Showing 126001 words to 129000 words out of 168541 words

Chapter 43 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9146

🔮🔮🔮🔮
*page 76*
Malika ce ta kirashi wacce tana gama waya dashi ta kalli qawar ta faiza dake tsaye kusa da ita a bakin gate ta rakota, tace"kinji my man a cikin kwanakin nn zae dawo amma wae sae yaje Germany tukun"
Faiza tace"yin me kuma?
Malika tace"mtsw ni bansan uwar me zae je yi ba wlh yanda na matsun nn ya dawo har ji nake kmr nayi tsuntsuwa naje na same shi amma shi na fahimci kmr ma sam ba missing d'ina a tare dashi sae harakar gaban sa da yake"
Fa'iza tace" haba ae kinsan dole yana cikin missing d'inki tunda shi ba qarfe bane,amma keda kike tare da switat d'inki yana d'an d'ebe maki kewa meye na damuwa"
Malika ta dalla mata harara snn tace"kinji ki nifa manage kawae nake dashi wlh don baza a ko ta6a had'a my man da shi ba, dmn my man qarshe ne gurin iya sarrafa mace samun irinsa a cikin maza sae an tona, shiyasa ko a mafarki bana fatan ganin rabuwa ta dashi.
Faiza tace"hm ae kuwa tunda kika koma a ruwa kina cikin had'ari dan duk rnr da man yasan kina tare da wani d'a namiji bayan shi sunanki sorry"
Malika tace"hm fa'iza knn hkn ma ba zae ta6a faruwa ba,don bazan ta6a sakacin barin sa har ya gano ni ba,dan haka kima daina min baki"
Fa'iza tace"hm ni ba baki na miki ba idan dae zaki daina to walillahi hamdu ni kinga tafiya ta sae gobe idan kin shigo, kuma dan Allah karki 6ata mana lokaci don nasan halinki da baqin African time kmr akan ki aka fara.
Malika tace"to naji"
Daga haka ta juya ta koma daga ciki yayinda fa'iza taja motar mijinta da tazo da ita ta bar layin.


Man kuwa yana gama waya da malika ya koma daga ciki yayi tsaye yana kallon Rynt sae ci gaba take da baccin ta.


Guraren qarfe biyar tuni Ryynt ta tashi suna zaune gefen gado ita da man wanda ke rungume da ita yana ciyadda da gasasshiyar kaza da fresh milk.
Ryynt bata wani ci sosai ba tace ya isheta.
man yace"No Ryynt ki d'an qara ko kad'an ne kinji"
Tace"um um ya isheni sae anjima ko zan qara"
Bae ce mata komai ba sae sauran fresh milk d'inda ke cikin cup ya qarasa shinyewa ya ajiye cup yana mai kallon yanda ta d'aura hannunta kan cikin ta nn shima ya d'aura hannun sa akan cikin nata yana mae kallon fuskarta da kulawa yace"mene ne?
Murya can ciki tace"ba komai motsi kawae yake min"
Mohd ya shafi cikin yace"motsin ae ba zafi koh?
Tace"um um babu zafi akwae damuwa dae"
Yace"shi motsin?
Tace"eh mana ni ban so"
Mohd yayi d'an nurmushi yana kallon Ryynt wacce ta qarashe zancen ne cikin shagwa6a.
Bae ce mata komai ba sae shafa cikinta da ya ci gaba dayi ita kuma ta lafe kmr mae bacci tana shaqar daddad'an qamshin turaren sa.
Sukayi shiru tsawon lokaci abinsu d'akin yayi tsit kmr ba kowa sae can mohd yaje zuwa janye jikin sa a hnkli Ryynt ta d'ago ta kallesa tace"fita zakayi?
Yace"eh zan fita ne me kike so?
Tace"zan bika"
Yace" yi haquri bari idan jikin ki yayi sauqi sosai sae mu fita koh"
Ba musu ta gyad'a masa kai shi kuma ya d'aura mata kiss kan goshi ya tashi tare da fad'in sae na dawo"
Ryynt tace"Allah ya tsare min kai"
Mohd ya tsaya cak ya dawo ya zauna yana kallon ta d'auke da murmushi yace"dan Allah maimai ta min me kika ce"
Ryynt ta sadda kanta qasa d'auke da murmushin jin kunya tana wasa da zoben yatsar ta wacce cikin murya can ciki mae dad'in sauraro tace"nace Allah ya tsare min kae"
Mohd dake kallonta sae yaji ya qara sonta cikin jin dad'i ya d'ago fuskarta d'auke da murmushi ya d'aura mata kiss kan lips yace"Amin my Ryynt ina sonki Allah ya bar min ke"
D'auke da murmushi tace"Amin"
Ta bisa da ido har ya fita snn ta kwanta tare da janyo pillow ta rungume a hnkli had'e da lumshe ido tana murmushi.




Sae da ya d'an jima kafin yake dawowa ya sameta zaune falo ita da mtr Amir sae fira suke abin su suna kallo,
Ryynt ce ta fara ganin sa,
ya sakar mata murmushi ta mayar masa yayinda take kallon ledodin da ke hannun sa tana son tashi ta tarbo sa amma kuma tana jin kunyar matar Amir wacce ta shiga gaisawa dashi,suna gama gaisawa da ita ya shiga daga ciki ita kuma ta kalli Ryynt wacce ke zaune abinta ba alamar zata tashi,ta saki baki tace"Ryynt ya haka mijinki ya dawo ba sannu da zuwa kuma ba alamar zaki je ki tarbe sa kika bar sa da kaya a hannun sa har ya shige"
Ryynt tayi murmushi kawae ta sadda kanta qasa, mtr Amir ma tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta miqe tsaye d'auke da Sadiq da yayi bacci tace"in dan nice nikam kinga ma tafiya ta"
Ryynt tace"Aa dan Allah yi zamanki"
Matar Amir tace"kinji ki da wani zancen kedai sae anjima Allah ya baki lafiya ya kuma tsare gaba"
Ryynt tace"Amin"
Matar Amir ta fita ita kuma ta shiga daga ciki.
Man dake tsaye jikin wardrobe sae jin yayi ta rungumo sa a hnkli ta baya tace"sannu da zuwa"
Ya juyo d'auke da murmushi ya shafo fuskarta yace" sannu my Ryynt ya jikin naki"
Tace"Alhmdlh bana jin komai sae zafin allurar da ka matse ni aka min"
Tayi mgnr ne tana kallon sa d'auke da yanayin shagwa6a a fuskarta.
shi kuma ya lakato hancin ta yace"to ai kece kika qi tsayi sae kuka da kike tayi kina qoqarin guduwa sae kace kinga mae d'aukar rae"
Ta turo baki a shagwa6e tace"to ai zafi ne da allura gashi har yanzu sae zafi take tamin"
Yace"to yi hqr bari na qara murza miki sae ta daina miki ciwo koh"
ya fad'i hkne yayinda ya qara janyo ta zuwa jikin snn yakai hannun sa a bayanta yana murza mata gurin ta yanda gurin zae yi saurin watsewa.
Ryynt tace"wash"tare da qara qanqame shi snn tace"uhm uhm ciwo kamin a hankali"
Ya qara rungume ta yace"sorry kar kiyi kuka kinji hkn zae fi saurin watsewa"
Nan yaci gaba da murza mata gurin ita kuma sae wash take fad'i tana qara shigewa jikin sa har ta fara masa kuka.
Kan dole mohd ya barta ya d'ago fuskar ta sae rarrashinta yake yana share mata hawaye yace"is ok kukan ya isa haka muje na nuna miki wani abu da na siyo miki.


Nan yaja hannun ta sae jin dad'i take taga mene ne.
Kan bed ya fara zaunar da ita snn ya jawo ledodin da ya shigo dasu ya ciro wata er qaramar leda mae d'an akwatiñ sarqa a ciki ya bud'e
ya ciro wata dakakkiyar sarqar diamond simple design mai matuqar kyau iri d'aya da zoben da ya saya mata.
Wani irin dad'i Ryynt taji har ranta ta qar6i sarqar tare da qanqame sa tana masa godiya yayinda man ke kallonta d'auke da murmushi
tace"ya naga iri d'aya da zobe na?
Yace"wlh nima haka kawai yau ina komawa shagon da muka siyo zoben nagan su wae ashe kowane zobe idan kana ra'ayi akwai sarqar su har ma da abun hannu, rigimar ki ce bata bar na fahimta ba"
Ya qarashe mgnr ne cikin zolaya tare da kai hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro bracelet yace"kinga abun hannun har dashi na siyo maki"
wani irin dad'i Ryynt taji fiye da na farko ta kar6i bracelet d'in tare da qara qanqame shi tana zuba mishi godiya man kuwa sae kallonta yake cike da so yana murmushi dmn yanzu bashi da wani burin da ya wuce yaga Ryynt cikin farin ciki ako yaushe.
Da kanshi ya saka mata sarqa da en kunne da kuma abun hanun ya jata sukaje gun mirror a nn fa ta kasa rufe bakinta dan sarqar ta mata kyau ba kad'an ba har ma ta rasa ta yanda xata qara gode mishi sae hugging d'in sa da ta qara yi tare da masa peck ,
shi kuma ya d'auke ta cak yana juyi da ita kmr wata er baby sae qyalqyatar dariya take har ya kaita kan bed ya sauke.


Washe gari da dare bayan sunyi shirin bacci suna zaune kan bed manne da juna suna cin popcorn suna kallo cike da nishad'i ,
man ya kalli Ryynt wacce ta kwantar da kanta a kafad'ar sa,yace"gobe kad'ai fa muke a garin nn inshaa Allah don haka gobe da safe sae ki shirya muje ki siyo en tsaraba"
Ryynt ta d'ago fuskarta tana kallon sa tace"to Allah kaimu goben,su maman Sadiq fa yaushe zasu koma ko a nn zamu bar su?
Yace"No ae Amir ya kammala abinda yazo yi tare zamu koma har ma Germany duk tare zamu je muyi kwana biyu sae mu wuce Nigeria.
Daga haka sukayi shiru Ryynt ta jawo wayarta ta soma chart man dake kallon ta ya kar6e wayar yace"baki san cewa idan ana tare da mai gida ba ba'a yin chat lokaci ne da zaki bashi kulawa"
Ya qarashe mgnr ne yana murmushi ita ma tayi murmushi tace"yi haquri ganin nayi wae ba ma yin komai sae kallo kuma ni na gaji da yin kallon"
Sae da ya kashe TV snn yaja hancinta yace" to ai nima na gaji da yin kallon sae kimin fira mae dad'i inji"
Tace"uhm sae dae idan kai zaka bani labari"
Yace"ke ba kiyi labari ba sae ni Ryynt"
Tace"To ni ina zan sami labari nida ba fita nake ba"
Yace"to ae ba dole sae labari zaki bani ba"
Nan takai hannu a hankali ta shafo cikin sa tace"ni kuwa me zan baka naga dae baka jin yunwa"
Yace"ae ba abinci kad'ai ne abinda mata zata bawa mijinta ba"
Tace"to ni kuwa me nake da shi da zan baka?
A hnkli ya shafo cikinta tare da fad'in"to tunda ba kya da abinda zaki bani ni inada abinda zan baki wanda zan qarawa babyna qwari"
Tace"uhm kmr y......bata qarasa fad'a ba kawae taji bakin sa a cikin nata yayinda yakai hannu ya kashe musu wutar d'akin.














Billy Giro😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [3/25/2017]


```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 77*
Washe gari da asuba mohd ne ya fara tashi ya kalli Ryynt dake bacci abinta lafe cikin qirjin sa.
Sae da ya yaye blanket d'in jikin su snn ya shiga shafa bayanta a hnkli yana kiran sunan ta.
Amma shiru ba alamar zata tashi gashi lokacin sallah yana gab da qurewa hkn yasa ya tashi zaune rungume da ita a jikin sa yana ci gaba da tashin ta kmr farko.
Da qyar ya samu ta shiga motsawa cikin muryar kuka irinta shahwa6a tace"uhm uhm mene ne"
Mohd yace"sorry tashi muyi sallah sae ki koma baccin kinji"
Tace"to"
Ta tashi tare da janyo blanket ta rufe jikinta tana lalubar rigar baccin ta kasancewar d'akin ba haske sosai sae mohd ne ya kunna wuta ya nemo mata rigar ya saka mata suka tashi suka nufi bathroom sukayi brush da arwalla suka fito.


Bayan sunyi sallah har sun koma kwanciya Ryynt ta kasa bacci sae juyi da ta soma yi da qarshe ma kwanciyar ta gagare ta sae tashi tayi zaune ta had'e kai da guiwa takai d'ayan hannunta kan cikinta ta dafe.
Cikin fargaba mohd ya tashi zaune yana kallon ta ya janyo ta zuwa jikin sa tare da d'aura hannu sa akan cikin ta yace"Ryynt me yake faruwa?
Murya can ciki tace"bazan iya bacci ba yunwa nake ji"
Ajiyar zuciya ya sauke a natse snn yace"olryt ina zuwa"
Nan ya tashi ya nufi kitchen ya bud'e fridge ya ciro gasasshiyar kaza da ya siyo jiya suka ci d'aya suka bar d'aya yasa a microwave yayi warming bayan tayi ya fitar ya saka a plate ya had'o da fresh milk da cup ya fito.
Ya same ta zaune kmr yanda ya bar ta.
Ya jawo stool ya d'aura akai snn ya zauna yayinda Ryynt ta matso gab dashi ta zagaya da hannun ta kan waist d'in sa tare da kwantar da kanta a qirjinsa ya fara ciyadda ita har sae da tace ya ishe ta snn ya bata fresh milk tasha ya zaro tissue ya goge mata bakinta ta lumshe ido tare da qara lafewa a qirjin sa ya shiga shafa bayanta sannu a hnkli har tayi bacci ya maida ta ya kwantar snn shima ya kwanta tare da rufa musu blanket ,yayinda take manne a jikin sa sae shafa cikinta yake har yayi bacci.


Basu suka tashi ba sae guraren qarfe goma ,
kai tsaye suka shiga bathroom sukayi wanka suka fito kowanen su sanye da white bathrobe suna tafe d'auke da murmushi a fuskar su rungume da juna kmr wasu couples.
Ryynt ce ta fara janye jikinta daga na mohd taje zuwa gyaran bed shi kuma yaje gun dressing mirror ya shiga shafa Vaseline bayan ya gama ya kalli Ryynt wacce har ta gama gyara gadon tsaf, ta nufo shi sae kallon d'an tulun cikin ta yake da ya tura bathrobe ,
tana qarasowa ya riqo hannunta ya zaunar da ita kan cinyoyin sa suna kallon juna ta jikin mirror ya d'aura hannun sa kan cikinta yace"wae kinga yanda cikin nn ya qara girma kuwa"
A shagwa6a tace"eh wlh ni har kunya nakeji yanzu kowa ya kalle ni lokaci d'aya yasan akwai ciki a tare da ni"
man yayi murmushi yace"Ryynt cikin da ba na shege ba meye na jin kunya kuma"
Tace"akwai kunya mana tunda ba haka kawae cikin ke fitowa ba dole sae da faruwar wani abu da kowa ya kanga yasan mene ne"
Ta qarashe mgnr ne had'e da turo baki Mohd dake kallon ta yayi er dariya tare da d'aurawa bakin nata kiss snn ya kafe idonsa a cikin nata yace"mene ne abun ni ban sani ba gaya min wane abu ne akeyi har a sami ciki?
Ryynt ta kalle sa kawae ta sadda kanta qasa tana murmushi .
Mohd yace"gaya min mana ina saurarenki ko ba kya son na shiga cikin masana ne nima"
Tace"uhm nidae muyi mu shirya kasan kace fita zamuyi fa"
Har Mohd zae yi magana sae kuma yayi shiru yana sauraren yanda cikin ta ke motsawa a hnkli,sbd still hannun sa na kan cikinta,
ya kalle ta d'auke da murmushi yace"bari to na qarawa babyna kuzari sae mu shirya mu tafi"
Cike da jin kunya taje zuwa tashi ya maida ta yace"jiya fa kad'an nayi kin sani"
Ryynt tayi saurin kallon sa don jiya ba qaramar gajiya ya saukar mata ba.
Ta shagwa6e fuska kmr zatayi kuka ya lakato hancinta yace" da wasa nake miki fa"
Nan tayi murmushi yaja hannun ta riqe da Vaseline suka je kan bed ya cire mata bathrobe ya kwantar da ita yana shafa mata mae cikin wani salo mae had'e da matsa mata jikinta yana gama shafa mata man ne yayi kwance kusa da ita suna fuskantar juna ,
ya kai hannu a hnkli ya shafo gefen fuskarta tare da d'aura mata kiss kan goshi yace"ko zamu fasa fita ne yau don naga daren jiya na saukar miki da gajiya sosai u have to rest,kina buqatar hutu"
Ryynt dake yawo da hannun ta kan qirjinsa cikin lallausar murya tace"ba gobe ne kace zamu tafi Germany ba?
Eh amma sae mu fasa har zuwa jibi don bana son jigilar ta miki yawa.
Tace"um um in dae gajiya ce ae tabi gado"
Ta fad'i hkne tare da saurin rufe fuskarta, mohd yayi murmushi tare da kai hannu kan qirjinta yana shafawa yace"to amma shine da nace zan qarawa babyna kuzari kika tsorata ko kina jin zafin abun sosai ne wae?
Ta girgiza kanta tare da tashi zata bar gurin ya janyo ta yace"gaya min da bakin ki inji kina jin zafi sosai ne?
Yafad'i hkne tare da janye hannuwanta da ta rufe fuskarta,a nn tayi saurin cusa fuskarta gabad'aya cikin qirjinsa tace"plz Mk ka canza wani zancen dan Allah kunya nake ji wlh"
Mohd ya d'ago fuskarta d'auke da alamar tambaya yana kallonta yace"Mk kuma me kenan kike nufi?
Ryynt tayi murmushi tace"kai da sunan ka kuma,to yi nazari ko zaka gano"


Mohd yayi shiru yana nazari cikin 3 scnds yace"mohd kabeer kike nufi koh?
Tayi murmushi tare da gyad'a masa kai,
Shima yayi murmushi tare da lakato hancinta yace"kin ganki wace irin kwanya ce Allah ya maki wae"
Tace"Uhm ai kaine mai kwanyar kaida ka gano cikin d'an qanqanin lokaci,inace ba wanda ya ta6a kiran ka da sunan dae ko?
Yace"ko d'aya kece first person amma meyasa kika yi nazarin had'a sunan nn?
Tace"sbd nafi so na kiraka da sunan da ba wanda ya ta6a kiran ka dashi sae ni kad'ai"
Yayi fari da ido Yace"ko meyasa to?
Tayi murmushi kawai ta riqo en yatsun sa tana wasa dasu tace"in tambaye ka meyasa kake bearing da mohd Aminullah Nasir baka bearing da sunan Abba?
Yace"Mohd Aminullah shine sunan da aka zana min,Nasir kuma sunan kakan mu ne nake bearing dashi.
Tace"to ya kaji Mk kana ra'ayin na riqa kiran ka dashi?
Yace"Ni kuwa nake so my Ryynt dmn sunan ya min dad'i sosai uwa uba kuma ke had'a shi amma kuma zan so nasan dalilin da yasa ba kya son kirana da sunan da kowa ke kirana da shi.
Shajen fuskar sa ta shafo tana murmushi tace"sbd a gurina kai na daban ne da zan so na ke6ace komai naka a daban dana kowa"
man dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login