Showing 18001 words to 21000 words out of 168541 words

Chapter 7 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9137

na shiga d'akin nata ban same ta ba"
Baaba hurera da har lokacin murmushi take tace"ai ta d'an fita ne ita da Nasiru amma tace bazata jima ba zata duba Fatima (pretty) ne dake jin jiki,to Baaba ace da wnn yrnyr ta kawo min abinci na,Baaba hurera tace "to"snn ta koma kitchen ta snr da Rayyanat.



Tun daga qofar kitchen mohd ya tsare Rayyanat da mugun kallo har ta qaraso ta ajiye masa abinci zata juya yace"ke xo nn"
Juyowa tayi tare da watsa masa manyan idanuwanta a cikin nashi,
guntun tsaki yayi ya kauda nashi idanun sae kuma ya sake kallonta snn yace"wae ke wace ce da kika raina ni haka meye matsalar ki dani?kauda idonta kawai tayi ba tare da tace dashi komai ba, ya saki tsaki yace"tafi ki bani guri amma wlh duk rnr da na qara jin kince min wnn d'in nn sae bakin ki ya gaya miki"


Ta juyo had'e da ta6e baki ta fara tako kenan taji yo sallama ta amsa sallamar ta tafi ta kar6o saqo ,
kitchen ta tafi da saqon dan inna ta gaya mata abinda za'a kawo wato nmn kaji,tas Rayyanat ta wanke nmn ta zuba a freezer.


Washe gari rnr juma'a Rayyanat taci er kwalliyarta ta juma'a tana zaune abinta a d'aki ta gama karatun srtl kahfi ta jawo litattafanta na islamiya tana mita.
Tana cikin haka taji inna na qwala mata kira ta fito da sauri taje falo ta sami inna dasu saliha da Ameera nn ta saki fuska suka gaisa da saliha akasin Ameera da ta qi ko kallon gefen Rayyanat.
Inna ta kalli Rayyanat washe da baki tace"dama yanzu nake shirin kiranki kixo kici abinci sae ga su saliha sun shigo kinga sae kije ki d'ebo maku abincin kuci tare"
Rayyanat taje ta d'ebo masu abinci a qaton plate ,
fried rice ce da akayita ta da qoda tayi kyau sosai har ta gaji d'auke da paper chicken da aka d'ora a gefe.
A nn falon sukayi zaune zasu ci ,
saliha ta kalli Ameera wacce ta maida hnkli kan TV bata da niyyar tasowa suci abinci ,tace"Ameera taso muci abinci ke muke jira fa"da d'an mamaki Ameera ta kalli saliha snn ta nuna kanta da yatsa tace"ni d'in nn'sae kuma ta wani yamutse fuska tana kallon Rayyanat kmr wata abar qyama tace"kuci kawai ni a qoshe nake sae dai zuwa anjima ko zanci"kafin saliha tace komai inna tace"kinga bana son iya shege tashi kuje kici cikin taro ai yafi"
Wlh inna a qoshe nake sae dai zuwa anjima,ke kika sani cewar saliha wacce tuni ta fhmci dalilin da yasa Ameera taqi tasowa suci abincin.
Suna cikin cin abinci saliha ke cewa "yauwa Ameera idan mun qarasa cin abinci ina son muje ki rakani gidan su yaya munir gun safiyya na kar6o house wears d'ina sbd dai dai su nake son amin sabbin da za'a d'inka min"
Ameera tace"to gama d'in muje ko banza ina son naje naga safiyya"
Wlh kam safiyya nada qoqarin ziyartarmu"cewar saliha wacce ta kalli Rayyanat tace"tare fa zamuje dan ki hanzarta cin abinci naga sae ci kike kmr ba kya so"Rayyanat tayi murmushi tace"to so kike ina cin abinci sauri sauri naje har ya sarqe ni ai komai sannu a hnkli yafi"
Murmushi saliha tayi tana mai kallon Rayyanat tace"hakane amma kin fiye shiririta gun cin abincin naki in nice ma sae ya girshe ni kafin na qoshi, shiyasa nake sauri abuna sae na kammala cin abincin ina mai marmarin sa don nafi son haka,kema idan kika gwada yin haka zaki fi jin dad'i.
A sanyaye Rayyanat ta kalli saliha tace"har abada bana son sauya tsarin cin abinci na sbd haka na taso na sami Abbana yana ciyadda ni.
Tana kawowa nn hawaye suka sakko kan kumatun ta tayi saurin tashi ta bar gurin yayinda saliha ta bita da ido cike da tausayi.
Ameera ta ta6e baki tace"kukan name kuma ana zaune qalau? Ajiyar zuciya saliha ta sauke tace"bari kawai Ameera wlh Rayyanat abin tausayi ce dmn ta bani labarin rayuwarta ciki har da mutuwar mahaifinta da shi kad'ai ne gatan ta a duniya kinga dole tayi kuka a duk lokacin da ta tuna shi,Ameera ta wani ta6e baki tace" to Allah ji qan mamata"
Amin cewar saliha wacce ta tashi taje ta lallaso Rayyanat ta shiryo suka fito .
Ameera kam ganin da Rayyanat za a tafi tace ta fasa bata zuwa su dai gaida safiyya, ko kad'an saliha bata damu ba duk da ta fhmci dalilinta.
Inna suka je sukayiwa sallama suka fita ta bisu da Allah dawo daku lafiya.


Gidan ba nisa sosai dan qasa ma suka bi ,suna shiga gidan Rayyanat ta tsaya ta kasa shiga ba don komai ba sae don hango munir da tayi zai shiga mota,
sosai gabanta ya fad'i don ta rasa wane irin mutum ne shi da duk inda taje sae ta had'u dashi.
Saliha ce ta riqo hannunta tana fad'in"zo muje mana"
Haka Rayyanat ta dake tabi saliha sbd tasan idan ba gamo tayi ba ba zai gane taba tunda kullum cikin niqab yake ganinta.
Da sauri ta sadda kanta qasa ganin irin kallon da yake mata har ma ya fasa shiga mota ya nufo su yazo ya tsaya gab da ita,gam ta qara riqe saliha dmn ta gama yarda gamo tayi, saliha kuwa sae washe baki tayi tana kallon munir tace"yaya munir ina wuni? Fuskar sa wasai ya amsa mata har yana tmbyr ya su umma tace"duk suna lafiya.


nn taja Rayyanah zasu wuce, yayi saurin dakatar da ita kan cewa "ki shiga kawai qawar ki zata same ki daga baya"
da qyar saliha ta iya qwace hannunta daga na Rayyanat ta tafi ta barsu d'auke da murmushi a fuskarta.
Da hanzari Rayyanat ke qoqarin bin saliha munir yayi saurin shan gabanta yace"yau kam ba inda zaki sae kin saurareni"
Kuka kawai ta fashe masa dashi dan gabad'aya ta gama tsorata dashi.


Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






2/1/2017






🔮```16```🔮
Cikin muryar sa mai saka natsuwa ya shiga bata haquri har ta tsagaita kukanta da takeyi marar sauti.
Cikin kulawa ya kalleta da kyau snn yace"kin tsorata dani ko shiyasa kike kuka,ko kad'an baki da laifi a bisa tsoratar da kikayi sbd ban ta6a ganin fuskar ki ba amma yau ina ganin ki na gane kece ,
kin san sbd me na gane ki?
D'agowa tayi tana kallon shi ,
Shi kuma kmr wanda ke tsaye da er shekara shida yace"to yi min magana man sae na gaya miki"
A sanyaye tace"sae ka fad'a"
Murmushi yayi tare da nuna gefen zuciyar sa yace"ta nn na gane kece sbd duk lokacinda na gnki zaki tafi islamiyya bugun xuciyata ya kan canxa har sae kin 6acewa gani na,shiyasa nake tunanin idan na rasa ki ya zanyi dmn nasan zuciyata zata iya lalacewa ta bar jikina,da haka nake roqon ki kan dan Allah ki amince dani kinji.
Kallon sa tayi shaye da toka tace"kaga malam ni zan shiga ciki"
Sosai ya langwa6ar da kansa cike da son kora mata wani bayani tayi saurin girgiza kanta alamar bazata saurare shi ba ta kuma kama hnya ta bar gidan sae kiranta yake yana rarrashi kan ta dawo ya shigar da ita cikin gida amma fafau taqi tsayawa.


Tana isa gida dai dai ta kai tsakiyar falo sae kawai taji ta fashe da kukan da ta rasa dalilinsa ai kuwa da gudu ta shige d'akinta don bata son wani yaga tana kuka,sbd sam hnklinta bai bata ganin kowa a falon ba alhali kuwa Mohd da Ameera suna nn zaune.
Ameera ta kalli mohd da ya tsure qofar Rayyanat da kallo kmr mai wani nazari can ya maida duban sa ga Amira yace"ita wnn daga ina ta fito? ta6e baki tayi snn tace"gidan su yaya munir ta raka saliha ,saurin kallonta yayi jin gidan da ta ambata ita kuma ta qarasa da cewa"wata qil qauyanci ta nuna musu shiyasa suka koro ta"
Komai bai ce mata ba sae tashi yayi ya fita.


Rayyanat na cikin kukanta taji an turo qofa tayi saurin tashi ta share hawayenta ,saliha wacce ta shigo taxo gab da ita ta zauna ta riqo hannyenta cikin murya mai kama da ta rarrashi tace"haba Rayyanat meyasa kike ma yaya munir haka yace tsawon lokaci yake bibiyarki amma kinqi ki saurare shi,don Allah Rayyanat ki taimaki yaya munir wlh na fhmci mugun sonki yake ,Hawaye ne suka gangaro kan kumatun Rayyanat tace"saliha ki bawa yayanki haquri dmn tunda yaya anwar ya mutu na ajiye soyayya ba kuma zan qara ba ko banza ma bazan iya soyayya da mutumin birni ba ,meyasa zaki ce haka Rayyanat naga ko yaya anwar a labarin ki da kika bani shi d'an birni ne,eh amma shi asalinsa d'an qauyen mu ne nace maki ba tashin birni bane ,amma Rayyanat d'an birni da na qauya ai duk abu d'aya ne dmn duk Allah ya yisu'"um um ba d'aya bane saliha,akan me zaki ce haka? Sbd ba d'aya bane,ajiyar zuciya saliha ta sauke tana mai kallon Rayyanat tace"indai hali kike tunani to wlh yaya munir yana da halin kirki....a zahiri ba dmn baki san meye bad'inin sa ba"
amma kinji ance labarin zuciya a tambayi fuska "banda hali saliha ba kuma xaki gane dalilin da yasa na tsani d'an birni ba sae nn gaba,da mamaki saliha tace"tsana kuma,to wani abu d'an birni ya miki ne dmn naga a cikin labarinki anwar kad'ai ne d'an birni kuma kince lfy kuka rabu dashi asali ma in rashin mutnci ne ai d'an qauyen naku ya muku wato bala da yasa kuka koma daji da zama,ko kuma kin 6oye min wani abu a labarinki ne?idanuwan Rayyanat tap da qwallah take kallon saliha tace"Saliha ki daina min tambayoyi haka don Allah"
Saliha ta nisa tace "shike nn amma ga dukkan alamu ba duka kika gaya min labarinki ba"shiru Rayyanat tayi dmn tasan tabbas bata snr da saliha dalilin mutuwar Baffanta ba kawai dai tace mata ya rasu.
Tace"hm saliha ki yarda dani mana ni ban rage miki komai ba a labarina ba,kawai dai bana ra'ayin soyayya har da d'an qauyen ma dmn tunda yaya anwar ya mutu naji bazan iya soyayya da duk wani d'a namiji ba wnn alqawari ne nayiwa kaina dmn inaji idan na kula wani tmkr nayiwa yaya anwar butulce ne.
Hm Rayyanat kenan kina nufin haka zaki tabbata ba aure, d'an guntun murmushi Rayyanat tayi snn tace"To ce maki akayi rayuwar tawa tsawo ne da ita nida ma nake roqon Allah yasa rayuwata zata kai ga na cika burina" hm har akwai wani buri a gun 'ya mace da ya wuce aure? Kallonta kawai Rayyanat tayi ta kauda kanta,snn tace"inada wnn burin amma a da wato kafin yaya anwar ya mutu.
saliha tace"nidai Rayyanat al'amuranki na bani mamaki rayuwar ki idan mutum ya kalla kmr so simple n easy amma ashe in kika dake kan abu kin dake
kenan.
Ba hk bane saliha yaya anwar yana da matuqar muhimmancin da bazan iya kula kowa ba.
Cikin nuna 6acin rai saliha ta tashi tace"tunda haka kikace shikenan shi kuma yaya munir Allah ya bashi wacce ta fiki da komai ma"
Nn ta fito falo ta sami mohd zaune yana cin abinci ya tsare ta da ido kmr wani mai tuhumar ta,ta sadda kanta qasa tare da gaida shi snn tace da Ameera tashi muje gida ,nn ta tashi sukayi wa inna sallama zasu fita mohd ya kira saliha tare da zaro kud'i a aljihunsa,
saliha taxo cike da ladabi,
Ameera kuwa ta biyota cikin rawar kai ,
mohd ya dalla mata harara yace"bana son shisshiga fa ke na kira ko saliha"
kmr zata yi kuka tace"saliha"
Girgiza kansa kawai yayi had'e da d'an guntun tsaki don ko kad'an baya son hali irin na Ameera nn ya miqawa saliha two thousand a cewar suyi kud'in a daidaita tayi masa godiya suka wuce.


Bayan ya kammala cin abinci yaje d'akin inna zai mata sallama inna dake zaune tana lazimi tace"yauwa d'an albarka yanzu nake qoqarin tashi na same ka,sbd ina son zamu yi wata magana mai muhimmanci da kai,a natse man ya zauna kan gefen gadon inna yace"ina jinki inna".






Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






3/1/2017






🔮```17```🔮
Muhammadu tafiya nake son zanyi a cikin satin nn zuwa qauyen mu dmn na jima rabona da zuwa shine nake son zan kai Rayyanah a can gidan ku har idan na dawo.
A natse mohd ya d'ago yana kallonta snn yace"shike nn inna amma kinyi magana dasu Abba kuwa.....Yo sae da izinin su zanyi tafiyar ne ko kuwa Rayyanah d'in ce baka son ta zauna gidan naku! Ba haka bane inna sanin dai nayi tafiyar ki idan kika yita sae wanda ya ganki,inna ta washe baki tace"ayyo ai muhammadu kasan en uwa dad'i ne dasu shiyasa nake d'an jimawa idan naje.
To inna wace rnr zaki tafi? Eh to rnr laraba nake son na tafi in Allah yaso,to Allah ya kaimu lokacin inna, Amin Amin d'an Albarka.
Tare suka fito shida inna ta nufi d'akin Rayyanat shi kuma ya fita daga gidan.


Zancen tafiyarta ne taje ta snr da Rayyanat ta fita ta bar Rayyanat cikin rashin jin dad'i da tunani sae take jin kmr kar inna tayi tafiyar nn ba don komai ba sae don sabon da tayi da inna.


Bayan kwana uku da faruwar haka cikin ikon Allah ynx munir ya fara shawo kan Rayyanat dan yanzu har tana d'an tsayi ta saurare shi.


Ko yauma tafe suke ta dawo daga islamiyya sae janta yake da fira ita dai iyakarta murmushi da kuma wasa da en yatsunta.
Har qofar gida ya rakota tana shiga gidan sae ga Muhummad ya fito zai tafi masallaci dan har an fara kirayen kirayen sllr magrib.
Cikin sakin fuska munir ya miqa masa hannu suka gaisa inda shaye da toka man ya zare hannun sa daga na munir ya wuce, munir ya bisa da murmushi dmn inda sabo ya saba da halin abokin nasa.
munir yaje ya nemi buta yayi arwala ya shiga masallaci sbd dama masallacin kusa da gidan yake .


Rayyanat kuwa tana shiga gida ta cire hijab, niqab da socks, ta jawo er akwatin ta da inna ta saya mata,ta ciro kayanta a wardrobe tana tsarawa da yake fashin sallah take shiyasa bata yi zancen sallah ba.

Komai da tasan zata buqata sae da ta zuba a ciki snn tayi zaune tana tunanin yanda zata yi rayuwa a gidan su man ,
sae roqon Allah take a ranta kan Allah yasa 6angaren su saliha zata zauna in hkne kam da sauqi.




Guraren qarfe takwas da rabi zaune suke a falo ita da inna suna cin abinci suna kallo inna tace"Rayyanah ina ce kin harhad'a kayanki dan kinsan na gaya miki sammako zanyi shiyasa ma na sallami baaba hurera tun yau, eh inna na harhad'a komai tun d'azun, tayi mgnr ne a sanyaye,inna kuwa ta washe haqora tace"to Allah miki albarka 'yannan idan kinje ki sakin jikin ki sosai don tamkar gidan ku ne kinji, Rayyanat ta gyad'a kanta wanda yayi dai dai da shigowar nasir d'auke da sallama a bakin shi,
inna ce ta amsa masa sallama, Rayyanat kuwa ta gaida shi cikin ladabi snn ta d'auki kwanon tuwonta ta shiga daga ciki.
Nasir kuwa bayan ya amsa gaisuwar Rayyanat ya gaida inna wacce ta amsa gaisuwar washe da baki snn tace"ka dai ji zancen tafiyar tamu yanda na snr da kai a waya ko, eh inna inshaAllah tunda sassafe zaki ganni,tace "amma fa ina son sae mun sauke Rayyanah a gidan naku, eh inna ai duk kin snr dani hk a waya.
To ya jikin Fatima da sauqi dai ko, wlh Alhmdlh inna taji sauqi sosai don harma tana cin abinci yanxu, to madallah Allah ya nuna mana ta sauke abinda ke cikin cikinta lafiya ,Amin amin inna.
Daga haka suka ta6a er fira ,
guraren tara da rabi snn ya wuce.


Washe gari tun da safe nasir yazo ya kwashi inna da Rayyanah suka tafi gidan nasu, inna taje kowane 6angare ta musu bankwana wacce duk 6angaren da taje tana riqe da hannun Rayyanah har saida tazo gun mota zata shiga snn ta saki hannun Rayyant tana mata sae ta dawo.
Su inna na wucewa Rayyanh ta ajiye kuka amma marar sauti,mohd dake tsaye sae kallonta yake don ya fahimci ba qaramar shagwa6a Rayyant zata yi ba.
Shida kanshi ya ja mata akwatin ta suka tafi 6angaren su,yana tafe Rayyant na bayanshi har suka tafi d'akin Ameera,sae da ya kalli Rayyanat ganin har lokacin kuka take snn ya kai hannu a hnkli ya fara qwanqwasa qofar.



Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






4/1/2017






🔮```18```🔮
Ya jima yana knocking snn aka bud'e qofar,wani mugun kallo ya watsa ma Ameera wacce ta fito cike da jin bacci sae miqa take ,tayi saurin daina miqar ganin kallonda yayanta ke mata, kmr da tsoro tace"yi haquri yaya ina bacci koda kake ta qwanqwasa min,bai ce da ita komai ba sae akwatin Rayyanat ya miqa mata tare da fad'in"ki ware mata gurin da zata saka kayanta a nn zata zauna har sae inna ta dawo.
Ba musu ta kar6i akwatin ta shigar da ita mohd kuwa ba tare da ya kalli Rynt ba yace"shiga daga ciki idan kika buqaci wani abu ki snr da ita Ameeran, daga haka ya wuce ita kuma tasa qafa zata shiga dai dai Ameera zata fito sae qunquni take ta bangaji rynt da qarfi har sae da ta nemi fad'uwa bata damu ba don dama da niya tayi snn tayi ficewarta sae d'akin hjyr su.
Ta shiga cikin kuka mai d'auke da shagwa6a tace"umma wlh ni bazan iya rayuwa da wnn yrnyr a d'aki d'aya ba, xaro ido Umma tayi tace"au wai a 6angaren nn zata zauna?eh yaya ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login