Showing 165001 words to 168000 words out of 168541 words
Chapter 56 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
jiya da yake jin kamar ya sake tsintar kansa a lokacin.
Ryynt dake kallon sa taje a natse ta hura masa iskan bakinta ya lumshe idanun sa d'auke da murmushi snn ya koma ware su a kanta,
Cikin shagwa6e ta kalle sa tace"ya ina baka abinci kaqi kar6a sae kallona kake"
Mohd bae ce komai ba sae kar6ar spoon d'in yayi ya ajiye ya janyota zuwa jikin sa sae kallon ta yake cike da so snn yace"my Ryynt ina sonki kuma har ko yaushe ina mae gaya miki cewa keta daban ce da sauran mata, hm shin kinji irin farin cikin da kika tsunduma ni a daren jiya kuwa"
Ryynt dake kallon sa tayi murmushi tare da saurin sadda kanta qasa mohd ya d'ago ta yace"uhm my ryynt knn meye na jin kunya kuma bayan duk burin mace ta gari shine taga cewa ako yaushe ta faranta ran mijinta,ni mijinki ne kin faranta min dole na nuna miki farin ciki na a fili dmn fiye da tunanin ki kin faranta min ba kad'an ba da har ma kikaci babbar kyauta a gurina da sae kin fara karatun ki snn ko zan baki amma yanzu gaya min bayan karatun ki meye kuma burin ki na gaba a rayuwa da kike son cikawa?
Cikin sassanyar murya mae d'auke da farin ciki tace"burina na gaba shine ina son idan na kammala karatuna ka bar ni nayi aiki"
Yace"kin samu my Ryynt sae kuma me kike so?
Tayi murmushi tace"kai nake so da kuma gangar jikin ka gabad'aya yayinda zan kasance taka ni kad'ae"
Yace"wnn kin jima da samun sa my ryynt sae kuma me?
Tace"um um bana tunanin yanzu akwai wani abu da nake so da dae baffana zae dawo da ina so"
Mohd dake kallonta yayi murmushi dan itama d'auke da murmushi tayi maganar amma kuma sae yaji tausayinta yace"Allah yaji qan baffa da Rahama"
Tace"Amin"
Snn ta d'auki spoon ta kae bakin sa taci gaba da ciyadda shi shima yana ciyadda ita har suka kammala cin abincin.
Yaja hannunta ya tafi da ita d'akin yaransa yana nuna mata yanda yasa aka tsara d'akin sae yaba d'akin take tayi dan an tsara d'akin sosai kmr ba a cikin Nigeria ba.
Bayan sati biyu da faruwar haka sosai su Ammar ke samun kulawa a gurin en renon su shiyasa sam Ryynt bata wani wahalar d'awainiya dasu sae dai shayarwa.
6angaren Malika kuwa zaune take gurin wani gurin shan iska lemuna a gaban su suna sha suna magana ita da sweetat d'inta wacce ke kallon sa tana fad'in"Aa wlh ba wani laifi da ka min,na hana maka kaina ne sbd wani dalili......wane irin dalili ne haka da kika hana min kanki har na tsawon watanni?
Tace"Aah me kake yiwa sauri ae dalilin ba wani abu bane sae wani babban albishir dana 6oye maka nace sae nayi idda tukun snn ko zan gaya maka dan nasan idan na gaya maka kafin na kammala zaka qosa ka ga na jima ban kammala iddar ba,Albishir d'in kuwa shine aure nake so zamuyi nida kae dmn zamu fi jin dad'in rayuwar mu ko ya kace"
Wani irin murmushi yayi da jin zancen nata banbara kwae yace"kema dae da wasa kike malika in banda abinki ina zancen aure a tsakanin mu"
Tace"kan me zaka ce haka saki uku fa man ya min kuma har na kammala idda me kuma ya rage"
Yace"Hm dan Allah ke yanzu idan nace zan aure ki zaki yarda"
Tace"why not zan yarda mana sbd nasan bakada wani burin da ya wuce mu kasance tare ako yaushe"
Yace"u are wrong ni sam baki fahimce ni ba dmn ni bani da burin da ya wuce na sami yarinya saliha kamila sabuwa fil a leda ba irinki da kika zubar da mutuncinki a titi ba da har kikayi aure baki daina yawon iskancin ki ba snn har kike tunanin wae zan aure ki tir"
Cikin tsananin mamaki tace"Rasheed ni kake gayawa haka bayan kaine mutum na farko daka fara sani na a 'ya mace kaine ka 6are ni a leda"
Cikin d'aga kafad'a yace"And so what ni nace ki bani kanki ko kuma na miki dole ne ko kuma ni kaid'ai naji dad'in bada ke ba"
Tace"kaga Rasheed idan har tunanin kake idan munyi aure zan iya kula wani bayan kae sam ka cire hakan a ranka dmn sanin kanka ne tun lokacinda muka fara sanin juna bana kula kowane d'a namiji bayan kae har nayi aure kuwa"
Yace"hm nifa ba sakaran namiji bane da kike tunanin zan yarda dake keda duk son da kike yiwa man bai hana kin cutar dashi ba kina yawon bin maza a titi"
Ran malika ne yayi mugun 6aci tace"kaga Rasheed mu daina wnn wasar dan ni har raina ya so6a 6aci wlh,gaya min yaushe zaka turo magabatan ka?
Yace"hm totally u have gone mad! na tura magaba ta na wa auren ki tuf! Allah sauwaqe na auri mace irinki wlh never"
Yana gama fad'ar haka ya tashi zae bar gurin ta miqe a fusace ta kama kwalar rigar sa tace"wlh baka isa ba Rasheed dan ubanka sae ka aure ni ko kuma na had'a maka tuggun da bazaka ta6a fita ba wlh"
Tana kaiwa nn yasa qarfin sa ya ture ta tare da kife ta da mari ya nunata da yatsa yace"kin sanni wlh na fiki zama tataccen d'an iska duk wani abu da zakiyi sae dae na juyar dashi zuwa kanki amma idan kina musu ki gwada ki gani shege ka fasa"
Yana gama fad'ar haka ya tafi ya barta dafe da kunce hawaye masu zafi na sauka kan fuskar ta dan tasan tabbas ba abinda zata iya masa da zata ci riba ya riga ya gama da ita.
Billy Giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```
*LAST PAGE*
🔮🔮🔮
*page 94*
Duk da cewa lalura ce kawae tasa taso ta aure shi amma sosai taji ciwon cin mutuncin da ya mata dmn bata ta6a tsammanin zae mata haka ba.
Amma ba komai tunda bashi kad'ai ne d'a namiji a duniya ba da akwai su birjik da kyaun ta kad'ai ya isa ta sami mae aurenta cikin lokaci yayinda zatayi gaggawar yakice wnn auren dmn taga cewa ta koma ga auren man,
fatar ta kawai Allah yasa har mutuwa kar man ya ta6a jin cewa ta ta6a bin wani namiji a waje dmn tasan koda ta cimma burin koma ma auren sa idan yaji wnn labarin zae sake ta ne ba makawa.
Tana gama qisa haka a cikin ranta ta kai hannu zata share hawayen fuskarta sae ta tsaya cak cikin tsananin mamaki tana kallon man da ta gani tsaye a gabanta yana mata mugun kallo kmr wanda zae bugota.
Kasan yin komai tayi dan ta rasa ta inda ya fito gashi yanayin kallon sa kad'ai ya isa ya fahimtar da ita ya gama jin komai tsakanin ta da Rasheed idan kuwa hakane tata ta qare dan duk wani burinta na koma ma auren sa ya gama lallacewa nn kawai ta saki jiki sakwaf ta kai qasa durqushe kan guiwoyinta ta had'e tafukan hannayen ta ta soma kuka tana ba mohd haquri a cewar ya yafe mata sharrin shaid'an ne.
Mohd bae bar ya saurare ta ba ya bar gurin a fusace don ya tabbatar ko minti d'aya ya qara a gurin ba duka ba komai zae iya faruwa.
Cike da nadama malika ta tashi tana dana sani a rayuwar ta taje ta shiga motar ta bata zarce koina ba sae gidan fa'iza.
Bayan ta isa gidan cikin kuka ta shiga yiwa fa'iza bayanin abinda ya faru tsakanin ta da Rasheed da kuma ganin man da tayi ba tare da tasan inda ya fito ba don sosai tayi mamakin ganin sa duk da cewa gurin,gurin shan iska ne da kowa kan iya zuwa.
Fa'iza da ke kallon ta tace"Hm dama ae duk wanda ya sayi rariya yasan zata masa yoyo kuma sanin kanki ne baza ki shuka gero ba ki girbe masara dole duk abinda ka shuka shi zaka girba yanzu ga irin ta nn ya gama amfanuwa dake ya nuna miki halin sa na d'a namiji kuma yanzu shike nan zancen kiyi auren d'ibar wuta bae taso ba tunda man ya riga ya gama jin komai babu wata hanya da zamu iya bi mu shawo kansa
ya maida ki tunda ba sakaran namiji bane shi.
Cikin muryar kuka malika tace"Ae shike
nn fa'iza nasan tawa ta qare min banida wani sauran farin ciki a rayuwa ta,
ayukka na marassa kyau sun sa na rasa abinda nafi qauna a rayuwata.
Ta qarashe mgnr ne cikin kuka.
Nan Fa'iza ta shiga rarrashin ta,
malika bata iya daina kukan ba sae cewa tayi" ya zanyi da rayuwata fa'iza abubuwa goma goma sun tara min zama d'aya,disire tablet d'in da nake sha tuni na daina amma still ko yaushe cikin buqatuwa nake jin kaina musamman da dare dako baccin kirki bana iya yi nabi duk wata hanya da nake tunanin zan daina ji amma abu ya faskara bansan ya zanyi ba fa'iza gashi bana son sake komawa gurguwar hanyar da na fito koda zan mutu kuwa.
Fa'iza ta nisa tace"u see ba yanda banyi dake ba kan ki daina sha amma fir kika qi saurarata gashi ni yanzu bani da wani abun da nasan zan iya miki sae dae kici gaba da neman magani har ki dace.
Shiru malika tayi bata sake cewa komai ba sae hawaye masu zafi dake gangarowa kan fuskarta tana ji ina ma bata zo duniya ba da wnn halin qunci da ta saka kanta a ciki.
Da dare guraren qarfe goma mohd ne cikin d'akin sa tsaye cikin shirin sa na bacci yana yiwa yaransa addu'a dake kwance cikin bed d'in su suna bacci,
Bayan ya ida masu addu'ar ne sae ga Ryynt ta shigo d'akin cikin shirinta na bacci itama, ta sami mohd still yana tsaye kan yaran sa sae kallon su yake yana shafa kansu a hnkli.
Ta qarasa gurin shi tare da rungumo sa ta baya mohd ya juyo yana kallonta kmr wani marar lafiya,
Ryynt dake kallon fuskar sa da kulawa tace"mk wae lafiya tun lokacinda muka fita a hanyar mu ta dawowa na ganka cikin wani yanayi,bamu ko dawo gida ba kaje damu asibiti sae gwaje gwaje kake mana dana tambaye ka lafiya kace min ba komai bayan da gani akwai abinda ke faruwa ka 6oye min ne kawae don gashi har yanzu akwai sauran damuwa a fuskar ka,plz dan Allah ka gaya min yaran mu ne ba lafiya ko kuma wani ne a cikin mu"
Mohd da tun lokacinda ta fara magana yake kallonta yaja hannun ta yaje da ita kan bed suka zauna a natse yace"my Ryynt kinsan fitar da mukayi a d'azun a gurin shan iska inda har mun gama abinda muke zamu tafi sae banga makullin motor ba na koma nema,na sami makullin zan bar gurin knn sae muryar malika naji suna magana ita da wani,ba wanda ya ganni a cikin su haka kuma banyi niyyar tsayi ba amma mgnr da naji sunayi ce tasa dole na tsaya ina sauraren su sbd na razana da jin mummunan abinda malika ke aikatawa a lokacinda muna tare har kafin ma mun kasance tare.
Nan mohd ya gayawa Ryynt kaf komai abinda yaji tsakanin malika da rasheed wanda shine dalilin da yasa kae tsaye ya tafi dasu asibiti dmn duba lafiyar su idan basa d'auke da wata cuta.
Ryynt dake kallon sa take idanunta suka ciko tap da qwallah a rud'e muryar ta na rawar kuka tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah yasa bata laqa mana wata cutar ba"
A hankali Mohd ya janyota zuwa jikin sa ya rungume ta yana fad'in "Haqiqa Allah ya kare mu my ryynt dmn sakamakon gwajin da na mana ya nuna bama d'auke da kowace irin cuta don haka is ok kar kiyi kuka kinji.
A natse ta sauke ajiyar zuciya ta gyad'a masa kae tare da qara lafewa a qirjinsa tace"Allah ya shirye ta ya qara tsare mu"
Mohd yace"Amin"
Daga haka sukayi shiru basu sake cewa komai ba sae shafa bayan ta da yake,
sae can ya kira sunanta a hankali yaji bata amsa ba koda ya duba har tayi bacci nn ya kashe musu wutar d'akin ya musu addu'a snn ya kwanta rungume da ita a jikin sa.
Bayan kwana d'aya da faruwar haka guraren qarfe tara na dare man ne zaune a falo kan doguwar kujera yayinda Ryynt ke kwance kan qafafuwan sa tayi fillow dasu sae wasa yake da gashin kanta suna firar su cike da nishad'i.
A cikin firar su ne man ke tambayar Ryynt me take son ta karanta tace mishi medicine idan na kammala sae mu riqa zuwa aiki tare da kae amma dai tukun gaya min nawa kake biya ma'aikatan ka?
Yace"um to tunda kece zan riqa baki 5k a wata"
Ta kalle sa a shagwa6e d'auke da dariya a fuskar ta tace"wlh da banyi ba"
Cikin dariya yace"nine fa my Ryynt tace"to ae nima nice"
Yaja hancinta yace"kin ganki son kud'in ki yayi wa"
Tace"ba wani nn ae da gaskiyata"
Few months later
Tuni Ryynt ta rubutu jarrabawa har ta fara karatun ta yayinda mohd ya cika mata alqawarin bata babbar kyautar da yace sae ta fara karatu zae bata wato mota ya saya mata Accord V6 sabuwa fil wanda tuni ya koya mata don itama ke kai kanta school.
Yaransu kuwa tuni sun qara wayo abin su don har sun fara rarrafe suna koyon tsayi and still suna nn 6ul 6ul sae qara shawa suke gasu da yawan dariya kuma sam basa da qiyuwa duk wanda ya miqa musu hannu zuwa suke d'auke da dariya a fuskar su koda kuwa basu san wanda zae d'auke su ba.
Idan Ryynt zata tafi school a hannun en renon su take barin su amma mostly gidan inna Mohd ke kaisu sae idan ta dawo snn ake d'auko su ,kuma duk mohd zae je family house dasu yake zuwa.
6angaren malika kuwa damuwa da dana sani yasa ta rame sosai gabad'aya ta fita kamannin ta duk kyaun da take kuri dashi ya tafi shiyasa har yanzu ba wani wanda ya fito da sunan zae aure ta gashi kullum sae fama da buqatuwa take dmn tayi neman magani har ta gaji amma abu ya faskara shiyasa kullum sae qara yin nadama take don wani lokacin ma zama take tayi ta kuka.
Bayan lokaci ya qara tafiya ne ta samu wani abokin mahaifinta ya aureta,abubuwa suka fara sauqaqa mata ta fara murjewa tana maida jikinta sbd ba kad'an ba akwai daula a gidan da kwanciyar hankali sbd ita kad'ai ce a gidan ba gida d'aya suke da uwargidan sa ba,
sae dai basu fi shekara d'aya cikin ta biyu ba ya saketa sbd ba don komai ya aureta ba sae don samun haifuwa ita kuwa da zarar ta sami ciki yana kae wata uku sae ya zube baya tsayi kuma duk cikin zae zube wahala take sha sosai kmr bazata rayu ba shiyasa likitawa suka cire mata mahaifar gabad'aya sbd a binciken da sukayi sun gano wani abortion pills tasha mai qarfi da ya 6ata mata mahaifa da sam ciki ba zae ta6a iya rayuwa a cikin mahaifar ta ba sae dae ma yayi yunqurin tafiya da rayuwar ta.
Tun daga lokacin nadama da quncin rayuwa suka sake dawowa malika ta soma ganin fa'iza ta cuceta dan bata ta6a shan abortion pills ba sae a dalilin shawarar da ta bata na sharrin da ta qullawa Ryynt,gashi yanxu tana gani tuni fa'iza ta haifi d'anta har ma tana d'auke da wani cikin amma ita gashi kwata kwata ma ta rasa mahaifar.
Da haka wasu shekarun suka sake tafiya inda da dama abubuwa sun faru dmn Ryynt har ta kammala karatun ta ta fara aiki asibitin man da kullum tare suke zuwa kuma tare suke dawowa.
Yaran su kuwa tuni sun fara zuwa school.
Haka ma Saliha,da Sarah har ma da Ameera tuni sunyi aure har ma kowannen ya haifu.
Ranar wata assabar da dare man ne da Ryynt tsaye a gaban mirror yana rungume da ita sae kallon fuskokin su yake kan irin hasken da yaga Ryynt tayi da kad'an ya rage ta kaishi.
Nan ya kai hannun sa kan cikinta yana shafawa,bakin sa saitin kunen ta yace"gaya min meye sirrin wnn haske haka kodai akwai babyna a tare dake shine baki gaya min ba kike 6oye min"
Ryynt ta bud'e ido tace"Rufan asiri dan Allah ae su Ammar sun ishe mu"
Yace"uhm kema dae da wasa kike ae haifuwa yanzun kika soma ba dai da kika kammala karatun ki ba"
Maqale kafad'a tayi tace"um um ba yanzu ba sae na qara hutawa tukun"
Yace"kae my Ryynt duk shekarun da kika kwashe kina hutawa"
Tace"wane hutun ina karatu dae samun baby kuma sae na saba da aiki tukun"
Mohd dake kallonta yace"hm my Ryynt knn babyna kam kin riga da kin samu don wnn hasken kema kinsan na babyna ne"
Tace"ba wani nn dama inada haske na dan wlh ba za'a kirani baqa ba"
Nan ya d'aura hannun sa kan qirjinta yace"to naji shi wnn qirjin da ya qara cikowa fa ko kuma shima ba daga babyna bane"
Da wasa ta harare sa tare da ture hannun sa tace"ni babynka bai qara min komai ba don kasan ko bayan na yaye su Ammar aka kalli qirjina ba za'a ta6a cewa na shayar ba suna nn daram tsaye abinsu a cike ko wata budurwa albarka ehe"
Ta qarashe mgnr ne d'auke da dariya zata bar gurin sbd mohd da ya kama towel d'inta