Showing 162001 words to 165000 words out of 168541 words
Chapter 55 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
wayar ya fito mota ya zagaya ta gefenta ya bud'e mata yaja hannun ta suka shiga ciki suka tsaya a falo sae kallon sa take yana waya.
Yana gama wayar tace"Mk kai da kace min family house zamu je ya kuma kazo damu nn"
Yayi murmushi yace"wayon manya na miki ba wani family house da zamu je nn nake nufin zamu zo"
Tace"to meyasa?
Yace"har kya tambaya ko kin manta na gaya miki cewa da kinyi arba'in zaki dawo ne"
Tace"uhm kaima dae da wasa kake Mk abu sae kace tulin wanki haka kawae ba shiri ka kwaso mu kace mun dawo knn,da akwai dae abinda ka shigo d'auka je ka d'auko mu tafi kasan mun bar alawiyya da yara a mota"
Yace"Allah da gaske nake miki mun dawo knn ba wani abunda nazo d'auka"
Tace"Mk bana son irin wasar nn dan Allah ka maida mu gida dan wlh ni ban shiryi dawowa ba"
Yace"Ryynt wane irin shiri kuma idan kayane gobe zanje da kaina gidan inna na kwaso maku komai"
Haba mk haka kawai zan dawo banje nayiwa kowa sallama ba nida nake son har qauyen mu sae naje.
Gaskiya Ryynt ni bazan iya harakar al'ada d'in nn ba wae ace don mutum yayi arba'in sae yaje yawo gidajen mutane kiyi haquri bana so ba kuma zakiyi ba amma zuwa qauyen ku bazan hanaki ba ko gobe kike so zan kaiki.
Ryynt ta girgiza kanta tace"gaskiya ni kawae ka maida ni bazan iya wnn abin kunyar ba ae sae ace da had'in bakina tunda ko inna bata sani ba"
Da mamaki yace"abin kunya kuma Ryynt kina mata ta dan na maida ki shine ya zamo abun kunya"
Tace"eh mana yau yau fa da yin arba'in se aji kawae na dawo haba gaskiya ni ka maidani"
Yace"wlh bari kiji ba inda zan maida ki kin dawo knn"
Cikin muryar kuka tace"wlh ni kuma bazan zauna ba sae na koma"
Rae 6ace mohd yace"shike nn gaki ga hanya jeki bazan hanà ki ba amma wlh kar ki kuskura kice zaki je min da yara ,kiga idan baza mu rayu ba dan ba ke"
A fusace ta fita tana fad'in ae dama bance da yaran naka zan tafi ba.
Cikin 6acin randa tafito d'auke dashi taje taja alawiyya zasu bar gidan ,
Alawiyya tace"Anti ina zamuje munbar su Ammar a mota?
Ryynt tace"ki barsu ubansu zae ji dasu"
Daga haka alawiyya bata sake cewa komai ba har suka fita suka tari napep suka wuce sae gidan inna.
Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```
🔮🔮🔮
*page 92*
Suna shiga gida suka sami inna zaune a falo tana kallo wacce tana ganin su tace"Aa lafiya jim kad'an da fitar ku sae gashi har kun dawo?
Ryynt bata iya ce mata komai ba sbd kukan da take ji sosai tayi sauri ta shiga d'akin ta ta zauna gefen gado tare da fashewa da kuka.
Sae ga inna ta shigo d'akin ta zauna a kusa da ita ta dafa kanta tana fad'in subuhanalillahi lafiya Ryynt me yake faruwa?
Cikin kuka Ryynt ta shiga yiwa inna bayanin abinda ya faru tsakaninta da mohd.
Inna ta jinjina kae tace"cabd'i! lallai muhammadu ba d'an rainin wayo irin sa daga cewa zaku tafi wancan gidan shine zae d'auke ku ya tafi daku gidan sa a cewar kun koma knn ba tare da ya ko snr dani ba bare zancen shiri,kinga yi shiru daina kuka zae zo ya same ni shasha shan yaro marar kunya fitsararre ae gwanda da kika masa haka ina nn zae zo ya sameni sae naji in ubansa kabiru ne ya turo sa yayi hakan.
Tana kaiwa nn sae ga allawiya ta shigo d'akin da sallamar ta mohd ya aiko ta a cewar yana da magana da inna ,inna ta tashi tana fad'in shashasha dama nace ina nn zae zo ya sameni bari inje inji da wane shashan cin kuma yazo min dashi.
Ta fita bata ganshi a falo ba sae d'akinta ta same shi sae safa da marwa yake yaransa na ajiye gefe cikin keken su na turawa sae da inna ta zauna snn ya zauna suna fuskantar juna.
Cikin fad'a inna tace"shasha sha wane kuma shashancin ka zo min dashi ne iye fad'i ina jinka"
Mohd dake kallonta yace"haba inna ni gaskiya abinda Ryynt ta min sam banji dad'i ba amma kuma kinxo kina ganin laifina"
Inna ta dunqule yatsunta biyar ta watsa masa tace"ungo nn dan uwarka idan banga laifin ka ba laifin wa zan gani ne iye shashashà marar kunya ace yarinya yau yau da yin arba'in haka kawae zaka wani d'auke ta ka maida ba wani shiri ba tare da kuma ka sanar dani ba sbd ban isa da kai ba bani na haife ka ba koh!
Ni inna kinsan ba haka bane harakar al'ada d'in nn ne na zuwa yawon sallama gidajen mutane ne bazan iyaba shiyasa kawae ban sanar da ke ba.
Inna tace"yo lallai muhamnadu abu tun kakannin kakannin kace kae baka yarda dashi ba to bari kaji ba inda Ryynt zata koma sae taje tayi sallama da mutane kuma har qauyen su sae taje kaji in gaya ma.
Rae 6ace mohd yace"gaskiya inna ina buqatar matata ta koma bazan iya haquri har tayi wnn yawance yawance ba ta bari in taje can tayi"
Inna tace"dan uwarka a ina ka ta6a ganin anyi haka kuma da kace baka iya haqurin jiranta tayi wnn yawace yawacen ae duk dad'ewar dae ba zae wuce kwana uku ko hud'u ba idan anyi ququwa sati d'aya a cikin na biyu.......haba habà inna gaskiya ni bazan iyaba, na gaji da kad'aicin da nake d'auke dashi a bani matata kawae mu koma idan baso ake na shiga wani hali ba.
Inna tace"yo ka jima baka shiga wani halin ba shasha shan yaro marar kunya ba inda Ryynt zata je kumà maza fita a nn in daina ganin ka"
A fusace mohd ya tashi zae bar d'akin inna tace"wa kuma ka bar ma yaran naka ne iye?
Mohd ya juyo ya kalli yaransa snn ya kalleta cikin marairaice fuska yace"inna ya zanyi ne idan na tafi dasu bayan Ryynt bata can kuma kince bazata koma ba"
Tace"yo ae sae ka tambayi kanka daa da kace ta bar maka yaran ya kake tunanin zakayi dasu ne iye"
Shiru mohd yayi dan shi kansa yasan a lokacin zafin zuciya ne ya d'ebe sa ya kaisa ga cewa hakan.
Inna tace"kana jina kayi min shiru"
Yace"inna wnn zafin zuciya ne dmn bana da nufin zaluntar su na raba su da mahaifiyar su da ita kad'ai ce zata iya kula dasu yanda ya dace"
Inna tayi shiru tana kallon sa tace"matsalar ka knn muhammadu zafin zuciya abinda sam bayada anfani,yana da kyau mutum ya riqa tausasa zuciyar sa kafin ya fad'i magana dan kaga yanzu ba wata riba kuma sanin kanka ne yanda ka 6ata ran Ryynt ba lallai bane ta kar6i yaran nn kai tsaye sae kayi kamar kanayi.
Mohd yayi shiru kafin yake cewa"inna kiyi haquri dan Allah na barsu a hannun ki nasan idan kika lalla6a min ita zata haqura ta kar6e su dan yanzu nasan ni ko naje ba zata saurare ni ba"
Inna tace"Aa ni baxa ka bar min yaranka ba,ba kuma zanje na lallashi Ryynh ba kaje da kanka ae da zaka maida ta gidan ka bakayi shawara dani ba sae ma qarya da kamin sbd ka maida ni shasha sha"
Mohd yace"inna dan Allah kiyi haquri naji nayi kuskure zan kuma bi duk yanda kuke so koma yaushe ne zan haqura,kawae bana son fad'an da mukayi da ita ya shafi yarana dan Allah inna kije ki rarrasheta.
Inna ta nisa snn tace"naji zanje na rarrashe ta d'in"
Mohd ya mata godiya snn ya fita a cewar zae tafi ya dawo.
Inna tayi zaune shiru dan sae duk taji mohd ya bata tausayi amma bata jin zata iya bashi Ryynt su koma yau d'in nn dan ko ba komai tana son qara gyara ta da kyau.
Nan ta tashi ta nufi d'akin Ryynt dmn rarrashinta.
Bayan awa d'aya da fitar mohd sae gashi ya dawo,kae tsaye d'akin Ryynt ya nufa ya sameta zaune kan bed d'aure da towel ta fito daga wanka tana shafa vaseline ya zauna kusa da ita sae kallonta yake yasan ta ganshi amma sae tayi kmr bata ganshi ba tana ci gaba da shafa Vaseline d'inta dan har lokacin ranta a 6ace yake duk da cewa sosai inna ta rarrasheta abinda bae mata dad'i ba shine jin cewa a cikin kwanakin nn zata koma.
Mohd dake kallonta ya kira sunan ta a hankali bata amsa ba sae tashi tayi zata bar gurin ,a hnkli ya maida ta ya zaunar, qwallah tap a idonta ta kae hannu tana son cire hannun sa daga riqon da ya mata mohd ya sakar mata hannu tare da kwantar da ita kan qirjinsa sae rarrashinta yake yana bata haquri cikin kalamae dake saurin sanyaya rae,da yasa ta lafe a qirjin sa tana fitar da qwallah had'e da sautin kukanta da ke fita a hankali,mohd ya d'ago ta yana share mata hawaye yace"am sorry bazan sake ba kinji ban kyauta ba is ok daina kuka"
Bata ce komai ba sae komawa tayi kan qirjin sa ta kwanta d'auke da wasu qwallah a idonta cikin muryar kuka tace"haba Mk wane irin rashin haquri ne da baza ka barni ba na qara samun hutawa ko na wata d'aya ne dan Allah"
Jiki sanyaye Mohd ya d'ago ta yana kallon ta yace"Ryynt har wata d'aya fa kika ce kin san fa kafin ki haifu na jima rabona dake sbd naga abun na maki wahala sosai kuma bana son takura ki shiyasa na barki har kika haifu yanzu kinyi arba'in kuma kice na qara miki har wata d'aya,am sorry plz kiyi haquri zan dae iya qara miki sati biyu dmn wata d'aya ta min yawa kinji"
Ta gyad'a masa kae yayinda ya kae hannu yana share mata hawayen fuskarta snn ya maida ta kan qirjinsa ya kwantar yana shafa bayanta a hankali.
Sukayi shiru d'akin yayi tsit kmr ba kowa mohd ya katse shirun da cewa"yarana fa suna d'akin inna still suna bacci ko sun tashi?
Tace"eh sun tashi"
Yace"Mamma fa sunsha ko madara aka basu?
Tace"duka sun sha"
Yace"Nagode my Ryynt bari na tashi naje na gansu nayi sallama da inna na tafi yau bacci nakeji da wuri"
Nan sukayi sae da safe kamar yadda suka saba snn ya tafi d'akin inna. A nn Ryynt ta tashi tayi shirin bacci koda ta gama taje d'akin inna tuni mohd yayi musu sae da safe ya wuce.
Tun a washe garin rnr inna ta soma gyaran Ryynt da kayan mata kala kala masu inganci da umman saliha ta aiko sbd taji Ryynt zata koma dan a cikin satin nn mohd ya kaita gidajen kowa wato gidan nasir da gidan Amir da kuma Aamil dmn tuni matar sa Khadija ta koma ta kuma ji sauqi sosai don har ma cikin nata ya fara fita.
family house shine farkon inda suka fara zuwa har ma mahaifiyar mohd taba Ryynt turarukkan mata kala kàla masu dad'in qamshi tsadaddi bayan wad'anda ummam saliha ta bata.
Snn gida na qarshe da suka je shine gidan su Sarah qawar Ryynt.
A cikin sati na biyu suka tafi qauye aka musu tarba mae kyau matan mae gari sae barikalli suke ta fad'i ganin su Anwar sun yi wayo sun qara yin 6ul 6ul abin sha'awa sbd da Ryynt ta haifu an sanar dasu har ma suna sae da suka zo.
Da zasu koma matan mae gari suka basu cimakar qauye na kayan marmari da kuma abubuwan kayan miya qwarya qwarya kmr su busasshiyar ku6ewa, ,tafarnuwa ,man shanu da dae sauran dmn ba kad'an ba sunjin dad'in alherin da Ryynt taje musu dashi wacce mohd ne ya bata yace ta basu a matsayin ita ce ta bayar.
Da itama a gurinta sosai taji dad'in yanda mohd ya mata.
3 dayz later
Yau ce rnr da Ryynt zata koma tana zaune gefen gado cikin shirin ta tsaf kanta qasa tana sauraren inna dake zaune gefen ta tana bata shawarwari akan yanda zata kula da kanta da kuma yaranta ta gefen tsafta da kuma tarbiya mae kyau da zata taso ma yaranta dasu snn tace"kuma kar ki ta6a sake da musu addu'a safe da yamma da kuma idan zaku shiga bacci,haka kema kanki kar kiyi sake da addu'a"
Tace"inshaa Allah inna zan kiyaye"
Nan inna ta riqa hannun ta tace"to tashi muje kinsan muhammadu na can na jiranki a falo tun d'azu.
Kmr mae jin kunya Ryynt ta tashi suka fito inna ta rakasu har mota taga wucewar su snn ta koma daga ciki.
Tafe suke cikin mota yaran su na baya tare da alawiyya ,
Mohd kuwa na gaba shida Ryynt wanda tuqi yake amma duk rabin hankalin sa na gun Ryynt sae kallon yanda tayi kyau yake sabon kitson ta ya qara haskaka fuskarta an mata zanen lalle mai kyau ga kuma wani daddad'an qamshin turare da yake jin yana fita a jikinta yayinda ita kuma kanta ke qasa kmr mae jin kunyar sa dan ko wani dogon motsi bata yi hkn yasa mohd ya riqa jin kansa kmr wani sabon ango.
Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```
🔮🔮🔮
*page 93*
Bayan sun isa gidan ne mohd ya tafi da yaransa d'akin sa Ryynt kuwa taje d'akinta haka ma alawiyya.
Da shigar Ryynt d'aki ta soma cire kayan jikinta dmn shirin bacci.
Duk da cewa jikinta baya buqatar wani wanka amma haka ta fad'a Bathroom ta sake wani wanka ta fito tayi zaune tabi koina na jikinta duk ta shafa turarukka masu daddad'an qamshi ta d'anyi er simple make up ta shiga bacci snn ta tashi taje jikin wardrobe ta nemo farar rigar bacci wacce sae da ta feshe ta da turare snn ta saka,
rigar er fincika ce sosai iya cinya gashi komai na jikinta ana hangowa dan ita kanta ma sae da taji kunyar kanta a lokacin da tana kallon jikinta ta jikin mirror.
Ta jawo farar er samar rigar baccin da tsayinta iya guiwa zata saka kawae ta hango man jikin qofa cikin shirin sa na bacci yana zuba qamshi sae kallon ta yake yana qarosawa sannu a hankali har ya qaroso gurinta yana kallon yanda ta sadda kanta qasa taqi yarda su had'a ido.
Man da duk qamshin turarenta ya soma rikitashi yakai lallausan hannun sa a kasale ya d'ago fuskarta yana bin fuskarta zuwa surar jikinta da kallo cikin wani irin kallon sha'awa,
murya can ciki mae d'auke da kasala yace"my Ryynt yau ni kuma kike jin kunya"
Ryynt bata iya ce masa komai ba sae wani d'an murmushi tayi mae natsuwa da janhankali da yasa man yayi tsaye ya kafe ta da ido cikin wani yanayi da yake jin kansa na kasalar da ta qara saukar mae,ya kar6i er samar rigar da ke hannunta cike da kasala ya saka mata snn ya d'auke ta cak suka tafi d'akin shi.
D'akin ba haske sosai sae dim light da kuma wani daddad'an qamshi da ke fita a d'akin ga sanyin splt.
A hankali mohd ya sauke Ryynt tare da kai hannu ya cire mata er rigar sama ya yar,
ya kama d'ayar rigar itama yana cire ta sannu a hankali har ya cire ta gabad'aya sae bin jikinta yake da kallo kamar yau ne ya soma ganin sa snn ya lumshe idon sa a hankali ya janyota zuwa jikin sa had'e da kae hannu kan mammanta yana shafawa ya kalli yaransa dake kwance cikin d'an bed d'insu suna bacci snn ya maida dubansa gun Ryynt a natse murya can qasa yace"hope yarana sun sha sun qoshi dmn daren yau namune mu kad'ai bana son su tashi su takura mu"
Ryynt tayi murmushi tare da gyad'a masa kae.
Tana kallo ya rage kayan jikinsa snn ya d'auke ta cak yaje da ita kan bed ya kwantar had'e da zira harshen sa a cikin bakin ta lokaci mae tsawo snn ya zare sae shafa jikin ta yake yana kissing d'inta ta koina har ta soma maida masa martani suka shiga romancing d'in juna har suka je ga duniyar ma'aurata da gabad'aya man ya fita hayyacin sa sae sambatu yake yiwa Ryynt da yaji tamkar yau ne ya soma 6are ta a leda.
Washe gari da asuba mohd ne ya fara tashi sae kallon Ryynt yake da ke rungume a qirjin sa tana ta sharar bacci abinta sannu a hankali ya zare jikin sa daga nata ya tashi ya nufi bathroom yayi arwala ya fito.
Yaje yayi zaune kusa da ita yana shafa gefen fuskarta a nn ta shiga bud'e idanun ta a hankali har ta sauke su a nashi,
d'auke da d'an murmushi cikin jin kunya tayi qasa da idonta dan sae ta tuna komai da ya faru tsakanin su jiya.
Mohd dake kallon ta
yayi murmushi tare da kai lips d'insa a hankali kan goshinta ya d'aura mata kiss snn yace"asuba tayi tashi kiyi sallah kinji"
Ba musu ta tashi ya bita da kallo har ta shige bathroom snn ya tashi ya nufi masallaci.
Guraren qarfe goma zaune suke kan dining kowannen su cikin ado sunyi kyau sae zuba qamshi suke suna ciyadda junan su a natse,
Suna cikin cin abinci Ryynt ta kai spoon zuwa bakin mohd bae kar6a ba sae tagumi yayi yana ta kallonta wanda ba abinda yake tariyo wa face daren su na