Showing 36001 words to 39000 words out of 168541 words

Chapter 13 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9159

bane da zakiyi abinda kika ga dama!
Sautin kukanta ne ya soma fitowa ta hana faruwar hkn ta komawarta ta zauna tana jin mami zata fito bathroom tayi saurin share hawayenta yayinda mami ta fito tana fad'in " gufranaka ya Allah"
ta washe baki tare da fad'in"hkne ko Anti?Rynt ta qirqiro murmushi tare da gyad'a mata kai"snn takai dubanta gun mohd da har lokacin yana tsaye bai fita ba mami taje gurin shi da gudu yaja hannunta suka fita.




Tayi awa d'aya kafin taga dawowar mami.
Wacce ta dawo d'auke da kayan wasa kala kala sae murna take taje kan bed tana fad'in"Anti yaya ne ya sayamin kayan wasa yace in ta wasa har su dawo wai baza su jima ba"Rynt tace"to zo kici abinci?ai anti sae da nayi breakfast kafin naje raka su yaya a airpot ,Rynt da ba tasan meye haka ba ta basar da zancen. can mami tace"lah anti na manta yaya nasir fa yana falo wae kije.

Koda Rynt taje kuwa ta same shi zaune a falo cikin ladabi ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa snn yace"ko da akwai wani abunda kike buqata?ta gyad'a masa kai tare da fad'in "eh"yace"me kenan"
tace"ina son na koma gidan inna da zama ne har idan sun dawo snn kuma ina son na koma islamiyya"yace"meyasa kike son komawa gidan inna? Sbd bana jin zan iya bacci daga ni sae mami a gidan, gidan nn ya mana girma sosai"indai wnn ne ai mai sauqi ne Rynh don da sannu zaki saba kuma idan wani abu kike tunanin zai faru ai akwai masu tsaro sosai a gidan kuma da yardar Allah ba abinda zai faru kinji? ta gyad'a masa kai snn yace"zancen islamiyya kuma gobe inshaAllah nn cikin anguwar zan nema miki wata islamiyya ta matan aure "tace"to nagode yaya nasir"
yace"sae kuma me kike buqata? Shike nn komai bana buqata, to ga wnn ki riqa a hannun ki, tace"Aa wlh ka barsu kawai nagode inada kud'i a hannu na da inna ta ban"murmurshi kawai yayi ya ajiye kud'in kan center table ya tafi tace"masa nagode snn ta d'auki kud'in ta juya cike da jin dad'in zata koma islamiyya,yayinda nasir ya fita cike da mamakin mohd ace zai yi tafiya bai bawa mtrsa komai ba.



Da dare kuwa duk ta cire wani tsoro a ranta sukayi baccin su ita da mami.




Washe gari da kanta taje kitchen tayi musu break fast sbd yinin jiya duk bata ga kuku ba bai kuma kawo musu abinci ba.


8:pm nn falo suke zaune su biyu abinsu suna kallon tom and jerry.
Sae ga nasir ya shigo da sallamar sa.
Bayan sun gaisa ya bata leda yace" hijabin makarantar ne a ciki kuma da qarfe biyu ake zuwa a dawo qarfe hud'u .
makarantar tana a nn bayan gidan ba nisa amma gobe zan zo na kaiki don kiga makarantar.
Sosai tayi mai godiya snn ya tafi.




Haka ko akayi washe gari nasir yazo ya kaita islamiyya mami kuwa ya kaita gida.
To tun daga rnr ita ke kai kanta ta kuma maida kanta amma sae da qarfe biyar ake maida mata mami.


Su mohd kuwa kusan sati uku sukayi a yawon honeymoon d'insu.


Rynt kuwa sosai ta maida hnklinta zuwa islamiyya kuma rashin kuku bai kawo mata wata matsala ba don koda 1:30 keyi har ta gama musu abincin su na rana sunci ita da mami bcs kafin qarfe biyu nasir ke zowa yakai mami gida,sbd Rynt ta samu taje islamiyya kan lokaci,idan kuma ta dawo qarfe hudu sae tayi sll snn take d'aura musu girkin dare,kuma duk abinda tayi ra'ayin dafawa akwai shi a gidan matsalar ta d'aya itace kewar inna da take sosai.


Rnr wata assabar ne Rynt ta dawo daga islamiyya ita da wata qawar ta suka shigo gidan kowanen su cikin niqabi,da kuma hijab d'insu har qasa da socks .
A nn harabar gidan ta had'u da malika da mohd wa'anda saukar su kenan, gaban Rnynt yayi mugun fad'uwa sbd tunanin abinda zai biyo baya ita da mohd idan yaga ta koma islamiyya bada sanin sa ba, hkn yasa ko gaida shi taqi tayi dan kar ya balbaleta gaban qawar ta.
Dashi har malika kallonta suke har suka shige, malika ta kalli mohd ta6e da baki tace"my man lokaci fa yayi da zaka gargad'a mana yrnyr nn, jifa har da wani kwashe kwashe take maka ,mohd yace"zanyi maganin ta ne ai ,in ni sa'anta ne ko kuma gidan nawa an gaya mata qwai da dunge duk shigowa suke suyi abinda suka ga dama"hm rainaka tayi wlh ita d'in kanta wace ce da har zata yo maka wani jajube jajube.



Su Rynt kuwa har suka shiga d'aki gabanta na dukan uku uku .
Byn ta nunawa wacce suka shigo tare bathroom tayo fitsari ta fito take ce ma Rynt "nikuwa Rynt
ba mai gidan ki bane ya dawo?Rynt tace"shine"
tace"ikon Allah sae kikayi kmr baki sanshi ba,"uhm"cewar Rynt yayinda er makarantar tasu bata sake cewa komai ba ta fita had'e da yiwa Rynt godiya.


Nn kan saukowa upstairs ta had'u da mohd ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa snn ya wuce sae d'akin Rynt wacce ya samu ta cire niqab d'inta kenan ,tana had'a ido dashi tasha mai toka, shima fuskar sa tamau yake cewa "wace ce kika shigo min da ita a gida?tace"qawata ce"
da wane dalilin ta shigo min gida? Lalura, shine kad'ai abinda tace ta kuma kama hanya zuwa bathroom haka shima bai sake cewa komai ba ya fitawar sa, fasa shiga batroom d'in tayi don dama tsoron kar ya dake ta yasa tayi niyar shiga bathroom,shiyasa ma tayi mamakin ganin ya fita bai yi mata fad'an ftr ta ba da kuma inda ta fito,ko meyasa,oho.




Da dare mohd ya dawo daga masallaci sllr isha'i ya tafi d'akin malika ya sameta kwance tana waya tayi saurin katse wyr ta tashi ta tarbo shi cike da kisisina tace"ya akayi my man ko wnn abar ce takai ma koina don naga fuskar ka kmr ba annuri ,yace"yunwa ce wlh na rasa ina d'an iskan kukun nn ya shiga ace tun d'azu da muka dawo bai kawo mana abinci ba kuma har yanzu ba alamar za'a kawo,,tace"oh no am sorry my man ai baya nn, ina yaje? Wlh nice na sallame shi da zamu tafi honeymoon ,da sauri ya kalleta snn yace "meyasa?
tace"me zai xauna yi to tunda bama nn"
yace"haba malika mami fa?
tace "naga fa a gabana ka damqa kulawar mami a gun yayanta nasir kuma kasan komai mami ke buqata nasir ba baqonta bane zata gaya mai kuma zai mata tunda ko baka bashi kulawarta ba ai dole ya kula da ita tunda qanwar sa ce,,kuma ai tun lokacinda mukayi tafiyar nn kullum a gida mami ke yini ko ba haka naji kana waya da shi nasir d'in ba?naji hkne ,kira shi kukun yazo ya dafa mana abinda zamu ci da daren nn don nikam ina buqatar naci abinci kafin na kwanta, to my man amma don Allah zanso na roqeka wani abu, fad'i inajinki,dama ina son naje gida ynz zuwa qarfe goma sae na dawo kaji, ya shafo cikinta tare da fad'in"to ki bari idan kinci abinci ko"um um lokaci zai tafi kuma idan naje gida ai zanci,to shike nn kira min kukun ni yazo ya dafa min nawa, tace"ok"snn ya fita.




Yana nn kwance a d'aki ta shigo cikin shiri na qananan kaya amma ta d'aura after dress akai sae zuba qamshi take kallon ta yake har ta qaraso inda yake kwance kan sofa ,ta duqa gab dashi d'auke da murmushi a fuskarta takai bakinta kan nashi ta had'e,inda cikin minti 1 ta zare bakinta
tana mai fad'in"ur food is ready sae kaje kaci then ni zan tafi "yayi murmushi yace"ok ki gaida su mama"tace"zasuji" snn ta fita.


Shi kuma mohd ya fito ya nufi gun dining ya zauna har zai fara cin abinci sae kuma ya tashi ya nufi d'akin Rynt,
Kai tsaye Rynt ta ganshi amma hkn bai hana tayi saurin 6oye littafanta na islamiya ba da ta ftr tana d'an dubawa,snn ta kalle shi kmr marar gsky ga hannyenta takai baya tana qara 6oye littafan a bayanta.
shaye da toka yace"lafiyar ki? tayi saurin cewa"lafiya ba komai"
ya qara shan mur snn yace"da bama nn a ina kuke samun abinda kuke ci keda mami? Tace"ina dafa mana ne kullum"
to ina mami take ne yanzu?tana gida har yanzu bata dawo ba"yace"shike nn amma ki sani daga yau kar na qara ganin kucakar qafar ki a kitchen"ta gyad'a masa kai kawai shi kuma ya fita
sae kawai ya had'u da mami ta wani maqalqaleshi tana mai murnar ganin shi.


Washe gari da qarfe biyu Rynt tayi shirin ta tsaf na islamiyya ta fito cike da tunanin yanda zata kaya da mohd idan ya ganta.
koda ta fito gate d'in gidan sae ko tayi kici6is dashi zai kunna hancin motar sa a cikin gidan.
Yana ganin ta ya fasa shiga gidan sae ma tsaida motar sa da yayi ya fito,a lokacin Rynt jin tayi kmr ta kwasa aguje kafin ya qaraso gareta amma hkn ta dake tayi tsayinta har ya qaraso gab da ita har ma tana jiyo qamshin turaren shi.


Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [1/18/2017]


🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮


















🔮🔮🔮
_*page*_ *```30```*
Taja baya da sauri tana fad'in"dan Allah kayi haquri ka barni na ci gaba da zuwa islamiyyar nn"
tsaki yaja yace"kinga ba wnn ba abinda nake son sani shine kin gyara min d'akina ko kuwa?
wane d'akin kuma,what!bangane wane d'akin ba kina nufin mami bata gaya miki saqona ba tun da safe? tace"bata gaya min ba"yace"to ai yanzu na gaya miki sae kije ki gyra min"badai yanzu ba kam don ni islamiyya zan tafi,yanzu kuwa er rainin wayo idan ba haka ba daga yau ma kin daina zuwa islamiyyar gabad'aya!
Kmr zatayi kuka ta yaye niqabinta tana kallon shi tace"kayi haquri wlh in na dawo zan gyra maka,ke kina hauka ne da Allah koma daga ciki kije ki gyara min d'aki bana son wani shirme,tace"bafa wani jimawa mukeyi ba da qarfe hud'u muke tashi"ok so kike na zauna har qarfe hud'u banje d'aki ba,ko kuma so kike na shiga d'akin da datti.
Kayi hqr kaje d'akin mtrka har in na dawo" kallonta kawai yayi ba tare da yace mata komai ba ya shigewar sa mota"
Rynt ta sauke niqabinta ta kama hnyr islamiyya dmn abinda ta fhmta da kallon da ya mata yana nufin ta tafi.


Mohd kuwa yana shiga gidan ya parker motarsa ya nufi cikin gidan bai zarce koina ba sae d'akin malika ya samu ummarta tazo.
Sae bayan sun gama gaisawa snn ya fito yaje falon downstairs ya zauna zaman jiran dawowar Rynt nn ne ya ciro laptop d'insa yana wani aiki sae ga kuku ya kawo mai abinci yace"no bana buqatar abinci yau fruits kawai nake buqata kuma sae idan nayi wanka tukun,
"ok sir"cewar kuku snn ya kwashi abincin ya mayar.




Koda Rynt ta dawo ta same shi still zaune a falo sae aikin gaban sa yake,tayi kmr ma bata ganshi ba tasa kai zata wuce yace"ke zo nn"
ba musu taje"
yace"Kin raina ni ko? Tace"me kuma nayi"yace"kin sani zaman jiranki kuma shine kika shigo kmr ma baki ganni ba har kike qoqarin ficewa sbd tsabar raini ko,tace"to......shiii! bana son jin komai,je kawai ki gyara min d'akina ,kuma ki tabbatar kin fara da bathroom,tace"to idan nayi sallah zanje"ta fad'i hakane tare da Kama hnya zata wuce d'akinta, ya daka mata tsawa yace"wlh kafin na dawo masallaci na same ki a d'aki na na gaya miki"daga haka ya tafi zuwa masallaci ita kuma ta tafi d'akinta.


Tana gama sallah ta nufi d'akin shi ta fara wanke bathroom kmr yanda ya buqata don tasan meye bathroom sbd tanaji a bakin mami.


Ta fito snn ta fara gyra mishi bedroom ya shigo d'akin shaye da toka yace"kin wanke bathroom d'in ?tace"eh"yace"oya fita nn da minti d'aya sae ki dawo"ba musu ta fita shi kuma ya cire kayan jikin shi ya sanya white bathrobe ya nufi bayi.
Koda ya fito daga wanka ya samu har ta gyra koina tsaf har ma tana batun fita yace"ke dawo ciro min kayan da zan sa"da sauri ta kalle shi sbd jin zancen sa wani iri ta dae basar tace "a ina kenan?bai yi mata magana ba sae nuna mata wardrobe da yayi ,ta nufi wardrobe d'in cike da tunanin ta ina zata bud'e don bata san kanta ba asali ma bata ta6a ganin irinta ba ko a film.
Hkn ta dake zata kai hannu a jikin wardrobe d'in kenan sae kawai taga wardrobe d'in ta bud'e da kanta ta hnyr sliding, ai kuwa Rynt ta saki ihu tare da ja baya ,sae tsaki taji mohd yayi yace"bagidajiya kawai! ni je ciro min kayana kar ki 6ata min lokaci.
Kmr zata yi kuka tace"kayi hqr bazan iya ba inajin tsoro".
Tsaki ya koma yi yaje ya ciro kynsa da kansa snn ya danna wani abu a jikin wardrobe ta rufe duk Rynt na tsaye na kallon shi ya juyo yace"malama ai sae ki tafi ko?kmr dama command d'insa take jira ta fita abinta.


Fitowar ta kenan ta had'u da malika zata raka mahaifiyarta ,yi tayi kmr ma bata gansu ba tayi ficewar ta.
Mhfyr malika tace"me zan gani haka ita wace ce da har zata je 6angaren mijinki?malika ta ta6e baki snn tace"umma ai itace er matsiyata nñ wacce nake gaya miki Abbansa ya tilasta masa ya aura........ Iyye cabd'i zafa ayi er iskar yrny jibi fa yanda ta wuce mu kmr ta had'u da wasu gumaka ko wata gaisuwa babu, to umma me zakiyi da gaisuwarta ma nikam,mhfyrta tace"ba wnn ba ma me takeyi a d'akin mijin naki byn kince ba sonta yake yi ba? Ita ke gyara masa d'aki daman....... Kul! kar ki koma yarda ta shigar miki d'akin miji,kina hauka ne da baza ki gyara masa d'akin da knki ba,ni gsky umma bazan iya...... kwa6e mata baki mhfyrta tayi snn tace"ai kuwa in kika ce lalaci kina sake da baki zata qwace miki mijin,ni kinga tafiyata.
Daga haka ta fita malika tace"wae tashin bomb ai ko sama da qasa zasu had'e tayi kad'an wlh!hm umma kenan ai ruwa ba sa'an kwando bane.
Nn dai ta wuce sae d'akin mohd ta same shi yana sanya kaya tace"wae sae yanzu kayi wanka "
,to ba kin share ni ba wae ke umma tazo ,to my man umma ce fa, yace"ko ba umma bace hlnki ne idan kika yi baqi sae ki shareni, hm my man kenan kaida ba yaron goye ba har wata kulawa zan maka da baza ka iya yiwa knka ba,kallonta kawai yayi yace"jeki ga kuku nn a bakin qofa"
Da yake dama duk wanda zai shigo 6angarensa yana sane don yana gani a jikin na'urar sa da ya saita.
Malika taje ta bud'ewa kukun qofa tace"ya shigo"
Wani qaton bowl ne kuku ya shigo dashi cike tap da 'ya'yan fruits kyace wani basarake ne zaici.
Byn ya ajiye ya fita malika ta d'auki Apple d'aya tana ci,mohd dake kallonta yace"tashi ciro min freshmilk a fridge "taje ta d'auko tana mai fad'in "hln dae baka ci abinci bane my man? Yace"ina zaki sani to"shiru ta mishi dan ta fhmci yau kmr baya in gud mood.




Bayan wata d'aya da faruwar haka kullum kuwa Rynt na zuwa islamiyyarta mohd baya hanata,sae dai duk zata tafi islamiyya in ta had'u da malika a falo sae tayi ta gaya mata maganganu marasa dad'in ji har da su zagi,ta uwa har ta uba duk don Rynt ta tanka ta,amma ko tak Rynt bata ce mata asali ma a marar tarbiya take kallonta.



Mohd ne shida malika suna zaune a balcony sae firar su suke cike da nishad'i.
Nan suka hango Rynt ta dawo daga islamiyya mohd ya duba wrist watch d'in shi 4:30 yace"me yarnyr nn ta tsaya yi har 4:30 bata dawo ba sae ynz"
malika tace"au kai yau ka fara gani kenan,ai kusan kullum haka take bata dawowa kan lokaci kuma har rnr da ba'a zuwa islamiyya,fita take, what!har rnr da ba islamiyya fita ke?ta6e baki tayi snn tace"hm to kana da tabbacin ko ranakun islamiyya ,islamiyyar take zuwa ne,kullum ace bata ta6a tsallake lokaci ai ko nn abin dubawa ne,kuma ni abinda yasa tun farko ban gaya ma ba sbd kace baka so ina maka zancenta, mohd yace"dani take zancen"nn ya tashi ya nufi d'akin Rynt,koda yaje ya samu har ta fara sallah hkn yasa ya fito.




Washe gari ta kasance rnr alhamis ba islamiyya gashi mami bata gidan tana gidan pretty ta kai musu yawo, Rynt kuwa ba inda take son zuwa irin gidan inna amma tunanin yanda zata tunkari mohd take.
Har dai akayi sllr zuhur tana tunani akai da ta gama sll ta yanke shawarar zata fita idan ta ganshi ta tambayeshi ko Allah zai sa tayi sa'a.




Koda ta fito kuwa yana nn zaune a falo sae dai shida wani abokin sa ne, ta juyawar ta zata koma d'aki yace"ke zo nn"

Tana isa gurin su bata iya ko gaida su ba yace"dama kuwa an gaya min fita kike har rnr da ba'a zuwa islamiyya, shine yanzu kin fito kika ganmu kika koma sae idan mun tashi sae ki sake fitowa ko?cikin rashin fhmta Rynt tace"nifa ba fita zanyi ba kawai na fito ne na tambayeka ina son zanje gidan inna sae na ganka tare da baqo"
qarya kike yawon iskancin ki dai ya fito dake, yawo kuma nida koina bana fita sae zuwa islamiyya,yau d'in ma islamiyya ta fito dake kenan? Gidan inna fa nace maka zan tafi....wace innar byn kullum sae ta tasani gaba na baki wayata kuyi waya! cikin muryar kuka tace"to ai waya daban yanzu ina son zan ganta ne.....to ba inda zakije don haka koma daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login