Showing 138001 words to 141000 words out of 168541 words

Chapter 47 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9167

jin dad'i Ryynt ta mata godiya don sosai take son turarukkan har dae yanda ta fahimci mohd na jin dad'in qamshin turarukkan ba kad'an ba.




8:30pm
Sae a lokacin zasu koma.
Mohd ya kalli Ryynt wacce ta shigo mota fuskar ta d'auke da damuwa yayi shiru yana kallonta shidai a sanin sa hjyr sa ta fara sake mata bare yayi tunanin ko ita ce ta mata wani abu bare kuma duk yinin nn a 6angaren su saliha tayi shi.
Hannun ta ya riqo ta kalle sa yace"me aka miki?
Cikin muryar kuka tace"umman saliha ce tace wae baza ta bar mami ta koma gurina ba sae dae kawae ta riqa zuwar min weekend da farko na d'auka wasa take ashe da gske take yi yanzu haka mami na can sae kuka take"
Mohd yace"to ae sae gobe ne ko zaki koma koh?
Tace"eh shine da zan fito nace gobe a shirya wa mami kayanta idan zan koma zan biyo mu d'auke ta a nn take gazgata min cewa itafa da gaske ne mami bazata koma ba"
Yace"meyasa ko kin ta6a yiwa mami wani abu ne da bata ji dad'in sa ba?
Tace"Aa ba haka bane wae zata takura mu idan ta koma"
Man yace "wace irin takurawa kuma?
sae kuma yayi shiru yana nazari can yace"haka ne Ryynt tayi tunani kuma"
Da sauri Ryynt ta kalle sa tace"kmr ya nifa banga wani takurawa ba tunda ba d'aki d'aya muke zaune da kai ba"
Yace"to ae rnr dutyn ki ne magana dmn dole a d'akina zaki kwana,
Kinga ba zae yiyu ki barta ita kad'ai a d'akin ki ta kwana ba koh.
Ryynt tace"to ae sae naje da ita mu kwana a d'akin naka mana"
Hm Ryynt knn wa ya gaya miki ana zuwa turakar miji da yaro.
Idon ta tap da qwallah tace"ba wani nn kai ma dae baka so ta koma d'in na fhmce ka"
Ryynt ba haka bane ki fhmce ni.....haka ne mana.
Ta qarashe mgnr ne cike da son fashewa da kuka hkn yasa yayi shiru bae sake ce mata komai ba yaja motar suka tafi.


Suna isowa gidan inna cikin fushi Ryynt ta fita mota ta wuce wacce bata zarce koina ba sae d'akin ta.
Mohd kuwa d'akin inna ya nufa d'auke da sallama abakin shi inna ta amsa sallama washe da baki tace"kun dawo?
Yace"eh inna mun dawo"
Nan ya nemi guri kan sofa ya zauna inna tace"Ryyh fa?
Yace"tana d'akinta rigima take ji yau"
Inna tace"rigimar me kuma ko so tayi ta kwana a can ka hanata?
Yace"Aa inna zancen komawar mami gurinta ne nn yayi wa inna bayanin komai wacce tayi shiru snn tace"to muhamnadu gsky fa kasan xama irin gidan ka ba d'an yaron da ke tayaka xama ba dad'i ne dashi ba,tunda kai dae ba zama kakeyi ba snn qarin abun ma kasan Ryynt bata iya bacci ita kad'ae a d'aki tunda kaga ba ita kad'ai ce matar ka ba da za'a ce kullum kuna tare don haka zancen rashin komawar mami a gurinta bae taso ba,
kawae abinda naga yafi shine zan samar mata er yarinya mae aiki da zata riqa kwana tare da mami idan ita tana naka d'akin ko kuwa hakan bai fi ba,don gsky bazan so a takura er marainiyar Allah ba bayan akwae yanda za'ayi.
Mohd ya nisa yace"hakane inna zan sami umman mami sae muyi magana"
Inna ta washe baki tace"to shike nn d'an albarka ko me tace sae kazo ka gaya min ni kuma sae nasa baaba hurera ta samo mata er yarinya mae hnkli da natsuwa,dan hk tashi maza je lallaso min ita.
Mohd ya tashi d'auke da murmushi ya tafi d'akin Ryynt ya same ta zaune kan bed ta had'e kai da guiwa sae kuka take.
Yaje ya zauna gab da ita tare da janyo ta zuwa jikin sa bata jira me zae ce ba ta zare jikin ta daga nashi ta sauka kan gadon ta shigewar ta bathroom ta rufe.


Mohd bae bita a bathroom d'in ba ya koma d'akin inna tace"ya naga har ka dawo?
Yace"inna mutuniyar taki tayi fushi da yawa inaga shiga bata ko tsaya ta saurare ni ba ta shigewar bathroom ta rufe"
Inna tace"muhammadu nasan halinka wata qil kan hanya fad'a ka mata sosai koh?
Haba inna meye abin fad'a a ciki sam wlh ni ban mata fad'a ba.
Inna tace"to jeka abinka ni naje na rarrashe ta"
Yace"to inna zan tafi d'in amma zan dawo zuwa an jima"
Tace"to sae ka dawo"
Daga haka ya tashi ya fita.
Inna kuwa ta tashi ta nufi d'akin Ryynt .
Ryynt na cikin bathroom zaune ta had'e kai da guiwa tana ci gaba da kukanta taji muryar inna ta kira sunan ta,da sauri ta share hawayen fuskarta tace"Na'am inna"
Inna tace"yi haquri bud'e qofa fito muyi magana kinji Ryynh"
Ba musu Ryynt ta tashi ta bud'e qofar ta fito.
Inna taja hannunta suka je kan bed suka zauna ta kalli Ryynt da kulawa ta dafa kanta tace"kwantar da hankalin ki Ryynh indae mami ce tare zaku koma kinji"
Ryynt ta gyad'a kanta snn inna tayi mata bayanin duk yanda sukayi da mohd sosai taji dad'i har ma tayiwa inna godiya.
Nan inna ta tashi ta koma d'akinta Ryynt kuma ta rage kayan jikiñta ta fad'a bathroom zuwa wanka.
Ta kwashe kusan awa d'aya kafin take fitowa d'aure da towel.
Bayan ta shafa Vaseline ta d'auko turarukkan ta na jiki ta shafe jikinta dasu tsaf sae zuba qamshi take snn ta nufi wardrobe dmn ciro kayan bacci sae jin tayi an rungumo ta,
a d'an tsorace ta juya taga mohd ne ta lumshe ido had'e da rungume shi murya can ciki tace"mk kaine har kasa naji tsoro"
Mohd dake shinshinar qamshin jikin ta ya shafo bayanta a hnkli yace"am sorry"
Nan ya qara qanqameta a jikin sa yana ci gaba da shaqar qamshin turaren ta kamar yanda itama take shaqar nashi suka jima a haka sae can ya d'ago yakai hannu a cikin wardrobe ya ciro kayan baccin da yaga zata ciro yaje da ita kan bed suka zauna yakai hannu zae yaye mata towel d'in jikinta dmn saka mata kayan baccin Ryynt tace"um um Mk kar inna tazo ta same mu bari naje bathroom na shirya"
Ba musu ya bata kayan taje bathroom ta saka ta fito ta same shi yayi kwance yana fuskantar silin idanuwan sa a rufe kmr mae bacci.
Taje a hnkli ta zauna kusa dashi nn ya bud'e idanun sa sae kallonta yake tana kallon shi can ya sauke idon sa akan cikinta ya jawota zuwa jikin sa yana shafa cikin.
A hnkli Ryynt ta tashi daga kan jikin sa ta zauna nn mohd ya tashi zaune yana kallon ta yace"Ryynt wae baki daina fushi dani bane duk da inna ta miki bayani"
A hankali ta riqo hannun sa tana kallon sa tace"No Mk ba haka bane nifa ina gudun kar inna ta same mu ne"
Sae da ya janyo ta ya kwantar kan qirjinsa snn yace"inna fa tasan ina d'akin nn bazata shigo haka kawae ba tunda tasan mata da miji ta ajiye"
Ryynt tace"to ai dare nayi ka tafi gida"
Yace"korata ma kikeyi to ae ni a nn zan kwana"
Ryynt ta kalle sa d'auke da murmushi tace"ae nasan da wasa kake"
Yace"ni da gaske nake dan yau kin tsakaloni da yawa bazan iya bacci ba ke ba"
Tace"me na maka"
Yace"ba ke bace kika zauna kina shafa turarukka ba towel a jikin ki"
Tayi saurin rufe fuskarta da tafin hannunta tace"haba MK ya zaka tsaya to kana kallona"
Yace"to sae kar na kalla nida matata kuma ae laifin ki ne da kika wani sakankance ba kaya a jikin ki kina aikin gabanki"
Cikin muryar kuka tace"to mutum da d'akin shi kuma har ya rufe qofa uhm uhm,wlh kuma ae ma duk laifin ka ne da ka koya min haka"
Nan ta d'auki pillow zata doka mai mohd ya riqe pillown yana dariya rungume da ita a jikin sa taje zuwa tashi ya qara rungume ta yace"nifa wlh da wasa nake miki ban ganki ba qamshin turaren ki ne kawai ya nemi rikita ni"
Tace"to meyasa kace ka ganni?
Yace"sbd na koya maki na kuma san zakiyi"
A shagwa6e ta bugo qirjin sa tace"shine kasa na tashi yin kuka da gaske"
Yace"kan me to ni ba mijinki bane dan na ganki sae ya zamo wani abu"
Tace"to ai ba dad'i ne mutum yana yin abu bae san ana kallon shi ba"
Yace"to yi haquri bari inga babyna na tafi"
Bata ce komai ba sae kallon sa take ya yaye rigar baccinta ya shafo cikin tare da d'aura masa kiss,ya tafi a hnkli kan qirjinta zae yaye rigar tayi saurin hanashi ya kalle ta yace"ayi haka an barni naga baby amma kuma a hanamin ganin abincin baby"
Ya qarashe mgnr ne d'auke da murmushi a fuskar sa,itama cikin murmushi tace"eh mana ayi sbd baby naka ne abincin baby kuma nawa ne da samun ganin sa sae an yanka ticket"
Yace"ok ai kuwa yanzun nn zan yanka ticket nn yaje zuwa had'e bakin su tayi saurin tashi tana ja baya tana dariya tace"nidai dan Allah ka tafi dare nayi"
Mohd da ya miqe tsaye yace"to zo mana muyi sae da safe"
Tace"me zaka min in nazo?
Yace"zanyi pecking d'inki ne kawae kema sae kimin na tafi"
Ba musu taje ya janyo ta zuwa jikin sa ya kai bakinsa a hnkli kan lips d'inta ya d'aura mata kiss itama ta mishi snn suka d'ago suna kallon juna ta cikin ido mohd yace"gobe da safe ki shirya xanzo mu koma gidan mu"
Tace"plz Mk ka bari sae dare dan Allah sbd gobe da safe so nake na cire en tsarabar kowa na aika mishi"
Yace"To ae ba wani aiki bane wnn zaki gama shi in time"
Sosai ta marairaice fuska tace"nidae dan Allah ka bari sae dare guraren bayan isha'i haka"
Yace" to naji Allah ya kaimu"
Ya fad'i hakane tare da d'aura mata kiss kan goshi snn ya mata bye bye ya fita.






Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 81*
washe gari guraren 11am man ne ya gama shirin sa tsaf na zuwa asibiti riqe da briefcase a hannun sa zae fito sae ga malika ta shigo d'akin cikin shirin ta itama fuskar ta a d'aure ta kalle sa tace"fita nake son nayi"
"Kifi ruwa gudu"
Shine kawae abinda yace ya ra6a ta gefenta ya wuce ta bisa da kallo har ya 6ace ma ganin ta snn ta fito bayan har ya fita gidan snn itama taja motar ta ta fita.
Bata zarce koina ba sae gidan fa'iza wacce dama ta san da zuwanta taja hannun malika tace"zo muje daga ciki"
Bayan sun shiga ciki sun zauna fa'iza ke cewa" malika matsala ta dake ba kya jin shawara wlh da nice ya ma haka ko shi kad'ai ne d'a namiji a duniya na yafe sa har abada amm ke wae ace har ya dubi tsabar idon ki ya gaya miki cewa kin fita a ranshi kuma kikayi sake da baki kika kasa d'aukar wani mataki sbd kawae kina gudun kar ya sake ki,mutumin da ke kad'ai ke haukar son shi,shi ya daina sonki meye amfanin rayuwa dashi to.
Malika tace"hm kefa ya fad'a ne kawae sbd zafin zuciya dmn tsawon shekarun da muka kwashe muna soyayya ba zae ta6a iya cire ni a ransa zama d'aya ba ya fad'a kawai dmn yaji dad'in bakin sa amma qarya yake yace na fita a ranshi.
faiza tace"To in hkne meyasa bazaki bi shawarar da na baki ba.
Wato fa'iza wlh ina tsoro sbd nasan halin my man yanda ya d'auki son haifuwa ya d'aura a ransa ba kad'an bane da zarar nayi kuskuren ta6a lafiyar wnn abar wlh zae iya sakina komai sonda yake min kuwa.
Fa'iza tace"hm ai ko in yasan wata bae san wata ba matso kiji"
Nan fa'iza taje saitin kunnen malika ta rad'a mata magana.
Daga haka suka kwashe da dariya suka lale malika tace"gud idea shiyasa nake son yin shawara dake wlh"
Fa'iza tace"hm bari kedai Allah ne ya ceci wnn abar da yasa bani bace ke ".
Malika tace"ko ni d'in ma ae ba dad'i na take ji ba wlh don ban ta6a d'aga qafa ba.

****
Da dare bayan isha'i Ryynt ce cikin kwalliya tayi shirin ta tsaf cikin babbar super Holland riga da rafa zane da sukayi matuqar kyau a jikinta tana sanye da gold sarqa da en kunnen ta masu kyau da aka saka a cikin lefen ta sae zuba qamshi take.
Ta d'auki jakarta da gyale kalar kayanta ta fito falo ta sami jikar baaba hurera zaune a falon wacce itace yarinyar da baaba hurera ta samo mata mai suna alawiyya tana zaune qasa kusa da gefen doguwar kujera ga tv kunne amma har ta soma bacci tana gyangyad'i rungume da jakar tufafinta a hannun ta.
"Allah sarki alawiyya har kin gaji da jira kin soma bacci"
Cewar Ryynt wacce ta nufi d'akin inna.

Man da tuni yazo yana jiranta tana shiga d'akin ya kafe ta da ido sae kallonta yake don sosai tayi kyau ba kad'an ba.
Hannun ta yaje riqowa xae zaunar da ita kusa dashi bata barshi ba taje gefen inna ta zauna tare da dalla masa harara da wasa,
inna dake kallon su tayi murmushi cike da jin dad'in ganin wae yau Muhammadu ne da Ryynh ke shiri haka abin sha'awa.
Nan ta sasu gaba ta d'anyi musu hud'uba snn suka fito falo aka tashi alawiyya inna ta rako su har mota tana tsaye suka tashi motar snn ta juya ta koma daga ciki.
Tafe suke amma gabad'aya jikin Ryynt a sanyaye don haka kawae taji kewar inna sosai.
Dukkan su suka yi shiru kmr ba kowa har suka isa family house suka d'auko mami.


Da suka iso gidan mohd tun daga kan harabar gidan Ryynt tasan cewa an qara qaya ta gidan sbd gabad'aya kujerun zama na shan iska an canza ba wad'an da ta sani bane haka da suka zo kan falo kaf komai yasa an sake sauya wa akan wad'anda malika ta farfasa kmr ma ba wata 6arna da ta ta6a faruwa a falon don an tsarashi matuqa Ryynt sae kallon falon take abin sha'awa kmr wata aljànnar duniya komai fari tas sae qawar da akayi da gold .
Da suka je d'akinta ma hakane Fari n gold duk an canza komai kmr d'akin turawa.
Dama tun da rana man yazo da kayanta kuma ta samu ya tsara mata komai sae akwatin mami ta kar6a dake hannun sa tasa a wardrobe ya bata makullin d'akin da ke kusa da ita wato inda alawiyya zata zauna wanda dama d'akin don baqi akayi shi.
Sae da ta kar6i makullin yace"idan kin kaita d'akin kizo falo ina son zanyi magana da kune keda malika"
Ryynt tace"to"
Snn ya fita ita kuma taje takai alawiyya a masaukinta ta d'an nuna mata yanda zatayi amfani da abubuwa ta fito taje downstairs ta samu har ya kiro malika taje tayi zaune ya soma yi musu bayanin tsari da kuma irin zaman lafiyan da yake so ayi a gidan shi baya son wani tashin hankali ko wani makirci da qulle qulle byn nn ya raba musu kwana wato two two days da kowace zata riqa yi a nata duty snn yace idan da akwae mai magana a cikin su sae tayi.
kowaccen su tayi shiru sae can Ryynt dake zaune qasa kusa da gefen kujera tace ita dae bata da abin cewa dmn tsarin da yayi dae dae ne a gurinta nn ya kalli malika dake zaune kan kujera kusa da shi wacce kmr ma bada su yake zancen ba ta wani d'aura qafa kan qafa tana chat yayinda take tauna chewing gum a bakinta.
Yace"kefa?
Ba tare da ta kalle sa ba tace"bani da abin cewa"
Daga haka ta tashi ta bar gurin ba tare da taji me zae ce ba.
Bae damu ba sae kallon Ryynt yayi d'auke da murmushi a fuskar sa ya sauko kan kujera ya zauna qasa kusa da ita yakai hannu ya tallabo fuskarta yana kallonta yace"kin san dae cewa dutyn ki ne yau don haka je ki sallami alawiyya da mami kizo ina jiranki a d'aki"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tare da gyad'a masa kai.
Nan suka tashi mohd ya nufi 6angaren d'akin sa itama haka.
Koda taje ta sami mami kwance akan bed tayi bacci.
Ta nufi wardrobe ta bud'e ta ciro farar rigar baccin ta irin wad'an da take sawa a mumbae sae dai wnn tana da er sama da zata rufe mata jikinta har qasa.
Bayan ta cire kayan jikinta sae da ta qara shafe koina na jikinta da turare snn ta saka kayan baccinta ,
ta cire wa mami kayan jikinta ta saka mata na bacci ta d'auke ta ta kaita d'akin alawiyya ta rufo musu d'akin ta fito.


koda tazo zata shiga d'akin mohd sae ga malika itama zata shiga da mamaki ta kalli Ryynt tace"jarababbiya me kuma zaki shiga yi a d'akin shi ke bada duty ba ko kuma nn d'akin uwarki ne da kike shiga duk lokacinda kika ga dama"


Man dake cikin d'akin shi yana kallon su ta ta camera setting

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login