Showing 81001 words to 84000 words out of 168541 words
Chapter 28 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
yanda ta rufe idonta sae ta mai kyau sosai har dae yanda eyelashes d'inta sukayi zara zara.
Ita kuwa Rynt jin iskan ya daina saukar mata yasa ta shiga bud'e idonta a hnkli har ta ware su a cikin idanun mohd,ta kauda fuskarta gefe yayinda man ya maida ta kan qirjin sa ya kwantar.
Yana jin zata fizge kanta yayi saurin cewa"um um bana so natsuwar ki nake so dmn zan tambaye ki ne idan kin gaya min gskyr amsa zan barki na tafi idan kumร kika min qarya ko kika min tsiwa ina nn dake har safe ba inda zanje.
Bata ce komai ba ya ci gaba da cewa ina son ki gaya min dalilin da yasa kika sakawa malika magani a abinci.
Tayi saurin d'agowa ta kalle shi cike da niyyar masa tsiwa se mohd ya girgiza kansa a hnkli alamar kar ta mae ,sae kuwa ta sadda kanta qasa tace"ni ba abinda na sa mata a abinci idan har ma ce maka tayi to qarya ta ma"
Yace"idan kin 6oye min?
Bazan 6oye wa ubangiji na ba.
Ya sauke numfashi yace"to meyasa kika ce mata zata gani a lokacinda zaki je girka mata abinci har kika bangaje ta kika wuce"
Cikin natsuwa tace"tsarine kawae irin nata dmn ni ba abinda nace mata a lokacinda muka had'u haka kuma ni bansan na bangaje ta ba"
Mohd dake kallonta yayi shiru sae can yace"to kina son ki koma gidana?
Tayi saurin girgiza kanta tana mae wani kallo na tsana snn daga bisani tace"Allah sauwaqe wlh bana so"
Yace"to ni ina so kuma sae kin koma don na riga da na maida auren mu tun ba yau ba"
Tace"kayi a banza don wlh ba inda zan koma"
yace"dolenki ki koma ko don cikina dake jikin ki"
Wnn karon fizge kanta tayi daga jikin shi tare da fad'in"ka ma cire ranka a wnn cikin dmn wlh zubar dashi zanyi don ba abinda zanyi da qaddararren abu a jikina"
Ta fad'i hnke tare da bud'e wardrobe zata saka abin hannun da take ta fmn 6oyo a hannunta bata so ya gani.
Mohd da ya fusata kan jin zancenta ya kama murfin wardrobe d'inda ta bud'e ya rufe da qarfi.
Nn Rynt ta fasa wani irin ihu dmn da yatsanta ya had'a ya rufe bae sani ba.
Kan kace me sae ga su inna da gudu sun shigo ita da su Aamil da Amir har ma da Baaba hurera.
Rynt dake riqe da yatsanta ta tafi da gudu jikin inna tana kuka yayinda man ya biyota a rud'e zai kama hannun ya gani. A fusace inna ta buge mai hannu had'e da kai masa wani irin gigitaccen mari ta kuma rufe ido tace"wlh maza fita a gidan nn in daina ganin ka kafin na bud'e idona!
Ba musu man dake dafe da kunce ya fita ya bar gidan yayinda en uwanshi suka shiga mamaki sosai.
Billy giro๐
๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro๐: [ 2/16/2017]
```๐ฎBAZAN BARSHI BA!๐ฎ```
๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
*```Page 54```*
Da fitar sa Inna ta kai hannu ta riqo hannun Rynt ta duba yatsar ,yatsar tayi jajir ga kuma jini da ya taru ya kwanta akan jikin qunba.
Cikin tausayi inna tace"garin ya hk ta faru?
Rynt bata iya cewa komai ba sae kuka da take tana yarfi da hannu.
Nan Inna ta ja hannunta suka je d'aki yayinda Amir da Aamil suka bi bayan su, Baaba Hurera kuwa kitchen ta koma dmn qarasa aikinta.
Bayan sun shiga d'aki ne inna ta zaunar da Rynt gefen gado snn ta kalli su Amir da suka nemi guri kan sofa suka zauna
Tace"d'ayan ku yazo ya duba mata yatsar ko da akwai maganin da za'a siyo mata tasha"
Aamil ne ya taso ya duba yatsar yaje da kanshi ya bud'e fridge ya ciro freshmilk ya tsiyaya a cup snn ya koma gun Rynt ya ciro farin handkerchief ya bata a cewar ta share hawayena ta,
Rynt bata kar6a ba sae cewa tayi"Aa nagode"
snn takai hannu ta share hawayen fuskarta .
Aamil dake kallonta ya bata fresh milk ta kar6a tasha kad'an ta bashi yaje ya ajiye ya kuma fita a cewar zai je ya siyo mata magani ya dawo.
Inna tace"to d'an Albarka a dawo lfy"
snn ta kama yatsar Rynt tana qara dubawa tace"shashashan yaro wae me ya daka miki a yatsar ne to don nsn ba makawa shine yaji maki ciwo"
A sanyaye Rynt tace"haka kawae ina bud'e wardrobe ya maida murfin da qarfi shine murfin ya daki yatsana"
Inna tace"kaji macucin yaro Allah zai isar miki ai yanzu kiran ubansa kabiru zanyi......
Yunqurin aman da Rynt ta shiga yi ne ya katse inna,
Rynt kuwa ta kwasa aguje sae bathroom tana ta kwara amae ta samu da qyar ya tsaya mata inna dake gefenta ta bata ruwa ta kuskure bakinta snn ta riqo hannunta suka fito taje da ita gefen gado ta zaunar tare da fad'in"sannu kinji"
Rynt ta gyad'a kanta tare da fad'in"inna zan sha agwalima"
Nan inna taje ta bud'e fridge ta d'auko mata sae ga Aamil ya shigo d'akin riqe da ledar magani a hannun shi yana waya.
Bayan ya gama wayar ne ya ba inna ledar maganin yace"kowanne d'ad'd'aya zata sha"
Inna ta kar6i ledar tace"to d'an Albarka sannu kaaji"
Aamil bai ce komai ba sae duban sa yakai gun Amir dake kishingid'e abinshi kan sofa yana ta aikin fmn dannar waya yace"tashi muje gida Abba ke son ganin mu"
Ba musu Amir ya tashi sukayi wa inna sallama suka tafi.
Sae a snn Rynt ta kar6i agwalima a hannun inna,inna tace"anya kinci abinci kuwa Rynh?
Rynt tace"Aa inna dama ina so zan sha fura ne"
Inna ta girgiza kai bata dae ce komai ba taje ta d'ebo mata furar, Rynt ta kar6a tare da ajiye agwalimar hannun ta da ta fara sha ta shiga shan furar yayinda inna ta 6alla magungunan da Aamil ya siyo ta ba Rynt ta had'iye had'e da furar da take sha.
Koda ta kammala shan furar inna ta shiga bathroom dmn yin arwalar sallar la'asar nn ita ma ta tashi taje d'aki wacce da shigarta d'aki tayi kici6is da abin hannun da ta tayar tayi saurin kai hannu ta d'auka taje ta 6oye snn ta tafi bathroom tayi arwala ta fito tayi sallah.
5:00pm
Man ne kishingid'e kan resting chair a cikin garden idanuwan sa a rufe kmr mai bacci.
Sae ga Amir ya shigo gurin d'auke da sallama ya nemi guri ya zauna yana mai kallon man da ya amsa mae sallama had'e da yunqurin tashi zaune cikin yanayi na kmr mara lafiya musamman launin idanuwansa da suka sauya zuwa ja.
Ya zauna yana mae kallon Amir yace"ya akayi kasan ina nn ne?
Amir yace"gateman ya snr dani bcs nayi kiran phone d'inka yafi a qirka baka yi picking ba"
Cikin damuwa man yayi d'an guntun tsaki snn yace"sorry na bar phone d'ina a mota ne"
Amir yace"No vex,but me yake faruwa tsakanin ka da inna ne haka?
Shiru man yayi sae can ya shiga snr da Amir abinda ya faru.
Amir ya sauke ajiyar zuciya
yace"to meyasa ka saki yarinya kuma kazo kana bibiyarta?
Man yace"Ina son maida ta ne"
Amir yace"kan me?
Yace"wato Amir sae bayan komai ya gama faruwa na fhmci cewa abinda nake zarginta dashi bata da hannu a ciki,it seems malika ce ta aikata hkn sbd kawae ta samu yrnr ta bar gidan"
Amir yace"ta yaya ka fhmci haka?
Man yace"waya na samu tana yi sae dae ban samu naji komai da suke cewa ba amma still ina kan bincikena da zan ga cewa na kama malika red handed.
But abinda na fiso farko shine na samu na maida wnn yarinyr sbd cikin da ke jikinta nafi son ta raine shi a gabana dmn nima na samu na bashi kulawar da nake so"
Amir yace"kaje ka bawa Abba haquri mana ko zai barka ka maida ta "
No Amir kasan da kamar wuya Abba ya barni na maida ta amma nasan tabbas idan itace ta nuna tana son ta dawo ba makawa Abba zai barta,amma sae gashi ita sam bata son dawowa"
Amir yace"meyasa ko tana fushi akan abinda ka mata ne?
Mohd yace"Aa dama fa yarinyar ba sona take ba ta amince da aure na ne sbd biyayya wa Abba,kaga kuwa dole Abba yaji zafi ace wacce ba er sa ba ma ta mai biyayya amma nida nake d'a a gurin shi ban mae ba dmn duk a tunanin sa na sake ta ne kan bana son ta bai yarda cewa laifi tamin ba.
Amir ya numfasa snn yace"kaga bari kawae zanje gun Abba na bashi haquri.....kai wae ka manta waye Abba wlh in kaje ma ka qara min laifi kawae abinda nake so dakai yanzu ka tashi kaje gun inna kafin ta kira Abba ta sanar dashi cewa naje gidan, ka bata hqr kar ta kirashi don in yaji naje gidan zai qara ganin na mai wata rashin d'a'ar ne tunda ya hanani zuwa gidan amma naje"
Amir yace"ai kayi letti don tun kafin mu baro gidan naji tace zata kirashi ta snr dashi"
No bata kira shi ba dmn da ya kirani ya min fad'a,
Amir yace" Ina fa zaka sani wayar ka na a mota"
Man yayi guntun tsaki yace"hkne fa, but muje naga idan bae kirani ba sae kaje ka bata hqrn.
Nan suka fito zuwa parking lot man ya nufi motar shi ya bud'e ya d'auko wayar shi ya duba miscalls ba na Abban su a ciki,ya kalli Amir yace"inaga bata snr dashi ba don bae kirani ba"
Amir yace"ok bari naje d'in"
Nn ya shiga motar shi yaja ya tafi ,man kuwa wayar sa ce tayi qara koda ya duba malika ce bai yi mamakin ganin kiran ba sbd yasan bata san cewa yana cikin gidan ba dmn koda ya shigo gidan 6acin ran marin da inna ta mae bai bar ya shiga cikin gida ba sae garden da ya nufa.
Wanda ko yanzu niyyar sa ya koma garden amma ganin kiranta yasa ya nufi cikin gidan.
Guraren qarfe tara da rabi na dare Rynt ce kwance tana bacci sae ga man ya shigo d'akin yaje a hankali ya zauna gefen gadon yana mai kallon fuskarta snn ya kai duban sa gun yatsar ta da ya jiwa ciwo.
Yakai hannu ya riqo yatsar yana dubawa wanda yana d'aura yatsar sa akan kunbarta sae kuwa ta tashi firgigit had'e da yarfi da hannu tana kallon shi kmr zata yi kuka.
Billy giro๐
๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro๐: [ 2/17/2017]
```๐ฎBAZAN BARSHI BA!๐ฎ```
_Mommy Ameena n Nafisat nagode sosai akan qaunarku a gare ni nayi matuqar farin ciki da samun saqon ku nagode!nagode!nagode! haka ma dukkan masoyana ina miqa saqon godiyata a gareku masu kirana har ma wad'anda basa kirana duk na gaida ku, n Luv u allโค_
๐ฎ๐ฎ๐ฎ๐ฎ
*```Page 55```*
Da sauri ta sauka kan gadon tana mae ci gaba da kallon shi. man kuwa ya tashi yaje gab da ita tare da jawota zuwa qirjin sa yana kallon d'an qaramin bakinta da yake qoqarin kai nashi akai ,
Rynt ta kauda fuskarta da sauri tace"um um bana so dan Allah kar ka min"
Bai mata ba d'in sae kumatun ta da ya riqo yana kallonta yace"kin gane ni knn"
Komai bata ce masa ba sae kallon sa da take shaye da toka tana yunqurin qwatar kanta tace"wlh ka sake ni ko yanzu na ma ihu"
ya riqo yatsar ta mai ciwo yace"kina min ihu zan matse yatsar nn ne sae kiyi ihu da dalili"
Bata kula shi ba sae yatsar ta taje zuwa fixgewa ya matse yatsar zata fasa ihu knn yasa hannunsa ya rufe mata baki yana mai kallon idanuwanta da suka ciko tap da qwallah, yace"duba ki kawae nazo yi amma tsiwar ki tasa na ji maki ciwo"
Ya fad'i hkne tare da janye hannunsa akan bakinta da ya rufe ,snn yakai hannun kan cikinta ya d'aura yana shafawa,
Rynt dake kuka riqe da yatsar ta sae ture hannun tayi ta fizge jikinta daga nashi ta kuma matsa nesa dashi.
Man ya tafi zai je gurinta ta fashe mae da kuka tace"wlh duk kazo sae na ma ihu sae dae ka kashe ni"
Ya tsaya cak yana kallonta snn yace"yi hqr kinji babyna kawae zan duba se na tafi"
Ta maqale kafad'a had'e da qara ja baya,ya kalle ta kawae yace"shike nn na tafi sae da safe"
Nan ya kama hnya ya fita d'akin.
Rynt da ta bishi da kallo shaye da toka ta share hawayen fuskarta snn ta fito taje d'akin inna zuwa bacci don dama daga kawae ta kwanta zata d'an huta ne bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari ta fito cikin shirinta na zuwa school sae sauri take dan ta soma makara amma koda ta fito bata samu drivern ta yazo ba sae wata had'ad'd'iyar farar mota ta gani fake a qofar gidan.
Bata bar ta ga wanda ke ciki ba sae dube dube ta shiga yi ko zata hango 6ullowar motar drivern ta.
Man dake cikin farar motar yana hango yanda Rynt ta jima tsaye tana faman dube dube wanda yasan jiran banza take don drivern nata yazo yace da drivern ya tafi abinshi shi zai kaita.
Gudun kar ya sata tayi letti ya bud'e gambun motar ya fito wanda har ya qaraso gurinta kallon shi take shima yana kallon ta,
bata gane cewa man bane haka shima bae nuna mata shine ba sae ma ina kwana da yayi mata.
Jin ya mata ina kwana yasa ta sadda kanta qasa had'e da mishi ina kwana.
Yace"lafiya lau,school zaki tafi ne?
Tace"eh"
Yace"taxi kk nema?
Tace"Aa mai kaini school nake jiran yazo"
Agogon hannun sa ya duba snn yace"muje na sauke ki"
Tace"Aa idan sauri kake ka tafi kawae zan nemi napep"
Yace"no muje kawae"
Ba musu tabi shi suka je suka shiga mota a nn ya tambaye ta sunan mrntar su da kuma anguwar da makarantar tasu take, ta gaya mai snn yaja motar suka tafi.
Cikin mota sukayi shiru ba mae ce ma wani har suka isa mkrntar,
Rynt tayi mae godiya snn ta bud'e gambun mota ta fita.
Mami ya hango taje da gudu ta rungume Rynt yayinda Rynt ta riqa hannun mami d'auke da murmushi a fuskar ta taja ta suka shiga makarantar.
Sae a snn yaja motar sa ya tafi wanda bai zarce koina ba sae gida.
Ya nufi d'akinsa ya sami malika kwance kmr yanda ya barta sae bacci take.
Kayan jikin sa ya rage yaje yayi kwance kan sofa yana tunanin hanyar da zai bi ya dawo da Rynt gidan shi.
Ya jima kwance a cikin tunanin sae wayar sa ta shiga ruri koda ya duba Aamil ne mai kiran ya d'aga wayar.
bayan ya gama wayar ne yaje ya tashi malika wacce ta tashi cikin yanayi na wacce bacci bae isa ba sae miqa take tana kallon shi.
Yace"tashi zaki yi baqi ne to 12"
Tace"su waye zasu zo?
Tsaki yayi yace"kinga ki tashi idan zaki tashi dole sae kinji ko su waye zasu zo"
Tace"me kuma yayi zafi my man daga tambaya"
Nan ta sauko kan gadon had'e da zowa gab dashi ta riqo kumatunsa tace"waya 6ata min ranka da safen nn pls koma waye kayi hqr ka gaya min su waye zasu zo don ya kamata na sani"
A hnkli ya janye hannuwanta da ta d'aura kan fuskar shi snn yace" su Aamil ne zasu zo tare da matan su"
Tayi murmushi tace"ok bari naje nayi wanka se nasa kuku ya girka musu kalolin abinci"
Bai ce komai ba sae kan sofa da yaje ya kwanta ita kuma taje ta shiga bathroom.
12:00
Sae kuwa ga su Aamil sun shigo gidan tare da kyakkywa matan su farare tas da kuma 'ya'yansu.
Matar Amir janye take da hannun d'anta kyakkywa d'an shekara uku mai kyau dashi.
Matar Aamil kuwa mace ce riqe a hannunta er 3yrs mai kama da ita sak .
Man suka tarar a falo wanda ya gaisa dasu cikin sakin fuska snn yaje ya kira musu malika da itama tazo ta tarbe su cikin murna da nuna farin cikin zuwansu.
Bayan sunci sun sha ne man yaja yaran ya tafi dasu shopping complex ya siyo musu kayan tand'e tand'e da na wasa suka dawo gidan sae murna suke suna wasa da abubuwan da aka siyo musu na wasa yayinda kowannen su ke riqe da giant lollipop suna sha.
Iyayen su kuwa suna nn zaune a falon sae fira ake tayi cike da nishad'i.
Basu suka bar gidan ba sae 4 suka nufi gidan inna.
Suna shiga gidan suka had'u da Rynt ta fito lesson teacher d'inta yazo zata fita.
Ba yabo ba fallasa suka gaisa da juna sae kallon yaran su take da sukayi matuqar bata sha'awa amma hkn bai sa taji kwad'ayin barin cikin dake jikinta ba.
Bayan ta dawo daga lesson ne taja yaran suka je suna ta wasa har da su wasan 6uya da guje guje,inna kuwa nacan d'aki ita da baqinta.
Sae qarfe 9 na dare suka bar gidan Rynt taji kmr kar yaran su tafi dmn akwaita da son yara sosai shiyasa duk ta had'u da yaro zata biye mae suyi ta wasa.
Washe gari koda ta tashi tana d'an jin kanta