Showing 144001 words to 147000 words out of 168541 words

Chapter 49 - Bazan Barshi Ba! Complete Hausa Novels By Billy Giro .txt

14 Jan 2025

9154

yake marmari ba ita ba,nn dae ta juya ta bar gurin cike da tunàni
kala kala a ranta na hanyar da zàta bi tasa Ryynt ta bar gidàn da qafafunta kuma ta tafi knn har abada.


Ryyñt kuwa tana shiga d'aki sae ga mami ta shigo aguje sae dariya take taje bayan Ryynt ta 6uya tace"Anti 6oye ni muna wasan 6uya ne nida alawiyya"
Kafin Ryynt tace komai sae ga alawiyya ta shigo d'akin nn mami ta fita aguje ta bar d'akin alawiyya ta bita sae sautin dariyar su kake ji,
D'auke da murmushi Ryynt ta girgiza kanta tace"aifah an had'u da an dace"
Taje ta zauna kan bed tare da jawo wayarta da ke ajiye kan bedside drawer ta kira duk wani nata da ta sani ta musu gaisuwar juma'a.
Bayan ta gama wayar ne ta soma jin bacci na fizgar ta nn ta d'an kwanta ba jimawa bacci ya kwashe ta.


Ta jima abinta tana bacci snn ta tashi wacce da tashinta ta cire kayan jikinta ta fad'a bathroom tayi wanka ta fito tayi shirin ta cikin wata doguwar riga ta material less mai d'an qyal qyali light brown ga rigar ta kama jikinta sae ta mata kyau sosai har dae d'aurin d'an kwalin da tayi sae ya qara fito da ita ,ita kanta har mamakin ganin yanda ta iya d'aurin d'an kwali take bayan gani kawae take a kan mutane ba koya tayi ba.
Mami ce ta shigo d'akin ta kalli Ryynt dake feshe jikinta da turarukka tace"Anti kinyi kyau fiye da kwalliyar d'azun hln fita zakiyi?
Ryynt tace"ba abinda zanje mami"
To amma kuma shine kikayi wani wankan har da canza kaya, uhm mami knn cewar Ryynt wacce taja hannun mami suka je downstairs gun dining ta samu kuku ya gama jera komai na abinci wacce dama tazo ta duba ne kar sae mohd ya dawo ba'a kammala jera komai ba gashi yau juma'a yana gab da shigowa.
Nan suka juya zasu koma upstairs suka ji qarar bud'e gate mami tace"eh! yaya ya dawo"
Daga haka bata jira me Ryynt zata ce ba ta fita da gudu jim kad'an sae gashi sun shigo ita da mohd yana riqe da hannun ta yayinda d'ayan hannun sa ke riqe da briefcase d'auke da murmushi Ryynt ta kar6i briefcase d'in tana mishi sannu da zuwa.
"Yauwa my Rynt"cewar mohd wanda shima yake d'auke da murmushi a fuskar sa,mami ta kar6i briefcase a hannun Ryynt tare da fad'in"Anti kawo na kai masa a d'aki"
Ryynt tace"zaki iya?
Eh anti zan iya,to ki riqa da kyau nn mami ta rataya briefcase d'in ta wuce.
Kamar jira mohd keyi ya janyo Ryynt zuwa jikin sa yace"Ryynt wnn kwalliya haka so kike na kasa zuwa masallaci"
Tace"uhm Mk knn abinci zaka fara ci ko kuma sae kayi wanka?
Muje na fara cin abinci tukun, ya fad'i hakane tare da jan hannunta suka je kan dining suka zauna sae ga mami ta dawo mohd yace"mami je gayawa Antinki malika tazo aci abinci"
Tace"to"ta tafi da gudu ba jimawa sae gata ta dawo taja gujera ta zauna.
Bayan malika ta fito har sun fara cin abinci Mohd sae kallon Ryynt yake d'auke da murmushi a fuskar sa ita ma sae kallon sa take tana murmushi sbd qafar sa da yakai kan tata yana shafawa har itama ta soma ramawa wanda duk abinda suke idon malika na kansu tana ganin yanda suke wasa da qafafuwan su ta under table.
Da qyar taga sun kammala cin abincin ta tashi zata bar gurin sae kuma ta juyo tana kallon mohd da ya zari tissue yana share hannun sa tace"ina so zanje gida"
Yace"sae kin dawo"
Daga haka yaja hannun Ryynt suka bar gurin ba tare da ya jira ko malika zata ce wani abu ba mami kuwa dama suna kammala cin abinci ta bar gurin.


Suna shiga d'aki man ya soma cire kayan jikin sa Ryynt na taya shi yasa bathrobe yaja hannun Ryynt suka nufi bathroom ta taya shi wanka suka fito ya zauna yana shafa mae Ryynt taje ta ciro masa kayan juma'a wani tsadadden farin yadi mae kyau da akayi wa aiki da light brown ta ciro masa hula mae klr aikin da kuma takalmi suma klr wato light brown bayan ya gama shafa mae ta taya shi ya shirya tana fesa masa turare sae kallon sa take dan ba qaramin kyau yayi ba,ya kar6i turaren ya fesa mata a wuya ta lumshe idonta a hnkli yace"wnn kallon fa my Ryynt?
Sae da taje kan qirjin sa ta kwanta snn tace"kyau kamin"
Ya shafo bayanta yace"ae kin fini yin kyau don yau da qyar ma ne zan tafi masallaci"
Ryynt ta d'ago d'auke da murmushi tana kallon sa tace"hm mk ka cika zolaya"
Yace"hm zolaya ko ai zakiyi bayani ne in na dawo daga masallaci"
A shagwa6e ta kalle sa tace"um um dan Allah yi haquri ni kwad'ayin fita ma nakeji amma sae ka dawo tukun sae mu tafi yawo"
Mohd yayi murmushi tare da jan hannunta suka fito ta rakashi har mota snn ta dawo wacce bata zarce koina ba sae d'akin ta.


Koda mohd ya dawo daga masallaci ya sami Ryynt ta ida sallah tana linke hijab yaje yayi kwance rigingine kan bed ya maida hannayen sa baya yayi pillow dasu had'e da lumshe idanun sa.
Ryynt tazo ta zauna a hankali kusa da shi tare da d'aura hannunta akan sajen fuskar sa,cike da kasala ya bud'e idonsa ya riqo hannun ta da ta d'aura akan sajen fuskar sa yana kallon ta kafin yake sauke idonsa akan cikin ta ya tashi zaune ya janyota zuwa jikin sa yana shafa cikin snn ya kalle ta yace"ya naga kmr babyna ya rage girma yau?
Tace"rigar ce ta 6oye girman shiyasa naji dad'inta wlh"
Mohd yace"ashe sae nasa a qara d'inka maki irin ta da yawa kafin ki haifu sae ki sami na sawa koh"
Ryynt tace"kayan ae zasuyi yawa tunda ko na lefe yaushe yaushe ne na fara saka su"
Mohd yace"um um ai doguwar riga tafi dad'in sawa ga mai ciki har dae irin ta jikin ki d'in nn kuma kayan lefen da kike magana idan cikin ya tsufa sae kiga kin nemi na sawa kin rasa duk sunyi kad'an sae dae ko bayan kin haifu.
Tace"to ae sae idan cikin yayi qatoto ne,ni kuma nafi so ma ya tsaya a haka ba sae ya qara girma ba"
Mohd ya kalle ta ba tare da yace komai ba don yasan cikin ba qaramin girma zae yi ba shiyasa take bashi tausayi yanda zatayi kayan cikin idan ya tsufa.
Ryynt tace"amma a d'inka min ko kala uku ne a cikin zannuwan lefen da naga ba'a d'inke ba"
Mohd ya gyad'a mata kai d'auke da idanun sa da suka soma canza kala,
Ryynt dake kallon sa tace"bacci kake ji?
Yace"eh tashi muje d'akina"
A shagwa6e tace"Mk yawon da nace maka fa"
Ryynt wane yawon ba inda za'a je ki huta abinki kawae.
Tace"um um ni yawo nake so"
Yace"to bari idan na tashi daga bacci zuwa bayan la'asar sae ki shirya na zagaya dake cikin gidan nn kiga guraren da baki je kin gani ba"
Kmr zatayi kuka tace"uhm uhm ni na d'auka ma ko cikin gari zamu je"
Mohd ya goga tsinin hancinta akan nashi yace"kar ki min kuka wasa nake miki bari idan na tashi daga bacci koina kike so za'a je"
Da sauri tace"har da gidan inna"
Yace"har ma da gidan gwaggo"
D'an kuka shagwa6a ta fashe masa da shi don ta fhmci knn zancen fitar ma da kmr wasa yake mata.
Mohd yayi er dariya yaja hannunta suka fito sae kukan shagwa6a take tana roqon sa ,
shi kuma yana janye da ita har suka je d'akin shi.
Da kanshi ya rage kayan jikin sa tayi zamanta tana kallon shi ya dawo daga shi sae singlet n boxer yazo ya xauna kusa da ita yana shan ruwan gora masu sanyi da ya ciro a fridge ya bata tace"um um tare da marairaice fuska tace"mk dan Allah dae wlh ban san me yasa ba kwad'ayin fita nake ji yau"
Yace"Ryynt ae da gske nake miki zamu fita d'in amma banda gidan inna don nasan fad'a kawae zata miki kin dawo da kwana biyu har kin fara fita,ki bari zuwa sati biyu haka sae na kaiki gidan inna kinji" Tayi murmushi tare da rungume shi tace"na gode"
Nan taji hannun mohd akan zip d'in rigarta yana zugewa ta d'ago tana kallon sa tace"bacci fa kace zakayi"
Idanun sa masu cike da sha'awa ya kalle ta da su yace"hm wae ke ba kya banbance sha'awa da jin bacci ne"
Sosai ta shagwa6e fuska tana kallon sa kafin tace komai sae bakin sa taji a cikin nata tare da kai hannu a cikin rigarta yana wasa da dukiyar fulaninta.




Sorry dan Allah wlh ina fama ne da rashin son typing gashi na matsu na kammala muku shi na huta amma kuma da zarar na d'auki waya sae naji gabad'aya typing ya fita raina kwata kwata shiyasa duk yanda naso nayi mae yawa nake kasawa.












Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```


































🔮🔮🔮🔮
*page 84*
Bayan sllr la'asar sae gasu sun fito bathroom mohd na sanye da white bathrobe Ryynt na sanye da baby pink sae dariya take had'e da d'an gudun ta bata so mohd dake biye da ita ya kama ta bata kai koina ba ya cafko ta zuwa jikin sa yaje da ita kan bed ya kwantar had'e da yi mata rumfa zae kai bakin sa a nata ta kauda fuskarta tace"Mk lokacin sallah fa na tafiye ka sani"
Yace"to ae kece bana gajiyawa dake kin sani"
Ryynt tace"uhm mk meyasa ka fiye son zolaya ne wae"
Yace"au so kike wnn karon ma na nuna miki ba zolaya nake ba"
Ya fad'i hakane yayinda ya kai hannu zae zare mata bathrobe tayi saurin cewa"Aa yi haquri dan Allah wlh na gaji "
Yace "to tashi muje muyi sallah"
Tace"banda abin sallah d'akin nn"
Yace to muje na raka ki ki d'akko nn ta miqa masa hannun ta ya kama ta suka fito yayinda Ryynt ke rungume a ajikinsa suna tafe sae shafa cikinta yake suna magana suna dariya ba tare da sun kula da malika dake zaune a falo ba ita da qawar ta fa'iza sae kallon su suke har suka 6ace ma ganin su.


Fa'iza da still ta kasa d'auke idonta ta jinjina kanta had'e da fad'in cabd'i! lailai samun guri"
Malika da duk kishi ya gama cikata taja hannun fa'iza tace"zo muje da Allah bana son ganin dawowar su"
Suna isa d'akin nata tayi zaune tare da dafe kanta fa'iza tace"meye kuma abin damuwa bayan kin san makomar er banza wnn abun da take duk na d'an lokaci ne dan da ganin wnn cikin nata duk dad'ewar sa bazae wuce nn da 3months ba ta haife shi.
Malika tace"ga dukkan alama hkne shiyasa naji dad'in shawarar da kika bani dmn itace mafi sauqi da zan rabashi da ita har abinda ta haifa ko ma nace abinda ke cikin ta dmn kafin ta haifu zan aiwatar da komai kawai fatana na san lokacinda ta fara naquda har zuwan su asibiti to da na sami hakan buqata ta biya kuma duk wani baqinci nayi sallama dashi a rnr har abada amma kuma tun ba'a je koina ba haquri na yana so ya qare kan abubuwan da ke faruwa tsakanin shi da ita musamman irin zumud'in da yake yi akanta ya soma kaini maqura ba kad'an ba, kiji fa wanka suka fito yanzun wanda na tabbatar wani abu ne ya faru tsakanin shi da ita.
Fa'iza tace"calm down my dear ki barta lokacin ta ne tayi abinta lokacin ki zae zo da zaki rabata dashi har ma kowa nata"
Hakane fa'iza i knew but abin ne da ciwo kawai daga sama wata banza can taxo tana qoqarin qwace maka miji wae har ace ko rnr girki na yafi lokacin ta akaina don rnr yana dawowa daga aiki gurinta ya fara zuwa kafin ni kuma har cikin dare fa tashi yake yaje d'akinta haka kawai......what!cewar faiza,malika tace"hm bari kawai ke dae ai har calendar na ajiye dmn na fara soke kwanan watan lokacin cin ubanta wato na ganin cewa na rabata dashi har abada ynx so kawai nake rnr girki na ta zagayo na tambaye sa hln cikin ta wata nawa ne dmn zanfi jin dad'in ci gaba qirgar watannin"
Fa'iza tace"hln zae gaya miki ne?
Hm ina mace kuma bare kuma yanda yake son cikin nasan zae ji dad'i idan yaji na d'auko zancen sa don duk qarin haukar son nn da yake mata bae wuce cikin da ke jikinta ba.
Fa'iza tace"hkne kam shiyasa nake son ki ajiye banzar aqidar ki kema ki sami cikin nn"
Malika tace"ae samun ciki mae sauqi ne aqida ta kuma dole na ajiye ta na samar masa baby sbd ina son na dawo da duk wata soyayyar da yake min a baya ina kuma son na goge laifin zubar masa ciki da nayi kuma ko ba komai hkn zae sa ya manta da wnn abar kwata kwata a rayuwar sa.
Fa'iza tace"da yafi miki ,ni zan tafi kinsan sauri nake zanje gida sae munyi waya.
Malika tace"to ai nima kinsan fita zanyi shigowar ki ne ya tsaida ni bari na jawo veil d'ina muje"
Nan malika ta ciro mayafin ta taja key d'in motar ta suka fita.


Washe gari da guraren qarfe biyar na yamma Ryynt ce riqe da hannun mami ta rako saliha wacce taxo mata yini tun safe.
Suna tsaye a bakin gate yayinda Ryynt ke cewa" yanzu saliha gobe idan kun koma shikenan kuma sae idan anyi hutu ko zamu sake had'uwa"
Saliha tace"inafa ai kinsan na gaya miki wnn karon ban d'auke maki kowane visiting ba kuma wlh idan baki zo ba munyi fad'a"
Ryynt tace"saliha ina kike son naje da wnn cikin ko kuma so kike a filin visiting d'in idon kowa ya koma kaina ne"
Hm kinjii ki da wani zancen wnn cikin ae baiyi girman da zae hana miki shiga mutane ba kawai kedai kice baza kije ba shikenan Allah bamu alheri kinga tafiya ta
Ta qarashe mgnr ne d'auke da fushi a fuskarta zata bar gurin
Ryynt tayi saurin riqo ta tace" Haba saliha kin san ba haka bane wlh kunyar shiga jama'a nakeji da cikin nn bare kuma lokacin nasan ya qara girma amma inshaa Allah zan zo ko visiting d'in farko ne kawae dae Allah yasa yayanki ya barni"
D'auke da murmushi saliha tace amin Allah yasa, ni zan tafi.
Ryynt tace"to Allah ya kiyaye hanya ki cewa umma na gode sosai"
Saliha tace"to"kafin take fita Ryynt kuwa ta juya riqe da hannun mami suka koma daga ciki.


Guraren qarfe tara da rabi na dare sae ga man ya shigo d'akin Ryynt ya same ta sae waya take tana qyalqyatar dariya tana fad'in"ni bazan rantse maki ba sae dae kinzo ki ganewa idonki ko zaki fi yarda"

Man yayi tsaye kawae yana kallonta wacce bata lura dashi ba har sae da ta gama wayar ,
da sauran murmushi a fuskarta ta gaida shi ya amsa had'e da qarosowa inda take ya zauna kan bedside drawer yace"da waye kike waya haka sae faman dariya kike?
Tace"hm qawata ce Sarah ke mamakin jin cewa ni matar aure ce har ma taqi ta yarda wae sae na rantse mata"
Mohd yace"a bakin wa taji ne to?
A guna taji da na gaya mata wnn karon bazan koma school ba shine ta nemi jin dalili na gaya mata,kuma qarin mamakin ta jin cewa kaine mijina wacce duk a tunanin ta kai yayana ne ban kuma gaya mata ainihin dalilin da ya hana ni komawa ba kawae dae nace oga ya hana.
Mohd yace"ashe idan ta ganki d'auke da babyna sae mamakin yafi haka"
Tace"ae kam har laifina ma sae ta gani ko ma tayi fushi dani don ita fa komai nata bata 6oye min,in tazo ban ma san ta inda zan fara ba.
Mohd bae ce komai ba sae hugging d'inta da yayi tare da kai hannu yana shafa cikinta snn yace"ae ko don albarkacin babyna zata miki haquri"
Uhm ko ta qara yin fushi ba kawae dae sauqin abun tana da sauqin kae wanda idan na mata bayanin yanda abun yake zata fhmce ni.
Mohd dake rungume da ita ya d'aura mata kiss snn ya miqe yace"sae da safe my Ryynt yau bacci nake ji sosai"
Tace"to sae da safe"
Nan ya fita ita kuma ta d'auki wayarta ta soma chat.


Bayan wasu en kwanaki da faruwar haka Ryynt ce zaune a a falo alawiyya na mata kitso sbd anjima da yamma ita ce zata kar6i girki.
Kallo suke abinsu suna kitso sae ga malika ta fito tayi tsaye riqe da qugu tana kallon Ryynt tace"cabd'i amma lallai yarinyar nn ba er iska irinki ko an gaya miki cewa kowa qazami ne irinki da zaki zauna ana maki kitso a main falo sbd gidadanci irin naki bari kiji wlh maza
ku tashi a nn ki koma can side d'inki ki barbad'a qazantaccen gashin ki a can"
Tana gama fad'ar haka alawiyya taje zuwa miqewa Ryynt tace"ke zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login