Showing 168001 words to 168541 words out of 168541 words
Chapter 57 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt
yana son cirewa wae sae ya nuna mata cikar da babynsa ya qarawa qirjinta"
Bata barshi ba ta kama towel din ta riqe gam sae zille mae take tana dariya har suka je kan bed ya samu da qyar ya cire towel d'in daga nn wasar ta canza salo zuwa wasannin su na ma'aurata.....
Malika kuwa duk shekarun nn da aka kwashe bata samu ta sake wani auren ba sae can da qyar ta samu wani dattijo ya aure ta matan sa uku itace ta hud'u kuma a gida d'aya suke zaune shiyasa sam bata jin dad'in rayuwar gidan tana zaman haquri ne kawai ga masifar matan sa da gorin haifuwa da take sha sosai a gurin su da kullum idan tana zaune shiru sae tayi ta kuka don sosai wani irin son haifuwa ya shigo ranta.
Qarin abin ma sun maida ta kamar wata er aiki da duk wani cefanen gidan ita ke zuwa tayi duk da akwai masu aiki a gidan dmn gidan ba talauci amma kwanciyar hankali da jin dad'i sun gagareta.
Wata rana taje super maket tana siyen kayan abinci kamar daga sama taga Ryynt tare da su Ammar, Anwar n Razeenah yaran da in ka gansu kamar ka sace sbd kyau da shiga rai shirin su a wayen ce kmr wasu 'ya'yan turawa,Ryynt kuwa ta qara haske sosai tayi fresh d'an cikin ta ya fito abin sha'awa da har yanzu in ka ganta kmr yarinya er 17yrs sae jiki da ta qara kad'an irin na jin dad'i da kwanciyar hankali.
Malika tayi tsaye sae kallon su Razeenah take cike da sha'awa tana ji kamar ace yaranta ne.
Ta kuma bi cikin Ryynt da kallo qwallah tap a idonta sae kuma a take tayi saurin had'iye hawayen ta qarasa gurin su Ryynt da suka gama siyayyar su zasu fita ta kira sunanta a hankli,Ryynt ta tsaya tana kallon malika tana son tuno ina ma tasan fuskar dan gabad'aya malika ta sauya ta dawo kamar wata er qauye.
Malika da ta fahimci bata gane ta ba tace"baki gane ni ba koh malika ce"
Sosai Ryynt tayi mamaki kafin take sake mata fuska suka gaisa har malika na tambayar sunan su ammar Ryynt duk ta gaya mata sae ga man ya shigo yana waya da gabad'aya hankalin malika ya koma kanshi sbd tsabar kyaunda taga ya qara wanda da gani kasan baya d'auke da wata damuwa sae kwanciyar hankali da jin dad'i.
Yana gama wayar malika ta gaida shi ya amsa mata sama sama yaja yaransa suka fita tare da Ryynt da duk tausayin malika ya cikata.
Nan Malika ta bisu da kallo hawaye masu zafi na sauka kan fuskar ta.
Tana ji ina ma rayuwa zata koma mata baya da bata bar ta aikata marassa kyaun ayukkan da suka kaita ga asara da da na sani ba.
Allah ya kare mu da aikata aikin da na sani da asara Ameen.
ALHAMDULILLAH A NAN NA KAWO QARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA INDA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MIN AMEEM.
KHALEESA HYDAR MY ADVISER AND EDITA I THANK U SO SO MUCH.
NA GAIDA ILHAM AND MUJAHEED.
MY LADY (FUTUHATULKHAIR)INA FATAR ALLAH YA BAKU ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A D'AYYIBA AMEEN.
LUV U ALL MY FANS ALLAH YA BAR MU TARE.
BILLY GIRO😊