Showing 9001 words to 12000 words out of 168541 words

Chapter 4 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9136

ta mata lahani a baya ta xuba mata ruwan zafi, inda Allah ya taimaka ma ba wani xafi ga ruwan ba" Hajiya ta gwalo ido tace "ni kuwa yaushe pretty zata yi hankali ne tukuna me ma ta mata da tayi mata wnn d'anyen aikin? Nasir yace "Kawai don tana jin haushin an hanata tuqin mota a dalilinta kuma kinsan halin pretty ta tsani talaka ba kad'an ba, cikin damuwa mamar tace "to kai nasir baza ka sallami yarinyar mutane bane ka huta, shawarar da nazo yi dake kenan umma don gsky bana son wani abu ya sake faruwa da ita duk da nayi ma pretty kashedi amma hankalina zai fi kwanciya idan ta koma ga en uwanta sae dai inna ce matsala don yanda Rayyanat ta kwanta mata a rai ba lalle bane ta yarda da hakan zata iya cewa a kaita gun en uwan Rayyanat d'in in yaso ta nemi alfarmar su bar mata ita ta riqa yi mata en wasu aikace aikace in yaso duk wata ta riqa biyanta kinga kuwa duk dai ba'a rabu ba dmn gsky nafi son Rayyanat ta komawarta gun en uwanta.
umma ta nisa tace"to ya kake ganin za'ayi haka? Ya dan yi shiru snn yace "Eh to ina ganin kawai zan maida Rayyanat ba tare da sanin inna ba sae bayan na dawo na snr da ita kinga dole zata haqura.

Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






19/12/2016






🔮```9```🔮
To shikenan Nasir amma ina son kafin Ku tafi kazo min da yarinyar na samu abinda na bata don yarinyar ta bani tausayi wlh har dai in na tuna ko wane hali en uwanta suke ciki na rashinta oho Allah kad'ai ya sani.
Wlh umma nima tunanina kenan kullum gashi taqi fad'a bare naji ko akwai lambar wayar su a kira a snr dasu halin da take ciki amma yanzu Alhmdlh tunda taji sauqi zan lalla6ata ta gaya min sae na maida ta.
Nasir Yayi mgnr ne yayinda ya tashi yace "to umma ni zan tafi "
Umma tace "To ka gaida innar" yace "to" snn ya fita.


Nasir na fita ya nufi 6angaren su pretty ya d'auki inna dasu saliha suka wuce.


Hajiyarsu pretty na fitowa daga bathroom sae ga mai gidanta ya shigo ransa a 6ace ta kalle sa da kulawa tace "lafiya Alhj me yake faruwa ne?" da taikaci ya kalle ta snn yace" ni nasara wace irin tarbiya ce kika bawa 'ya'yanki? kaf dangin nn ba wanda yakai su rashin mutunci idan suka tashi, musamman ma Fatima" nn cikin fad'an duk ya kwashe abinda inna tazo ta gaya mai har da yaron da pretty ta kad'e kwanaki don duk shi bai sani ba.
A fusace ya d'ora da cewa "kiramin ita yanzun nn tazo ina son ganinta, kwata kwata daga yau ma ta daina jan mota na hanata"
Umma ta dan tabe baki tace "ni dae kayi haquri Alhj, ai ba laifinta bane tsautsayi ne da kuma qaddara...." Rae bace Alhj yace "idan wnn tsautsayi ne me yakaita gidan inna har taje ta watsa ma er mutane ruwan zafi a jiki ko shima tsauyayin ne! Ku fa kiyaye ni ke da 'ya yan ki" ganin ynda ransa ya bace yasa tace "Ayi haquri Alhj bata kyauta ba dae, amma zancen tuqa mota tuni yayanta ma ya kar6e motar," Alhj yace "yayi dai dai don in kece baza Ki kar6e ba duk kinbi 'ya'ya kin lalata da baqin so sae kace kanki aka fara haifuwa.


Nasir na sauke su inna gida ya wuce office bayan sun shiga gidan, saliha da Ameera suka shiga kallon Rayyanat da ke zaune ta lanqwashe qafafu tana shan fura a falon, kallo d'aya Ameera tayi mata ta kauda kai sbd ta gano ita ce yarinyar da inna taje tana faman masifa akai don a gabanta akayi komai ita da saliha.
Saliha kuwa kallon Rayyanat take da d'an murmushi a fuskarta ta kalli inna tace "inna wnn itace Rayyanah?" Inna ta washe baki tace "eh ita ce er albarka babu ruwanta wlh" Saliha tace "eyyah sannu Rayyanat ya jiki?" D'an guntun murmushi tayi snn tace "Alhmdlh" a takaice.
Ameera ta ta6e baki taja hannun saliha tace "ke ni tashi mu tafi gidan inna hajjo mu gaidata" (wata makociyar inna dake nn kusa bbu nisa)
Inna ta washe baki tace "to in kunje ku kar6o min nono na samu na dama furar anjima" nn ta kwance ha6ar zanen ta ta basu nera d'ari tace "ku siyo na duka," Ameera ce ta kar6i kud'in tana walwale su tana dariya ganin yanda suka tamure tace "kai inna wai har yanzu baki daina dunqule kud'i a ha6ar zani ba" bata jira cewar Inna ba ta ja Saliha suka fice daga falon, sae a snn Rayyanat ta gaida inna da ladabi, inna ta amsa da fara'a tace "sae ynxu kike shan hurar, ya bayan in ga ni?" Rayyanat ta dan xuge zip din rigar jikinta inna ta duka da sauri tana kallon bayan, kmr xata yi kuka tace "Allah ya Isar maki, da bayan nn ya tashi yau da anga xube xuben ruwan xafi a jiki don duk sae na tafasa ruwa na bi ta har gidan mijinta na kona ta ni ma" Hurera dake kitchen ta fito tana dariya tace "A'a ba ayi hka ba Inna, Allah dae ya tsare" inna tace "ae ynxu ma daga gidan ubansu nake, kuma yace anjima da daddare xae xo ya gane ma idonsa" Bude kofar falon aka yi, duk suka juya don ganin wnda xae shigo, inna na ganinsa ta tsuke fuska, ya karaso falon fuskarsa a tamke, Rayyanat tayi saurin gyara rigarta, a fusace yana kallon inna ya soma magana "don me xa ki je ki hada ni da Baffana kan wata bnxa can yar kauye Hajiya," inna ta tabe baki tace "sae dae kae ne bakauye ko uwar ka amma ba yar nn ba," xaro ido yyi yana kallonta, ita ma ta yo waje da ido tace "kwarae kuwa!" Rayyanat da tun shigowarsa falon ta sunkuyar da kanta hawaye ya shiga bin kuncinta, ya huzar da iska ya cije lebe lkci daya idonsa ya kada, ya juya fuuu ya fice daga falon, inna tace "Wawa kawae." Baaba hurera ta sauke ajiyar xuciya tace "Ayi hkuri dae inna" mikewa Rayyanat tayi har lkcn hawaye na bin kuncinta, Inna na ganin hka ta rude ta shiga tambayarta lfya, Rayyanat ta kasa bata amsa, hkn yasa inna ta fashe da kuka tace "yo baki ji nace shine dan kauyen ko uwarsa ba, ni dae na shiga uku da 'ya yan kabiru" lkci daya Rayyanat ta hadiye kukan da take tace "kiyi hkuri inna, ni ba shi yasa nake kuka ba, naga ina ta hada ki da jikokin ki ne" cikin kuka ta karashe mgnr, inna ta hade rae tace "suke dae hadani da ke, kuma Allah ya fi su" Baaba hurera tayi murmushi, Rayyanat ta duka ta dauki sauran furan da take sha ta nufi kitchen.
Da rana nasir ya shigo gidansa, ya nufi dakin pretty ganin bbu kowa falon ga ko ina kaca kaca, xaune ya sameta sae fushi take, yaje kusa da ita ya zauna ya shafi gefen fuskarta yace "nasha gaya miki ki daina fushi baya miki kyau," hararar sa tayi snn taja tsaki tace baka son nayi fushi shine zaka kaini qara gun daddy," Nasir ya xaro ido yace "au kin dauka nine, to inna ce taje da kanta ta gaya mai aikin da kikayi don haka ko yanzu kika sake gigin aikata wani abu akan Rayyanat zata je ta snr dashi ne," cike da bacin rae ta tashi tana masa mugun kallo tace"ni yanzu banda lokacin wnn er qauyen bare na qara kulata" ta ja dogon tsaki daga haka ta wuce fuuu! ta barshi nn zaune" girgiza kansa kawai yayi ya tashi yaje ya bud'e fridge ya tsiyaya ruwa a cup yasha.


Washe gari ya gama shirin sa tsaf yaje d'akin pretty wacce yanzu ne tashinta zata shiga Bathroom dmn yin wanka.
Bai qarasa inda take ba a iya gun dressing mirror ya tsaya ya ajiye mata kud'i yace "zanyi tafiya ne ban kuma san yau ko gobe zan dawo ba" ta hade rae tace "ina zaka tafi?" Ya daga kafada yace "Kina da sako ne?" daga haka yyi ficewarsa, ta6e baki tayi gami da jan tsaki tace "aikin banxa, kadda Allah yasa ka dawo ma"


Nasir bai zarce ko ina ba sae gidan inna cike da niyyar ya d'auki Rayyanat ya maida ta gun en uwanta. Bbu kowa falon Inna, hkn yasa ya nemi gu ya xauna yana tunanin ynda xae fita da Rayyanat ba tare da sanin Inna ba, Baaba hurera ce ta shigo falon daga kitchen, da mamaki tace "A'a Nasiru yaushe kuma ka shigo" yyi murmushi ya gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa ya kwanan pretty, ya amsa da Alhmdllh snn yace "Baaba Rayyanat xa ki kira min amma fa kar ki bari inna tasan da ina gidan nn" tace "to bari in kirata" ba a dau lkci ba ta dawo falon Rayyanat na biye da ita a baya, hijab ne har kasa jikinta yasan inna ce ta sa aka dinko mata, ya kafa mata ido har ta karaso ta xauna kasa kanta a sunkuye ta gaishesa, ya amsa yana murmushi ya tambayeta ta tashi lfya, kai kawae ta gyada masa, bae kuma cewa komae ba har na kusan minti biyar hkn yasa ta dago kai tana kallonsa da manyan idanuwanta, murmushi ya sakar mata ta dukar da kanta da sauri, ya kira sunanta a nutse ta amsa ba tare da ta kallesa ba, yace "nasan yan uwanki na cikin tashin hnkli Rayyanat, kiyi hkuri ki gaya min ina ne garin ku" Rayyanat tayi kkrin ganin hawaye bae sakko idonta ba a karo na farko ta gaya masa sunan garin a hnkli, ya gyada kai da gamsuwa yace "to ina xa ki pretty ta kade ki da mota?" Ta girgixa masa kae da kyar tace "garinmu xan ko ma" yyi shiru snn yace "to da me ya shigo da ke kano? Shiru tayi taki cewa komae hkn yasa yace"kin shirya komawa garin naku gun yan uwanki ynxu?" Gyada masa kai tayi kawae, yyi shiru na wani lkci snn yace "to tashi ki dauko ledan kayan ki, amma kar ki Bari Inna ta ganki" tace "to" snn ta nufi dakin da Inna ta bata tana murmushi a ranta tace "don xan tafi ba yana nufin na bar shi bane, har abada baxan bar shi ba, nemo sa baxae min wahala ba tun da na ga gari."












Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZANBAR SHI BA!```🔮










```Na Billy giro😊```






22/12/2016






🔮```10```🔮


A sanyaye Rayyanat ta dawo falon rike da ledan kayanta ta samu har nasir ya fita xuwa gun motarsa, ita kad'ai yake jira taje ta bud'e gambun motar a hnkli xata shiga ta tsaya cak jin murya inna a bayanta tana fad'in "Rayyanah me zan gani hka ina kuma zakije har da leda a hannunki?"
Sake gambun motar tayi ta juya tare da sadda kanta qasa ta ki barin su had'a ido da inna, ba shiri Nasir ya fito daga cikin mota ya tsaya yana d'an kame kame sbd yanda inna ta tsare shi da ido baki bude.
Kmr xata yi kuka tace " kaddai mayadda rayyanah zaka yi baka ko snr dani ba Nasiru"
Ya dan sosa keya yace "Aa inna, dama wae da.." sae kuma yayi shiru. inna ta fashe da kuka tace "dama me nasiru! mayadda ita zakayi d'in knn, na rasa dalilin da yasa aka rainani hka, ynxu da bn fito ba sae dae in nemi yar nn in rasa" ta fashe da wani matsanancin kuka har da dukawa, Nasir yyi murmushi yace "kiyi hkuri Inna, kuskure ne" inna ta dago ta tsuke fuska tana kallonsa tace "rufe min baki munafuki kawae" dariya yyi yana shafa kansa yace "na yarda, amma inna baki tunanin halin da yan uwanta da iyayenta ke ciki ynxu? Ynxu misali lkci daya a nemi pretty a rasa wani hali kike tunanin xa mu shiga gaba daya" lkci daya inba ta marairaice tace "ni fa ban ce kadda a mayar da ita gun iyayenta ba, kawae rashin sanar dani da ba ayi bne ya bata min rae" Nasir yace "to ayi haquri inna," ta galla masa harara tace "yo da ban hkura ba da ban tara maka mutan anguwar nn ynxu ba," dariya yyi yana kallonta, tace "ynxu dae dani ya kamata muje gun en uwan nata su ganni nima na gansu na samu ko zasu bar min Rayyanah in rike, ni dae yarinyar ta kwanta min in sonta" ta karashe mgnr cikin kuka, tana matsar kwalla tace "ka ga idan Allah ya kawo mata miji na gari sae tayi auranta,"


Ba yanda nasir ya iya yace "to shiknn inna jeki d'auko mayafinki mu tafi"
Inna ta washe baki ta ja hannun Rayyanah tace "zo ki rakani er albarka bazan barki a nn ba don tunda yayi niyya zan iya dawowa na samu ya tafi dake ne kawae,
ko meye dalilin hkn da yyi ne oho," nn dai inna ta jata suka tafi ciki don dauko mayafinta.
Har yaja mota inna bata bar mitan da take ba, hkn yasa nasir sam ya manta da zancen kaiwa umman shi Rayyanat kamar yanda ta buqata.
Tafiya sukayi ba mai wani nisa sosai ba dmn da kano zuwa qauyensu awa biyu ne sae dai tun lokacin da suka kama hanya Rayyanat keta zubda qwalla a boye har suka isa.
A bakin shiga garin tace da Nasir ya tsaya a nn, ya juya ya kalleta yace "garin naku ba'a shiga da mota ne?" Rayyanat ta daure tace "Ana shiga da ita amma ku sauke ni kawai nagode, zan iya qarasawa da kaina," inna ta yo waje da ido tace "yo Rayyanah ai ni en uwan naki nake son gani ko zan samu sumin alfarmar bar min ke"
Shiru Rayyanat tayi hawaye suka shiga silalowa a hnkli kan kumatunta ta, inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Rayyanah ko ba kya son komawa gu nane?" da sauri ta girgixa kanta muryarta na rawa tace "inna ni bani da kowa duk sun rasu"
Inna ta rafka salati da karfi ta fashe da kuka tana cewa "wayyo ni Hajara, wayyo ni" Nasir dae yyi shiru yana kallon Rayyanat amma ya kasa yrda da abinda tace, inna ta ci kukanta ta koshi Rayyanat na taya ta kmr a lkcn aka yi mutuwar, daga karshe tana fyace majina cikin kuka tace "Allah ya rahama masu, wayyo ni rayuwa" Da kyar Nasir ya iya bude baki yace "Allah ya ji Kansu" ba don ya yrda ba gani yake kmr karya tayi masu.
Cikin muryar kuka Inna yace "to nasiru muje muga mai garin nasu dmn haqqi ne akansa yasan Rayyanat zata zauna gun mu ko?" Nasir ya gyada mata kai kawae ya tada motar ya shiga tafiya a hnkli Rayyanah na nuna mai hanya har suka isa qofar mai gari.
Cikin girmawa aka tarbe su mai garin yyi mamakin ganin Rayyanah ya shiga tambayarta daga ina take, nn Nasir ya dan ji dama dama gnin mai garin ya santa, bayan an gama gaggaisawa Nasir ya zayyano abinda ke tafe dasu yana kallon Rayyanah, mai gari bai musa musu ba ya amince da abinda suka buqata ya Dora da cewa suyi kkrin ganin sun riketa amana don marainiya ce sun samu lbrin rasuwan mahaifinta, Inna tace "ka ji ka da wata mgna, kasan wacece ni kuwa," mikewa tayi tana washe baki tana kallon Rayyanat tace "tashi mu je jikata, Allah xae taya ni riko"


Bayan sun koma gida da kwana biyu inna ta fito cikin shirinta Rayyanat ma dake shirye cikin wani atamfa da aka dinko mata da hijab jiya tace "to Rayyanah jeki snr da hurera mu zamu fita."
Rayyanat ta nufi dakin hurera, dae dae nn Man ya shigo falon yana waya murmushi dauke a lebbansa, inna ta washe haqora tace "Allahu Akbar, sannu da xuwa d'an albarka dama kmr kasan neman wanda zai kaimu anguwar nake, sae gashi Allah ya jefo min kai"
Ya katse wayar da yake yana kallonta yace "kai Inna, ina xa ki cikin ranan nn" inna tace "yo ni rana da yana gasa mutum da bae gashe ni ba, kasan irin wahalar da na sha gidan mijina kuwa" ya tabe baki ya juya ya fita yace ina jiran ki a waje, tace "to to ynxu xa mu fito" tare inna suka fito da Rayyanah, yana jingine jikin motar yana jiranta don duk a tunaninsa ita da baaba hurera xa su fita, suna karaso gun motarsa ya zaro ido yana kallon innar yace "wae ke da wa xa ku fita?" Inna tace "yo Rayyanah mana" ya kuma xaro ido kmr wanda yaji abin tsoro cikin shan toka yace "nifa gasky baza ta shigar min mota ba, mgnr gskya knn, idan dai ke kad'ai ce to muje," inna ta tsuke fuska tana huci tace "yo naga ja'irin yaro, kai baka san tafiyar tata bace ma gaba daya, xuwa fa zanyi da it cikin dangi tasan kowa, kowa ya santa."

Girgixa kai yyi yana masu wani irin kallo yace "to ba da motata ba, ki kira Nasir da yyi maki hanyar ta ya kai ku" inna ta fashe da kuka tana girgixa kai tace "Ni ban san meyasa bn dace da jikoki ba a rayuwa duk sun rainani uwa ba ni na haifi ubansu ba" Muhammad ya girgixa kai yana kallon innar yace "bari to in kira wani ya kai ku inna kin ga fa sauri nake" inna ta hade rae tace "A'a sae dae ka kira ubanka Kabiru ya kai mu, idan ba shi ba kam al-quran bbu motar shegen da xan shiga" Muhd ya fuxa isa ya juya yana kallon Rayyanah yace "ke shiga muje" inna tayi murmushi tace "shiga Rayyanah" kasa shiga motar Rayyanah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login