Showing 66001 words to 69000 words out of 168541 words
Chapter 23 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
bata iya cirewa ba ta kwanta sae bacci.
Mami kuwa ta cire uniform taje ta watsa ruwa ta saka er doguwar rgrta ta kanti da iyakarta guiwa taje d'akin yayanta ya bata abinci taci byn ta gama ya sama ta kallo nn malika taxo ta same su tace"my man wnn abar fa banga ta fito ba bare zancen d'aura min girki kuma kaga dae ba yanzun ne dawowar su ba zamanta ne kawae tayi "Yace"jeki zanje na taso ta "
Nifa i cnt wait any more don yunwa nakeji sosai kuma kar ma mai lesson d'insu yazo ta wani ce zata zauna ma lesson ,hannun ta yaja suka fito yana mai fad'in "ai mae lesson d'in nasu bazai sami zuwa ba yau yayi tafiya"
Ta6e baki tayi tace"hm lesson d'in ma nsn ba komai take ganewa ba don da gani kwañyar kifi ce da ita....wyr tace tayi qara tana ganin qawar ta faiza ce mae kiran ta nufi d'akinta shi kuma man ya wuce zuwa d'akin Rynt.
Tsaki yayi ganin ko uniform bata cire ba amma tayi kwance tana bacci yace"lallai yrynr nn kinji dad'inki"
Nn yaje yana tashinta da doka mata jiki ta tashi cikin mugun 6acin rae tana kallon shi tace"wae meye!?
Yace"tambayata ma kike oya tashi kije ki d'aurawa malika girki"
Tace"cab ni wlh bazan iya ba don bana jin dad'i"
Yace"bana son raini maza tashi kije ki d'aura mata girki ko kuma wlh nayi maganin ki"
Cikin marairaicewa tace"wlh bana jin dad'i ko tsayuwa ma fa da qyar nake yi"
Yace"Bari kiji ko a kwance ne sae kin d'aura mata girkin stupid girl!
Cikin muryar kuka tace"wae kai meyasa baka da tausayi ne,na gaya maka bazan iya ba bana jin dad'i wlh.
Zowa yayi gab da ita yakai hannu ya d'ago fuskarta da kyau yana kallon ta yace"shin kin manta abinda na gaya miki ne na dole kibi abinda nace idan ba haka ba karatunki"
Da mugun tsana take kallon shi tace a ranta
_"mugu kayi abinka lokacinka ne nawa na nn zowa da zan rabaka da farin cikin ka gabad'aya don wlh bazan barka ba"_
Daga hk tafita ta bar shi tana saukowa downstairs ta had'u da malika wacce ta sha gabanta tana gaya mata maganganun banza.
Tsaki kawai Rynt tayi ta ra6a ta gefenta ta wuce.
Cike da azama malika tayi niyyar fizgo Rynt sae kawae ta hango man tafe nn tayi saurin sakin glass cup d'inda ke hannunta ya fad'i qasa ya tarwatse ta duqa kmr zata tsince glasses d'in dae dae man ya iso ya tada ta tsaye yana fad'in"ya akayi cup d'in ya fashe kuma har kk qoqarin saka hannun ki,da mamaki
tace"hm wnn abar ce fa hk kawae ta biyo tamin muguwar bangaza ta wuce har ma tana fad'in wae zan gani"
Yace"what!
Tace"hm wlh"
A fusace ya kama hanya zai tafi kitchen tayi saurin shan gabanshi tace"no my man kayi hqr ka barta kawae ni yanxu bana son wani tashin hnkli"
Yace"da zanso naji me take nufi da zaki gani"
common my man wnn abar me ta isa tamin ne shirme ne kawae take fad'i kaima ka sani,yi hqr kaji barta.
Tsaki yayi yace "ya zama dole nayi maganin yrnyr nn sbd rainin nata ya fara isata"
Tace"da Allah shareta ta zo muje"
Nan taja shi suka je suka zauna kan two seater malika ta kira cleaners aka kwashe glasses d'in,snn ta kalli man tare da jawo hannunsa ta d'aura kan cikinta tace"my man wae nikam yaushe babyn mu zai fara motsi duk na qagu wlh"
Wani murmushi yayi mae nuna jin dad'i har ransa yace"3 to 4 month ne yake farawa"
Ta kalle shi zata ce wani abu knn wyrta tayi qara tana ganin qawar ta faiza ce tace da mohd "ina zuwa umma ce mae kiran"
Bata jira me zai ce ba ta tafi.
Tana shiga d'aki ta d'aga wyr .
faiza"tace ya ake ciki ne kinsha maganin?
Tace "Aa ynz nake shirin sha dae sbd so nake dai dai wnn abar ta gama min abinci maganin ya fara min aiki sbd zan fi son ina saka loma d'aya ta biyu sae kawae na fasa ihu kan aje asibiti na tabbatar cikin ya gama lallacewa,amma kuma wlh ina tsoron azabar da zanji kafin cikin ya zube
Faiza"ta kwashe da dariya tace"kin fiye tsoro azabar da kwata kwata ta minti nawa ce yayinda ita waccan matsiciyar kin rabata da mijinki har abada"
Tace"wlh kam yau dolenta ta rabu dashi,bari kedai nayi sauri nasha maganin kar taje ta gama abincin bansha ba,tace"ok bye sae mun had'u asibiti knn.
Nan suka katse wyr malika ta ciro tablet a jakarta tasha snn ta fito ta sami man zaune inda ta barshi sae waya yake.
Taje ta zauna kusa dashi tare da jinginwa a jikinsa wanda bae wani jima sosai ba ya gama wayar.
Rynt kuwa da qyar taga ta kammala dafa indomie sbd wani irin bacci da takeji.
Tana gamawa ta zuba indomie a plate ta fito wacce tun lokacinda ta fito kitchen man ke mata mugun kallo har ta qaraso gurin su,shi ya kar6i plate d'in indomie da taikaci yayinda Rynt bata damu da ganin yanda ya kar6i plate d'in ba tayi ficewarta ita dae ta samu ta ganta kan bed.
Rynt na wucewa malika takai hannu zata kar6i plate d'in don har ta fara jin maganin ya fara mata aiki.
Man yace"da zafi malika bari ta d'an sha iska tukun"
Tace"my man yunwa fa nakeji sosai"
Yace"Baza kici da zafi haka ba kam"
nn gabanta ya shiga fad'uwa don in har yace sae abincin ya rage zafi asirinta zai iya tonuwa don gadan gadan ta fara jin maganin na mata aiki.
Nan ta shagwa6e mae tace"pls my man kawae barni naci don zan ma fi jin dad'inta"
Ba musu kuwa ya bata plate d'in ta kar6a ta fara ci tayi loma d'aya biyu a ta ukun ta ajiye plate ta fara riqe ciki man yayi saurin kallonta ya kuma kalli plate d'in indomie yace"lafiya?
Tace"nima dae haka kawae ina fara cin indomie na fara jin cikina yana 6ird'a min"
Yace"what!me tasa miki a indomien ne to?
Bata iya bashi amsa ba sae zamewa tayi daga kan seater tana yarfi da hannu yayinda ta matse cikinta sosai da d'ayan hannunta.
A take man ya rud'e ya jawota jikinsa ita kuwa sae ihu ta fara tana fad'in"wayyo my man cikina zan mutu na shiga uku ka taimaka min da magani nasha"
Da sauri man ya tashi yaje d'akinshi yana shiga ya sami mami kwance kan sofa tayi bacci tana qoqarin fad'owa da saurin sa ya d'auketa ya maida kan bed snn ya d'auko magani da ruwa ya fito yana isowa ya saki magani har cup d'in ruwa sbd ganin yanda malika ta fara bleeding ba wata wata ya d'auke ta ya fita da ita yana qwalawa driver kira,driver yazo suka shiga mota aguje sae asibiti.
Duk wani qoqari na ganin jinin ya daina zuba man yayi amma bai yi nasarar ceto cikin ba ya riga da ya zube,baqin ciki bai bar ya qarasa kula da malika ba sae wata docta yasa ,ya baro asibitin yayo gida a fusace wanda bai zarce koina ba sae d'akin Rynt riqe da belt a hannun shi.
Rynt dake bacci sae saukar duka ta fara ji ta koina.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 2/7/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
*page* *```46```*
Cikin firgici ta tashi tana ihu tana neman guduwa man kuwa sae binta yake yana ci gaba da kai mata duka ta koina baji ba gani.
Can ta samu ta fito d'akin aguje shima ya biyo ta yana duka harsuka sauko downstairs nn sukayi kici6is da umman saliha ta shigo ita da nasir,cikin kuka Rynt ta fizge daga hannun man zata je gun umman saliha kafin ta qarasa jiri ya d'ebe
ta tafi suu zata fad'i umman saliha tayi hanzarin tarbota ta fad'a jikinta,yayinda nasir ke kallon man da mugun mamaki.
Man kuwa qala bae ce dasu ba sae ma murtuqe fuskar sa da yayi ya fita yaja motar sa ya bar gidan.
Umman saliha da ita ma duk mamaki ya cikata ta kalli nasir da yabi man da kallo tace"kama min ita mukai kan seater"
Nan nasir ya kamata suka kaita kan 3 seater snn ya d'auko ruwa a fridge ya yayyafa mata,bata iya bud'e idonta ba sae ajiyar zuciya kawai ta ftr.
Umman saliha ta kira sunanta kusan sau biyu amma Rynt bata amsa ba, nn umma ta kalli Nasir tace"ai da mun kaita d'akinta sae a kira Dr"
Nasir yace"Aa umma kawae muje asibiti tukun daga can sae mu kaita gidan inna sbd nsn fa'iz mai iya zuwa ne yana ci gaba da dubata"
Fa'iz ( cewa da wani abokin sa likita).
Umman nasir tace"meyasa zamu kaita gidan inn ai sae hnklinta ya tashi kawai mu maida ta nn gdn in yaso kullum na riqa zowa ina dubata.
Nasir yayi saurin yace"Aa umma baza mu maida ta gidan nn ba dmn wnn rashin tausayi da cin zali yayi yawa gsky bazan iya barin Rynt a cikin halin nan ba ai ko me ta masa bai kamata ace ya dake ta ba kodan kasancewar ta qaramar yarinya snn umma idan har kinzo da rana wa zai riqa kula da ita da dare har zuwa wayewar gari don wnn uban dukan rashin imani da ya mata ya kamata ace koyaushe tana da mae kula da ita shiyasa naga gsky ba inda ya dace aje da ita face gidan inna don shi dae na tabbatar bazai kula da ita ba.
Umman saliha ta sauke ajiyar zuciya tace"shikenan nasir kamata muje mu saka ta a mota"
Bayan sun saka ta a mota ne suka bar gidan suka nufi asibiti.
Tafe suke kan hnya umman
Saliha dake seat d'in baya rungume da Rynt sae kallon Rynt take cike da tausayi wacce in banda numfashi ba abinda take iya yi.
Umman saliha ta nisa snn tace da nasir"ni ina mamakin wane irin abune Rynt tayiwa mohd da har ya iya mata wnn dukan"
Nasir yace"ni nasan ba abinda Rynt ta masa da yakai ga duka kawae dae rashin imanin sa ne ya motsa,kuma umma dama fa Rynt zaman haquri kawae takeyi a gidan shiyasa nake son inna tasani ko hkn zai sa man ya daina quntata mata sbd idan inna taji tamkar Abbansa yaji ne , Abba kuwa kai tsaye zai gyara masa zamansa ne don bazai ta6a barin sa ya ci gaba da cutar da Rynt ba.
Umma tace"lallai kam ba makawa zai gyara masa xamansa"
Daga haka basu sake cewa komai ba sae Nasir da ya ciro wyrsa a aljihu ya kira abokinsa yana gama waya dashi se juya alkalar motar sa yayi zuwa canza hanya ummar shi ta tambaye shi lafiya
yace"Fa'iz ne yace mu had'u can gidan inna sbd ya rigada ya baro asibiti.
Tace" haka yafi sauqi amma hlnda inna zata ga Rynt nake tunani"
Nasir bae ce komai ba don shima nazarin da yake yi kenan don yaso ace koda zata ga Rynt an ciyo kan matsalar sae dae kawae taji lbrn abinda ya faru.
Suna isa shima abokin nashi na isowa.
Dukkan su suka shiga gidan har shi fa'iz d'in wanda ga dukkan alama ya saba shiga gidan dan shine gaba sai sauri yake ya bud'ewa nasir qyallen qofa.
Nasir dake d'auke da Rynt ya ajiye ta kan 3 seater abokin nasa ya shiga dubata sbd sunyi sallama har sun gaji ba amsa.
Bayan abokin yayi en gwaje gwajen sa akan Rynt ya nemi akaita kan bed sbd yana son zai mata qarin ruwa .
D'akin inna aka kaita snn aka d'aura mata ruwan sae a snn ne inna ta shigo gidan wacce ga dukkan alama maqota ta fito dan riqe take da qullin nono da fura a hannu,ai kuwa tana shiga d'akinta ta saki furar da nono tana taslima inda a rud'e ta shiga tambayar abinda ke faruwa da Rynt.
Sae da nasir ya kwantar mata da hnkli snn ya snr da ita abinda ya faru.
Kukan su na tsafi ta shiga yi tana sirfawa mohd zagi ciki da waje snn ta d'auko waya a cewar zata kira Abban mohd yazo yaga d'ayen aikin da yayi wa Rynt.....bata kae ga kiran sa ba taji abokin nasir na cewa da nasir
"Haqiqa anyi babbar nasara dan duk irin dukan nn da tasha juna biyun da ke jikinta yana nn lfyrsa qalau"
Da kmr mamaki Nasir yace"juna biyu ne da ita? Yace"tabbas kuwa tana d'auke da juna biyu don hk sae a kiyaye a riqa bata kulawar da ta dace"
"InshaAllah"
Shine abinda nasir yace kafin abokin sa ke rubuta masa magunguna ya bashi.
Nn Nasir ya maida dubansa gun ummar sa da inna wad'anda kallo d'aya zakayi musu kasan sunyi farin ciki matuqa da jin zancen Dr musamman inna da kukanta ya koma dariya.
Yace musu"zanje siyo magani na dawo"
Inna tace"to d'an albarka sae ka dawo ,kai kuma Hafizu Allah sa ka gama da iyayenka lafiya don wnn lbr da na ji a bakinka ya kore min duk wani baqin ciki.
Da shi har nasir sae da sukayi murmushi suka fita sbd fa'iz yasha fhmtar da ita sunan shi amma sae tayi ta kiran shi da hafizu tun yana gyara mata har ya daina sae dae kawai yayi murmushi idan ta kirashi da Hafizu.
Suna fita inna taje kusa da Rynt dake ta sharar bacci tace "um! um! baiwar Allah, Allah iskar miki ga shashan yaron nn muhammadu ai zai zo ya sameni ne zai kuma had'u da ubansa kabiru dan sae na snr dashi komai kaf ba abinda zan rage shashan yaro kawai marar tausayi da baisan daraja mace ba.
Nn ta d'auki fura da nonon da tayar a kan fridge wad'anda umman saliha ce ta d'auke ta d'aura akai.
Ta d'auki furar tana mae fad'in"bari naje na dama ma er albarkar nn Rynh ita kafin ta tashi tayi sanyi sae tasha"
Tana gama fad'ar hk ta kama hnyr fita d'akin umman saliha ta tashi da sauri tana qoqarin cewa da inna ta kawo furar ta dama sae ga man ya shigo d'akin shaye da toka riqe da mami a hannun shi wacce taje da gudu kan jikin mamarta.
Mohd kuwa yana had'a idô da inna ya wani qara d'aure fuska dan karma inna taga damar shi .
Amma hkn bai hana inna ta shiga sirfa mae masifa tana"fad'in shashan yaro me kuma ya kawoka ko kazo ka qarasata ne iye!
Komai mohd bai ce da ita ba sae zuwa yayi kan gadon da Rynt ke kwance ya ajiye wata farar takarda ya fita .
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [2/8/2017]
Billy giro😊:
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
*page* *```47```*
Inna tace yau naga shahan yaro me kuma ka ajiye mata kan gadon da har ina ma magana zaka wani wuce ni.
Nn umman saliha ta tashi taje ta d'auki takardar ta karanta wacce tana gama krntawà ta saki takardar ta zauna sakwaf kan gado tana taslima had'e da fad'in innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
A rud'e inna ta d'auki takardar tace"lafiya me ya rubuta mata a takardar ne?
Umman saliha tace"saki ne inna!
Da qarfi inna ta dafe qirjinta tare da fiddo ido waje tace"saki!
Sae kawai ta fashe da kuka tana"fad'in innalillahi wa inna ilahi raji'una anya kuwa muhammadu yana son ya gama lfy, me wnn er albarkar ta masa da zai had'a mata zafi biyu a lokaci d'aya nn ta koma fashewa da wani kuka inda cikin kukan ne ta kira Abban mohd ta snr dashi komai.
Kafin yazo sae ga nasir ya dawo da siyen magani ya qaraso jiki sanyaye ganin yanda inna keta fmn shar6ar kuka har da su fyace majina, a hnkli ya ajiye ledar maganin hannunsa kan bed yaje ga inna yana tmbyr me kuma ya faru?
Takardar hannunta ta miqa mae tace"gane ma idonka abinda d'an banzan yaron nn ya rubutawa Rynh ,yana kar6ar takardar ya hango saki 6aro 6aro nn ya cire hular kanshi tare da kallon Rynt dake kwance still tana bacci yace"ya saketa!
Daga nn shima ya zauna gefen gadon dafe da kai yana tunanin me Rynh ta ma mohd ne wae.
Yana cikin hkne yaji sallamar Abban mohd.
A hnkli ya d'go tare da zamewa kan gadon ya durqusa yana gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa yayinda ita ma umman saliha ta gaida shi ya amsa snn suka fito d'akin suka barshi shida inna.
Cikin damuwa Abban mohd yaje gun Rynt yana mae kallon yanayinda take ciki can ya nisa yace da inna"shi mohd d'in bai ce ga abinda ya had'a su bane?
Inna tace"meko yace sae shigowa kawai da yayi yaje ya ajiye mata takarda ya fita wanda har ma magana nake masa amma yaqi ko kulani.
Abba ya jinjina kansa snn yakai hannu ya ciro wyrsa a aljihu ya kira mohd
Yana d'agawa yace"duk abinda kake ka ajiye shi kazo ka sameni a gidan inna.
Daga hk Abba ya katse wyr.
Mohd dake zaune a asibiti gurin malika wacce tasa shi gaba tana ta kuka wae ita kukan baqin cikin zubewar cikinta take yayinda shi kuma duk ya wani sukui kuice yana fmn lallashinta.
Shine ya samu da qyar ya lalla6ata tabar shi ya fita.
Fa'iza wacce daman tana cikin d'akin.
Tana ganin mohd ya fita taje ta ba malika hannu suka lale ,malika tace"Abbansa ne ya kira shi nsn kan sakin nn ne da yayiwa wnn abar "
Faiza