Showing 42001 words to 45000 words out of 168541 words
Chapter 15 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
kan qirjinsa had'e da cewa "sorry".
Cikin tsananin mamaki da jin haushi ta kalli abinda yake shirin yi don sae a lokacin hnklinta ya gama dawowa jikinta,ai kuwa tayi saurin hana faruwar hkn ta tashi da sauri zata bar gadon ,by mistake hannunta ya latsa wani guri a jikin gadon abin mamaki da ban tsoro a gun Rynt sae kawai taga wasu silalan fararen qarafe na fitowa kowane gefe ta jikin gadon,ihu ta saki ta sake komawa jikin mohd ta qanqame shi amma ta kasa d'auke idon ta akan abinda ke ci gaba da faruwa don wani farin qyalle tagani shar shar kmr net yana biyo ta jikin qarafen har ya lullu6e su sae gadon ya zama kmr suna cikin wata kyakkyawar rumfa ne mai kyan gaske.
Kuka ta fashe masa dashi tace"wlh na gaya ma d'akin nn aljanu ne dashi dan Allah ka ftr dani ,na roqe ka"
Kallon ta mohd keyi yanda ta rud'e sosai tana kuka don jikinta har qyarma yake,yakai hannu ya danna wani guri a jikin gadon sae kawai komai ya shiga komawa a hnkli har gadon ya zama tamkr ba shine ya musu rumfa a d'azun ba.
Ya kalli Rynt dake qanqame a jikin shi snn yace ni d'akina ba aljanu gidadanci ne kawai irin naki sae ki tashi ki fita duk kin wani cumuimuyen min a jiki haka"cikin kuka had'e da masifa tace ba aljanu amma d'azun aka kwasheni akayi sama dani"yace"wnn kuma ya rage naki nidai ki fita nace"tace"ai ko baka ce va ynxn fita zanyi"
ta fad'i hakane kawai amma kuma bata iya sauka kan gadon sbd tsoron kar ta sake ta6a wani gurin, ganin haka yasa mohd ya saukar da ita, ta kalle shi shaye da toka snn tabar d'akin,cike da alqawri a ranta bazata qara tako qafar ta a d'akin ba.
Haka ko akayi don tun daga rnr Rynt bata qara komawa d'akin mohd ba ,wanda yanzu an d'auki lokaci sosai don har su saliha sun dawo hutun makaranta suna batun komawa first term.
Duk tsawon lokacin nn mohd shi ke gyara ma kansa d'aki sbd duk lokacinda ya aika mami Rynt taxo ta gyara mai d'aki sae tace bata jin dad'i.
Malika kuwa takaici ma ne yace ta gyara mai d'aki don acewar shi in banda qara lalata mai d'aki ba abinda ta iya.
Yau ya dawo a gajiye daga asibiti ga d'akin nasa yana buqatar gyara ya aika mami yace taje ta gaya ma Antinta tazo ta gyara mai d'aki ta dawo masa tare da saqon wae anti tace bata jin dad'i.
Tashi kawai yayi ya tafi sae d'akin Rynt ya sameta zaune tana duba littattafanta na islamiyya sbd rnr,rnr alhamis ce basa zuwa islamiyya .
A fusace ya d'auke littattafan ya d'aura su kan bedside drawer snn yace"bana son raini tashi kije ki gyara min d'akina! Shaye da toka tace"nifa bana jin dad'i"da Allah maza tashi ai baki zo nn gidan dan kiji dad'i ba!tace"nifa ina nufin bana da lafiya.....cikin mugun hasala ya nuna ta da yatsa yace"kar ki kuskura na koma jin wnn kalmar a bakin ki, yau wata kusan nawa kenan duk nace ki gyara min d'aki kice ba kya jin dad'i sbd kin raina ni ko shine har kike tunanin zan ci gaba d'aukar miki rainin,to bari kiji wlh duk baki je kin gyara min d'aki ba ,ba ke ba zancen bokon nn kuma ba wanda ya isa ya tilsatani na saki!daga haka ya fita kmr zai tashi sama, yabar Rynt qwallah cike tap a idonta tana tunanin in taje aljanun d'akinsa zasu iya sake cirata sama su yar wata qil ma wnn karon mutuwa zatayi ba suma ba, gashi kuma bokon nn tayi bala'in qwallafa ranta akai har kullum ma qidayar kwanaki take inda yau sauran ta kwana uku ta fara zuwa mkntr boko gashi har ma an d'inka mata uniform saura littattafai da takalmi.
Tana cikin share hawayenta ne sae ga saliha ta shigo, tace"Rynt lafiyar yaya naga yaja mota a hasale ya fita! Rynt tace"Yauwa saliha tun da ya fita dan Allah taimakamin kije ki gyara masa d'akin sa...ke wlh ni bazan iya da halin yaya ba kawai kije ki gyara masa keda yasa,saliha bazan iya bane d'akinsa tsoro ake ban dan Allah ki taimakamin kije ki gyara masa kafin ya dawo wlh yace idan ban gyara masa ba bazan yi boko ba kuma kinfi kowa sanin yanda nake son nayi bokon nn"ta qarashe mgnr kmr zatayi kuka saliha tace"nifa fad'an sa nake yiwa gudu ba komai ba"Rynt tace"kawai kije ki gyara duk fad'an da zaiyi aini zai yiwa tunda bai san cewa ke kika gyara d'akin ba, shiyasa ma nake son kiyi sauri kafin ya dawo dan Allah.
Da qyar dai saliha ta yarda ta tafi,wacce ta fara gyra masa d'akin kenan sae ga mohd ya shigo d'akin fuskar d'auke da 6acin rai sosai.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [1/22/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
_*page*_ *```33```*
Gabad'aya saliha ta gama tsorata da ganin yanayinsa,yayinda take roqon Allah yasa ta 6ace 6at kafin ya qaraso gareta.
Mohd kuwa a fusace ya qaraso gab da ita sae huci yake yace"uban me kika zo yimin a d'aki !dake nake ki bani amsa!! A tsorace tace"yaya wlh qaddara ce amma don Allah kayi haquri wlh Allah bazan sake ba"
Kunnen ta ya kama ya shiga yi mata fad'a sosai sae kuka take tana bashi hqr sae can ya sakar mata kunne yace"Oya fita na daina ganin ki a nn stupid gal!da sauri ta fita d'akin har tana had'awa da gudu,sae ga malika ta shigo d'akin wacce dama ita ce ta kira mohd a waya ta snr dashi cewa Rynt fa taqi zuwa ta gyra mai d'aki kmr yanda yace,sae saliha tasa a cewar ita ta gaji da gyarawa qaton banza d'aki.
Dmn duk wani abu da ya faru na fad'an da mohd yaje yayiwa Rynt tana la6e,har ma lokacinda saliha tazo duk sae da taje ta la6e,shine fa ta had'e qarya da gsky ta gaya mai.
Tace "wlh my man wnn abar ta rainaka da yawa amma ka kasa maganin ta na rasa meyasa,yace"ni kaina malika na rasa meyasa ta raina ni haka wlh!
Hm my man maganinta ne bakayi shiyasa.
Tsaki kawai yayi ya fita daga d'akin.
Saliha kuwa tana fita d'akin Rynt ta nufa tana shiga Rynt tace"ya akayi ne saliha ko ya dawo ne? Komai saliha bata ce ba sae d'aukar jakarta tayi ta fita.
Rynt ta biyota tana fad'in "saliha kimin bayani mana"
sam saliha bata saurara mata ba tayi ficewarta.
Ita kuwa Rynt tana kawowa bakin qofa tayi kici6is da mohd da qarfi ya turata ta koma ciki ya kuma rufe qofar da key.
Inda kai tsaye ya yakai hannu kan wuyan hijabinta ya rabashi biyu, a firgice Rynt tayi saurin kama hijabin ta riqe tace"malam meye haka dan Allah!
bai kulata ba sae hijabin ya fizge ya yar ,ta koma d'auka ta rufe jikinta.
Sai kawai yaje yayi zaune abinsa kan sofa ya d'aura qafa kan qafa yana juya belt d'in hannunsa a hnkli snn ya kalli Rynt da taje jikin wardrobe zata nemo wani hijabin yace"ki ma daina wahaladar da kanki don kaf kayan jikin ki ne zan raba ki dasu sbd ni sam bana dukan mutum da kaya a jikin shi, ta fiddo ido waje cike da tsoro tace"kenan kai d'an iska ne"yace"eh sosai yanzu kuwa zan nuna miki"ya taso gadan gadan zai zo gurinta.
Tace"Aa dan Allah kayi haquri wlh zanje na gyra ma d'akin ka indan shine "
Idan na gama dukan ki ba ya fad'i hankane tare da fizge hijabinta ya jefar ya kamo wyn rgrta zai yaga...tace"wayyo dan Allah kayi hqr"ta qarashe mgnr tare da fashe masa da kuka tana roqon shi yace"shin saliha bata gaya miki horon da nake musu bane da suna en yara"cikin kuka sosai had'e da girgiza kanta tace"wlh Aa bata gaya min ba"yace"to kiji kaf qannai na duk wanda yamin laifin duka se ya cire tufafin sa nake dukan sa sbd ni ba sakaran mutum bane da zan daki mutum da kaya a jikin shi, kuma duk na daki mutum sau d'aya to ko da kuskure bazai qara min laifin da zan sake dukan shi ba, amma ke sbd a iya qafafun ki kad'ai na daka shine kika sake min wani laifin duka wae har ni zaki duba ki kira qaton banza,yana kawo nn sae jin tayi bata tare da rgr jikinta don zama d'aya ya yage ta ya jefar ,ya zamo vest kad'ai ke jikinta sae kuma zani ,wani irin kuka ta fashe dashi mai cin rai had'e da saurin durqushewa qasa,tana girgiza mai kai tana ja baya sbd yanda yake matsowa kusa da ita, cikin zafin nama ya miqar da ita tsaye tayi saurin sa hannayenta ta kare qirjinta tace"idan kai musulmi ne na roqe ka da girman Allahn da muke bauta ma kar ka rabani da kayan jikina"hannu yakai ya jaye tsorayen kalabarda suka soma rufe mata fuska snn ya d'ora hannayensa kan kumatun ta da hawaye keta fmn sintiri yace"na barki sbd girman fiyayyen halitta amma ki sani bake ba boko har abada!
Nn ya juya ya fita ,ita kuwa taje kan bed cikin tsananin kuka taja blanket ta rufe jikinta har wuya nn ta had'e kai da guiwa tana ci gaba da kukan da duk wanda ya gani zai d'auka ko kaf duniya an mutu ita kad'ai aka bari a raye sbd baqin cikin yanda ya rabata da hijabinta har rgrta sae duk taji duk duniya ba wanda ta tsana kmr shi,sbd still cikin su ukun nn tafi yarda a ranta cewa shine dai makashin babanta.
Qofa taji an turo tayi saurin d'agowa don ta d'auka ko shine ya dawo, sae taga malika ce wacce ke d'auke da shu'umin murmushi a fuskar ta tace"kad'an kenan daga cikin sharrin na,dmn ni ba'a taka ni a zauna dai dai,inace yanzu kin fara ganin kuskuren ki na auren mijin da ba naki ba,wanda kwata kwata ba'a halitto shi wa kowa ba sae ni kad'ai,amma sbd kwad'ayin duniya irin naki kika shigo sabgar da ba taki ba,kika lalata min tsarin rayuwata gabad'aya, to bari kiji wlh idan har bakiyi gaggawar rabuwa da mijina ba nice zan zamo ajalinki.
Kmr bada Rynt take zancen ba don tun lokacinda Rynt ta d'ago taga wace ce ta maida kanta kawai taci gaba da kukanta,har kuwa ta fita.
Har kusan kwana biyu Rynt bata bar kukan abinda mohd ya mata ba sbd taji ciwo sosai fiye da zaton mai karatu,dmn idan aka cire mutuwar mahaifinta to shine abu na farko da tafi jin ciwon sa a duniya.
Duk kwana biyun nn mohd na shigowa d'akin Rynt da safe kafin ya tafi asibiti,wanda duk shigowar da yake ganin ta yake zaune kan bed ta had'e kai da guiwa kuma har ya fita bata d'agowa bare zancen gaida shi.
Sallar zuhur ta gama snn ta tashi tayi shirin islamiyya ta fita.
Bayan sun tashi da qarfe hud'u a maimakon ta koma gida sae napep ta nema ta tafi gidan inna.
Mohd na zaune shida malika kan dining inna ta kirashi a waya sae masifa take mai,
kan dole ya ajiye zancen cin abinci ya tafi gidan inna.
Inna tasa shi d'aki shida Rynt tace"sae naji Rynt tazo min da wani zance wae ba zaka barta tayi boko ba,yace"bata snr da ke laifin da tamin bane inna.....Yo dan bata je ta gyara ma d'aki ba har shine wani laifin da za kace ba za tayi boko ba,to bari kaji ubanka kabiru ma bai isa ya hanata bokon nn ba bare kai,boko kam sae Rynh tayi shi kmr kowa don ba za'a barta a baya ba,kuma dolenka ka d'auki nauyin krtn tunda mtrka ce,yace"gsky inna kiyi hqr don na riga da yanke hukunci.....inna ta dunqule yatsu ta watsa mai tace"ubanka! nace ubanka kabiru! yo har ni zaka duba kace ka rigada ka yanke hknci sbd ban haifeka ba ko,ko d'aya ba hk bane inna sae fa da na gaya mata duk bata je ta gyara min d'aki ba bokon ta ne haka wae shine don ta raina ni ta saka saliha wai ita ta gaji da gyrawa qaton banza d'aki har ni zata kira qaton banza !Rynt tace"wlh Allah inna bance masa qaton banxa ba..... A fusace mohd ya taso xai bugewa Rynt baki, tayi saurin tashi ta koma bayan inna ta la6e ,inna ta tashi tace"yo da dukanta zakayi to"cikin yanayi na 6acin rai yace"to inna ni sa'anta ne da zata qaryata"
inna tace" lallai Muhammadu sam albasa bata biyo hln ruwa ba indai kace dukan mace kake, don ubanka kabiru duk iya shegenda uwarka take mai bai ta6a sa hannu ya dake ta ba, kai kaf ubannanka ba mai dukan matar sa, sae kai zaka ce ka fara sbd baqin zuciya irin taka,
nn ta maidà dubanta gun Rynt da ta soma kuka tace" zo zauna abinki ya dake inga inshi shashan yaro ne.
Sae da ya koma ya zauna snn Rynt ta iya zama yace"inna ki barni kawai da yrnyr dan Allah ki ftr da bakin ki a cikin zancen nn......naqi na ftr d'in shashan yaro ai kwanaki kafin aurenka zowa kayi nn ka nemi na roqa maka alfarma agun mahaifinka don ka samu kaga ka auri wnn yrnyr er marasa mutunci ,shine yanzu tunda burinka ya gama cika har ni kake cewa na daina sako bakina a cikin zancen ka ,iye lallai Muhammadu yau ka nuna min ban isa dakai ba.
Ta qarashe mgnr ne cikin muryar kuka irin nasu na tsafi d'in nn.
Cikin nuna damuwa mohd yace"inna ba haka bane wlh yrnyr nn tafa ranani sosai wanda dole ya kamata ace na d'auki mataki akai......yo muhammadu ita Rynh d'ince ta rainaka yrnyr er albarka wacce ba ruwanta da kowa, kuma ai tunda na sako bakina a ciki ya kamata ka haqura koma mene ne idan kuma banda wani matsayi a gurinka shikenan sae ka tashi ka tafi ai inada kud'in da zan sata mkrntr ba wai rasawa nayi ba.
Kauda kansa yayi gefe cike da takaici yace"ki barshi kawai zan sata d'in"
inna tace"bama so! kuma idan kaje gidan naka ka aiko min da duk kayan Rynh don a nn zata zauna tayi bokon ta"
Nan Mohd ya shiga ba inna hqr ba don yaso ba har ya samu ta haqura.
A tare suka fito shida Rynt wacce har takai hannu zata bud'e murfin mota ta shiga ya daka mata tsawa yace"bana son raini tare mukazo ne!
Kallon sa kawai Rynt tayi snn ta juyawarta ta kama hnyr fita riqe da er ledar ta da inna ta bata mai d'auke da kular d'an wanke a ciki.
Tana fitowa gate d'in gidan sae mota ta gani a gabanta ta faka, snn aka zuge glass d'in motar a hnkli
qoqarin kaucewa take sae taji muryar munir yana cewa"Rynt ina yini"kallon sa tayi sae kuma tayi saurin sadda kanta qasa tace "yaya munir barka da wuni"yace"lfy lau yasu inna da mohd tace"suna lafiya"
Dukkan su sukayi shiru can munir yace" Rynt sae kuma naji.... yayi shiru sbd hawayenda suka cika mai ido, Rynt ma hkn ce ta kasance a gurinta,kmr daga sama taji muryar mohd yana cewa"ke je shiga mota gani nn zuwa.
Ba musu ta wuce sbd kar kukan da take ji ya qwace mata mohd kuwa ba yabo ba fallasa ya ba munir hannu suka gaisa har ma yana tmbyrsa mutanen gida.
Sai da suka gama gaisawa snn munir yaja motarsa shi ma mohd yaje ya shiga tasa motar,
Da shigar sa ya kalli Rynt wacce tayi saurin sa hannu tana share hawayenta,kauda kansa yayi had'e da tsaki snn yace"da kina sonsa meyasa baki aure sa ba sae ni kika cutar"komai dae Rynt bata ce mai ba sae kauda kanta tayi gefe tana kallon titi.
Da dare Rynt ce ta gama sllr isha'i tayi zaune shiru tana tuna irin wnn lokaci ne byn sllr isha'i mutanen qauyen su suka d'auki gawar mahaifinta izuwa maqabarta har tabi su tana ta kuka har sae da matan qauyen suka rirriqe ta......shigowar mohd ne ya katse ta ta kalle shi sau d'aya ta kauda kai tare da kai hannu ta share hawayen fuskarta.
Yazo ya miqa mata wata babbar leda dake hannunshi yace"kar6i"ta kai hannu ta kar6a ba tare da ta ko kalle shi ba"yace"fito da duk abubuwan da ke cikin ledar"
Sae da ta qara share hawayenta snn tayi komai yanda yace.
School bag ce baqa mai kyau wankan gefe da littafan makaranta da biros da duk wani abu dai na aikin aji sae takalman mktrnta baqaqe da farar socks har da sabon niqabi yace" ki gwada takalman idan sun miki shikenan idan kuma basuyi ba kibawa mami ta maida min"
Still sae da ta sake share qwallah snn ta gyad'a masa kai, shi kuma ya fita ba tare da ya damu da ganin kukan da take ba.
Koda ta gwada takalmin dai dai qafar ta takai ta ajiye komai a cikin wardrobe d'inta sae ga mami ta shigo d'akin itama da nata kayan makarntar sae murna take itama za'a sata boko.
Washe gari da safe mohd ya shigo d'akin yace da Rynt ya kyn komai yayi?tace"eh amma uniform sun min yawa, yace"u are very stupid! tun yaushe uniform d'in suke hannun ki baki tashi gaya min ba sae yau, wae ke bagidajiya ko, nifa ba haka bane ban duba kayan bane sae yau, oya je gwada kayan kixo in gani,tace"kawai ni a rage min ba sae na gwada ba"yace"ai sae kiyi ta zama dasu hkn nn tunda baza ki iya gwadawa ba, ya fad'i haka ne tare da juyawa zai bar d'akin tayi saurin cewa "dawo zan gwada,nn yaje kan sofa