Showing 147001 words to 150000 words out of 168541 words
Chapter 50 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
qarasa min ba inda zamu je wlh"
Malika tace"hm lallai yarinyar nn dani kike zancen zaki gane kuren ki ne idan man ya dawo wlh"
Daga haka ta wuce fuuuu!Ryynt ta bita da kallo le6ace da baki tace"in yazo ki gaya masa har ma abinda ba'ayi ba inga ko kashe ni zae yi ki huta da gani na"
Alwiyya tace"um um anti dan Allah tashi muje ko d'akin da nake zama ne sae mu qarasa a can"
Hm ba inda zanje alawiyya nn nake ra'ayin zama kuma a nn za'a qarasa kitson.
Alawiyya bata sake cewa komai ba suka ci gaba da yin kitson su basu jima ba suka kammala dan dama sunyi jima da farawa.
Da suka gama Ryynt ta kwashi kayan kitso ta koma d'aki alawiyya kuwa ta tsaya zata share falon.
Da shigar Ryynt d'aki wayar ta da ke hannunta ta shiga ring Sarah ce mae kiran ta d'aga wayar cikin murna tace"da gaske to shikenn gani nn zowa na shigo dake.
Nan ta jawo qaton hijab d'inta mae kai mata har qasa tasa ta fita jim kad'an sae gashi sun shigo ita da qawar ta sarah da duk ta cika da mamaki dan kan aje koina ta gama yarda Ryynt matar aure ce sbd cikin da ta gani bayyane a jikinta sae duk ta kasa cewa komai sae bin Ryynt take da kallo tana binta kmr raqumi da akala har suka je d'aki.
Bayan ta zauna ryynt taje ta bud'e frigde ta kawo mata lemu da ruwa snn ta kira kuku a landline a cewar ya kawo abinci.
Bayan kuku ya kawo abincin ne Ryynt ta kalli sarah tare da murgud'a mata baki tace"kallon fa"
Sarah ta nisa tare da fad'in "hm lallai Ryynt kin nuna min ba kowa nake a gurin ki ba gwara ma na tashi na bar gidan nn tun wuri kafin na qara had'uwa da wani takaicin kuma"
Daga haka Sarah ta tashi zata fita Ryynt ta sha gabanta tace"dan Allah Sarah ki tsaya ki saurareni wlh yanda kike tunani ba haka bane yi haquri muje ki zauna kinji dan Allah"
Ba yanda Sarah ta iya ta koma ta zauna Ryynt ta mata bayanin komai koma nace ta bata labarin ta komai bata rage mata ba.
Sosai Sarah ta tausaya mata matuqa tace"Allah sarki Ryynt labarin ki abin tausayi"
Ryynt tace"ae Alhmdlh yanzu komai ya wuce"
Sarah tace"shi Aamil daga rnr da ya tafi har yau bae dawo ba?
Ryynt tace"bae dawo ba ni matar sa ma tausayi take ban dan rnr da mukaje family house a 6angaren su na ganta gabad'aya ta canza ta rame sosai sbd damuwa da kuma sabon cikin da ya tafi ya barta dashi.
"Toh Allah ya kyauta"
Cewar Sarah, Ryynt tace"amin"snn ta bud'e lemu ta tsiyaya mata a cup ta bata.
Bayan har taci abinci Ryynt tace"bari na kira maki mk yazo ku gaisa"
Tace"to"
Ryynt kuma ta jawo wayar ta ta kira mohd ring d'aya biyu ya d'aga ,bayan ta gaida shi take gaya masa Sarah tazo.
Yace"to kinsan bana gida fa amma idan na tsaigaita aikin da nake a asibiti zan shigo mu gaisa"
Tace"to shike nn sae ka shigo"
ta kashe wayar tana mai kallon Sarah tace"yana asibiti amma yace"idan ya kammala aikinda yake zae shigo ku gaisa d'in"
Tace"ok"
Snn ta d'aura da cewa"ni kuwa Ryynt idan zaki yi waec n neco a school d'in mu zakiyi ko kuma zauna miki za'ayi?
Aa ni nafi son na rubuta da kaina don koshi haka yace kawae fatana Allah yasa a lokacin na haifu.
Sarah tace"kai ae har ma abinda kika haifa ya soma wayo dan kinsan akwai sauran lokaci kawae fatana Allah yasa ki haifa mana baby boy"
Ryynt ta kalle ta d'auke da d'an guntun murnushi ,
Sarah tace"ko kinfi son ki haifo mana baby girl?
Tace"um um Allah dae ya bani mae albarka "
Sarah tace"wlh kinyi magana amma dae cire qaton hijabi d'in nn haka kisha iska kin wani qunshe mana baby wae ke ba kya so a gani"
Ryynt tace"uhm Sarah knn ae ko baki ce ba da niyyar cirewa nake sbd kitso aka min da zafin shi ko iska bae sha ba sae ga kiranki kinxo.
Sarah tace"muga kitson"
Nan Ryynt ta cire hijab d'in ta ta nuna mata
Sarah tace"wayyo Allah wa ya miki wnn shuku mae kyau haka wlh tayi kyau ba kad'an ba don ina mugun son side weaving hln saloon kika je?
Ryynt tace"um um wlh wata yarinya ce tamin alawiyya"
Sarah tace"er maqotan ku ce?
Aa yarinyar da aka samar min ce.
Sarah tace"kai amma dae gaskiya ta iya kitso wlh da nice na iya kitson nn haka saloon kawai zan bud'e"
Ryynt tayi er dariya tace"kai sarah Allah ya shirye ki shi zanen lallen da kika iya ae banga kin maida shi sana'a ba"
Sarah tace"hm wlh da ace Abba da umma sun barni da tuni na maida shi sana'a don ina sha'awar sana'ar hannu fiye da yanda ba kya tsammani dmn har kuka sae da nayi da aka hana min en gidan mu kawae nake yiwa idan sun buqata"
Ryynt tace"Allah Sarah sae naji kin qara birge ni sosai sbd rashin girman kanki ina sha'awar naga mutum haka wlh"
Murmushi kawae sarah tayi don ta fhmci inda Ryynt ta dosa wato na ganin ita er mae kud'i ce amma kuma sam bata kai kanta a wata ba tace"hm Ryynt knn"
Ryynt tace"me nayi ae gaskiya na fad'a"
Ae bance kinyi qarya ba na gaida ke ne kawai.
Ryynt tace"to na amsa kyauta,amma kuma ina neman wata alfarma"
Ta me knn?
So nake ki zana min lalle d'an simple mae kyau sbd yau nike da oga.
Ta qarashe mgnr ne tare da saurin rufe fuskarta da tafukan hannyen ta.
Sarah tace"hm yau kuma ni kike kunya nida rnr kikace da kiji kunya ta gwara kinyi kunyar desk d'inda muke zaune"
Ryynt tace"nidae zaki min ko kuwa sae kin tsaya dawo da abinda ya wuce"
Tace"tashi d'auko kayan lalle idan kina da"
Kai tsaye Ryynt ta tashi ta d'auko kayan lalle suka fara.
6:00pm
Ryynt ce ta fito raka Sarah da zata koma gida dan tuni ta gama mata lallen har ma ta wanke.
A bakin gate suka tsaya Ryynt tace"kiyi hqr Sarah inaga mk aiki ya masa yawa shiyasa bae samu yazo kun gaisa ba"
Tace"Allah ba komai amma mami fa ba kince min gurinki take ba?
Eh bata nn ne taje yini a gidan yaya nasir.
Tace"olryt ni na tafi nagode sosai sae munyi waya"
Ryynt tace"nima nagode Sarah ki gaida su umma"
Tace"zasu ji"
Nan ta wuce Ryynt ta koma daga ciki"
Bayan isha'i zaune suke gabad'ayan su zasu fara cin abinci Ryynt na tsaye cikin kwalliyar ta mae kyau kmr wata amarya ta jawo kula zata zubawa mohd abinci tana bud'e kular tayi tsaye turus tana kallon abincin, mohd yace"lafiya"
Ya fad'i hakane yayinda ya kai idon sa a kan abincin,rae 6ace yace"what! me zan gani suma a cikin abinci garin ya haka,nn ya soma qwalawa kuku kira cikin d'aga murya.
Malika tace"ba laifin kuku a ciki laifin ta ne ta sani don zaune tayi a nn falon ana mata kitso da na mata magana tace ba inda zasu je har ma ta nemi ta zageni"
Mohd ya kalli Ryynt yace"wae hakane?
Ryynt bata ce komai ba sae zaro gashin tayi tana kallo don bae koyi kalar sumar ta ba gashin kanti ne tsintsa wanda tasan ba makawa malika ce tayi aikin.
Tace"ae wnn ba.......no Ryynt bana son jin wani surutu gaya min eh ko a'a.
Maurya can ciki tace"eh amma....kinga bana so kar a sake,
Tace"shike nn kayi haquri inshaa Allah baza a sake ba.
Bae ce komai ba sae tashi yayi ya bar gurin itama taja hannun mami zasu bar gurin malika tasha gabanta tana mata shu'umin murmushi wacce ba haka taso abin ya kasance ba sosai taso mohd yayiwa Ryynt fad'a amma ko hkn ya mata dad'i kafin tace komai Ryynt ta ra6a ta gefen ta ta wuce sbd tasan ko minti d'aya ta qara a gurin baza ayi ta da kyau ba gashi bata son ta fara biye mata.
Guraren qarfe goma mohd ya shigo d'akin Ryynt dmn yayi kiranta a waya har ya gaji taqi d'agawa.
Tana kwance abinta kan bed sanye da kayan bacci riga da wando da ya tsaya mata iya guiwa yayinda mami ke kwance gefen ta sae sharar baccinta take.
Yace gab da ita ya zauna yana kallo ta juya masa baya bae ce komai ba sae kallon kitson ta da yake had'e da zanen lallen da aka mata mae kyau
Yakai hannu yana shafa kitson snn yace"tashi muje d'akina kinji"
tace"ka tafi kawae ni a nn zanyi bacci na"
yace"haba Ryynt don kinyi laifi an miki magana kuma sae ki d'auki fushi da mutum bayan kinsan abinda kikayi ba dae dae bane"
Cikin muryar kuka tace"to ai kaine kaqi ka saurare ni sae fad'a da da kake ta min"
Kafin yace komai sae da ya tada ta zaune had'e da rungume ta a jikin sa yana mae shafa bayanta a hnkli snn yace"Ryynt ba fad'a bane magana ce"
Tace"fad'a ne mana tunda har ma baka bari na qarasa zanje na"
Yace"to yi haquri raina ne ya 6aci sbd na tsani ganin gashi a cikin abinci amma yi haquri kinji"
Idon ta tap da qwallah ta d'ago tana kallon sa tace"to meyasa baka zo kun gaisa da Sarah ba har ta tafi kuma har kiranka na sake yi amma kaqi d'aga waya"
Wlh Ryynt har zan zo aka kirani za'ayi family meeting amma kiyi haquri da kaina zan d'auke ki muje har gidan su ki kai mata ziyara kinji"
Ta gyad'a masa kai tare da komawa kan qirjinsa ta kwanta.
Sorry plz munyi biki ne kwana biyu shiyasa kuka jini shiru.
Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
*page 85*
Ya riqo hannunta yana duba zanen lallen da aka mata yace"wa ya miki lalle da kitso ?
Tace"alawiyya ta min kitso Sarah kuma ta zana min lalle"
Yace"dama mutanen qauye sun iya kitso haka"
Tace"hm MK knn me ka maida mutanen qauye ne wae"
Yace"um um fa kar ki canza min manufa ganin nayi kitson yayi kyau sosai"
Tace"hkne kam nima nayi mamaki sae dai kuma kitso sana'ar ta ne shiyasa ta qware sosai don ba kalar kitson da bata iyaba ba a yanda ta gaya min sbd ban ma san ta iya kitso ba jin tayi ina magana kan ina son zanje kitso tace ae in zo ta min ta iya shine nayi zaune ta tsantsara min abuna don haka duk wanda ya kalli kitson sae ya biya kud'in kallo har ma da na lalle"
Yace"har da wanda akayi domin shi?
Eh mana ae shi ma yafi cancanta ya biya kud'in.
Yayi murmushi yace"naji zan biya kud'in har ma da kud'in wanda za'a sake min dan dae yau kam wnn zae sha ruwa"
Murmushi tayi mae d'auke da jin kunya tace"to ae kitso ne ba zae lallace zama d'aya ba"
Yace"a cikin kwana biyun nn kin san iya shan ruwan da zae yi ne to"
Kallon sa tayi tace"Ae kana da tausayi na sani baza ka wahalladda ni ba"
Kinji an wayo ,wae dae tukun me kika bawa Sarah da tazo?
En tsarabarta na bata kayan bacci, turare da kuma makeup kit.
Yace"banji dad'i ba naso ace nazo mun gaisa"
Nima banji dad'i ba amma da ka min bayani na fahimta kuma ae kace zamu je koh?
Yace"eh zamuje my Ryynt amma se next weekend sbd kinga an koma school"
Tace"wlh kuwa duk sae naji ina son komawa amma babyn ka ya hana min"
Ta qà rashe mgnr ne had'e da turo baki.
Mohd ya kalle ta tare da shafo cikinta yace"afwan ae da kin haifu zakiyi boko har ki gode Allah"
Tace"to Allah yasa muna da rae da lafiya"
Yace"amin"
Wanda ya fad'i hakane tare da yaye rigarta yana kallon cikin ta da ke ta faman motsi yakai hannun sa sae shafa cikin yake yana murmushi tace"yunwa nakeji Mk muje d'akin ka in da akwai abinda xanci"
Ya d'ago ya kalle ta yace"tun d'azun kiranda nake ta miki knn kixo ki sami abinda kika ci ,
ki kaiwa su mami nasu amma kika qi d'aga wayar wae ke fushi gashi kinsa sunyi bacci da yunwa "
Tace"ae basuyi bacci ba sae da suka sha tea"
Yace"to muje ke ki sami abinda kikaci"
Tace"hln mene zaka ban naci?
Sae da ya d'auki mami snn Yace" kaza ce da hollandia yogurt ,amma ke da fresh milk zaki had'a dan ban cika son kina shan zaqi ba"
Tace"um um gaskiya ban so"
Yace"to naji muje"
Nan malika dake la6e tayi saurin barin gurin su kuma suka fito suka kai mami d'akin alawiyya snn suka tafi d'akin mohd.
Washe gari malika ce tsaye a balcony tana kallon Ryynt da man da suka fito harabar gidan kowanen su cikin shiri sunyi kyau sosai sae zuba qamshi suke tana rataye da briefcase d'in shi,shi kuma yana rungume da ita a jikin sa suna tafiya har suka isa gun motar sa ya kar6i briefcase d'in tare da d'aura mata kiss kan goshi snn yaje a hankali kan cikinta ya d'aura mata ya shiga mota yana mata bye bye haka itama, bata daina masa bye bye ba har sae da motar sa ta fita gate d'in gidan snn ta juya ta koma daga ciki.
Malika ta koma ta zauna cike da baqin ciki dan ita ko ta rako man bae wuce ya kar6i briefcase dinsa ya shige mota ya tafiyar sa, ba wani zancen ya mata kiss bare shi bye bye.
Da dare Ryynt ce zaune a falo tana sanye da riga da wando rigar milk ce handless iya cinya da aka d'an tsage gefe gefen ta yayinda wandon jikinta ya kasance maroon da ya kama jikinta dae dae,tana d'auke da er simple makeup a fuskarta amma sae tayi kyau sosai gashi ba d'ankwali a kanta sae qaton ribbon maroon da ta d'aure shukur ta dashi yayinda jelar shukur keta reto a bayanta tana riqe da waya sae chat take abinta can ta gaji da chat d'in ta ajiye wayar ta kunna TV tana kallo wacce kallon kawae take amma hankalinta na gun man da tun fitar sa da safe har yanxu bae dawo ba haka dae taci gaba da yin kallon ba wae don tana jin dad'i ba tana cikin hakane sae ga malika ta fito wacce kai tsaye ta d'auki remote ta canza tasha tayi zaune tare da d'aura qafa kan qafa tana kallo Ryynt ta kalle ta zata yi magana knn ta jiyo sallamar mohd ya shigo cike da murna ta tashi cikin sauri mae kmr gudu taje tayi hugging d'insa tare da fad'in"oyoyo my Mk i really missed u"
Sae da ya d'aura mata kiss kan goshi snn yace"me too my Ryynt i really missed u aiki nake amma sae faman tunanin ki nake keda babyna"
Ya qarashe maganar ne yayinda ya shafi cikinta snn ya zauna kan one seater Ryynt kuma ta durqusa kan guiwoyinta tana cire masa takalmi da socks, yayinda hannun sa ke kan jelar shukur ta yana wasa dashi tana gama cire masa takalimi da socks ya janyo ta ya zaunar kan cinyoyin sa sae shafa cikinta yake yace"ya lafiyar babyna kinji motsin sa a yau"
Ryynt dake cire masa buttons d'in rigar sa ta gyad'a masa kai yace"to me kika masa da ya motsa?
Me kake so na masa nikam?
D'auke da murmushi a fuskar sa yaja hancin ta a hnkli yace"ki shafa min shi mana a hnkli kamar yanda kika ga inayi idan ya motsa miki.
Tace"uhm to naji"snn ta shafo cikin sa tace"cikin ka ya lafe sosai muje kaci abinci ko wanka zaka fara yi tukun?
Eh wanka zanyi amma sae na fara bawa matata goron kwaliyya tukun,kafin Ryynt tace komai sae jin lips d'insa tayi a goshin ta ya d'aura mata kiss snn yaje kan kumatun ta ta kowane gefe ya mata ya kuma je a hankali zae kai bakin sa a nata
Malika dake kallon su ta buga uban tsaki had'e da tashi ta bar gurin Ryynt da sam ta manta da zamanta a falon ta kalle ta kawae ta maida dubanta gun man da bae ma san da zaman malikar ba gabad'aya sae tsakinta da yaji ya kalle ta kawae ya maida duban sa gun Ryynt yakai bakinsa a nata ya d'aura mata kiss ta sakar masa murmushi had'e da riqo hannun sa tace"muje kayi wankan koh"
Nan ya tashi rungume da ita a jikin sa suka tafi d'akin shi da taimakonta ya cire kayan jikin sa suka nufi bathroom ta taya shi wanka suka fito.
Bayan ya shirya yaci abinci suna zaune kan bed sae shan fruit suke abinsu suna kallo mohd yace" wae mami tayi bacci ne?
Ryynt tace"inafa suna can sae wasa suke ita da alawiyya an gamu da an dace dan alawiyya akwai son wasa kmr wata er shekara biyar"
Mohd yace"ko ke da kika girme mata ae naga biyewa mami kike kuna ta yin wasar"
Ta kalle sa d'auke da murmushi tace"ae wnn daa ne ka sani"
Yace"ba wani nn ko yanzu kika sami dama nasan zakiyi babyna ne kawae bae