Showing 27001 words to 30000 words out of 168541 words
Chapter 10 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
Ya zama dole yaje ya jirata kan hnyrsu ta islamiya don yau sae ta fad'i wanda ya aiketa .
Yana fita da motar sa yayi kici6is da Malika ta parker motar ta ta fito, dole ya tsaida tasa motar ya fito yaje gab da ita ya tsaya yana mata wani irin kallo,ita kuwa ta wani langwa6ar da kanta snn tace"my man wai ya ake ciki ne tun jiya da mukayi waya naji shiru har yau "
yace"to shine zaki wani biyo ni har gida da kuma wnn banzan dressing d'inki salon Abbana ya ganki yace bakida kamun kai kuma,in yaso Komai ya qara cakud'e mana! Kayi haquri my man wlh banda wasu kaya sae ire iren su kuma ka sani,to me ya hana ki kirani a waya muyi magana? Ina mgnr zata yiyu a waya nida kwata kwata daren jiya ban samu nayi bacci ba,amma malika kinsan bana son damuwa koma mene ne ai zanje na sameki har gida,kayi haquri na damu ne sosai ,tayi mgnr cike da qwallah tap a idonta, yayi saurin cewa"shikenan kar kiyi kuka gaya min me kike so yanzu?so nake ka gaya min abinda ake ciki ,ajiyar zuciya ya sauke snn yace"wnn yrnyr ta lalata mana komai don ta amince da buqatar Abba snn kuma Abbana har yanzu dai yana kan bakarsa na bazan aureki ba,amma kar ki damu zan shawo kan matsalar komai inshaAllah ,matsalata d'aya yanzu shine anjima za'a sa rnr aurena da wnn yrnr shiyasa at all kaina ya kunce bansan ma wane hukunci zan yanke ba, ga umma ta sani cikin wata chakwakiyar wae bani ba ita idan ban nemo mafita ba har akayi aurena da wnn yrnyr.... Wae da kana nufin zaka yarda ayi auren ne to! Malika uba ba abin wasa bane idan kuma ya yanke hukunci ba yanda za'ayi kuma ya rantse cewa in ta amince tofa shikenan ba fashi aurena da ita, but my man be wise mana,idan ba yrnyr ai ba auren shike nn dole Abba ya haqura, aikin hnkli dai malika ina mai gaya miki 6atar wnn yrnyr tmkr tsinuwace na jawa kaina don dole Abba yasan nine, kawai dai zan aureta amma na d'an wani lokaci .....Wlh! my man bari kaji in gaya ma ba maccen da ta isa ta aure ka bayan ni don ka ma daina wnn sa6on!daga haka taja motar ta a tsiyace ta bar gurin.
Har zai shiga mota sae ga kiran Abba yana son ganin shi,dole ya juya ya tafi ga kiran Abba.
Yau Rynt ita kad'aice kan hnyr dawowa islamiya sbd da safe munir bai cika zowa ba sae da yamma.
Tana cikin tafiyar ta har takai titi zata tsaida napep sae ga wata tsaleliyar mota ta tsaya a gabanta.
Malika ce ta fito daga motar taje gab da Rynt tare da kai hannu ta yaye mata niqabi,nn malika ta yamutse fuska kmr wacce taga kashi tace"hm rainin wayo wai kece ke shirin shiga tsakani na da my man,ta nuna ta da yatsa snn taci gaba da cewa" lemmi tell u 1 thing ruwa ba sa'ar kwando bane haka kuma ramin kura ba gurin shigar akuya bane,a bisa yanda ma na fhmta kwata kwata tsabar talauci ne ke d'ibar ki da haka zan taimaka miki na baki check ki rubuta duk iya kud'in da kike so after that ki sani inda dare ya miki ma'ana kwata kwata ki 6acewa duniyar mu ki tafi can taku duniyar ta matsiyata wnn umarni ne dmn in kika sake kika dawo gare mu wlh sunanki gawa!
gama fad'ar haka ta zaro cheque da biro ta miqawa Rynt ,sae kuma tace "koda yake nasan duhun kai na tattare dake bare har ki iya rubuta wani abu nn ta rubuta million biyar snn ta ce ungo kud'i ne masu yawan gaske da nsn ko ubanki bai ta6a riqa irin su ba bare ke!
Kallonta kawai Rynt keyi wacce batada niyar kai hannu bare har ta kar6i cheque d'in .
Malika tace"gwanda ki kar6a don wlh kanki kika yiwa idan baki kar6a ba sbd ynzu hk ni a shirye nake da nasa a yanke miki hukuncin da yake dai dai a guna.
Komai Rynt bata ce mata ba sae ma ra6awa tayi ta gefenta zata wuce ,sae kawai ta sami kanta da ganin qarti zagaye da ita.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:43PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/9/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
_*page*_ *```23```*
wayar malika ce tayi qara koda ta duba Man ne mai kiran,
ta d'aga wyr sae jin tayi yace"malika kibar er mutane ta wuce"
tace "my man.... sae taga ya katse kiran.
Kallon mutanen ta tayi tace"ku barta ta tafi.
Bayan Rynt ta wuce suma mutanen nata ta basu izinin wucewa snn ta shiga rarraba ido ta inda zata hango man dmn tasan tabbas yana gurin.
Kmr daga sama tana juyawa ta ganshi a bayanta kallonta yake da mamakin yanda akayi tasan Rynt har tasan makarantar su sae kuma nn take ya basar sbd sanin bincike ba abinda baiyi yace"daso kikayi mahaifina ya tsine min ko kuwa?my man.....No kawai kar ki sake min shisshigi irin wnn bana so!
Daga hk yayi tafiyar sa ya barta.
Hjyr su pretty kuwa sae sa ido take taga ko Rynt zata dawo amma shiru haka Man bai dawo gidan ba.
Wasa wasa kuwa har yamma ba Rynt ba labarinta, dad'i taji sosai har ranta don ganin take dabarar tace tayi.
Taja Ameera zuwa d'aki wae ta rubuta takarda a cewar Rynt ce ta rubuta ta yanda idan Abba ya gani ba zai zarge su ba haka kuma ba zaisa neman Rynt ba.
umma ce ke fad'in abinda za'a sa Ameera na rubutawa har suka gama tace "yi maza kije kisa a qarqashin pillown ta kina jin shigowar Abbanku kije masa cikin kuka a cewar kin nemi duk gwalgwalanki ki ransa har ma kud'in provision dinki da ya baki jiya da dare ni kuma zan fito da nawa tuggun ta yanda koshi waye bai isa ya gane plan bane wlh,yi maza jeki........ Ameera!Ameera! kiran ya fito daga Abba umma tayi saurin kar6ar takardar dake hannun Ameera ta tura mata cikin zane,nn suka ji knocking umma ta bud'e qofa Abba ya kalli Ameera yace"ke je ki ftr da kayan Rynt za'a maida su gidan inna ne, umma tace"ina ita Rynt d'in da baza ta ftr ba sae Ameera? Da mamaki Abba yace"ai Rynt bata dawo gidan nn ba tun safe sbd ana tashi daga makaranta inna ta aika Nasir ya d'auko ta, yanxu haka ma tana gidan inna har ma taje islamiyyar yamma ta dawo.
wani irin baqin ciki umma taji tace"ai sae tazo da kanta ta ftr da kayan tunda Ameera ba boyar gidansu bace"tsawa ya dakawa Ameera yace "ke je ftr min da kayan Rynt nace"
Ameera ta wuce kmr xata yi kuka,ya kalli umma yace"keda kanki wae kike lalata rayuwr 'ya'yanki Allah dai ya shirye ki".
Abba ya fita ya bar umma cikin takaici da jin haushin mohd.
7:00pm
Mohd ne ya shigo gidan inna,inna ta fito daga kitchen kenan tana ganin mohd ta washe baki tace"ka ganmu muna can nida baaba hurera da Rynh muna had'awa iyayenka liyafar da xasu ci idan sunxo sa rnr aurenku kaida Rynh.
Kauda kansa gefe yayi dan shi ko sunan Rynt baya son ji.
Inna tace"akawo maka naka abinci? Aa inna magana nazo muyi, inna ta washe baki tace"ayyo to bari na kira ma Rynh d'in"ransa ne ya qara 6aci yace"na mata me ni dake zanyi magana"
Washe da baki inna ta nemi guri ta zauna shima haka tace "ina jinka maigidana angon Rynh"
Ba yanda ya iya hk ya dake ya basar awa bai ji ta ba yace "inna so nake dan Allah ki roqa min Abba ya barni na auri malika.... Inna ta fiddo ido waje tace"yau naga shashashan yaro ita Rynh d'in fa? Ai inna ba ina nufin wani abu a kanta ba kawai dai so nake Abba ya barni harda malika d'in na had'a na aura sbd gsky ni ita ce za6ina.... To bakaji da kyau ba wnn er marasa mutunci tayi kad'an ta shigo cikin dangin mu ta watsa mana mugun iri,dan Allah inna ki saurare ni fad'in ra'ayin Abbanta ba shine rashin mutunci ba ai ,kaga mohd indai wnn maganar ce zaka tamin gwanda ka tashi kayi tafiyarka don ba saurarar ka zanyi ba,cikin damuwa sosai yake kallon inna kmr zai mata kuka yace"inna wae dan Allah meye dad'in aure ba ka auri wanda kake so yake sonka ba... Yo mu kenan duk kana nufin ba muji dad'in aure ba muda duk had'in iyayene amma muke zaune qalau har Allah ya d'auki ran marigayi,amma inna daa da yanzu ba d'aya bane kin sani...ina ko zasu zama d'aya tunda daa iyaye ke za6awar 'ya'yansu mata kuma ba'a jin kansu amma kai yanzu gashi kazo min da zancen za6in ka kake son ka aura mu daa har akwai wani za6i da ya wuce na iyaye.
Nidai inna kiyi haquri ki roqa min Abba kafin su shiga meeting d'in nn....yo kana nufin za'a had'a baki dani ne a cuci Rynh ,haba inna aini ake shirin cuta shin ba kya jin tausayi nane a matsayina na jikan ki ace duk tsawon shekarunda na d'auka a matsayina na lafiyayye banyi aure ba ina nn ina jiran malika ta kammala karatu se kuma ace bazan aureta ba,fisabilillah inna ya kamata a duba min,ya qarashe mgnr ne ta yanda duk wanda ke saurarensa dole ya tausaya masa,inna ta sauke ajiyar zcy tace"shikenan mohammadu zanyi magana da mahafin naka amma idan bai amince ba tofa sae dai ka haqura don bazan tilasta masa ba.
Ba komai inna nagode ya tashi zai fita tace"abincin ka fa?
sae anjima idan na dawo, to a dawo fly.
Daga haka ya fita ita kuma ta koma kitchen.
Sae tara da rabi mohd ya dawo gidan ya samu Abba a nn falo shida inna sauran iyaye kuwa an kammala meeting d'in sun tafi.
Cike da ladabi ya gaida Abbanshi ya juya zai fita Abba yace"zauna dama kai nake jira muyi magana.
Bayan ya zauna Abba ke cewa naji na kuma amince da buqatar ka amma fa ka sani ya zama dole kayi adalci a tsakanin su snn bayan aure idan term ya zagayo zaka saka Rynt a makaranta yayinda nauyin karatun ta zai kasance a qarqashin ka.
Abinda ya rage yanzu shine ka snr da iyayen malika zancen auren naku wanda za'a d'aura a qarshen wnn satin rnr juma'a idan kuma basu shiryi hakan ba su suka sani don baza a fasa naka dana Rynt ba.
Daga haka Abba ya tashi ya fita mohd ya d'ago ya kalli inna tare da fad'in nagode inna.
Yana fita gidan inna bai zarce koina ba sae gidan su malika ya snr da ita Abban sa ya amince suyi aure amma cikin satin nn za'ayi komai dad'i taji sosai har da su hugging d'inshi wacce kwata kwata bai nuna mata still auren Rynh na kanshi ba,ita kuwa ta d'auka an fita zancen Rynt.
Sae shirye shirye ake tayi a cikin satin har ma ya zamo inna ta hana Rynt fita ko ina wae ta shiga lalle kenan saliha kuwa tarewa ma tayi a gidan, Rynt kuwa sae kallon su take tana tunanin hln da munir zai shiga idan yaji.
6angaren hjyr mohd kuwa tun daga rnr ko gaisuwar mohd bata amsawa wae a cewar fushi take dashi tunda yaqi neman mafita duk da cewa wani 6angaren taji dad'i jin cewa harda malika zai aura.
Rnr juma'a aka d'aura aure akayi walima 6angaren su malika kam shagugula akayi ba kad'an ba.
Da dare za'a kai Rynt sae kuka take kan rabuwa da inna haka ma inna kukan take kmr baza su qara had'uwa ba.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/10/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
_*page*_ *```24```*
Bayan ankaita kowa ya watse ita kad'ai a d'aki sae autar su saliha da suke kira da mami.
Ambar mata ita ne sbd ita Rynh d'in ta nemi haka sbd mugun tsoron bacci ita kad'ai take ji.
6angaren su mohd kuwa bayan an kawo amarya suka tsiri wani party maxa da mata sae shagali suke duk Rynt ta kasa samun baccin kirki sbd hayaniyar su hkn yasa ta tashi ta d'auro arwala ta shiga yin nafilfili yayinda autar mama keta sharar baccinta.
Sae kusan qarfe d'aya da rabi en party suka watse amma hkn bai hana mohd da malika suka sha amarcin su ba.
Washe gari sae da Rynt tayiwa mami wanka snn ita ma tayi nata wnkn.
Ta gama shiri kenan taji an turo qofa saliha ta shigo mami taje da gudu ta rungumeta Rynt kuwa tazo cikin sakin fuska saliha tace "amarsu ta ango ya amarci?murmushi kawai Rnyt tayi snn tace"nidai yasu umma? Lafiyar su qalau tana ma gaida ke ,ta fad'i hkne tare da ajiye basket d'inda ke hannunta tace"ga break fast inji umma,Rynt tace"mun gode"
Byn sun zauna saliha
ke cewa yaya fa?Rynt tayi kmr ma bata ji ta ba tace"wai shin saliha yaushe ne kika ce zaku koma makaranta?
Saliha tace "kinsan na gaya miki cikin satin nn hutun mu ya qare sae aurenku yazo ya tsaida mu amma yanzu rnr lahadin nn zamu koma,Rynt tayi shiru can tace"to yaushe ne ake saka sabbin d'auka? Da zarar mun tafi yanzu munyi third term muka dawo gida mukayi hutu se mu koma first term to a lokacin ne ake kai sabbin d'auka sbd anyi canjin aji,yanzu za'ayi kmr wata nawa kafin haka don ni tunda inna tamin albishir d'in bokon nn na qagu naga na fara boko nn wlh,saliha tace"hm boko ko wahala ,komai wahalar sa zan so nayi saliha sbd a rayuwa ba abinda ke birge ni kmr ilimi, gskyr ki ne Rynt sbd ba abinda ya kai ilimi dad'i.....qofa suka ga an tura koda suka duba Ameera ce yamutse da fuska tace da saliha"wae ke a nn kika shigo, nikam ki sameni 6angaren anti malika, saliha tace"to sae idan zamu koma xaki ganni"
nn Ameera ta ka6a kai ta fita,Rynt tace"ai da kin bita kun tafi d'in"saliha ta ta6e baki tace"um um sae idan zamu koma"
Rynt bata sake cewa komai ba sae zama sukayi zasu ci abinci sae ga wani saqon abinci daga gurin inna, sosai Rynt taji dad'i sbd abincin da take mugun so ne inna ta aiko mata.
Ameera kuwa koda taje 6angaren su malika ko bud'e qofa basuyi ba sae da tayi ta fmn danna door bell snn sae can ta samu aka bud'e .
Man ne da malika rungume a jikinshi da gani yanzu ne tashin su don malika farin bedsheets ma ne a jikinta man kuwa yana sanye da white bathrobe yayinda fuskar sa take d'aure tamau yana kallon Ameera yace"lfy zaki mana wnn sammako hk?kafin Ameera tace"komai malika tace"haba my man ba qanwar ka bace? Ko qanwa tace sae tazo ta takura ni, kiss ta d'ora masa a gefen fuska tace"kuma fa tayi laifi amma ayi haquri ta shigo ta zauna sae muje muyi wanka ko,lumshe mata ido yayi alamar suje d'in ,ba tare da kowanen su yace da Ameera ta shiga ta zauna ba suka juya zasu tafi, malika ta kalli mohd tace"my man me xai hana ta d'aura mana break fast kafin mu fito don wlh yunwa nake ji"ba musu ya juyo ya kalli Ameera da bata riga ta shigo ba yace"ke shigo kije kitchen ki d'aura mana girki"
Ameera ta shigo tare da rufe qofa tana ji kmr ta fasa ihu don ta tsani aiki ba kad'an ba.
Mohd kuwa suna shiga d'aki malika ta jefar da bedsheets din jikinta ta dawo nakedness,hm mohd sae d'aukar ta yayi suka je toilet.
Bayan sati 1 da faruwar haka tuni su saliha sun koma school ,mohd da malika kuwa sae cin amarcin suke inda ko sau d'aya mohd bai ta6a leqa 6angaren Rynt ba.
Sam Rynt bata damu ba wacce har yanzu inna na aiko mata abinci,kuma bata da wani kad'ai ci sbd still mami na nn da kullum tare suke cin abincin su suna kallo.
Yau tun da safe da suka tashi mami keta kuka ita gida take son zuwa gun ummarta duk Rynt ta shiga damuwa tayi rarrashi har ta gaji amma fafau taqi shiru ita sae taje taga mamarta.
Ba yanda Rynt ta iya dole ta shirya dmn kaita gida tunda ba waya ne da ita ba bare ta kira azo a d'auke ta kuma ko banza tana son zuwa gida don zaman banzan nn ya isheta tana son komawa islamiyya.
Hijabinta har qasa ta zuba ta jawo hannun mami suka fito suna kawowa harabar gidan ta sami kanta da mamakin ganin mohd zaune kan resting chair shida wani mai kama dashi sak har ma baka babance su,sam mami bata kula dasu ba sae kuka ta ajiye wae Rynt ta d'auketa ita bacci take ji,nn Rynt ta d'auke ta tare da d'aura ta kan kafad'a sae jin tayi tace "lah anti ga yaya da anti amarya sun fito"a hnkali Rynt ta juya bayanta don ganin wad'anda mami ke nufi sae kawai taga mohd shida malika ta kalli gun resting chair taga still wad'an can su biyun suna nn zaune abinsu suna fira ga kuma mohd shida malika tsaye mutum uku kenan fa iri d'aya nn kan Rynt ya d'aure sosai tana tunanin shin dama su en uku ne.
Kuyi hqr da wnn.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/11/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
_*page*_ *```25```*
Ita tasan a qauyen su akwai en uku amma biyu ke kama da juna se d'ayar ta fita daban amma su wad'anan su duka uku kama suke har ba'a banbance su........Malika ce ta katse ta da tunanin da