Showing 15001 words to 18000 words out of 168541 words

Chapter 6 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9133

sae da ta dan yi nisa snn ta dan juya don ganin ko yana kallonta,Xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin biyo ta ma yake, ta kara sauri gabanta na faduwa ssae, gashi bbu alamar mutum a layin, ganin duk saurinta har ya kusa cim mata yasa ta kwasa a guje ko minti biyar ba ayi ba ta isa gida har lkcn gudu take har da kukanta, mai gadi na tambayarta me ya faru bata ko sauraresa ba ta nufi kofar shiga falo da gudu, a bakin kofa suka ci karo da Muhd dake tsaye yana jujjuya makulin motarsa alamar xae tafi, suna mgna da inna, hkn yasa Rayyanat ta fasa ihu, ya koma baya da sauri lkci daya ya turata da karfi ta fadi nn kasan falon, inna ta mike da sauri ta karaso bakin kofar tana salati tana tambayar me ya faru, Rayyanat da ke mayar da numfashi ta fashe da kuka ssae, inna duk ta rude ita ma ta saka kukan ta xube nn gabanta, baaba hurera ta fito da sauri tana tambayar lfya, sae ga mai gadi shima ya taho da sauri yana tambayar me ya faru, Muhd kam don takaici komawa gefe yyi ya tsaya, cikin kuka inna ke kallon mai gadi da Baaba hurera tace "nima ban san kukan da take ba" baaba hurera ta shiga tambayar Rayyanat me ya faru, da kyar ta tsaida kukanta muryarta na rawa tace "wani mutumi ne sae yyi ta kallona idan xa ni makaranta, shine yau ya biyo ni sae na fara gudu yana ta bi na kuma" ta karashe mgnr cikin matsanancin kuka, juyawa Muhd yyi ya fice daga falon mai gadi ya bi bayansa, lkci daya inna ta tsuke fuska ta miqe tana share hawayen fuskarta tana huci tace "dan gidan uban waye shi xae biyo min ke da gudu, hurera dauko min gyale na" hurera tace "A'a inna, ba ga su Muhammadu sun fita ba" inna tace "da'alla bani mayafina in je in masa rashin mutunci" hurera ta dauko mata gyalenta ta bata, ta fixge ta fice daga falon kmr xata tashi sama, a bakin gate suka hadu da Muhd da mai gadi, Muhd yace "ina xa ki kuma inna" ba tare da ta kallesa ba tace "nemo dan iskan xan je yi mana" yace "bbu kowa a waje na duba, ita bakauyiyar wace gari ce da xata d'aga ma mutane hankali hka, kila ma harkan gabansa kawae yake xata shigo ta daga ma mutanen gida hnkli, tsiyar yan kauyen nn knn"


Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






30/12/2016






🔮```13```🔮
Cikin gida suka koma tunda ba a ga wanda ake neman ba, inna dai sae masifa take tayi kmr wacce ta sami wanda ake nema a gabanta.
Mohd kan takaici tun daga kan gate bai ma dawo ba jan motar sa kawai yayi yabar gidan.
Inna ta rarrashi Rayyanat ta samu har ta daina kukan da take taje d'akinta ta ajiye jakarta ta cire niqab da hijab da socks ta nemi guri xata kwanta sbd har yanxu jikinta bai daina rawar tsoro ba. Inna ce ta shigo d'akin riqe da kofin fura a hannunta,
ba ita tabar d'akin ba har sae da Rayyanat ta shanye furar tas.




Har dare Rayyanat bata sake kmr kullum ba kallo suke amma sae tunanin gobe take idan zata je islamiya.
Nasir ne ya shigo gidan da sallamar sa ,suna gama gaisawa inna ta bashi lbrn abinda ya faru da Rayyanat d'azun ,
ya kalli Rayyanah da kulawa yace"bai dai maki komai ba ko? Sae da ta girgiza kanta snn tace"bai min komai ba amma nasan ko gobe zan ganshi in na fita don kullum sae na ganshi idan zan tafi makaranta"
ta qarashe mgnr kmr wacce zata yi kuka.
Nasir ya nisa yace har da safe kike ganin sa idan zaki tafi makaranta? Aa bana ganinsa da safe sae da yamma"
To shikenan da yamma zanzo kiyi tafiyar ki kar ki nuna tsoron komai don so nake na gane dalilin bibiyarki da yake,kar kisa tsoro dmn ina nn a bayanki kinji,a sanyaye ta gyad'a masa kai .
Inna tace"ai kowane d'an iskan ne gobe ma kwashe ta nida shi"
Nasir yace"ai ba girmanki bane inna ki barni dashi kawai"...yo shi girma ya sani ne da zai biyo er qaramar yarinya haka duk yabi ya tayar mata da hnkli gabad'aya yau ta rasa sukuni.
Ai inna ina ganin irin en iskan samarin nn ne da basa da abinyi sae zaman banxa.
Inna ta tsuke fuska tace"to Rayyanah kam baza tayi komai dashi ba don ya ma kama
gabansa tun wuri.
Nasir yayi murmushi ya sauya wata firar suka ci gaba dayi,
can inna ke tambayar sa wai ina er banzar nn Fatima ta shige da na daina jin d'uriyar ta, Nasir ya shafi kansa yana murmushi snn yace"inna ai pretty ta jima bata jin dad'i sbd laulayin da take fama dashi"
Dad'i inna taji sosai har da su taka rawa ta kusa samun kama kunne tace"ai bari shi kuma d'an banzan nn yazo marar son aure ,yazo yayi auren nn ko shima zanga abinda ya haifa kafin nabar duniya.
Duk cikin taka rawa inna ke maganar nn Rayyanat har da er dariyar ta don rawar inna ta bata dariya sosai.




Washe gari da yamma har Rayyanat taje ta dawo bata had'u da kowa ba,
tare suka shigo ita da Nasir inna na ganin su ta shiga tambayar ko anga mutumin ?Nasir yace"ba muga kowa ba sae wasu masu zama gurin"
wani dogon tsaki muhd dake kishingid'e yaja yace"wai inna me yasa kike biyewa bagidajiyar yarinyar nn nikam,kawai mutane na harkar gaban su ta wani ce ya biyota in miji take nema taje can qauyen su mana ta samo irinta ba tazo nn tana fakewa da wani ya biyota ba,
wane kidahumi ma zata samu a nn da har zai yi lokacin ta in ba wanda uwar sa ta masa baki ba.
Sosai maganar mohd tayi wa Rayyanat baqiqirin a rai duk yanda taso 6oye hawayenta sae da suka gangaro kan kumatunta tayi saurin share hawayen ta shige daga ciki ,mohd dake kallonta cikin 6acin rai sae a snn ya kauda idonsa ya maida su gun inna da ta shiga sirfa mai masifa kan yafita harkar Rayyanah har tana fad'in "sae na had'a ka da ubanka kabiru idan baka fita harkarta ba wlh.
Nasir ne ya shiga bata haquri shida baaba hurera dake aiki kitchen ta jiyo fad'an ta fito"
mohd kam barin gidan yayi sai haushin inna yake ji dake fifita Rayyanah akan shi har tana sako ubansa a ciki.




Yau kusan kwana biyu mohd bai zo gidan inna ba inna bata damu ba sai ma harkar gabanta take.


Rayyanah ce a bayan gida ta gama wankin kayanta dana inna tana shanya wacce sae ta sharce zannuwan kafin take shanyawa.


inna tazo ta same ta tace"oh ni wai Rayyanah wanki kika xo kina mana keda ya kamata ace kinyi shirin islamiya !uhm inna ai na kammala yanzu zanje in shirya "to Rayyanah yi maza amma dan Allah ki daina wankin nn nasha gaya maki akwai mai min wanki har ma naki d'in duk ki daina wankewa idan sun taru ki kawo na had'a da nawa kayan na bawa abu mai wanki ya riqa wanke mana kinji.
Rayyanat ta gyad'a mata kai inna ta washe baki snn tace"to yayi er albarka yi maza ki shirya ki tafi makaranta.

Tafe take cike da fargaba don har yanzu bata cire ran zata sake ganin wanda ke bibiyar ta ba gashi yanxu nasir yayi tafiya bare ya rakota kmr yanda yayi mata a kwana biyun nn da suka wuce.
Sai sauri take har tana hard'e qafafu jin alamar ana binta a baya dmn har sautin tafiya tana ji ,
kan tsananin tsoro bata iya juyawa ba sae ma duqawa tayi zata kwashi takalmanta ta banka da gudu.
Sae taji an mata sallama cikin murya mai mugun taushi da sanya natsuwa ga duk wanda yaji hkn yasa ta fasa abinda tayi niyya sae dai cike da 6acin rai ta miqe dmn ganin wanda ke neman takurata a rayuwa.




Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






30/12/2016






🔮```14```🔮
Murmushi ya sakar mata duk da ba ganin fuskar tata yake ba kansancewar niqab d'inda ke sanye da ita.
Kafin ya ce komai ta buga mai uban tsaki tace"wai malam lfy kake faman bibiyar rayuwata!wani murmushi ya sake sakar mata yakai hannu cike da natsuwa ya shafo sumar kanshi snn yace"sbd ina sonki"harara ta dallah mai had'e da tsaki "ta tafi ta barshi nn tsaye,
Bai bita ba sae tsayuwar sa ya gyara tare da hard'e hannuwan sa a qirji yana kallonta har ta 6ace ma ganin sa.
Juyowar da zaiyi ne sukayi ido hud'u da Man dake masa wani mugun kallo na tsana yace"kai amma ka bani kunya wlh kai yanxu baka ga abin bibiya ba sae wnn abar "uhm man kenan wnn ce abar yrnyr da ta koina ta amsa kiran mace har mace ga natsuwa da kamala .....mtsw! Man yaja tsaki yace"ga dukkan alama ka fara shaye shaye shiyasa kake ganin abu baibai,nn ya tafi ya barshi kmr wanda zai tashi sama.
Gidan inna ya nufa ya sami inna da baaba hurera zaune a tsakiyar gidan suna fira.
Ya gaida su sae baaba hurera kad'ai ce ta amsa gaisuwar ,
inna dake harararsa ganin zai shigar mata d'aki tace"me kuma zakayi min a cikin d'aki bayan duk gamu nn a waje"baaba hurera tace"ke ko dai inna mai gida ne fa ai kya tashi ku shiga ciki kiji dame yazo,
ai nasan ba abinda yazo dashi face tambad'a da iya shege,ni kwana biyun nn ma da baka zo ba sae naji sat kmr an cire min qaya.


Kujerar zaman mata naga man ya jawo wacce su inna ke zaune kan irinta yasa farin handkerchief d'insa ya share snn ya zauna yana fuskantar inna d'auke da murmushi a fuskar sa yace"ashe inna in na mutu kin huta dani kenan... zaro ido tayi tace"me kuma ya kawo zancen mutuwa ana zaune qalau, to inna ke kika ce kinji dad'i da banzo kwana biyun nn ba, yo dan nace haka Muhammadu ai bazan yi ftr ka mutu ba nida nake son ganin 'ya'yanka kafin na bar duniya tukuna ma wai kai don ubanka yaushe zakayi auren ne kullum kana mana yawo da hnkli baka ko son ana zancen,
ni ka gaya min idan kana fama da rashin lafiya ne inji dan insan ta inda zan fara nemar ma magani, sajen fuskar sa ya shafo yana kallon inna wanda har lokacin da murmushi d'auke a fuskar sa yace"inna me kuka dafa yau? Ban sani ba ina ma magana kana wani zancen, oh ni Hajara wai ko dai muhamnadu gamo kayi da aljana da duk ana ma zancen aure sae ka canza da wata maganar,ta qarashe mgnr cikin kuka irin na tsafi d'in nn, mohd ya kalle ta da kulawa yace"nifa inna kinsan na tsani na ganki kina kuka indai aure ne nayi kusa nn bada jimawa ba inshaAllah"
Kai zo kuka farin ciki gun inna har da su rawa tana yiwa man kari kan irin farin cikin da yasa ta yau ta jashi zuwa d'aki sae zuba
masa albarka take yayinda baaba hurera tabi su da kallo tana dariya dn har lokacin inna rawa take man kuwa sae murmushi yake don shi yana son ko yaushe yaga inna cikin farin ciki .
Inna da kanta taje ta kawo mai abinci wacce yinin rnr duk cikin farin ciki tayi shi.



6:5pm
Rayyanat ce ta shigo gidan ta dawo daga makaranta ta sami man kwance a falo kan 3 seater kmr mai bacci don idanuwan sa a rufe suke, tsaye tayi tare da yaye niqab d'in fuskar ta tana masa kallo mai cike da tsana,
karaf idanuwansu suka had'u tayi saurin kauda idonta tare da gaishe shi ba tare da ta damu da ya amsa ko kar ya amsa ba tayi ficewar ta zuwa d'akinta.
Da sauri man ya tashi ya bita ya finciko hannunta da qarfin tsiya har sae da jikinsu ya had'u sae kuma yayi saurin ture ta daga jikin nashi ya nuna ta da yatsa yana fad'in"ba nayi warning d'inki kan wnn d'an iskan kallon da kike min ba ,wlh ina mai gaya miki duk na qara kama ki kina min irin wnn kallon na lafira sae yafi ki jin d'adi!dan ubanki inni sa'anki ne ko kuma abokin wasarki!
Zama d'aya qwalla ta ciko a idon Rayyanah kan jin zafin zagin da ya mata,ta d'ago tana kallonsa haka shima kallonta yake har hawaye suka fara sakkowa a hnkli kan kumatunta .
Ya watsa mata mugun kallo snn ya bar d'akin Rayyanah kuwa share hawayenta tayi snn ta ajiye jakar hannunta ta cire hijab da socks ta kai su a muhallinsu.
Tayi zamanta a d'aki har sae da ta tabbatar mohd ya bar gidan snn ta fito taje d'akin inna wacce tana ganinta ta washe baki tana tarbon ta da murna kyace ta kwana bata ganta bane.





Bayan sati d'aya da faruwar haka Mohd ne zaune a office d'insa yana waya kan cewa "a bashi ixini ya shigo"ya ajiye wyr ba jimawa aka turo qofa ya kafe wanda ya shigo da ido har ya zauna.
Hannu suka bawa juna suka gaisa snn wanda ya shigo ke cewa"Man magana naxo muyi mai muhimmanci kuma dan Allah kar kayi poking d'ina"man dake jingine ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya snn yace"ina jinka"
Kallon sa yayi da kyau yace"about wnn yarinyar ne da nake bibiya idan zata tafi islamiya ashe ma ka santa"da sauri man ya bud'e idonsa dake rufe yace"aka ce maka na santa who say so? Nop ba wanda yace kawai ni naga hkn sbd a kullum gidan inna nake ganin tana shiga haka kuma gidan take fitowa"to ban santa ba nima ganinta kawai nake a gidan"
A sanyaye mutumin yace"to naji ganin ta kawai kake da haka nake so ka taimaka min kamin jagora muje ko yrnyr nn zata fara kulani dmn wlh nayi nayi ta kulani taqi gashi ni kuma dgske nake sonta wlh"
Man da tunda ya fara zancen sa yake masa kallon ka ta6u yaja dogon tsaki tare da girgiza kansa yace"tabbas munir ynx na tabbatar ka fara shaye shaye amma ka 6ata kanka wlh ka kuma cuci iyayenka da tarbiyar da suka maka"
Cikin damuwa munir yace"wai Man meye hk duk a cikin frnds kafi kowa sanin halina fa....banda yanzu da ka sauya halayen ka don haka ni ka ma ftr min daga office,pls man.... Munir!nace ka fita ko!
Cikin 6acin rai munir ya tashi ya fita ya bar mohd dake juyi a hnkli kan kujerarsa yaja guntun tsaki yace"na rasa wace irin qwaya ce yake sha dake sauya mai tunani gabad'aya da har ya fad'a jin son wnn abar har ma wai yake cewa na masa jagora sae kace ni d'an makauniya ne ko makaho"




Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






1/1/2017






🔮```15```🔮
Munir yaro ne kyakkyawa mai matuqar mutunci da kamala haka kuma yaro ne mai girmama manyansa ya kasance mai tausayin talakawa sosai sbd haka ya taso ya sami iyayen shi da son taimakon talakawa duk da irin kud'in sa kuwa basa da wulaqanci ko kad'an asali ma gidan su munir gida ne da ko yaushe zaka sami jama'a wad'anda ake bawa taimako.
Su biyar ne a gun iyayen su ,shine na farko snn hameed ,Hasheem,Hafsat snn er autar su safiyya.
Munir ya jima yana son yayi aure amma bai sami wacce ta kwanta mai a rai ba sae akan Rayyanat wacce ko da kuskure bai ta6a ganin fuskarta ba amma rnr farko da ya fara ganin ta yaji ta kwanta mai a rai ya kuma ji a ransa irin matar da yake son aura ce.



Ranar alhamis ba islamiya hakan yasa Rayyanat tayi zaune tana ta mitar littafanta,
ita kad'ai ce a falon tana karantawa da larabci tana fassarawa tamkar tana a gaban malami yanda ta taqarqare.
Ba komai yasa taxo falo tana yin karatun ba sae don inna ta fita anguwa baaba hurera kuma tana kitchen,gashi inna tace xa'a kawo saqo shiyasa taxo falo ta zauna kar wanda inna tace zai zo ya kawo saqo yazo basu ji ba.
Rayyanah yarinya ce mai tattara hnklinta gabad'aya akan abinda ta sa ma gaba hkn yasa bata san da shigowar Mohd ba duk da kuwa sallamar da yayi sae ganin mutum kawai tayi tsaye a kanta, a tsorace ta saki ihu tare da jefar da littafanda ke hannunta zata kwasa da gudu kenan man ya dakatar da ita cikin daka mata tsawa, sae kawai ta fashe masa da kuka tana kallon shi ,wacce sae a snn ta gane waye,ai kuwa kai tsaye ta had'e girar sama da ta qasa tare da share hawayen fuskarta, Mohd kuwa tsaki yaja yayi tsaye yana kallonta yayinda hannyen sa ke cikin aljihun wandonsa,ciki ciki ta gaida shi ta duqa ta kwashi littafan ta ta wuce ta kaisu d'akinta ta ajiye snn ta nufi kitchen dai dai baaba hurera ta shigo ta qofar baya duk a rud'e, tace"Rayyanah ba kece naji ihun ki ba ina bayi?
Kmr wata qaramar yarinya ta 6ata fuskarta tace"nice Baaba wnn d'in nn ne ya shigo ban sani ba sae ganin sa nayi shine na tsorata"
Baaba hurera tace"waye kuma wnn d'in nn ?Rayyanah tace"wnn d'in nn dake zuwa gun inna kullum.
Baaba hurare kam bata gane ba sae falo ta tafi dan ganewa idonta ,
tana ganin mohd ta washe baki snn tace"ayyo wai muhammadu kaine Rayyanah ke cewa wnn d'in nn sae duk ban gane ba shine nace bara na fito naga waye.
Murmushi ya sakar mata tare da gaida ta snn yace"inna fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login