Showing 132001 words to 135000 words out of 168541 words

Chapter 45 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9864

ci abinci ba?
Yace"zanje inda za'a bani ba tare da na roqa ba"
A nn tayi saurin sadda kanta qasa d'auke da hawayen da suka cika mata ido don sae taji wani irin kishi duk da taga yanda suka kwashe shida malika a airpot.
Murya can ciki tace"yi haquri muje na baka"
Yace"tafi kawae kici inda kike son ci d'in ni ki barni na tafi abuna"
Hawayen da suka cika mata ido ne suka silalo a hnkli ta share hawayen jiki sanyaye ta juya zata bar gurin,
Jiki sanyaye mohd ya riqo ta yace"meye na kuka kuma Ryynt inace kinfi ra'ayin kici abincin a tare da su shiyasa nace ki tafi"
Ryynt tace"Allah ba wani nn fushi kayi "
Ya janyo ta zuwa jikin sa yace"to yi haquri kuma ni ba fushi nayi ba dama na gwada ki ne kawai inga ko kina son mijinki da gaske sae naga ashe ke dad'i miji ce da ba kya son ganin fushin sa.
Da wasa ta sha toka tace"me kake nufi?
Ya d'aura mata kiss kan lips yace"abinda kika fahimta shi nake nufi"
A shagwa6e ta maqale kafad'a tana doka qafafun ta qasa tace"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"
Ya lakato hancinta tare da fad'in"ba wani nn na gano ki ae"
Kuka ta fashe dashi ta shiga kai masa duka irinta ta shagwa6a tana fad'in"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"
A nn Mohd ya shiga kare dukan sae dariya yake ita kuma sae ci gaba da dukan sa take tana fad'in ita ba dad'i miji bace shidai ne haka ba ita ba nn ya kama yatsan ta ya gantsara mata d'an qaramin cizo ya gudu ya barta sae kukan shagwa6a take tana yarfi da hannu yaje kan darduma ya zauna tabi shi ta kama yatsan sa ta rama ya shiga yarfi da hannu sae dariya take masa dan da gaske ta cije shi, ganin zae kama hannun ta ya rama ta tashi da sauri ya biyota dai dai inna ta fito taje bayan inna ta la6e sae gwalo take masa tañà dariya.






Sorry 4 dis one


Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 79*
Nan mohd ya shiga qoqarin ganin ya janyota inna bata barshi ba sae fad'in take wae muhammadu lafiyarka?
Yace"Inna cizo na fa tayi"
Ryynt tace"wlh inna shine ya fara ni kuma na rama"
Ta qarashe mgnr tare da yi masa gwalo bata ankara ba sae ganin tayi ya jawota tace"wayyo Allah yi haquri inna zae rama dan Allah ce yayi haquri bazan sake ba wlh"
Inna taje zuwa qwace ta mohd yace"inna wlh ba abinda zan mata abinci zamu ci"
Ryynt tace"inna ba wani nn ramawa zae yi"
Ta fad'i hkne yayin da take yunqurin komawa ga inna amma bata iya ba dan man sae d'aukar ta yayi cak tana wuntsil wuntsil da qafafu har yaje da ita kan darduma nn inna tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta tafi ta basu guri dan ta fhmci mohd ba kunya ne da shi ba.
Ryynt kuwa cikin fushi ta kalle sa tace"wae meyasa kake min abubuwan da kake sa ina jin kunya dan Allah ban so ka daina"
Ta qarashe mgnr cikin muryar kuka mohd ya d'aura mata kiss kan lips yace"to naji yi hqr muci abinci"
Ta tashi tare da fad'in"banci"
Mohd ya riqo ta ta buge masa hannu yayi saurin kama hannun nasa had'e da fad'in "Ash!
ya yaye hannun rigar sa wata irin babbar yankuwa ta bayyana yayinda hannun farar rigar sa ta ciki duk ta lalace da jini.
Da sauri Ryynt ta koma ta zauna ta riqo hannun sa tana kallon gurin ta kalle sa idon ta tap da qwallah tace"mk me ya same ka haka?
Bae ce mata komai ba sae kallon yankuwar yake yana tuna lokacinda yaja malika zae kaita d'aki ne wuqar hannunta ta yanke sa garin fizge fizgen ta.
Ya kalli Ryynt wacce duk ta rud'e tana basa haquri had'e da tambayar me ya same shi .
ya shafo fuskarta yace"d'an wani tsautsayi ne ya same ni d'azun da na fita amma kar ki damu kinji"
Ryynt da hawaye suka silalo kan fuskarta ta kalle sa tace"wnn ne d'an jifa yanda yankuwar tayi babba sosai warkewar ta ma zae yi wuya"
Ta qarshe mgnr ne cike da son fashewa da kuka.
Mohd da saurin kukanta ke bashi mamaki gashi baya son ganin kukan nata ko kad'an ya janyo ta zuwa jikin sa yace"don't cry mana Ryynt jikina baya da matsala take naji sauqi kar ki damu kinji"
Ryynt ta d'ago tare da share hawayen ta ta tashi tare da fad'in "to ina zuwa"
Ya maida ta yace"no yi zamanki bana so inna ta sani"
Tace"ba gaya mata zanyi ba first aid case zan d'auko"
Yace"yi zamanki kawae idan na fita zanyi dressing d'in gurin don idan inna taga kin d'auko first aid kit d'in dole zata nemi dalili"
Ryynt ta gyad'a masa kai tana kallon yankuwar da ya maida hannun rigar sa ya rufe.
Ya sakar mata murmushi yace"to muci abinci koh"
Fuskar ta cikin damuwa ta bud'e plate suka fara cin abincin tana bashi yana bata har suka kammala cin abincin.
mohd ya tashi zuwa sllr magrib.
Ita kuma ryynt sharp sharp ta kwashe kwanikan abincin ta kai kitchen snn ta tafi d'akinta ta sami su saliha tuni sun kammala cin abincin su,
Saliha na bathroom gurin yin arwala mami kuwa sae fmn game take da game tap d'in ta.
Ryynt ta kar6e game tap d'in ta kashe tace"mami ana yin kirayen kirayen sallah kina yin game ki daina ba kyau kinji"
Mami ta washe baki tace"to Aunty na daina amma yaushe zamu koma gidan yaya"
Ryynt tace" idan kun koma gida ki gaya ma umma a had'a maki kayanki idan zan koma sae mu koma kinji"
Mami ta daka tsalle ta rungume Ryynt tace"da gaske Aunty?
Ryynt tayi murmushi tare da gyad'a mata kai.
Sae ga saliha ta fito daga bathroom Ryynt ta tashi ta shiga.


Sae da suka ida sllr magrib da d'an jimawa Nasir yazo ya kwashe su ya maida su gida.
Ryynt kuwa d'akin inna taje sae firar bayan rabuwa suke cike da nishad'i.

Mohd kuwa tunda ya fita sllr magrib ba shi ya dawo ba sae bayan isha'i.
Kai tsaye d'akin inna ya nufa ya gaida inna dake jikin wardrobe ta saka dardumar sallah ta amsa gaisuwar yayinda man ya saki baki yana kallon Ryynt wacce zata shiga bathroom sanye da zani d'aura gaba da hijabi har guiwa riqe da brush a hannunta
yace"keda nazo muje gida kuma wankan me zakiyi"
Tayi murmushi tace"nifa a nn zan kwana"
Yace"hm da wasa kike kema yi sauri je yi wankan ina jiranki kizo mu tafi"
Inna tace"kai dae keyin wasa muhammadu ae Ryynh ba inda zata je sae ta min kwana biyu tukun"
Mohd yace"dan Allah inna daina zancen nn"
Inna tace"yo muhammadu kmr ya na daina zancen nn ,kwanaki da yawa bana tare da Ryynt su en kwana biyun da zata min na rage kewar ta kuma kace a'a"
Inna ba haka bane indai Ryynt ce gobe sae na kawo maki ita,
Inna tace"to muhammdu nuna min ka fini iko da ita.
Fuskar sa d'auke da damuwa yace"ba haka bane inna ina laifin dae ko kwana d'aya"
Inna tace"Aifa sae ka d'auke ta ku tafi ban hanaka ba"
Ba yanda mohd ya iya yace"Aa inna yanda kike so haka za'ayi"
Nan ya tashi cikin damuwa had'e da kallon Ryynt wacce kanta ke qasa yace"idan kinyi wankan ki sameni falo muyi sallama"
Ta gyad'a masa kai snn ta bisa da kallo har ya fita taje cikin murna ta qanqame inna tace"inna na gode nsn da nice ma ba zae bar ni ba"
Inna tace"inafa koni ai dan nasha masa toka ne amma ke kuma Ryynh meyasa baza ki bisa ku tafi ba naga fa kmr ya shiga damuwa sosai"
Ryynt tayi shiru ita kanta tana son bin sa amma kuma tasan idan ta bishi zata kwana cikin quncin rashin sa a kusa da ita dmn in ga adalci gun malika ya kamata ace ya kwana,shiyasa take son ta kwana biyu tukun in yaso idan ta koma sae ta fara koyon sa ma kanta haquri.
Tace"inna ni nafi so kawae na kwana a nn"
Inna tace"to shike nn ae tunda yana da wata mtr ba matsala bane jeki abinki kiyi wanka amma fa kar ki jima kinsan fa yace yana jiranki"
Nan Ryynt ta wuce bathroom tayi wanka sharp sharp ta fito ta shirya cikin riga da wando na bacci ta saka hijab ta fito tayi tsaye jiki sanyaye ganin mohd baya falon knn ya gaji da jiranta ya tafi ko kad'an bata ji dad'i ba amma hakan ta juya zata koma ciki sae ga mohd ya shigo ta sauke ajiyar zuciya a hnkli tana kallon sa tare da sakar masa murmushi tace"ae na d'auka ko ka gaji da jirana ka tafi har banji dad'i ba"
Sae da mohd yaja hannunta suka zauna kan doguwar kujera snn ya kalle ta yace"dan na tafi ae ba damuwar ki bane farin cikin ki ne tunda har kika yarda zaki kwana biyu ba tare da ni ba"
Tace"yi haquri kwana biyu ae kmr yanzu ne in ga rae da lafiya da kuma yardar ubangiji"
Yace"a gurin ki ba amma ni a gurina tamkar shekaru biyu ne"
Tace"uhm bacci ne fa kawae baza mu riqa yi a tare ba dan nasan zaka shigo gobe ae ko?
Yace"um um bazan shigo ba"
Tace"meyasa ko ka manta da zancen zuwan mu family house"
Ban manta ba driver zan turo maki tunda ni kin gaji da gani na.
A shagwa6e tace"wlh Aa ba haka bane sae dae in kaine ka gaji da gani na"
Yace"ta yaya Ryynt nida na shiga damuwa jin zaki kwana har biyu ba tare dani ba amma ke ko a skin har ma Allah Allah kike kar nace ban yarda ba"
Ryynt ta marairaece fuska tace"Mk ba wae ban damu bane dole zan damu ae kasani,kuma kayi haquri kar ka turo min driver kazo muje tare kaji,sae dae kuma kmr mun shiga haqqin mtr ka ko?
Kallon ta mohd yayi dan shi ya ma manta da wata malika yace"hm nifa wasa nake miki da kaina zan zo muje bari naga baby na tafi dare nayi"
Nan ya kai hannu zae yaye mata hijab ta riqo hannun tare da fad'in"in ga"
Nan ta yaye hannun rigar sa a hnkli taga har yayi dressing d'in gurin da ya yanke ta kalle sa da damuwa tace"sannu"
Ya lumshe ido tare da gyad'a mata kai sae kuma ya saki murmushi yana kallonta kmr wanda zae ce wani abu sae kiss ya d'aura mata kan lips yace"ina sonki Ryynt"
Ryynt tayi lallausan murmushi tare da sadda kanta qasa shi kuma yakai hannu ya yaye hijabin ta har rigar ta ya shafi cikin ya duqa ya d'aura masa kiss ya d'ago ya kalli Ryynt dake kallon sa d'auke da murmushi ya shafo gefen fuskarta tare da d'aura mata kiss kan kumatu yace"sae da safe koh"
Nan suka tashi a tare mohd ya nufi qofa Ryynt ta bisa da ido har yasa qafa zae fita ta kira sunan sa a hnkli ya juyo a natse yana kallonta taje kmr mae jin kunya ta d'aura masa kiss gefen fuska snn ta sadda kai tace"Allah ya tsare min kae"
Mohd da har ransa yaji dad'i ya shafo fuskarta d'auke da murmushi yace"Amin my Ryynt nagode"
Snn ya fita had'e da yi mata bye bye ta juya jiki sanyaye ta shiga ciki.


Man kuwa yana isa gida d'akin malika ya nufa ya bud'e d'akin ya same ta tana waya da fa'iza yayinda take cewa"wlh kuwa da gaske nake gaya miki fa'iza duk makircin da na qulla mata a banza ya maida auren wae har ma tana d'auke da ciki tulele dashi ,
Shine d'an baqin son haifuwa ya wani kwasheta suka tafi waje abinsu suna holewa ashe shine dalilin da yasa yace min kar inje.
Fa'iza tace"wlh duk kuskuren ki ne malika in banda wauta irin taki ta yaya zaki gayawa qanwar sa pretty yanda komai ya faru, ae kin san dole ta gaya masa kin ma ci sa'a da yaji bae sake ki ba ya fita harakar ki kawae.
Malika tace" faiza ba haka bane pretty sam bata snr dashi ba dan na kirata tayi min bayanin komai abinda ya faru da bana nn ashe er banzar tun kafin ya sake ta ne ta sami cikin nice kawai ya maida er iska yana nuna min sam bata gaban sa bayan komai yana wankana a tsakanin su.
Fa'iza tace"lallai ya kamata ki d'auki babban mataki don wlh yaci zarafinki da yawa.
Malika tace"Hm bari kawae fa'iza wlh sae tayi nadamar sanin my man a rayuwarta don sae nayi ajalinta da ita har abinda ke cikinta kuwa"
Fa'iza tace"hm ni wlh man har mamaki ya ban da har ya iya kula wnn abar har ya bar wani abu ya shiga tsakanin sa da ita .
Malika tace"fa'iza yarinyar ce akwai diri da kyaun jiki shiyasa tun farkon ganinta nayi qoqarin ganin na raba ta dashi dmn nsn yau da gobe zata iya janye masa hnkli na dawo er kallo.
Fa'iza tace"ita wnn abar er qauye baqa da ita ma"
Malika tace"itafa kallon tsaf ne baki mata ba,dan idan ma kika ganta yanzu to wlh sae kin raina kanki.
Fa'iza tace"hm ta raina kanta dae don wlh in nice tun a airport sae dae wata ba ita ba kai har shi d'in ma in ya matsa sae na had'a dashi don nafi gwammace mu rasa gabad'ayan mu.
Malika tace"kinsan ina son my man ba kad'an ba baxan iya masa haka ba kawai dae ita zan hallaka wlh don ba'ayi macen da zata ra6e sa na barta ba.
Fa'iza tace"hm aini duk rnr da mijina yamin irin haka to kuwa na barsa har abada duk sonda nake masa wlh ki tsaya nn garin kallon ruwa kwad'o ya maki qafa,baqin cikin d'a namiji ya kashe ki a banza yanxu gashi ya rufe ki a d'aki ya barki ya tafi abinshi da ace lokacinda ya same ki kin fara ta kanshi ai da tuni itama kin gama da ita.
Malika tace"hm fa'iza bazaki gane irin son da nakeyiwa my man bane kuma shima yana matuqar sona ta yaya zan cuci kawunan mu akan wnn abar kawae dae yanzu jiransa nake yazo ya bud'e ni,
to kuwa ko ta halin qaqa daren yau bazan bar barta ba wlh........qarar wayar man ce ta katse ta don sam bata ji shigowar sa ba duk mgnr nn da suka jima suna yi kuwa.
A tsorace tayi saurin katse wayar tana kallon man dake zaune kan sofa ya jingina bayan sa ya d'aura qafa kan qafa yayinda ya bar wayar sa naci gaba da ring a cikin aljihun sa ba alamar zae ciro ya d'aga sae malika da yake kallo.
Ya tashi cikin tako d'ai d'ai har ya qaraso gurin ta yana mata wani irin kallo ita kuma gabad'aya tasha toka dan kar ma yaga damar ta.
A natse cikin deep voice yace"qarya kike ba kya sona malika babu wata soyayya ta a tare dake, kina sona zaki hallaka min abinda nayi matuqar qwallafa raina akan shi don kawae biyan wata banzar buqatar ki,to bari kiji wlh ni duk kin fita a raina sakin ki a gurina ba komai bane kuma idan kikayi gigin wani abu ya sami Ryynt kin san sauran amma dan Allah ki fara gwadawa tukun ki gani shege ka fasa kije tana can gidan inna kin dad'e baki hallaka ta ba.
Daga haka ya kama hanya ya fita.
Malika ta bi sa d'auke da idanun ta da suka kad'a sukayi jajur suka ciko tap ta qwallah.
Aguje hawayen suka fito suna sauka akan kumatun ta ,ta share hawayen da takaici tace"wlh in kasan wata baka san wata ba.


Washe gari guraren qarfe goma man ne ya fito cikin shirin sa na farar suit sae zuba qamshi yake yaje ya shiga farar motar sa da aka wanke masa aka goge yaja ya fita ya bar gidan.
Malika dake tsaye a balcony tana kallo koda ya fita snn ta juyawar ta ta koma ciki.
Man kuwa kai tsaye gidan inna ya nufa bai sami kowa a falon ba haka ma d'akin inna nn ya tafi d'akin Ryynt ya sameta kwance taci kwalliya abinta cikin wani dakakken less black mai d'auke da pink big flowers tana riqe da waya a hannun ta tana chat yayinda d'an qaramin bakinta mae d'auke da pink lipstick ke d'an motsawa a hnkli alamar tana cin wani abu.
Qamshin turaren sa ne yasa ta d'ago ta kalli bakin qofa ta ganshi jingine jikin qofar hannuwansa a cikin aljihu yana kallonta d'auke da murmushi sbd ba qaramin kyau yaga tayi mishi ba itama sosai taga ya mata kyau ta sakar masa murmushi kafin take tasowa ta rungume sa a hnkli tana mishi sannu da zuwa.
Mohd ya shafo bayanta a hnkli yace"mun tashi lafiya?
Tace"lafiya lau"
Ya d'ago ta ya shafa cikin ta yace"to ya babyna"
Tace"shima qalau"
A nn ya kalli d'an qaramin bakinta dake motsi yace"me kike ci?
Tace"chewing gum ne"
Yace"da safen nn Ryynt kinyi breakfast ne?
Tace"eh"
ok inna fa naje d'akin ta ban sameta ba?
Tana bathroom wanka take,ya hannun naka kaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login