi.
Nan ta juya da sauri zuwa dakin ta sai gata da wani dan kulin magani ta kada a ruwa tace tashi ki sha maryam .
Dakyat maryam ta mike tasha maganin ta koma ta kwanta fita umma tayi ta samo mata magani a chemest din unguwan su.
Sai zuwa dare sosai maryam ta dan samu sauki ganin haka Umma ranan a dakin su maryam ta kwana da ita.
Washe gari tun da sassafe bayan Umma ta sa maryam tai hayaki da wani garin magani ta fita gidan sai gidan laure.
Babu ko sallama ta fada gidan ta samu laure zaune a dan madafin ta tana dama wani bakin koko a roba.
Laure na ganin ta tace a,a mama Ali kece da farar safiyan nan haka Umma tace eh nine laure kin san ance a rama takwarkwari nazo ne yadda kika shiga muna gida da magariba shine nima nazo in maki kashedin hakan.
Wallahi laure idan kina cin kasa ki kiyayi na shuri don kayan gidan malam mai Allo ba taki bace idan kuma kin ki ji bakyaki gani ba .
Na fada maki wallahi ki kiyayi duk wani abin gidana in ba kina son watan tonon asurin ki ya kama a garin nan bane.
Mama Aliyu ban fahinci may kike nufi ba ne ni tace zaki fahinta wallahi kiyi gagawan sake min matar da ko asirin ki ya tonu a garin nan.
Wa ni mama Ali don Allah kada ki kulla min sheri idan ma sheri ne ai zaki gani kada ki sakar min sarakuwa kisha mamaki wallahi.
Umma ta juya tafita gidan tana fada laure tai tsaki bayan fitan umma tana cewa ni dama gwadawa nayi wane ni da wanan yarinyar da take a tabaibaye bani ba jinin kuma ai.
Umma na fita ta hadu da wata makwaciyar su tace a,a manan Aliyu ina aka fito haka da safen nan kuma.
Tace daga gidan laure nake jiya daga shiga wai neman gishiri ashe sheri ne yakawo ta sai kawai ga yarinyar nan maryam jiki ya gashe mata a tsatsaye muka kwana da ita.
Shine nazo nai mata kashedi akan gidana tace kinyi daidai wallahi watau ashe kudundumin nan da ake wa laure ta hurhura da gaskiya ke nan.
Kafin wani lokaci sai maryam taji wani wasai a jikin ta nan ta mike kamar ba ita ba ta fara aiyukan ta kamar kullun.
Tun wanan ranan Umma duk marance sai ta hake gidan nasu da hayakin miyagu don neman tsari.
Maryam kan har ta manta da zancen laure don yanzu wasai take jin kan ta kamar ba abinda ya taba samun ta a baya.
Maigidan maryam Aliyu dan Umma Rabi ma aikacin custom ne na kasa shi kadai Allah yabar wa umma duk haihuwan da takeyi basu tsayawa sai su koma.
Akan Aliyu ne tun tana da ciki ake ta neman maganin wabi don ance wabi take yi ko ta haihu yaran da sun dan tasa sai su rasu.
Allah da ikon shi saiga Aliyu an haifa sannu sannu Allah yaraya matashi har yakai ga girma yai karatun secondry inda ya tafi karatu a A B U zaria ya karanta engineering kuma ya fito da first class.
Kasancewan yadda kasamu ta koma babu aiki ga fanin da mutu yai karatu dole ya joner da hukuma shige da fice na kasa watau Custom.
Anan yanzu yake aiki da farko Enugu aka kaishi yai shekara uku acan yana can ne ya auri maryam diyar malam babba na garin su Auna wani gari dake can cikin yakin kasan kwantagora na Niger state.
Tun da sukai Aure da maryam bai tafi da ita ko ina ba rana zaune ne tare da mahaifiyam shi na gida su na garin Auna.
Har yakai sun kai ga haihuwan diya uku yanzu tsakanin su Umma tana jin dadin zama da sarakuwarta maryam don irin yadda maryam ke daukan ta tankar uwa a gare ta.
Ko itace ta haifi maryam abin ya tsaya a haka don irin yadda maryam ke bata hakkin ta na uwan mahaifiya a gare su .
Wani lokaci zakaga har suturan su kusa kala dayane da umma sai dai kala ya dan banban ta kawai.
Umma ma tana matukar son maryam don halin maryam na dabian arziki a gare su.
Maryam bata taba damuwa da rashin zuwa inda mijinta baiyi ba da ita don komai na bukatan su yana aje masu.
Gashi kuma mutum ne Aliyu wanda yasan daraja da hakkin iyalin shi daga su har yaran su a wadace suke da sutura abinci da sauran su.
Duk karshen wata Aliyu yake zuwa gida duba iyalinshi sai dai idan aiki ya tare shine zai kara yan kwanaki akai.
Yauma ya kasance karshen wata ne don haka maryam take ta faman gyaran jikin ta irin yadda ta saba yi idan zai zo garin.
Daga gida har jikin ta ita da yara wani lokaci ma har umma takan tilstawa sai tai mata kitso da kumshi don dai kada yazo ya samay su a kazance kawai.
KUYI HAKKURI DA WANAN SAI KUN JI NI KUMA
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu ๐: ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆBAMU KADAIBANE ๐ฉโ๐ฉโ๐งโ๐ง
GA MASU SON NOVEL DINA NA KUDI ZAKU IYA KIRA DA WANAN NOBAN 08036959257 DON SAMUN SARAUTAN MATA DA A LOKACIN MUKE,,,
Da sauri yau na kamala komai don kada ya dawo ya samay mu a cikin kazanta daga girki har gyaran gidan mu duk da dai gidan namu bawai ginan zamani bane.
Amma sai ta koma tsab dashi nai wanka na shirya cikin wasu material din buje da riga daga kasan buje a bude yake kamar fish tail daahi.
Yaran suna gurin umma tun yamma nasan shigowan dare yake muna don isan dake tsakanin kaduna da mu.
Dakin Umma na koma cikin su sai dai duk abinda nakeyi idona naa kofan gida don naji sallaman masu shigowa gidan.
Gashi yar wayata nokia mai tocila babu caji tun da rana ta dauke ga neper basu kawo wuta ba har lokacin.
Kawo wutan neper yai daidai da dirin motan da ya tsaya a kofan gidan mu a lokacin.
Van kawo cewa shi bane don nasan baida mota shiga shi sai dai kuma baifi minti biyar ba muka ji sallaman shi a tsakar gida.
Daga ni har yara rage rige mukeyi gurin taron shi har umma tafito dauke da Nusaiba da ihun mu ya tayar daga barci a lokacin.
Yana tsaye cikin kanan kaya da leda a hannun shi mukai kan shi da murnan ganin shi.
Yaran sun kankamay shi suna murna na karaso inda yake fuskana dauke da murmushi ina mashi sannu da zuwa.
Common yau ba zan samu hoging din bane da ido nai mashi signal da ga Umma nan waje.
Hakan bai hana shi dan rugomo ni ba a jikin shi nai mashi sannu da zuwa tare da karban ledan dake hannun shi.
Dakin Umma na nufa da ledan inda na barsu suna gaisawa da ita a tsakar gida.
Bai shigo ba ya juya yafita daga gidan sai ga yaran makwabtan mu dake wasan dare a waje suna shigowa da kayan tsaraban da yazo muna dashi.
Duk a kofan dakin Umma aka jibge komai da yazo dashi sai yar jakar kayan shi kawai na dauka zuwa dakina.
Nafito bayan na aje jakar ne nafito don na shiga da kayan daga cikin dakin Umma.
Sai dai nai matukar mamakin ganin yawan tsaraban da yazo muna dashi wanan karon don yafi karfi abinda ya saba kawo muna abaya.
Bayan nagama saka kayan daga ciki su doya da irish nabarsu a wajen juyawa nayi kitchen na juye mashi ruwan wanka a lokacin.
Nasama shi tsaye a tsakiyan daki yana kokarin cire rigan shi don nasaba mai da ya iso yai wanka kafin ya zauna cin abinci yana ci muna gaisawa dashi.
Juyowa yayi inda nake tsaye yana kallona cikin sha,awa yake cewa miss you maryam .
Murmushi nayi nace nafi ka kewa ai baban Abba yanzun dai ga ruwa can kai wanka kazo kaci abinci.
Yafita zuwa wanka nikuma na kara gyara dakin yadda naga ya kamata duk daba baci yayi ba kafin yafito nafitar mai da kayan da zai saka na aje mai a saman gado daga gefe daya.
Koda ya fito ina zaune saman kujera ina shayar da Nusaiba nono a lokacin.
Ina zaune ina kallon yadda yake shirin shi a tsanake tare da sake min murmushi yana tambayana ya bayan robo da kuma yara duk da dai muna waya dashi kusan sau biyu a rana.
Yana gama shiri muka kwasa sai dakin Umma mun samay ta da yara suna fira muka shigo dakin nata.
Nan suka kara gaisawa da Umma ga tv yana aiki daga gefe daya can cikin hiran su da Umma naji tana cewa yau sai muka ga tsaraba haka dayawa amma kan kasha kudin mota wanga uban tsara ba haka mai yawa.
Murmushi yayi yace umma ban fada maku bane dai amma maryam ta samu kishiya ai.
Da sauri na dago daga kallon tv da nakeyi nake kallon shi ita ma dai Umma din kallon mamaki take mashi.
Yace tana waje yanzun haka da ita nazo ma sai da safe zaku fita ku gan ta aiko ?
Baba kace min alheri ya samu ke nan bamu da labari nikan da nai mutuwan kasko a zaune ban fahinci maganan su kuma gashi naji umma har da murnan ta.
Sai da naji yace ban dade da sayen taba don batakai sati biyu ba ma hannuna.
Sabuwa ce dal Umma na samu dama na dade ina son sayen mota don nagaji da shiga motar haya hakanan.
Sai a lokacin na dan saki murmushi a fuskana da na fahinci motace ashe yasayo nan muka shiga murna mun kagara ya gama cin abinci mu fita tare dashi mu gani.
Sai da ya gama muka kwasa har yaran da basuyi barci muka fita waje ganin motan nashi.
Sabuwar motace ta zamani 406 launin blue sai sheki takeyi a cikin farin wata.
Ko ina na motan sai da muka duba muna yaba kyawon ta muka dawo cikin gida da murnan mu.
Wanan karon bai koma dakin Umma ba dakin mu ya shiga nima ban bata lokaci va nabi bayan shi zuwa dakin.
Shimfida na fara yiwa Nusaiba kafin na juyo inda yake zaune yana waya da abokin aikin shi.
Fita nayi na kara watsawa jikina ruwa nazo na shafa maina mai kamshi daya sayo min wancan zuwan da yayi don ya san ni da balain son kamshi sosai.
Ina gamawa ban tsaya bata lokaci ba naje naiwa su Umma sai da safe na dawo na rufe kofan dakin mu.
Kamar kullun yadda yake dawowa a matse xa bukata na yau ma hakane ya kasance a tsakanin mu dashi.
Sai bayan komai ya kamala ne yake cewa maryam ina ganin fa idan Umma ta yarda zan dauke ku dake da yaran mu koma kaduna don yaran nan su samu karatu ingantace a rayuwan su.
Sosai naji dadin magan nan shi har na kasa boye farinciki na a ciki nace Allah yasa umma ta yarda ka tafi damu danafi kowa farin ciki da hakan kasancewan zamu zauna a guri daya dakai.
Hira muke tayi dashi har barci ya dauke mu don yana da gajiya a jikin shi sosai ga kuma wanda yazo ya kara a tare dani.
Washe gari tun da nai sallah ban kwanta ba kuma nashiga hada muna abin karyawan mu.
Kafin sani lokaci na hada na shiga daki na samay shi still yana barcin gajiya wankan shiga kafin wani lokaci har na gyara jikina inda na saka wani dogon rigan wani atamfana ja mai kyau dashi.
Sallama da yaro yayi ne yasani lekowa yana fadin wai ana sallama da