Showing 135001 words to 138000 words out of 168541 words

Chapter 46 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9909

sauqi?ya gyad'a mata kai tare da fad'in Alhmdlh.
Tace"muje inga"
Nan taja hannun sa suka je kan bed suka zauna ta yaye hannun rigar sa tana kallon gurin da ya sake mishi sabon dressing ta maida hannun rigar ta d'ago ta kallesa a hnkli tace"wae mk me ya same ka ne?
Ya lumshe ido tare da kwantar da kanta a qirjin sa yace"My Ryynt ba wani abu bane tsautsayi ne"
Ta d'ago ta kalle sa kawae bata ce komai ba ta sake maida kanta tana wasa da buttons d'in rigar sa yace"me zan samu naci banyi break fast ba na fito sae yunwa nake ta ji"
Ryynt ta d'ago tana kallon sa tace"Arish mukayi da soyayyen qwai sae farfesun kaza ,kuma akwai ruwan zafin tea a flacks,na kawo maka"
Yace"eh kawo min"
Sae da ta shifid'a qatuwar darduma a nn qasa kusa da gefen gadon snn ta fita ta dawo d'auke da kayan break fast d'in gabad'aya cikin tray ta ajiye kan darduma snn ta koma fita taje d'akin inna ta d'auko masa fresh milk da ruwa ta kawo kan darduma ta jera ,
man dake zaune har ya fara zuba ma kansa ya kalle ta washe da baki yace"wae nida wa wad'an nn kayan haka?
Tace"uhm kai kad'ai mana"
Yace "so kike na kasa tashi knn"
Tace"Aa so dae nake nayi fata fata da yunwar cikin ka"
Yace"to ae sae ki zauna ki bani da kanki dmn zanfi ci sosai"
Nan ta zauna ta qarasa zuba abincin a plate ta d'ebo a fork spoon zata fara bashi yace"Aa da yatsun ki nake son ki ciyadda ni yau"
Murmushi tayi ba tare da ta musa ba ta ajiye fork d'in tasa yatsunta ta soma ciyadda shi.
Sae can bayan har ya kusa qoshi ,ya d'ibi arish da qwai zae kai bakinta tace"um um nifa a qoshe nake"
Yace"wae kar kice sae ci nake ban taya miki ba"
Tace"uhm bayan duk dae kuma kaida kazo kwaraka ma"
yace"ai kece ogar kwarakar da kika kwana gidan mutane kika bar mijinki cikin kewa"
Tace"uhm gidan innan ne na mutane?
Yace"to na aljanu ne"
Tace"hm gidan ka ne na aljanu ae da ake kwasar mutum a yar"
Ya kalleta had'e da er dariya yaja hancinta yace"ni gidana ba aljanu kece dae da baqin tsoron ki sae kace farar kura"
A shagwa6e ta turo baki tace"ba wani nn kawai kai dae ba ka so a fad'a"
Zae ce wani abu knn suka ji inna na qwala ma Ryynt kira tayi saurin zaro tissue ta share hannun ta ta fita.
Koda taje d'akin inna fitowar ta daga bathroom knn tana zaune kan bed tana shafa mai.
Inna tace"sae naji kmr muhammadu ya shigo ko,dan naji kmr sallamar sa da ina bayi.
Ryynt tace"eh ya shigo"
Inna tace"yanzu zaku tafi can gidan nasu ko kuwa?
Ban tambaye sa ba tukun yana cin abinci ne.
To shike nn jeki.
Nan Ryynt ta juya ta koma d'akinta.
Ta sami man na waya yana ganin ta yace da wanda yake waya bari zan kiraka anjima daga nn ya tsinke wayar ya maida aljihu.
Ryynt tace"meyasa baka bar kun qarasa wayar ba?
yaja hannunta ya zaunar da ita kusa dashi tare da fad'in"ina tare da mata ta ina zanyi lokacin wani can"
Ryynt dake kallon sa tayi murmushi tare da kwantar da kanta kan kafad'ar ta sa ta shafo cikin sa tace"a qara maka abincin ko ya ishe ka?
Yace"ya isheni zuba min fresh milk kawae nasha"
Nan ta tashi daga kan kafad'ar sa ta zuba masa ta bashi yasha snn yasha ruwa ya zaro tissue ya share bakin sa da hannun sa Ryynt kuwa ta kwashe kwanika ta fitar dasu.
Koda ta dawo ta same shi zae fita daga d'akin yace"ki shirya idan na dawo daga gun gaida inna sae mu tafi kinga 11 har ta gota ya fad'i hakane tare da kallon wristwatch d'in hannun sa,Ryynt tace"to"snn ya fita taje ta zaro gyale kalar kayan jikinta ta yafa tasa takalmi ta jawo jaka da wayar ta taje ta same can d'akin inna.
Ba jimawa sae gashi sun fito shida ita sae kallon ta yake tayi wacce ta fhmci tunda ta shiga d'akin inna yake kallon ta har sukayiwa inna sallama suka fito.
Har zatayi magana knn taga yaja hannun ta ya tafi da ita d'akin ta yana qoqarin cire mata mayafi tace"mk lafiya"
Yace"har kya tambaya bayan kinga irin tsabar kyaun da kikayi, ae idan na barki kika fita kin nemi wani ya qwace min ke,don haka nemo wasu kayan a canza shirin nn"
D'auke da d'an murmushi a fuskarta tace"hm kaima dae da wasa kake don kasan duk duniyar nn ba wanda ya isa ya qwace maka ni sae mutuwa"
Mohd yace"to so kike wani ya kalla min ke ya shammace ni ,wae ma dae ya akayi keda ba kya saka gyale sae gashi kin saka yau?
Tace"saliha ce wlh jiya ta za6ar min kaya da taji ina tunanin kayan sawa shine ta ciro min su a cikin akwatinan lefe"
Yace"to nemo hijab d'in su don gsky baza ki fita da gyalen nn ba"
Tace"to ae babu hijab gyalen ne kawai koni da ta ciro min kayan nace bana son gyale ta duba min hijab koda ta duba babu klr kayan"
Yace"to nemo wasu kayan da keda hijab"
A shagwa6e tace"oh oh mk wlh ni baxan iya canje canjen nn ba kayi haquri dan Allah"
Man yayi tsaye riqe da waist d'inshi yana qare ma fuskarta kallo.
Nan kawae taga ya jawota zuwa jikin sa ya had'e bakin su sae tsutsar lips d'in ta yake sae can ya janye bakin nasa yana kallon lips d'inta yakai babban yatsan sa ya shafo lips d'in nata ya duba yatsan sa yaga ba komai yayi murmushi had'e da girgiza kansa yana kallonta yace"wae ke wane irin lipstick ne haka kika sa da baya fita kanshi ne fa kawai na tsotsi lips d'inki ko xae fita don na fhmci ba qaramin kyau ya miki ba,
dmn wnn ba na fita bane sae wa ni kad'ai ya kamata ace kinyi wa kwalliya dashi.
Ryynt tayi er dariya mae kmr murmushi tace"ai gwanda da bai fitan ba don da ka 6ata min er kwalliya ta"
Nan Man ya harare ta da wasa yace"koh? yayi yanzun kuwa zan tsotse shi tas"
Yana gama fad'ar haka yaje zae kai bakin sa a nata,cikin dariya tayi saurin cusa fuskarta a qirjinsa tana fad'in"yi haquri dan Allah idan ba so kake lips d'ina su kumbura ba don wlh baya da saurin fita"
Ya d'ago fuskarta tare da jan hancinta yace"shike nan naji na barki amma yau kad'ai"
Tayi murmushi tare da gyad'a masa kai yaja hannunta suka fito daga cikin gidan.
Wushil man yaga kmr mutum ya fito daga qarqashin motar shi ya wuce da sauri.
Ya kalli Ryynt kmr zae ce wani abu sae kuma ya basar ya tafi da ita suka shiga motar ya tashi motar suka bar layin.







Billy giro😊
[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 80*
Basu kai koina ba sae gashi sun dawo Ryynt ta fito da sauri ta shiga cikin gida jim kad'an ta fito riqe da wayar ta a hannun ta wacce ta manta da ita a d'akin inna.
Taje zata bud'e gambun mota knn sae saukar ball taji tim a kan cikin ta, a tsorace ta fasa ihu ,yayinda mohd ya fito motar a fusace ya nufi yaron da ya jefo ball d'in cike da niyar kai masa mari Ryynt tayi saurin zuwa ta riqe masa hannu tace"Mk dan Allah kayi haquri yaro ne fa"
Yace"dan ubansa ko yaro ne kan me zae jefo ball akan cikin ki ko kuma shi abinda ke cikin ki ba rayuwa bane!
Yi haquri dae dan Allah tun da kaga bada gayya bane.
Mohd dake kallon yaron rae 6ace yace"oya duqa ciro ball d'inka a qarqashin mota ta ko kuma wlh na taka ta na wuce"
A tsorace yaron ya duqa ya ciro ball d'in sa zae wuce man ya bisa da ido yace"kae xo nn"
Jiki sanyaye yaron ya juya,
mohd yace"wa na gani ya fito a qarqashin mota ta d'azun?
Yaron ya sadda kansa qasa yace"nine"
Mohd yace"uban me kamin a qarqashin motar to?
Yaron yace"ball d'ina ne da ya gangara na d'akko"
Mohd ya kalli Ryynt yace"u see kince bada gayya bane bayan wnn ne karo na biyu koma fiye dmn muna fitowa naga lokacinda ya fito a qarqashin motar da sauri ya fice shiyasa sam ban cika son barin mota na a waje ba dan irin yaran nn marassa ji sae su maka 6arna a banza,bari kaji idan na qara ganin kana ball a guraren gidan nn wlh sae nayi maganin ka,oya tafi in daina ganin ka a nn very stupid!
Sim sim yaron ya bar gurin.
Ryynt ta kalli man tace"dan Allah ka rage yawan fad'an nn bana so wlh"
Mohd yace"Ryynt nasan yaron baya ji wlh ko kad'an,
musamman yake da filin ball a cikin gidan su banga uban me yasa ya fito yana ball a waje ba har yake qoqarin hallaka min ke da babyna ,
wlh gwara ma ace motar ce ya daka glass d'in motar ya fashe kan ya doka min ke .
Tace" to yi haquri dae dan Allah ya wuce.
Yayi murmushi had'e da jan hancinta yace"ni a gurina bae wuce ba sae naga lafiyar babyna tukun"
Tayi murmushi yayinda yaja hannunta suka shiga mota yakai hannu ya yaye rigarta yana shafa cikin yace"ya kika ji a lokacinda qwallor ta dake ki?
Tace"naji zafin saukar ball d'in ba sosai ba na kuma tsorata don har sae da abinda ke ciki ya motsa.
yace"da qarfi sosai ya motsa ko kuwa?
Tace"da qarfi ba sosai ba"
Man yayi shiru yana kallon ta can yace"Ryynt ya zama dole muje asibiti nayi scanning dmn naga lafiyar babyna"
Ryynt tace"plz Mk ba sae ka duba ba inshaa Allah ba wata matsala"
A natse ya girgiza kansa yace"No Ryynt abinda zaki d'auka ba matsala ba shi zae zo ya zama matsala kuma hankalina zae fi kwanciya idan na duba kiyi haquri muje kinji baza mu wani jima ba"
Ta gyad'a masa kai snn yaja motor suka tafi sae asibitin shi.


Kan hanyar su ta dawowa daga asibitin ne Ryynt ke kallon man wacce gabad'aya jikinta a sanyaye tace"mk nifa na tsorata don sae naga kmr yara har uku a cikina"
Saurin kallon ta yayi don sae da fa yace ta rufe idonta ashe ta bud'e bae sani ba,bae dai ce mata komai ba yayi d'an guntun murmushi yace"Ryynt knn kije ina da yara har uku photon ne kawae ya rarrabu"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"ai ni har na soma shiga tension wlh"
Yace"tension name dan Allah ya baki babbar kyauta.
Tace"um um wlh ni ko biyu ne bazan iya ba bare uku"
Yace"to idan Allah ya baki fa sae kiyi yaya?
Tace"hm nima ban sani ba amma na tabbatar cikin da kanshi zae zube kan tsananin tashin hankalin da zan shiga"
Mohd yayi murmushi kawae ba tare da yace komai ba yaci gaba da jan mota.


Suna isa family house basu zarce koina ba sae 6angaren iyayen sa.
Basu sami kowa a falon ba mohd ya umarce Ryynt da ta zauna bayan ta zauna ya haura sama jim kad'an sae gashi ya fito shida mahaifiyar sa da suka qaraso Ryynt ta zame kan kujera ta russuna cike da ladabi tana gaida ta.
Ba yabo ba fallasa mahaifiyar sa ta amsa mata har tana tamvayar ta ya hanya tace"Alhmdllh"
Mohd yace"Abba fa ko har yayi tafiyar dan jiya da na shigo gaida shi naji yana waya kan cewa zae je abuja"
Tace" Aa bae tafi ba tukun sae gobe yanzu haka yana d'akin shi bari naje na dubo maku shi.
Nan ta tafi zuwa sama mohd ya kalli Ryynt wacce ke durqushe still bata koma kan kujera ta zauna ba sae zama tayi a takure nn qasa gun gefen kujera.
Yace"Ryynt koma mana kan kujera ki zauna kin wani takura kanki haka sae kace kinxo baqon guri"
Tace"um um barni a nn kawai ya isa"
Bai ce komai ba sae hannun ta ya riqo zae maida ta kan kujera tayi saurin qwace hannun cike da jin kunya sbd Abba da ta hango tafe shida umma.
Mohd da bai gansu ba yaje zae sake riqo hannunta tayi mai wani kallo na alamar ga fa su Abba nn tafe suna kallon mu.
Nan ya juya had'e da d'an sosa bayan kansa alamar jin kunya suna qarasowa ya durqusa cike da ladabi yana gaida Abba,Abba ya amsa snn ya kalli Ryynt wacce tayi qasa da kanta tana gaida shi ya amsa d'auke da murmushi a fuskar sa yana tamvayar ta ya hanya tace"Alhmdlh"
Bayan sun gama gaisawar ne Abba ya koma daga ciki umma ta kira mai aikin ta ta kawo musu ruwa da lemu da kuma abun motsa baki.
Umma da kanta ta zubawa Ryynt lemu a cup ta bata ta kar6a ta samu da qyar ta kur6a kad'an ta ajiye don gabad'aya kunyar hjyr take ji gashi sae kallon ta take.
Kuma su biyu ne kawae zaune a falon sbd mohd ana kawo masu ruwa da lemu aka kirasa a waya ya fita.
Hjyr mohd kuwa tana kallon Ryynt ne sbd ganin yanda Ryynt ta canza tayi kyau klr ta ta koma kmr tashin er abuja ga natsuwa sae duk taji ta soma son Ryynt sosai a ranta,nn ta tsinkayo muryar Ryynt na tambayar Ameera fa.
Allah sarki taga dae ko kad'an Ameera bata ta6a nuna mata so ba amma kuma har take tamvayar ta ai kuwa sae taji ta qara sonta,
ta sakar mata murmushi tace"Ae Ameera na can gidan pretty,pretty taje da ita dmn ta samu ta riqa rage mata wani aikin kafin hutun makarantar su ya qare.
Ryynt da kanta ke qasa tayi d'an guntun murmushi tace"Allah sarki"
daga hk tayi shiru bata sake cewa komai ba .
Sae ga mohd ya dawo yace"umma bari muje other parts mu gaida su"
Tace"to sae kun dawo"
Nan Ryynt ta tashi suka tafi.
Sae da suka tafi d'ayan 6angaren snn suka je 6angaren su saliha.


Da murna sosai umman saliha ta tarbe su yayinda man da Ryynt suka gaida ta ta amsa musu cikin sakin fuska tana tambayar su ya hanya suka ce Alhmdlh nn Ryynt ta wuce d'akin saliha ta bar mohd suna qara gaisawa da umman saliha.


Ryynt na shiga d'akin saliha tayi tsaye tana kallon saliha dake chat tana qyalqyatar dariya.
Ryynt ta girgiza kanta taje ta zauna kusa da ita tana fad'in"keda waye haka?
Da sauri saliha ta kalli Ryynt tace"yaushe kika shigo har kika zauna ban ko ji ba?
Ryynt tace"hm inafa zaki ji hankalin ki na gun chat.
Saliha ta tashi zaune tare da fad'in"wlh kedai wata qawata ce er ban dariya keta sani dariya har cikina yayi ciwo wlh.
Ryynt tayi murmushi tare da ajiye jakar hannun ta saliha da ta kafe ta da ido tace"waih barikallah yau sae kika qara yin kyau sosai wlh har dae pink lipstick d'in nn da kika shafa kan d'an mitsilin bakin nn naki mae matuqar kyau kmr na qwace maki shi na gudu.
Da wasa Ryynt ta harare ta had'e da turo baki tace"kin fara koh saliha?
Saliha tace"to ae gsky na fad'a ina kika samo kalo d'in nn da na jima ina neman irinta bana samu daga dark sae mae haske sosai nake samu,
Ryynt tace"wlh a dubai kedai na siyo wata er kit ta cosmetics ciki sae ki samu komai da kike so,kema taki na nn na siyo miki ae"
Ihun murna saliha tayi tare da rungume Ryynt tace"kai amma wlh naji dad'i na kuma gode"
"oyoyo Aunty!
cewar mami wacce ta shigo da gudu, Ryynt ta d'auke ta cike da murna ta d'aura ta kan qafafunta.
Umman saliha da suka shigo tare da mami tace"Ah sauketa kar ta zunguren min d'an jika"
Sosai Ryynt taji kunya tayi saurin sadda kanta qasa tana murmushi .
Umman saliha da ita ma murmushin take taje zuwa sauke mami,mami ta qanqame Ryynt tace"um um mama nifa ba inda zanje tare zamu koma nida Aunty idan zata tafi"
Umman saliha tace" mami nafa gaya miki baza ki koma ba gwanda tun wuri ki fidda ranki"
Ryynt ta d'ago ta kalli umman saliha tace"meyasa mama?
Umman saliha tace"Ryynt takuraku kawae zata yi dan yanzu ba d'aya bane da wancan lokacin kawae dae zan riqa barin ta tana zuwar miki ko weekend ne.
cikin fushi mami tace"wlh mama ban so"nn ta sauka kan jikin Ryynt ta fita daga d'akin cikin kukan shagwa6a.
Umman saliha ta bita da ido d'auke da dariya a fuskarta,Ryynt kuwa ta qwala mata kira a cewar tazo umma wasa take mata amma mami taqi dawowa.
umman saliha ta kalli saliha da ke bin mami da kira itama, tace"kinga tashi je kawo ma Ryynt lemu da ruwa ae kinsan mami in ta fara fushi ba rarrashi take ji ba dan kanta zata sauko ta dawo.
Ba musu saliha ta tashi ta fita umman saliha ta kalli Ryynt tace" gobe ne zaki koma koh?
Ryynt tace"eh inshaa Allah mama"
Umman saliha tace"dama wasu turarukka ne nasa aka sake had'a miki dan nasan wad'an can sun isa qarewa koh?
Tace"Aa mama akwae saura,
Tace" to indae kin tashi zan baki ki tafi dasu .
Cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login