Showing 129001 words to 132000 words out of 168541 words

Chapter 44 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9160

kallonta d'auke da murmushi yace"idan na fahimce ki kina nufin nayi gurbi a cikin zuciyarki knn?
Ryynt tayi murmushi tare da sadda idanun ta qasa tace"eh hkne d'in ka fahimce ni "
Farin cikin da Mohd yaji a ransa ya kasa barin sa a kwance hkn yasa ya tashi zaune tare da tada Ryynt itama ,
ya d'aura tafukan hannuwan sa kan kumatun ta yana mae kallon cikin idanunta snn yace"my Ryynt samun gurbi a cikin zuciyar ki yana nufin kina sona koh?
Sae da Ryynt tayi qasa da kanta cikin jin kunya tace"eh haqiqa ina sonka bazan 6oye maka ba, ba kuma zan kasa furta maka ba dmn ka cancanci fiye da haka a gurina sae dae ina tsoro kar sae na sakankance da soyayyar ka kazo ka juya min baya.
Ta qarashe mgnr ne cikin muryar kuka.
Mohd da ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki kan jin kalamanta,
ya d'ago fuskar ta yana kallon idanuwanta da suka ciko tap da qwallah yace"No my Ryynt ta yaya kike tunanin zan iya juya miki baya duk da irin sonda nake miki ko a ganin ki duk yaudara ce ba wae da gaske nake sonki ba"
Tace"Aa ba haka bane ina tsoron kar sae mun koma wnn matar taka ta qwace min kai ta yanda bazan sake samun kulawar ka ba"
Mohd yace"To kuma ke sae kiyi sake da baki ki barta har ta qwace miki ni"
A shagwa6e ta kalle sa tace"to ae kaine in ta gaya maka abu kake yarda kana biye mata kan duk abinda tace har ma baka yin bincike.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka,
mohd yayi saurin rungume ta yana shafa bayanta yace"no Ryynt wlh wnn kuskure ne da rashin sani amma nayi miki alqawari inshaa Allah bazan qara kuskure makamancin sa ba,I beg u kiyi haquri kinji kuma ki cire a ranki cewa zan iya juya miki baya wlh ko a mafarki hkn ba zai ta6a faruwa ba inshaa Allah,yi haquri daina kuka kinji.
Nan ta d'ago tana share hawayen fuskar ta mohd dake taya ta yace"kin haqura ko?
Ta gyad'a kai masa yace"to idan kin haqura yi min......
ya qarashe mgnr a cikin kunnen ta,
da sauri ta maqale kafad'a tana dariya zata bar gurin ya janyo ta da sauri yana dariya shima yace"sae fa kin min idan ba haka ba yau ba inda zamuje ko kuma na tafi ni kad'ai abuna bada ke ba gashi su maman sadiq ma duk fita zasuyi"
A shagwa6e tace"um um gsky bazan iya ba kunya nake ji ka fad'i wani abu dae"
Yace"shi d'in dae nake so idan kuma baza ki min ba shike nn bari na tashi na shirya na fita abuna ni kad'ai"
Yana gama fad'ar haka yaje zuwa tashi,tayi saurin riqo hannun sa tace"um um to zan maka d'in amma sae ka rufe idonka"
ba musu ya rufe idonsa Ryynt takai bakinta a hnkli ta had'e da nashi tana tsutsar lips d'in sa da harshen sa cikin wani salo kmr ta sami alawa,after a while taje zuwa zare bakin nata a hnkli,
man bae barta ba ya koma had'e bakin su ya soma yi mata nashi salon ,
bayan hannun sa dake kan qirjinta yana wasa dashi a nn Ryynt ta kasa in ma kanta sae kwanciya tayi ya bita tare da xare bakinsa ya maida kan qirjinta yana kissing d'in jikinta ta koina Ryynt bata iya hana shi ba sae kama masa tayi suka shiga romancing d'in juna.
Basu su suka iya barin junan su ba har sae da suka gamsar da juna.

Sukayi shiru rungume da juna sae numfashi da suke fitarwa a hnkli.
Man dake shafa bayan Ryynt ya shafo fuskar ta tare da d'aura mata kiss kan goshi yace"yau dae ba zancen fita kin gaji da yawa koh"
Tace"um um MK wlh nasa raina a fitar nn dan Allah muje"
Yace"ae tunda kina so za'a je d'in,tashi muje to muyi wanka sae mu shirya mu tafi"
Tare suka tashi zaune Ryynt ta rungumo sa tare da shafo cikin sa tace"cikin ka kmr kana jin yunwa"
Yace"wlh kuwa yunwa nakeji sosai kema nasan kina jin yunwar koh?
Tace"um um ba sosai ba kasan kafin mu koma bacci naci nmn kaza bari na kawo maka kaima kaci sae muyi wanka koh"
No kawo min fresh milk kawae nasha idan muka fito wanka sae muyi breakfast gabad'aya.
Nan ta tashi ta jawo bathrobe ta saka snn taje ta tsiyayo masa fresh milk a cup ta dawo ta same shi shima ya saka bathrobe d'in sa yana zaune akan bed yana duba missed calls d'in da ya gani a wayar sa don tun zasu koma bacci ya saka ta a silent.
Yana ganin ta dawo ya ajiyar wayar ,
ta zauna a kusa dashi ta bashi fresh milk d'in da kanta har sae da ya shanye snn suka je zuwa wanka basu wani jima sosai ba suka fito suka shirya snn sukayi break fast suka fita.


Da dare mohd ne zaune a falo kan doguwar kujera yana sanye da farar singlet n boxer yana kallon labarai yayinda Ryynt ke kwance kan qafafuwan sa tana sanye da farar rigar baccinta silk mae d'an siririn hannu da tsayinta ba zae wuce iya cinya ba ,wacce tuni tayi bacci sbd gajiya dmn yau yawo sukayi sosai a cikin garin mumbae wato gurare daban daban na bud'e ido da kuma gurin shaqatawa sukaje kuma duk inda sukaje sae da mohd yasa aka musu photo shida ita snn sukayi dasu Amir da matar sa da kuma d'an d'ansu sadiq dan duk tare suka fita shiyasa basu dawo ba sae yamma da kaya niqi niqi na en tsarabar da Ryynt ta siyo.
Da ya gama kallon labaran sa ne ya kashe TV ya d'auki Ryynt ya shiga ciki da ita.

Washe gari ne suka je Germany kwanan su biyu a can suka kammala abinda suka je yi suka tafi dubai sukayi kwana biyu dmn hutawa inda a germany har dubai sae da man yaja Ryynt suka zaga gari dmn ta bud'e ido.
Bayan sunyi kwana biyu a dubae ne washe gari suka kama hanyar dawowa Nigeria.

6anaren malika kuwa safiyar yau sae murna take tayi dan man ya kirata ya snr da ita yana hanya har ma ya snr da ita lokacinda jirgin nasu zae yi landing ai kuwa tasa aka shirya masa hadaddiyar liyafa wacce tana ganin lokacin saukar jirgin su ya kusa taje tayi wanka ta tsala ado taja motar ta sae Airpot dmn tarbon mohd wacce kwata kwata bata san cewa tare da Ryynt yake ba dan har yanzu bata da labarin komai asalima shaf ta shafe babin Ryynt a cikin rayuwar ta.








Billy giro😊
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 78*
Da isar ta ne jirgin nasu ya sauko mutane suka fara firfitowa kan farin ciki bakin ta baya ko rufuwa sae rarraba ido take ta inda zata hango mohd.
Kai tsaye duk wani farin cikin nata a take ya tafi numfashinta ya nemi ya d'auke,
ganin mohd tafe cikin baqar suit maqale da Ryynt a jikin sa tana sanye da arabian gown baqa tayi rolling da black top kmr wata balarabia dan gabad'aya ta canza mata ta qara kyau da haske da ita har mohd d'in sae sheqi suke ga wani murmushi da suke da ya qara musu kyau suna tako cikin natsuwa.
Sam malika ta kasa gazgata abinda take gani musamman hannun mohd da ta hango ya zagayo dashi ta kunkunmin Ryynt yazo dashi har izuwa kan tulun cikinta da ya fito 6aro 6aro da cikin ne abinda yafi matuqar bata mamaki don har suka qaraso ta kasa gazgata abun wae kodai mafarki ne ba gske ba gashi ko qaramin yatsanta tama kasa motsawa sae dasqarewa da tayi a guri d'aya ta kafe su da ido tana kallo Nasir yaje ya tarbe su cike da murna.
Yayin da su saliha da mami dake tare dashi suka qanqame Ryynt cike da murnar ganin ta kafin suke zuwa gun matar Amir itama suka tarbe ta.

D'auke da murmushi mohd ke kallon malika dake qarasowa gurin su wacce tana isowa cikin tsananin 6acin rae ta damqo suit jacket d'in mohd da hannuwanta duka biyu ta jijjiga shi tace"gaya min shin mafarki nakeyi ko kuwa da gaske ne dae wnn abar ce nake gani a tare da kai!
Da qarfi mohd ya buge hannuwanta ya jawo Ryynt zuwa jikin sa yace"kin ganta gata ba mafarki kikeyi ba dagaske ne kuma wlh kar ki kuskura ki sake kiranta da wnn abar idan ba haka ba wlh zanyi mugun sa6a miki very stupid!
Nan kawae malika tayi kukan kura zata shaqo wuyan Ryynt man yayi saurin ture ta gefe
snn ya nuna ta da yatsa yace" Ryynt she is my wife n my life bazan ta6a yarda kici zarafinta ina tsaye ba and idan har kinsan tashin hankali ya kawo ki maza bar gurin nn in daina ganin ki ko kuma wlh na miki dukan tsiya a nn!
Tsaf tasan zae iya aikata abinda yace ta kalli Ryynt ta qyasta yatsunta tare da nuna ta tace"wlh wlh yau sae na zamo ajalinki"
Daga haka ta wuce fuuu a fusace.
Mohd dake kallonta ya buga tsaki dan shi a shirme ma ya d'auki zancen nata ya kalli Ryynt wacce still tana a jikin sa yace"Ryynt are u ok bata ta6a ki ba dae ko?
Ryynt ta girgiza kanta tana qoqarin maida hawayen da suka cika mata ido ba wae don ta tsorata da jin furucin malika ba sae don ko kad'an bata ji dad'in abinda ya faru ba har dae yanda gabad'aya gurin idon kowa ya tsaya a kansu har ma wasu na nuna su suna magana.
Nasir da Amir ne suka ce da mohd "wae me yake faruwa ne?
Mohd ya buga tsaki yace"da Allah ku fita batun mahaukaciya kuzo mu tafi"
Daga haka suka wuce ba wanda ya sake cewa komai.


Amir da matar sa da d'ansa motar su suka shiga da driven su yazo da ita yaja su zuwa family houshe.


Mohd da Ryynt kuwa motar Nasir suka shiga dasu har su saliha wanda basu zarce koina ba sae gidan inna wacce tana ganin Ryynt ta washe baki cikin tsananin murna suka rungume juna inna ta d'ago riqe da baki sae kallon Ryynt take cikin jin dad'i ganin yanda kallo da'ya zaka yiwa Ryynt kasan cewa tana samun matuqar kulawa da jin dad'i musamman yanda fatar ta tayi smooth da haske tayi fresh da laushi kmr ftr sabon jinjiri sae sheqi take tana qyalli.
Washe da baki inna ta qwalawa baaba hurera kira baaba hurare taxo da murna ta musu sannu da zuwa wacce itama ta kasa rufe baki sae kallon yanda Ryynt ta canza take.
Washe da baki inna tace"kema kinga yanda Rayyanah ta dawo ko awa wata balarabiyar saudia ai Alhamdulillahi ba abinda zance da kae Muhammadu sae nace Allah shiyi maka albarka dmn ba makawa Ryynt ta sami sauyi da kulawa a gurinka haqiqa naji dad'i wlh ubangiji Allah sarkin halitta shi qara yi maka albarka.
Mohd yace"Amin Amin inna"
yayinda yake kallon Ryynt dake murmushi tana fmn 6oyon tulun cikinta da take jin kunyar a gani.
Kai tsaye taga mohd ya d'aura hannun sa akan cikin nata yace"inna kalli d'an jikanki ki fa yanda ya taso"
Wata irin kunya Ryynt taji kmr ta nutse tayi saurin ture hannun sa zata bar gurin mohd ya janyota zuwa jikin sa yana dariya,a shagwa6e ta fashe masa da kuka ta qwace kanta ta koma jikin inna ta 6oye fuskarta a qirjinta tana ci gaba da kukan da ta soma maida shi da gaske don rugumar da ya mata yasa ta qara shiga wata kunyar.
Ya riqo hannunta yace"zo ni na 6oye ki a nawa qirjin tunda kunya kike ji.
Da sauri Ryynt ta fizge hannun ta yayinda inna ta girgiza kanta d'auke da murmushi tace"Allah ya shirye ka muhammadu snn ta shafo bayan Ryynt tace"qyalesa Ryynh yi shiru daina kuka ae yau ya jawa kansa don baza ki koma gidan sa ba
sae ya zo biko"
Mohd yayi saurin kama kunnen sa yace"Aa inna amin afuwa bazan sake ba na tuba"
Inna tace"kaja kunnen ka ma yafi na zomo tsayi bazan haqura ba sae kazo biko tunda har kasa min ita kuka.
Mohd ya shagwa6e fuska kmr qaramin yaro yace"inna nine fa"
Tace"kaiwa daga ina"
Mohd yace"mai gidan naki kuma inna Baaba hurera kinaji fa"
Baaba hurera dake kallon su ita da su Nasir suna murmushi ta girgiza kanta d'auke da murmushi taje da sauri dmn kawo musu abinci da lemu da ruwan sha kmr yanda inna ta umarce ta.


A nn tsakiyar falon aka shimfid'a qatuwar darduma Baaba hurare ta jera kulolin abinci akai da ruwa da lemu wanda dama musamman dan su aka had'a.


Zasu fara cin abinci knn wayar mohd ta shiga ring koda ya duba mae kula da harkokin gidan sa ne ya kirashi yake snr dashi irin 6arnar da malika ke aikatawa a gidan shi don sae farfasa abubuwa take.
A natse ya kalli Nasir yace"plz bani makullin motar ka"
Ba musu Nasir ya miqa masa makullin yace"lafiya dae ko"
Yace"ba wani abu bane yanzu zan dawo inshaa Allah"
Daga haka ya fita Ryynt ta bisa da ido sae ga inna ta fito daga ciki d'auke da fruits salad mai sanyi da ta ciro a cikin fridge taga bata ga mohd ba tace"Aa ina kuma muhamnadu ya tafi"
Tayi mgnr ne tana mai kallon Ryynt wacce bata iya cewa komai ba sae Nasir ne yace"an kira sa ne ya d'an fita ya dawo"
Inna tace"ayyo"
tare da ajiye fruit salad d'inda ke hannun ta.


Mohd kuwa yana isa gida yayi tsaye a cikin falo hannuwan sa cikin aljihu yana kallon yanda gun dining duk yayi kaca kaca malika duk ta watsar da liyafar da tasa aka shirya mae ta kuma farfasa duk sabbin kayan da yasa aka zuba a falon na gyaran gidan da yasa akayi gabad'aya duk wani abin fashewa bata bar shi ba har TV kuwa.
Yana tsaye sae gata ta fito kitchen riqe da wuqa sabuwa dal zir sae qyalli take.
Tayi kmr ma bata ganshi ba ga mamakin sa sae sauri take ta fita yayi hanzarin fizgota yace"ke ina kuma zaki je da wuqa"
Bata masa magana ba sae qwatar kanta da take qoqarin yi ya qara damqar ta had'e da daka mata tsawa yace"ina zaki tafi nace!
Ta fizge kanta tace"so kake kaji to gurin wnn abar zan tafi don wlh yau bazan barta da rai ba sae na hallaka ta na kuma hallaka abinda ke cikin cikin.....bata qarasa fad'a ba taji saukar wani irin gawurtaccen mari ya kuma ja hannun ta ya tafi da ita sae fizge fizge take har ya kaita d'akin ta ya jefar ya fito ya rufe d'akin ya xare key ya saka a aljihun sa ya fita yana mamakin hauka da baqin kishi irin nata.


Gidan inna ya koma Nasir ya kar6i makullin motor sa ya fita zuwa aiken da inna ta mai wacce tana bashi saqon ta koma daga ciki sbd wayar ta da taji tana ring.
Ya kasance falon ba kowa don mohd yana fita Ryynt taja su saliha suka tafi d'akinta da inna tasa aka share tun jiya da taji zasu dawo.
Ya nufi d'akin kai tsaye ya same su zaune su uku suna cin abinci a mazubi d'aya sae firar bayan rabuwa suke cike da nishad'i.
Ba tare da yace musu komai ba ya riqo hannun Ryynt ya fito da ita zuwa falo suka zauna kan darduma da abincin sa ke ajiye da aka sa d'ayan plate aka rufe ya bud'e abincin yace"muci wnn sae ki bar musu wancan suci gaba da ci"
Tace"meyasa abincin fa yana da yawa baza su iya cinye sa ba na mu uku ne muka d'iba"
Yace"eh ki bar musu kawae"
Ya fad'i hakane tare da d'ebo abinci a spoon zae kai bakinta tace"mk nifa ina jin kunyar inna tazo ta same mu muna cin abinci a tare"
Nan kawae ya tashi yaja hannun ta riqe da abinci suka tafi d'akinta da niyar suci a can ,
gashi ita ko a gaban su saliha d'in bata iya cin abinci a tare dashi,
tace"plz Mk tafi kawae kaci abinka ni sae na ci gaba da ci tare da su saliha kaji.
Man da har ya zauna kan sofa ya kalleta kawae bae ce mata komai ba ya tashi ya fita d'auke da alamar fushi a fuskar sa.
Jiki sanyaye Ryynt ta zauna dmn ci gaba da cin abinci tare da su saliha.
Saliha dake kallonta tace"is better ki tashi kije ki bashi haquri kici abincin dashi dmn ga dukkan alama fushi yayi"
Ryynt da qwallah suka taru a idon ta tace"Saliha kunya nakeji da dae mu kad'ai ne zan iya"
Saliha tace"olryt bari to mu koma falo nida mami sae ku dawo a nn kuci"
Saliha ba haka nake nufi ba ,saliha da ta fhmce ta tace"to ai sae ki zauna mijinki na fushi dake mala'ikun Allah na tsine maki"
Ryynt ta kalli saliha ,mami tace"kije mana Anti meye abin kunya dan kinci abinci da yaya nima fa da muna gidan sa a tare muke cin abinci kin sani"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tana kallon mami snn ta tashi taje falo ta samu mohd ya mayarda abincin ya rufe zae fita don har ma yakai bakin qofa.
Ryynt ta kira sunan sa a hnkli.
Ya tsaya kawae ba tare da ya juyo ba.


Taje ta riqo hannun sa ya juyo yana kallon ta tace"MK ina zuwa kuma baka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login