Showing 156001 words to 159000 words out of 168541 words

Chapter 53 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9174

Kwalla tap a idonsa ya kalli ryynt wacce ke kallon sa ta kama hannun sa ta riqe gam a cikin nata cikin muryar kuka tace"Mk zan mutu"
Da sauri ya girgiza kansa yana mae share mata zufar goshinta da d'ayan hannun sa yace"Baza ki mutu ba my Ryynt ki nisa inshaa Allah yanzun zaki haifu kinji"
Ryynt da ko numfashin kirki bata iya yi muryar ta na rawa tace"Mk bazan iya ba mutuwa ma zanyi na sani"
Girgiza kansa yayi had'e da saurin kai hannu yana share mata hawayen da ke sauka kan fuskarta yace"um um my ryynt inshaa Allah baza ki mutu ba ki daina fad'ar haka dan Allah"
Tace"uhm uhm mk nayi qanqanta da haifuwa ka sani kuma wnn qaton cikin bansan ma ya zan iya haifo abinda ke ciki ba"
Yace"my Ryynt Allah zae taimake ki kawae rufe idonki ki nisa kinji dan Allah"
Ba musu ta rufe idanunta a hnkli tayi iya qoqarin ta na ganin ta nisa amma ta kasa sae kuka ta fashe masa dashi muryar ta na rawa tace"bazan iya ba mk dan Allah kiramin inna in ganta dan Allah"
Nan mohd yasa aka kira mata inna tazo Ryynt ta kama hannun inna sae kuka take tana roqon inna ta yafe mata mutuwa zatayi inna ta shiga rarrashinta tana mata addu'a tana tofa mata man kuwa duk yabi ya rud'e komai ya kasa yi sae shafar goshin Ryynt yake yana ta rarrashin ta wacce ta soma salati tana qoqarin miqewa sbd wata irin azaba da ta soma ji ta koma da qarfi ta saki hannun inna ta kama hannun mohd sae kuka take tana roqon ya yafe mata ga kuma salatin da take ta faman yi a bakinta yayinda take ta faman qoqarin miqewa man yana maida ta sae addu'a yake ta mata dan ya fahimci haifuwar tazo mata gab.
Da qarfin tsiya Ryynt ta qara riqe masa hannu sbd wani irin nishi mae qarfi da yazo mata a nn man yayi qoqarin cire hannun sa daga nata yaje da sauri yana bata taimako ta hanyar sa hannun sa ya soma ciro 'ya'yan sa d'aya bayan d'aya santala santala dasu biyu maza mace d'aya kuma kowanen su cikin qoshin lafiya.




Plz sorry 4 diz one


Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```




























🔮🔮🔮
*page 89*
A take nurses suka kar6i yaran dmn zuwa gyara su.
Cikin tsananin murna inna ta fita ta snr da Nasir abinda aka haifa.
Mohd kuwa ya kama Ryynt sae kissing d'inta yake yana mata sannu ita kuwa sae kallon sa kawae take qwalla tap a idonta.
Mohd da kanshi ya gyarawa Ryynt jikinta snn aka tafi da ita d'akin hutawa.
Nasir kuwa a lokacinda inna ta snr dashi ba qaramin farin ciki yaji ba wanda a nn take ya ciro wayar sa ya kira family house ya snr dasu.
Snn suka tafi d'akin da aka kae Ryynt sae barka suke mata shida inna suna mata sannu ,da aka shirya yaran aka kawo musu inna ta kar6i yaran d'aya bayan d'aya sae rawa take tana murna tana godewa ubangiji.
Haka ma Nasir bae yi rawa ba dae ya kar6i yaran cikin tsananin murna yana ta kallon su snn ya bawa mohd wanda bakin sa har kunne sae kallon kya wawan yaran sa yake da sak mazan shi suka biyo macen kuwa kamar an tsaga kara ita da Ryynt sae dae hasken duk na mohd ne.
Cike da so mohd ke kallon Ryynt yana nuna mata 'ya'yan su Ryyñt ta kalle su kawae bata ce komai ba shi kuma yayi zaune yana wa yaran sa addu'a.
A nn cikin asibitin mohd yasa aka had'awa Ryynt tea mae kauri tasha.
Basu bar asibitin ba sae ga mahaifiyar mohd tazo it da umman saliha.
Murna a gurin su ba'a cewa komai musamman mahaifiyar mohd da wani tsabar son Ryynt ya qara shiga ranta da duk motsi idan Ryynt tayi sae tace ya akayi ne Ryynt ba abinda ke maki ciwo dae ko, ko kina buqatar wani abu ne a kawo maki.
Ryynt kuwa kae kawae take girgiza mata d'auke da jin dad'in yau itace ke samun kulawa haka sosai a gun mahaifiyar mohd duk da cewa tuni ta fara samun kulawa a gurinta amma yau kulawar ta daban ce da kowa na cikin d'akin sae da yaji dad'in hakan musamman mohd wanda sae kiran wayar sa ake ana masa barka dan ba family ba har en uwa da abokan arziki duk an sanar dasu.


Sae da Ryynt ta sami hutu aka kuma tabbatar she is ok ba wata matsala snn suka nufi gida.
Gidan man suka nufa kmr yanda ya buqata snn ko za'a tafi gidan inna daga baya.
Suna shiga gidan da gud'a inna ta fito mota tana taka rawa dan farin cikin da take ciki ya ma wuce misali kuma irin tsafin nn ne da basa iya 6oye farin cikin su a koina.


Malika ta fito daga kitchen knn riqe da plate da abinci akai yayinda d'ayan hannun ta ke riqe da glass cup da ruwan lemu a ciki.
Ta tsaya cak tana sauraren ina ne gud'a ke fitowa.
Kafin ta iya yin komai sae gasu sun shigo falon ba shiri ta saki plate da glass cup d'inda ke hannun ta tayi saurin dafe mararta da taji ta wani irin tsinka mata sae ga jini agurguje yana fitowa ta qafafunta yàyindà ta saki ido tana kallon Ryynt da suka fara shigowa ita da man tsaye a qafafuwanta lafiyar ta qalau ga kuma jarirae uku da ta gani a hannun su umma da inna wacce still sae gud'a take ci gaba dayi shiyasa da kmr ba wanda ya lura da malika a cikin su bare zancen jin qarar fashewar glass cup da plate d'inda ta yar har suka haura sama zuwa d'akin Ryynt.
Malika kuwa kmr wata zautatta ta nufi hanyar d'akinta ba tare da ta lura da jinin dake ci gaba da fita a jikinta ba har ta isa d'aki ta d'auki wayar ta kai tsaye ta kira fa'iza muryar ta na rawa tace"Wayyo Allah fa'iza na shiga uku wlh wnn abar bata mutu ba haka ma abinda ke cikinta da ta haifo har su uku"
Da qarfi fai'za tace"what! she is still a live fa kikace! kuma ta haifo en uku hm never ga dukkan alama tashin ki knn daga bacci kinyi mafarki shine kika zo kina gaya"
Malika tace"wlh maganar gaskiya nake gaya miki fa'iza yanzun nn suka shigo da ita har da yaran"
Hm!plan ne kawai suka had'a maki malika dan inaga akwai wanda ya ganki a lokacin da zaki saka mata wnn maganin"
No fa'iza na tabbatar wlh ba wanda ya ganni a lokacin da nake saka mata maganin dan duk yaran da take tare dasu sunyi bacci kuma man baya ko gari kin sani.
Faiza tace"malika ki yarda da zance na wnn maganin qarfin tsiya ne dashi kuma kince kin had'a mata overdose snn young girl like her ace ta haifi yara har uku haba ae hankali hanji ne wa ita nn"
Hm fa'iza na gaya miki fa a gaban idona wlh ina la6e ina kallo tasha ruwan da na saka mata maganin a ciki snn girman cikinta kad'ae ya isa na yarda cewa ita ta haifi yaran, at all yanzu nasan shike nn ta gama saye min miji"
Ta qarashe mgnr ne cike da qwallah tap a idonta.
Fa'iza tace"ae wlh bata isa ba tayi kad'an"
Qwalar da suka taru a idonta ne suka zubo cikin muryar ta mae d'auke da rawar kuka tace"to yanzu fa'iza me kike ganin zanyi wanda zanci riba a kanta kuma, na farko na xubar da ciki na a banza wanda da yanzu qila ma nice na haifa masa yaran,na biyu maganin da muka kar6o a qauye gurin boka na sawa man a abinci dmn ya tsaneta har ya fara aiki yazo ya karye kuma tun daga lokacin maganin bae sake ci ba yanzu na sa mata maganin da nake ganin da ita har abinda ke cikinta ba wanda zae yi survive amma sae gashi she is still a live an dawo da ita lafiya qalau da ita har yaran,known fa'iza how can i do, me kuma ya rage da zan mata yanzu .
Fa'ixa tace"wlh baza mu barta ba sae kin dawo da mijinki hannun ki ,ki shirya yanzu yanzu nn kizo gidana muje wani qauye gurin wani shaharren boka aikin sa kmr yanka wuqa yau yau d'in nn sae a neme ta a rasa da ita har 'ya'yan kuwa kuma sae a lafira ko za'a ganta ta wlh dan nasan wacce tasa akayiwa kishiyarta haka kuma har yau mgnr da ake shekara uku da suka wuce ba ita ba labarinta har iyayenta sun haqura da nema.
Malika tayi saurin share hawayenta tace"shikenan gani nn zuwa yanzun.
Nan ta tsinke wayar had'e da juyowa cikin hanzari sae kawae ta tsaya cak ko tako d'aya ta kasa yi tana kallon man dake tsaye a bakin qofa ga kuma jinin da ta hango tun daga wajen qofar har zuwa inda take tsaye a lokacin suma ne kawae bata yi ba ta dasqare guri d'aya dan tasan tata ta qare man ya gama jin komai dan jikin sa har rawa yake kan tsananin 6acin rae ga wani irin mugun kallo da yake mata har ya qaraso gareta wanda kae tsaya ya kai hannu kan qugun sa ya zaro belt d'in wandon sa a nn malika tayi saurin durqusawa kan guiwoyinta ta kama qafafunsa sae girgiza kanta take tana fad'in"my man dan girmañ Allah kayi haquri wlh kasan duk abinda nakeyi a dalilin sonda nake maka ne dan Allah kayi adalci akan hukuncin da zaka min na roqeka"


Da qarfin tsiya man ya ture ta ba tare da yace mata komai ba sae zabgar ta da ya fara yi ta shiga ihu tana roqon yayi haquri amma ina kmr ma ziga shi take qara yi dan sae dukanta yake ci gaba dayi ta koina baji ba gani ita kuma bata fasa ihu tana bashi haquri ba.
Ganin yana neman hallaka ta yasa ta fito d'akin aguje yana biye da ita yana duka har suka sauko downstairs zuwa falo aguje ta nufi hanyar fita ya fizgota yana ci gaba da dukanta sae ihu take sosai tana bashi haquri.
Sae gasu umma sun fito gabad'ayan su suna tambayar sa lafiya me yake faruwa bae basu amsa ba sae aikin ci gaba da dukan ta yake nn Nasir da shigowar sa knn ya samu da qyar ya riqe mohd wanda sae faman huci yake yana kallon malika da duk ya farfasa mata jiki,cikin 6aciñ randa yake d'auke dashi ya nunata da yatsa yace"kije na sake saki uku kuma yanzun yanzun nn fita a nn in daina ganin wlh"
Subuhanalillah!
Shine abinda su umma da nasir suka fad'a inna kuwa sae salati ta soma yi,
Ryynt bata iya cewa komai ba sae kallon malika take da ta d'oro hannu akae ta fashe da wani irin matsanancin kuka mae cike da nadamar abubuwan da ta aikata"
Tazo gabanta tana kuka sosai ta kama qafafuwan ta tace"Dan Allah Ryynt ki roqa min shi ya janye sakin wlh bazan sake yunqurin cutar da ke ba na rantse"
Ryynt bata iya cewa komai ba sae mohd ne yazo yaja malika ya tafi da ita qiiiiiii kmr kayan banza ya tura ta waje ya rufe qofa sae kuka take tana dukan qofar tana bashi haquri da qarshe ta gaji ta zame jikin qofar tana ci gaba da matsanan cin kukan da take tunanin shike nn rayuwarta ta lalace ta rasa mohd a rnr da take tunanin rnr farin ciki ce a gurinta amma ta zamo mata rnr baqin ciki mafi soyuwa da komai ya ca6e mata har d'an cikin da take kurin ta samu wata biyu da suka wuce taqi snr dashi akan sae burinta ya gama cika ko zata snr dashi gashi ya 6are,burin bae cika ba,ga saki uku ga kuma irin dukan da tasha, cikin ma bae ji d'aya daga cikin mugayen ayukkan da take aikatawa ba tukun.
Rayuwa knn shiyasa aka ce idan zaka gina ramin mugunta to ka gina shi kad'an dmn wata rana zaka iya fad'awa ciki.
Allah dae ya shirye mu yasa mu dace amin.


Mohd kuwa tun da ya fitar da malika ya rufe qofa su umma sukayo kanshi cike da son tambayar sa abinda ke faruwa bae bar sun kae ga tambayarsa ba yayi saurin barin gurin ya tafi zuwa d'akin sa.


Ba yanda suka iya nan suma suka juya suka koma daga ciki amma mafaiyar mohd da Nasir fita sukayi dan dama ta kirashi ne dmn ya maida ta gida tana so zata d'an shiryawa Ryynt abincin da masu biqi ke ci.


Bayan har inna tayi wa yaran wanka an shirya musu ita ma Ryynt umman saliha ta had'a mata ruwan zafi tayi wanka ta shirya.
Mohd ya shigo d'akin ba tare da yace da kowa komai ba yaja hannun Ryynt ya tafi da ita d'akin shi sae kallonsa kawae ryynt keyi har ya zaunar da ita a hankali kan bed snn shima ya zauna yana kallonta ,a natse yace"still ba abinda ke maki ciwo koh?
Ta gyad'a masa kae yace"to wa ya miki wanka?
Murya can ciki tace"ni nayi da kaina"
Yace"kin tabbatar kin gasa jikiñ ki da kyau kuwa?
Ta gyad'a masa kae yace"ryt to yarana fa sun sha mamma ko har yanzu mamman bae kawo ba?
Kallon sa tayi kmr zata yi kuka tace"ko ya kawo ya kake son na shayar dasu har su uku"
Mohd ya girgiza kansa dan tun asibiti ya fahimci fushi take tun a lokacin da ya nuna mata yaran.
Ya d'an janyo ta zuwa jikin sa yace"yanzu Ryynt dan Allah ya azirtamu da yara har uku a lokaci d'aya shine ba kya so ga wasu sae nema suke ko d'ayan ma su samu"
Tace"ni ba haka bane wlh d'awainiyar shayar war su ne bansan ya zanyi ba"
Zaki iya my Ryynt kawae ki d'auki abun da sauqi kinji ae Allah ba zae d'aurawa bawa abinda yafi qarfin sa ba koh.
Ta gyad'a masa kai tare da kwanciya kan qirjinsa tanà shafa qirjiñ nasa a hnkli snn tace"kayi haquri zan tambaye ka"
Yace"ina jinki my Ryynt"
Tace"me yayi zafi tsakanin ka da mtr ka da har ka mata saki uku a lokaci d'aya abinda Allah baya so"
Yace"ki barta kawae my Ryynt so take taga bayan ki keda yarana kuma Allah ya fi ta,ni a ma daina zancen ta bana so kinji, gaya min a nn kike son zama ko gidan inna?
Ryynt wacce tayi shiru murya can qasa tace"gidan inna mana ka sani"
Yace"ni kuma gashi a nn nake son ki zauna shiyasa ma nayi wayon cewa a fara zowa nn gidan mu d'auki wasu kayan dan kawae na samu na lalla6i inna dmn ta zauna nn tare da mu"
Tace"ni gaskiya um um gidan inna nake so"
Yace"to shike nn my Ryynt amma kisani nima zan d'au jakata na bi ku sae ki la6ani a d'akin ki nida yarana"
Ta d'ago fuskarta d'auke da d'an murmushi tana kallon sa tace"kai ma dae da wasa kake ka sani dan inna ma bazata barka ba da kae har jakar ka zata koro ka ne"
Yace"to ke kuma kina kallo har ta koro ni baki ce komai ba"
Da wasa tasha toka tace"eh bazan hana ba sbd ni fushi ma nake da kae"
Yace"ni d'in nn kan me to?
Tace"sbd ka 6oye min ko yarana nawa ne a ciki na bayan rnr na gani kace min wae photon ne ya rarrabu"
Yayi murmushi tare da jan hancin ta yace"ae halin ki na sani zaki iya hargitse min idan na gaya miki amma kinga yanxu ba yanda zakiyi"
Tace"koh,ni koh nake da yanda zanyi dan yau ruwa kawae yaranka zasuyi ta sha bazan ba su mamma ba.
Yace"ae kuwa dana tsulaleki da zariyar wandona dan kinsan ban had'a komai da yarana ba don haka muje ma ki basu idan kina son zaman lafiya.
Ryynt dake kallon sa tayi murnushi tare da girgiza kanta tace"nifa kunyar su inna nake ji kuma yaran ma ana gama musu wanka sukayi bacci.
Yace"ba wani nn ko bacci suke sae kin basu kar yunwa tayiwa yarana illa"
Daga haka ya tashi ya fita Ryynt tabi sa da kallo d'auke da murmushi jim kad'an sae gashi ya dawo da yaransa duka uku cikin keken jarirai da ake turawa mae d'an fad'i kmr bed.
Ryynt ta kalli yaran sae wuntsil wuntsil suke kmr zasuyi kuka tace"har sun tashi daga baccin knn"
Mohd yace"inafa zasuyi bacci mae tsawo kin bar min su da yunwa tunda aka haife su gashi har kuka suke son su fara"
Ryynt tace"ae ba laifi na bane mamman ne bae kawo ba kai da kanka ka sani"
Yace"to naji ungo dae fara ba macen dan nafi ji da ita sbd kmr da kukeyi duk da dae hasken nawa ne"
Ryynt tayi murmushi tasa hannu biyu ta kar6i jaririyar ta d'aura ta kan cinyarta yayinda d'ayan hannun ta ke tallabe da kan jaririyar d'ayan kuma yana kan mammanta na gefen dama tana qoqarin fitarwa ta qasan rigar ta,da ta fitar mohd yasa tafin hannun sa ya share mamman snn Ryynt tayi bisimillah tare da sakawa jaririyar a baki ta soma sha dan lokacin ruwan mamman ya kawo.


Bayan sun gama shan mamman ne suka kwasa zuwa gidan inna har dasu alawiyya da mami.
Da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login