Showing 159001 words to 162000 words out of 168541 words

Chapter 54 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9889

je gidan inna mutane sae zuwa barka suke tayi dan su Aamil da matan su har da pretty mtr Nasir duk sun tafi haka ma Sarah qawar Ryynt taje ita da mahaifiyar ta sbd Ryynt ta kira ta a waya ta snr da ita.





Billy Giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```




























🔮🔮🔮
*page 90*
Da dare Ryynt na d'akin inna ta gama shayarda yara sunyi bacci tana zaune tana shan farfesun naman kaza yayinda mohd ke zaune kan sofa yana sauraren inna dake tambayar sa abinda ya had'a sa da malika har ta kai ga saki uku.
Nan Mohd ya gaya mata komai bae 6oye mata ba har ma zubar da cikinta da tayi ta laqawa Ryynt.
Inna ta jinjina kae tace"cabd'i lallai wnn ba matar zama bace ja'ira gwanda da ka sake ta dan dama tun farko ni bata kwanta min a rae ba ashe kuwa da mugun nufi take ,Allah kuwa ya fita dan inshaa Allah bazata ta6a yin nasara ba har abadah.
Mohd yace"ae har umma da Abba sun so ganin laifina akan saki ukun da na mata zama d'aya amma dana musu bayani suka fahimta har ma Abba ya bani wasu addu'oin tsari yace mu riqa yi nida Ryynt har ma da yaran mu.
Inna tace"lallai ba'ayi sake ba Allah dae ya qara tsarewa"
"Amin"cewar mohd wanda ya miqe tsaye yaje gun 'ya'yansa sae kallon su yake sunata sharar bacci abinsu cikin d'an qaramin gadon su da kowannen su ke kwance cikin wali.
Sae da mohd ya gama kallon 'ya'yan sa snn ya musu sae da safe ya fita.
Inna ta kalli Ryynt dake ci gaba da shan farfesu abinta ba alamar zata raka shi
tace"yo ryynt ke har yanzu baki san hausar ki raka miji ba idan zae fita ae kya tashi kije ki masa sae da safe koh"
Ryynt tayi murmushi ba tare da tace da inna komai ba ta zari tissue ta goge hannunta da bakinta ta fito ta samu mohd har ya kae qofar fita falon ya juyo yana kallonta dan yaji motsin fitowar ta,ta qaroso gurinsa yana kallon ta yace"ae har zanyi fushi dan na d'auka baza ki fito muyi sae da safe ba"
Tace"uhm ni kuwa naga kmr ma baka ci abinci ba gashi har zaka tafi"
Yace"to ba ke bace kikayi zaune kina shan farfesun ki baki koh taya min ba"
Tace"eyyah ban d'auka zaka ci ba bari na d'auko maka akwai wani a kula amma na qassan naman rago ne"
Yace"um um da wasa nake miki ni naci abinci kawae dae zan kwana da kewar ki keda yarana"
Tace"uhm su yaran da aka haifa yau yau"
Yace"baki san yanda nake jinsu a raina bane Ryynt da bazaki fad'i haka ba inaga ma da anyi biki zan d'auke ku ne mu koma dan bazan iya baqura ba har ayi arba'in"
Tace"uhm kaima dae da wasa kake nida komawa gidanka sae nayi wata biyar"
Mohd yayi er dariya tare da jan hancinta yace"da wasa kike kema dan kina wuce arba'in baki koma ba kayan mu kawae zan kwaso mana gabad'aya sae mu dawo nn da zama"
Tace"shike nn ko inna ta sami abokan zama"
Yace"to lallai dae kam sae ki gaya mata ta tanadar min gurin da zan zauna nida matata da yarana inda zan sakata na wala ba wani wanda zae je ya takura mu"
Tace"Aa aiko d'akinta kad'ai ya ishemu mu dukkan mu har ita sae ma ka sakata ka wala ba wanda zae hanaka"
Mohd ya girgiza kansa d'auke da murmushi yace "kin ganki koh muyi sae da safe dan naga alamar tsokanar ki ba qarewa zatayi ba"
Ryynt tayi murmushi yayinda mohd yakai lips d'insa kan goshinta ya d'aura mata kiss snn ya d'ago yana kallonta yace"ki shafa min kan yarana ki masu addu'a kafin ki kwanta bacci kinji"
Ta gyad'a masa kae tare da fad'in"inshaa Allah,Allah ya tsare min kae sae da safe"
Yace"Amin my Ryynt"
snn ya fita.
Ita kuma ta juya ta koma daga ciki.


Washe gari fa'iza ce taje gidan su malika dmn jajanta mata abinda ya faru,ubanta baya gari sae mahaifiyar ta kad'ae da abin yayi mata zafi sosai har tana ikirarin sae tasa mohd qara kan irin dukan da yayiwa malika na fitar arziki.
malika bata barta ba tace ta barshi kawae don ita ta jawo komai har abin yakae ga haka,kan dole mahaifiyar ta ta bar zancen amma ba don taso ba dan ganin take ba qaramin cin zarafi akayiwa erta ba duka da saki uku a lokaci d'aya duk da cewa sane tasan abinda malika ke aikatawa na mugun nufinta akan Ryynt amma bata ga laifin ta ba sae laifin mohd da ta gani.
Malika na kwance sanye da drip a hannun ta fa'iza na zaune gefen ta tana mata sannu d'uke da alamar tausayawa a fuskarta tana kallon malika dake kallonta tana fitar da qwallah a idonta wacce ta bud'e bakinta a hankali tace"fa'iza wlh ina matuqar son my man bana jin zan iya rayuwa bashi amma gashi ya sake ni har saki uku ba wani gyaran da za'ayi na koma gareshi,shike nn yanzu gabad'aya rayuwata ta lalace ko ma nace na lalata rayuwata da kaina dmn nice na janyo faruwar komai.
Ta qarashe maganar ne cikin muryar kuka sosai.
Fa'iza ta nisa tace"malika ni kaina na tausaya miki dmn ban d'auka haka abun zae kasance ba duk a tunani na mune zamuyi nasara sae gashi Allah ya nuna mana ikon sa akan mu amma abinda nake tunani shine tunda man bae ta6a sanin kina tarayya da wani bayan shi ba zaki iya koma masa"
Da sauri malika tace"ta yaya fa'iza bayan saki uku ya min"
Fa'iza tace"ta hanyar auren d'ibar wuta"
Ni kuwa wa zan aura fa'iza?
Sweetat d'inki mana amma kar ki yarda yasan auren d'ibar wuta zakiyi dashi kinga idan anyi auren sae ki samu hanyar da kika bi ki fito masa sae ki koma ga man d'inki.
No fa'iza ko nayi hakan nasan my man ba zae maida ni ba ya riga da ya tsane ni.
Hm kawai kedae kiyi abinda nace sae dai ko idan kina shakku ko sweetat d'in naki ba zae yarda ya aure ki ba koh?
No fa'iza nasan ma zae aure ni sbd ba kad'an ba yana matuqar son kasancewa dani a ko yaushe kinga kuwa kae tsaye zae amince da aure na,matsalata d'aya shine man dana nasan ko nayi aure na fito ba zae maida ni ba.
Fa'iza tace"kedai ki gama idda kiyi auren ki fito ni nn zan gaya miki hanyar da zaki bi har ki samu ya maida ki ba boka ba malam.
Malika tace"nagode fa'iza da wnn shawara taki da tasa naji sanyi a raina domin bani da wani burin da ya wuce naga cewa na koma ga my man na kuma haifa masa yara kmr yanda yake so kuma har abadah bazan sake tarayya da wani d'a namiji ba face shi sbd bana son mu sake samun sa6ani nida shi bare zancen rabuwa.
Fa'iza tace"that's gud tun daga yanzun ma kar ki sake bari wani abu ya shiga tsakanin ki da sweetat d'inki har sae kunyi aure"
Malika tace"zan kiyaye"


6angaren Ryynt kuwa kullum man na zuwa gidan kuma sosai take samun kulawa a gun inna ita da yaran ta,ga yaran sam basa da rigima kwata kwata dan ko suna farke sam basa kukan banza sae dae idan sunji yunwa suke d'anyin kuka da kuma ta basu mamma aka had'a musu da madara shike nn suyi bacci abinsu kuma suna jimawa kafin suke farkawa.
Koda rnr biki ta matso su saliha sunyi hutu ae kuwa ba qaramin dad'i Ryynt taji ba duk da dae saliha tafi ta jin dad'in haka ma Ameera taji dad'i dan yanzu ta fara sakewa da Ryynt ba kmr daa ba ,don ko preety ma yanzu alhmdlh bata nuna tsana ga Ryynt sae ma wani janta take a jiki.
Ranar suna sosai akayi biki shagali da mohd ya darje yasa aka yankawa 'ya'yansa kowannen su
Sa da Rago biyu yayinda yaran suka ci suna.
Muhammad Ammar, Muhammad Anwar,and Aishatu Razeenah.






Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```




























🔮🔮🔮🔮
*page 91*
Bayan sati d'aya da yin biki Ryynt ce zaune a d'akinta tana shayar da Razeenah sae ga saliha ta shigo d'akin da sallamar ta,Ryynt ta amsa mata sallamar d'auke da murmushi a fuskarta,saliha ta zauna tana fad'in"maman yara kina nn sae shayarwa kike tayi ina Ammar da Anwar?
Ryynt tace"Ammar na gun Baaba hurera ta goya min shi hakama Anwar na a bayan alawiyya ta goya shi"
Saliha tace"ok dana shigo gidan sae naji tsit kamar ba kowa"
Suna baya suna shan iska ni kuma muna nn muna bacci nida Razeenah shine ta farka nake bata mamma.
Saliha tace"zakiyi fama kam idan kuka koma sauqin ki d'aya yaran basa da rigima"
Ryynt tace"wlh kuwa kuma naji ma mk yace idan mun koma en reno zae samar musu had'i da alawiyya"
Saliha tace"da yafi kam nama ji umma na fad'in wnn kàron mami bazata koma ba"
Ryynt tace"ae banji dad'i ba umma ce wae d'awainiyar zata yi yawa"
Saliha tace"ai kam abun zae yi yawa wlh"
Ryynt tace" haka dae kuke gani ya ita umma da mami suna lafiya?
Lafiya qalau suke umma ta ma ce in gaida ki keda yaranki ga ma wnn tace na baki sae ta kiraki a waya zata miki bayani.
Rryynt ta kar6i ledar da saliha ta bata tayi godiya had'e da jawo bedside drawer ta saka a ciki.
Saliha tace"tun yanzu an fara yiwa yaya gyara"
Hm saliha knn bafa kayan da kike nufi bane.
Ba wani nn kan me to za'a ce sae an kiraki a waya snn za'a miki bayani ni ba amin bayanin ba na miki.
Ryynt tayi murmushi
tace"ina jin kunyarki saliha a daina zancen nn kuma in banda abinki idan ba'a fara gyaran tun yanzu ba yaushe za'ayi?
To Ryynt ina na sani na d'auka wani abun sae kana tare da miji kake sha.
Eh akwai abinda dole sae kana tare da miji amma wnn basu bane na gyaran jiki ne tukun dan kinga tun rnr da na haifu na soma tsalki da ruwan bagaruwa sbd tana saurin warke miki ,
take kuma take matse mutum,sae dae kinyi aure zaki fi fahimta dan wani abun ma in kika sha shi sae kin qwaci kanki wlh.
Saliha tace"cabd'i da wahala knn?
Uhm kedai sae kinyi auren koma mene ne kyaji da kanki ba sae kin sami labari a bakin kowa ba.
Saliha tace"wlh Allah Ryynt ni har ko yaushe mamakin aure nakeji da bana ganin mata da miji na jin kunyar junan su wae ace rnr da aka kae amarya ko sakewa basu fara yi da junan su ba sae kiga abu ya shiga tsakanin su inyi mamakin ta yaya ma zan barka nikam.
Ryynt tace"hm saliha knn duk da dae ba haka nawa yazo ba amma wlh mazan ne da shegen wayo sae kiga suna miki laf laf sae lalla6aki suke suna kashe ki da dad'in baki har su kae ga cimma burin su kawae da safe ke ya bari da jin kunya dan dae shi ba jin kunyar zae yi ba.
Saliha tace"kae bazae ji kunya ba fa kika ce"
Ryynt tace"inafa namiji kuma ae sae dae ma yayi ta sa ki qara jin kunya dan wani ma sae ya tsinto abubuwan da kikayi fad'a a cikin faruwar abun yana fad'a miki kin jima baki nutse a cikin qasa ba shi ina ruwan sa.
Dan haka wata da muka had'u a chat da aka mata aure a kwanaki take gaya min wae ashe haka maza suke basu da kunya rnr da aka kaita ya neme ta taci kuka tana kiran umma da Abba da gari ya waye sunyi wanka sunci kwalliya suna zaune a d'aki suna breakfast kanta qasa ko kallon sa bata iya yi daga rad'a ya mata a kunne yace ni'ima mene ne ko zamu je gun umma da Abba ne naga daren jiya sae kuka kike kina kiran su,nayi dariya nace to ke me kika ce masa tace"inafa ji tayi kmr ta nutse anyi sa'a baqi sunyi sallama tayi saurin fita ta bashi guri,kuma kiji fa ni'iman ba sunan ta bane Aysha ne sunanta kawae dan yaji ta yanda yake so shike nn ya maida ta ni'ima kuma a gaban kowa kiranta yake da sunan da duk lokacin da ya fad'a sae taji kunya tunda tasan dalilin da yasa yake kira mata sunan tayi tayi ya daina yaqi ta gaji ta barshi.
Saliha tace"hm lallai maza ba kunya"
Ryynt tace"uhm kedai bari kawae"
Nan suka bar zancen saliha ta kar6i Razeenah da ta gama shan mamma sae kallonta take cike da sha'awa tace"gaskiya Ryynt mamman ki yana da kyau ji yanda yaran nn suka qara yin 6ul 6ul kamar ba en sati biyu ba wlh"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tace"ae dole wnn kunun hakukuwa na gyaran nono da inna keta d'ura min wani lokacin ma idan suka jima suna bacci mamman har zuba yake.
Saliha tace"to kuma shine ake had'a musu da madara"
Ryynt tace"eh mana nonon baya fa isar su har su uku dole sae an had'a musu da madara"
Saliha tace"kina ma qoqari wlh, ko d'aya ya aka qarasa dashi bare uku"
Ryynt tace"ae bari rnr da akayi suna da dare bayan isha'i ina cikin baccin gajiya da ya d'auko dad'i kawae naji Mk na tashi na wae in tashi in ba yaransa mamma sun tashi ae bansan lokacinda na fashe masa da kuka ba a take ya shiga rarrashina yana bani haquri,snn ya had'awa yaransa madara ya basu ni kuma tuni na koma bacci ban san ma lokacin da ya tafi ba.
Saliha tayi murmushi dan rayuwar mohd da Ryynt na matuqar birge ta bata dae ce komai ba sae tashi tayi tare da d'aura Razeenah a kafad'ar ta ta kwantar tana fad'in "bari naje na gaida su inna na dawo"
Ryynt tace"to"
Kafin saliha ke fita daga d'akin.
Da dare Ryynt ta fito daga gurin wanka ta sami mk kwance akan gadon ta idanuwan sa a lumshe kamar mae bacci sae shafa bayan Ammar yake dake kwance kan qirjinsa yana bacci,
Ryynt tazo ta zauna kan gadon tana kallon Mk da ya bud'e idon sa yana kallonta tace"Anwar fa da Razeenah ko sunyi bacci ne?
Yace"Eh suna can d'akin inna sunyi bacci amma shi ammar ya kasa baccin sae kuka da yake da alama yunwa yake ji shine nazo ina ta jiran fitowar ki amma naji shiru hkn yasa na had'a masa madara na bashi yasha yayi baccin"
Ryynt ta kae hannun ta a hankali ta shafo kan Ammar tace"Allah sarki na manta d'azun yana bacci koda aka basu madara da kuma ya tashi ba'a bashi ba shiyasa"
Mohd bae ce komai ba sae kallon jikin Ryynt yake wacce ke d'aure da towel iya guiwa tayi haske sosai ta qara kyau ga cikinta da ya koma tsaf kamar ba itace tayi kayan cikin en uku ba.
Yace"my ryynt kinyi kyau kuma jikin ki ya qara fresh me inna ke baki haka dani ta barni duk na rame"
Ryynt ta kalli jikinta d'auke da murmushi snn ta kalli nasa jikin lumui lumui kmr jikin zomo sbd laushin fata irin nasa da baka babance shida Ryynt wa yafi wani laushin jiki.
Tace"ni kuwa Mk banga wata rama da kayi ba"
Yace"Allah koh ni kuma ji nake kamar na rame"
Tace"um um gaskiya baka rame ba kana nn yanda kake,me ma zai sa ka rame to"
Yace"kewarki mana kwata kwata wlh tunda kika bar gidan baya min dad'i so lonely gashi nasan inna bazata barki ki koma ba sae kunyi arba'in"
Yana maganar ne kmr wani qaramin yaron da ke cikin damuwa.
Ryynt tace"kana fad'in arba'in nifa sae munyi wata ko uku ne"
Mohd yayi murmushi yace"ae ke nasan idan aka barki ko shekara d'aya zaki iya yi babu ruwanki da damuwar da zan shiga"
Tace"uhm Mk knn idan ban damu da damuwarka ba damuwar wa kake so na damu da ita?
Yace"to gashi kina fad'in sae kunyi wata uku bayan yanzu yanzun nn na gama gaya miki irin damuwar da nake ciki"
Tace"ka fahimce ni mana ba wae ban damu da damuwar ka bane"
Yace"ba wani nn ae na gano ki"
Ya fad'i hakane yayinda ya tashi zaune sannu a hankali rungume da Ammar a jikin sa ya tafi dashi zuwa kafad'ar sa snn ya tashi yaje ya kae shi d'akin inna ya dawo.
Ryynt na jikin wardrobe tana ciro kayan bacci yaje sukayi sae da safe kmr yanda suka saba snn ya wuce.



Sannu sannu lokaci keta tafiya wanda tuni su saliha hutun su ya qare sun koma school Ryynt kuwa har tayi arba'in.
Su Ammar sun qara yin 6ul 6ul da kyau abin sha'awa don duk wanda ya gansu sae yaji yana son d'aukar su har dae yanda sukayi saurin wayo dan idan ba'a gaya maka arba'in kawae akayi ba zaka d'auka ko en wata uku ne.


Da dare guraren bayan isha'i mohd ne tafe cikin mota shida Ryynt yaransu na baya tare da allawiya.


Mohd dake driven bae zarce koina ba sae gidan sa wanda tun lokacin da ya shigo gate d'in gidan Ryynt ke kallon sa da mamaki har ya parker mota kafin tace komai wayar sa tayi qara ya d'aga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login