Showing 3001 words to 6000 words out of 168541 words

Chapter 2 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9129

shike nn yanzu bata da kowa a duniya sae wanda yaga Allah ya taimaka mata,yanzu bata san wace irin rayuwa zata shiga ba kawai dai tasan duk rnr da Allah ya had'a ta da wanda ya kashe mahaifinta Baza ta bar shi ba! koda kuwa itama zata bar duniya ta dalilin hakan.
Zaune take kusa da wani gidan mai sae rusar kuka take kamar yanzu ne mahaifin nata ya rasu.
Mabaratan da take zaune kusa da su sae kallonta suke abin tausayi dmn ganin suke har sunfi ta dama a yanayin da suka ganta ciki.
Ta jima sosai a gurin ga yunwa ga qishi ta tashi tsaye da qyar sbd jirin da ke d'ibar ta, kallon mabaratan da ke kusa da ita take ta hango er gorar ruwa aje kusa dasu ta fara tako cike da son taje tace su en mata ruwan tasha ba tare da ta damu da ganin su mabarata bane ita dai ta samu ta kawadda qishin da take ji.
Gab take da isa gurin su wata irin tsaleliyar mota ta tsaya a gurin wanda ke ciki ya sauke glass d'in motar a hankali yana kallon mabaratan cikin wani yanayi na qyama kamar wanda zai yi amai.
Hannu yasa ya zaro kud'i a aljihun sa 1k bunch ya jefa musu kud'in dai dai Rayyanat ta juyo kan ganin yanda taga mabaratan sun qure guri d'aya da kallo, yanayin yanda ya jefa musu kud'in yasa gabanta yayi mugun fad'uwa kuma tabbas kalar motar da ta kad'e mahaifinta ce take gani tsaye a gabanta


Mabaratan sukayi ruu! dmn d'aukar kud'in da aka jefo musu sae qoqarin kada Rayyanat suke da kud'in ke tsakiyar qafafunta ita kuwa ko qwaqqwaran motsi ta kasa sae qarewa motar kallo take ba tare da ta iya hango wanda ke ciki ba dmn tuni ya mayarda glass d'in motar sa ya rufe.
Tako ta fara a hnkli dmn ta kai idonta ga numbar motar,taga ba ko shakka ita ce numbar motar da ta kad'e mahaifinta wani irin yanayi Rayyanat ta tsinci kanta a ciki marar misaltuwa idanuwanta suka ciko tap da qwalla ta samu da qyar ta d'aga yatsarta tana nuna numbar motar, cikin rasa iya motsa koina na ga66an jikinta take ci gaba da kallon numbar.
firgigit tayi ganin motar ta fara tafiya sauri sauri ta shiga bin motar wacce still yatsarta na kan numbar motar tana nunawa........"ke! ke!! ke!!!" shine abinda mutanen gurin keta fad'a amma sam hanklin Rayyanat na tare da motar hakan yasa taji an kwashe ta kai tsaye kanta ya daki wani guri tun daga lokacin bata qara sanin inda take ba.


Matar da ta kad'e Rayyanat ce keta faman zarya a asibiti cike da takaici se faman duba wristwatch d'inda ke hannunta take....wayar ta ce ta shiga ringing ta d'aga cikin sauri tace"yauwa honey pls kazo *MAN HOSPITAL* na kad'e wata yarinya ne"
daga haka ta katse wayar ba jimawa ya iso sae ga doctor ya fito yace taje yanzun zata iya ganin yarinyar.


Sosai Rayyanat ta samu rauni har dai saman goshinta sae dai bata farfad'o ba sae bacci take ana mata qarin jini.
"Garin yaya haka ta faru?cewa da mijinta
Tace
"Honey kasan matsalar talaka da baqin hassada duk inda motar mai kud'i ta wuce sun fara binta da ido kenan shine fa ita bata tsaya a kallo ba har bin motar take kamar motar ubanta! sae wani qoqarin kamo motar take ana faman kiranta amma a banza! gashi yanzu duk ta 6ata min tsari har yaya ya tafi ya barni may be ma har jirgin su umma ya sauka ya kai su gida,eyya sorry yanzu ki tafi kawai in yaso ni na tsaya.


Tunda Rayyanat ta farfad'o bata da aiki sae na kuka duk yanda yaso tayi mai magana taqi har kusan kwana biyu snn aka sallameta .



Gidan shi yaje da ita suna shiga falo yaji qarar fashewar glass da sauri ya kalli inda yaji sautin yaga matar sa ce ta saki glass cup tana masa wani mugun kallo cikin tsananin kishi .
Da mamaki yace"lafiya pretty"har ka tambaya! wnn wace er iskar ce ka shigo min da ita a gida!
Yace"ikon Allah yarinyar da ki kad'e ce fa aka sallame ta yau......to dan ita ce sae ka wani kwasota ka kawo min ita a gida har da wani riqo mata qunshin ledar ta,to pretty ina kike son taje bata qarasa jin sauqi ba kuma kinsan har yanzu ko magana batayi ba bare asan daga inda ta fito....fuuu! tazo ta fizge qunshin Rayyanat dake hannun shi tace"Ai tunda ba gidan ubanta bane wlh sae ta fita!da gani ma irin shegun yaran nn ne da iyayen su ke jefarwa suna gantali a hanya shine tayi shiru taqi fad'in inda ta fito ita ala dole taga ta samu mafaka,nn ta jefa ma Rayyanat qunshinta tace"oya! fitar mana daga gida shegiya! kije can ki qarata da baqin gantalin ki da uwar ki taja miki!
A hnkli Rayyanat ta duqa ta tsince en kayanta da suka fito cikin ledarta snn ta tashi tana mai share qwallah a idonta ta fita.




```Billy giro๐Ÿ˜Š```
๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro๐Ÿ˜Š: ๐Ÿ”ฎ```BAZAN BAR SHI BA!```๐Ÿ”ฎ


















```Na Billy giro๐Ÿ˜Š```










11/12/2016










๐Ÿ”ฎ```4```๐Ÿ”ฎ
Cikin hanzari mijin pretty yabi Rayyanat yana fad'in ta dakata.
Kamar kar ta tsaya sae kuma ta tsaya ba tare da ta juyo ba sbd kuka take yi sosai har yana so yaci qarfinta. Kafin ya qarasa gurinta pretty tayi sauri tasha gabanshi tace"wlh bafa zata zauna a gidan nn ba!bai kula ta ba sae qoqarin wucewa yake tana tare mai hanya ya tsaya tare da nuna ta da yatsa snn yace"kinga pretty kar ki kaini qul fa!
daga haka ya ra6a ta gefenta ya wuce yace da Rayyanat "muje"ta sake shan gabanshi
tace"ban gane kuje ba ina zaka tafi da ita? Koma ina ne ba ruwanki yanzu,tunda ke baki san ki tasauya ma bayin Allah ba!ta wani le6ace baki tace"meye abin tausayi wa talaka ko talaka mabaraciya wad'anda basu da burin da ya wuce ganin bayan dukiyar mutum kullum cikin roqo da fad'in a basu,basa nema sae dai a nema a basu sbd baqin lalaci irin nasu.
Ki iya bakin ki pretty kullum cikin aibata talaka kike talaka ba abin gori bane dmn kema baki wuce Allah ya jarrabace ki da talauci ba........ Tuf!bakin ka ya sari d'anyen kashi wlh ni Allah tsare ni da baqin bakin ka!
Ganin abin na son zama musu fad'a Rayyanat tace"ka bar shi kawai nagode ni zan tafi koma ina ne"
Yace"Kwantar da hnklin ki ba nn gidan zaki zauna ba gidan kakata zan tafi dake har ki qarasa jin sauqi tukun....cabd'i!lallai ma Nasir kai baka ji me tace bane "wai zata tafi koma ina ne" hakan fa na nuna ba tada asali amma shine har kake qoqarin kaita gidan kaka!
Wai pretty me yake damunki ne ya zaki kama fad'ar magana akan abinda baki da tabbacin sa! Murgud'a mai baki tayi tace"wane tabbacin kuma zan nema bayan sanin kanka ne duk er asali bazata kama gantali kan hanya ba har ma tana fad'in koma ina ne zata tafi ai duk d'an asali ba zai ce haka ba sae dai yace zai koma gurin en uwansa!
Guntun tsaki yayi snn ya kalli Rayyanat yace"baiwar Allah gaya min sunanki"
Sae da ta share hawayen da keta faman sintiri a kan fuskarta snn tace"sunana Rayyanat..... Mtsw kaji wani kilinbibi d'an qauye ne yasan ya qawata suna haka ai sae dai Rayyanatu hm!wai Rayyanat....yi mana shiru a nn pretty meye ruwanki da sunanta kuma!
yace"Rayyanat yi haquri sanar dani abinda ya kawo ki garin nn dmn na fahmici kamar ke ba er garin nn bace ko"kuka kawai Rayyanat ta fashe dashi ,Nasir yayi shiru yana nazari inda ya fahimci tabbas akwai abinda ya faru da Rayynat wanda bata son a tambaye ta inda ta fito tunda ko asibiti haka take ajiye mai kuka idan ya tambayeta nn ya tsara a ransa bazai qara mata tambayar ba har se taji sauqi tukun.
Yace"daina kuka zo muje"
pretty tayi saurin riqo hannun shi tace"honey bafa inda zaka je da ita"wani mugun kallo ya watsa mata ya kuma fizge hannun shi,cikin tsiwa tace"ai ko wlh sae dai ka za6a ni ko ita! don duk ka fita da ita nima sae nasa qafa na bar gidan nn na tafi gidan mu"yace"in kin iya kivar duniya gabad'aya ba ma gidan ba!
Daga haka yasa qafa ya fita shida Rayyanat.




Billy giro๐Ÿ˜Š
๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro๐Ÿ˜Š: ๐Ÿ”ฎ```BAZAN BAR SHI BA```๐Ÿ”ฎ
















```Na Billy giro๐Ÿ˜Š```










11/12/2016










๐Ÿ”ฎ```5```๐Ÿ”ฎ
Suna shiga gidan kakar ta tarbe su da murna kamar har
Rayyanat d'in ta sani dmn akwai ta da son mutane sosai.
Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa snn ita ma ta zauna suka qara gaisawa tace"daga ina haka muka samo baquwa nasir?, Nasir yace "wlh kaka pretty ce ta kad'e ta a bisa qaddara shine bayan ta kaita asibiti da kwana biyu aka sallamota to har yanzu dai bata fad'i ita wace ce ba dmn duk na tambayeta sae tayi tamin kuka ,
kawai dai ta sanar dani sunanta Rayyanat ,naso ta zauna can gidana har ta qarasa jin sauqi amma kinsan halin pretty shine naga kawai na kawota gurinki dmn zata ma fi jin dad'in zama a nn.
Kakar da ta bude baki tun fara mgnr sa tace "ikon Allah, wani irin tuki take har xata buge yar mutane snn kuma ta ki Bari ta xauna gidanta har ta warke, ni dae yaran Kabiru suna bn mmki da irin halinsu" Nasir dae yyi shiru bae ce komae ba, ganin sae fada kaka ke tayi kmr xata ari baki yasa yace "ynxu dae kaka kiyi hkuri hka, sae ta xauna gun ki har Allah ya sa a samo yan uwanta" kaka tace "yo in bata xauna nn ba ina xata xauna da" Nasir yyi murmushi yace "gskya ne kaka" Rayyanat kam sae kallon tsohuwar take nn da nn taji ta kwanta mata taji kuma xata iya xama da ita.


Kakar ta tashi ta shiga kitchen ta d'ebo abinci ta kawo mata tace "ki saki jinkinki fa ki d'auka nan tamkar gidan ku ne kinji, ita kuma xata xo ta sameni har gida, tukin ma daga ynxu sa xanyi Khabiru ya hanata tunda abun nata har da buge mutum, kwanaki ma hka ta buge dan mutane" Nasir dae bae ce komae ba,
Rayyant ta sunkuyar da kanta tana mai share qwallah had'e da ajiye d'an ledar da ke hannunta.
Kakar tace "kawo ledar na shigar miki da ita idan kin kammala sae ki watsa ruwa ko kyaji d'an damar jikin ki, ki kwanta ki huta"
Bayan takai ledar ta dawo tana mai duban Nasir tace"ina ce ka siya mata magungunan da zata ci gaba da sha? Nasir yace Eh akwai magunguna a cikin ledar ta idan ta gama cin abinci sae tasha kafin tayi wanka dmn lokacin shan magunan ma yayi.
Yana gama fad'ar haka ya tashi yace"inna ni zan tafi sae anjima idan na dawo " inna ta washe baki tace "To Allah yyi maka albarka" ya amsa da Ameen yana murmushi ya nufi kofa xae fita, juyowa yyi yace "am yau man bai shigo bane inna? Inna tace " waye kuma hka?" Nasir yyi dariya yace "Mai gidan ki mana" ta tabe baki tace "Tun da safe ya shigo da dan rashin mutun cin sa, amma na taka masa burki, to har ynxu dae bn gansa ba" Nasir yyi dariya yace "to shknn" inna tace"ko da wani abu ne?" Aa ba komae naga ko yaushe na xo yana nane da ke ne,"


Har gurin motar sa ta rakashi ta dube shi da kulawa tace"Nasir gaskiya yarinyar nn da akwai alamomi ban tausayi a tare da ita jifa tunda kuka shigo bata da aiki sae na share qwallah,ai ma inna kad'an kika gani baran idan aka tambayeta inda ta fito, shiyasa yanzu nafi son sae taji sauqi tukun ko zan sake tuntu6ar ta.
To Allah yasa ta kirki ce kamar yanda nake ji a raina ni dae ta kwanta min wllh, Nasir yace Amin inna.
Daga haka ya shiga motorsa ya wuce, inna kuwa ta koma daga ciki.


Nasir kuwa yana zuwa gida ya samu gidan a hargitse duk pretty ta farfashe abubuwa ta kuma tafiyarta gidan su kamar yanda tace.




6angaren pretty sae kuka take sosai a jikin wata mata da nake sa ran ummanta ce ita kuwa sae masifa take inda take fita ba nn take shiga ba na ganin har dare Nasir yaqi zuwa ya sasanta shida pretty.
Wani gaye ne ya shigo d'akin Alhmdlh ya had'u ta koina baya da makusa tamkar balarabe fari tas dashi,yana d'auke da d'an siririn saje kan fuskarsa .
D'ayan hannunsa yana riqe da suit baqa kalar wandon da ke jikin sa,yayinda rgr jikinsa ta kasance fara mai ratsin layi layi.
D'ayan hannunsa kuma yana sanye a cikin aljhun wandonsa.
tsaye kawai yayi yana kallon su ba shi da niyyar cewa komai .
Mamar ce ta fara ganin shi ,ya gaishe ta ta amsa inda cikin nuna damuwa sosai tace"man kaji abinda Nasir yayi wa qanwar ka pretty.


Nan mamar ta zayyana mai abinda pretty ta fad'a mata.
Bai ce da mamar komai ba ya kalli kanwar tasa fuskar sa ba yabo ba fallasa yace "garin ya akayi kika kad'e ta? Kmr xata yi kuka tace yaya ina lokacinda zamu tarbo su umma har ka tsaya wani gidan mai ka bada sadaka? Yyi shiru yana kallonta, hkn yasa ta turo baki tace yaya ni fa ba laifi na bne yarinyar ce Jaka, ina ga daga kauye ta fito, wani mugun kallo ya shiga yi mata, ta dauke kai tana murguda baki, ya gyada kai yace "daga yau kar ki kuskura ki kara jan mota" ta xaro ido tana kallonsa tace "sbda me, ko mijina fa bae hanani va yaya" tsawa ya daka mata yace "nace kar ki kuma jan mota"
Daga haka ya fita ba tare da ya tsaya jin me zata ce ba .



Tafiya yake a hnkli har ya isa 6anfarensa.
D'akin sa wani irin d'aki ne mai masifar kyau da tsari komai fari tas sae qawar da akayi da golden ga tsarin d'akin ba wani tarkace kamar tsarin d'akin turawa.
Frigde ya bud'e ya ciro gorar ruwa ya bud'e ya tsiyaya ruwan a glass cup yasha snn yaje ya cire kayan jikin sa ya sanya white bathrobe ya nufi bathroom.


Billy giro๐Ÿ˜Š
๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro๐Ÿ˜Š: ๐Ÿ”ฎ```BAZAN BARSHI BA```๐Ÿ”ฎ










```Na Billy giro๐Ÿ˜Š```






11/12/2016








๐Ÿ”ฎ```6```๐Ÿ”ฎ
Ya jima sosai kafin yake fitowa yana gama shiri yaji ana masa knocking yaje ya bud'e qofa idanunsร  suka sauka kan qanwar sa pretty dake tsaye riqe da trayn abinci fuskar ta fam kamar zata fashe don fushi tace"amma dai yaya zancen na daina tuqi da wasa kake min ko?mugun kallo ya watsa mata ya juyarwarsa ya koma daga ciki,ta shiga ta ajiye trayn sea qunquni take ita ba wanda ya isa ya hanata tuqin mota kan wata jaka can er qauye marar asali ma,
Bai kulata ba har ta qaraci surutunta ta fita.



Washe gari sallah kawai tayi tace da ummarta"ni xan koma"
Umma ta saki baki tana kallonta snn tace"amma pretty ni nasara ke wace irin mace ce wlh kowace mace na ganin ta samarwa kanta enci amma banda ke ,wane irin abu ne da baza ki bari sae nasir yazo da kansa ba ko zaki koma ,wlh kwata kwata kin 6ata kanki da sonda kike yiwa nasir kmr ba nice na haife ki ba....nifa umma ba haka bane naji kina waya da Abba yana kan hanya shiyasa zan tafi kar yazo ya sameni ya min fad'a kuma kinsan jiya da dare nasir yazo har yayi ta kiran wayata naqi na d'aga,to shi baqon gidan nn ne da bazai shigo ba sae ke zaki fita ki same shi ai inace yaje 6angaren uwar sa amma yaqi zowa nn,ai umma barshi don ni bama gidan sa nayi ba wlh gidan inna zan tafi,to idan inna ta tambayeki lafiya fa? Ai inna ce zan kwashe da ita dai dai ba kamar Abba ba ,to ai sae ki tashi kiyi niyya dmn gab yake da isowa garin nn.
Sauri sauri taje tayi wanka ta shirya sae neman makullin motar ta take duk ta jigata kamar zata yi kuka ta kalli ummarta da ta shigo tace"umma ina makullin mota ta? Yayanki yazo ya kar6a....haba umma meyasa kika bashi, kije ki roqe sa mana ai zai baki ,Allah umma kinsan da kamar wuya kidai roqa min shi ya bani, Aa ba ruwana can tsakanin ku ne kije ki gwada sa'ar ki idan ya baki to.
Wani abu yace miki da zai kar6i makullin motar ne?ba abinda yace min kawai dai ya kar6a ya tafi.
Cikin 6acin rai ta fito tayi kici6is da yayanta da kuma mijinta Nasir a nn harabar gidan kallo d'aya tayiwa Nasir ta kauda kai ta kalli yayanta tare da marairiace fuska tana roqon ya bata makullin motar ta,kallon nasir yayi yace"sae kaja matar taka ku tafi"
Ya sa qafa zai wuce tayi saurin shan gabanshi tace"pls yaya kayi haquri ka bani"
tsawa ya daka mata yace"wai ina wasa dake ne da kike tunanin zan kar6e abu na baki!
Le6ace baki tayi zuwa kuka tace"yaya ba fa laifi na bane na gaya ma"
Wayar sa da tayi ringing ya d'aga ya bar gurin ,kuka ta fashe dashi nasir yazo yaja hannunta ta fizge hannun taje ta shiga mota shima ya zagaya ya shiga yaja motar tana ganin ya hau titin zuwa gidan su ta dalla mai harara tace"nifa ba gidan ka zan tafi ba don ka sani gidan inna zanje gara tun wuri ka sauya hanya don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login