Showing 24001 words to 27000 words out of 155717 words

Chapter 9 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

630

me har yanzu fa ya Agrif bai taba furtamin maganan aure ba sai de yace idan na gama secondary zai gaya min wata magana dana gama na nemi ya gayamin yace sai yazo yanzu de sai yazo din GOBE DA LABARI kunnuwa na zasu jiye min abin da na jima ina son ji".
Zahra ta ce'' in sha Allah za ki ji nima ba ga ya Ayman ba ya gama nuk'u-nuk'unsa ya fito kema zaki ji".
Nasrim tasa iho woow gobe akwai party dinner na musamman a 3'brother family'
ta kalli Humairah tace'' kema Humee wakika tsayar ya kamata a goben duk mufito da mazaje ita ko Izza sai ruwan ido ka mazan nan birjik a kanta".
Humairah dan ta bawa Nasrim haushi tace'' ai ni sai babban gora NASARA KO GANI GAFI MUTUM NASARA ME WUYAR FADANCI nake so".
"dariya Nasrim tayi tace'' in ma dan naji haushi kike yiwa kanki mummunar fata wllh ba ruwana idan kika fada abakin ma'lakiku".

Zarha ma dariya tayi tace'' kai wai mummunar fata auren Nasara ai sai me sa'ar gaske narasa me yasa k'iyayyar sa ba ta raguwa a zuciyar ki Nasrim bayan shi yanzu baya ma nuna yasan ki dama de inaga k'uruciya ce fa yanzu kuma kunyar abin da yayi na dane yasa yake miki haka kin kasa gane halinsa ko mu da muke gai dashi ba sai ya ga dama yake cewa Weldon shikenan bakin amsa gaisuwar kenan".
Humairah tace
"Ai ita tana jin maganan Inna Harira ne ni fa wllh ban yarda da abinda take fada ba, wai shi ya karya miki yatsa ai so nake wata rana ta zauna tana gilla miki k'aryar mommy ko shi Nasara yaji naga bakin gilla k'arya".
Zahra tace'' wllh kuwa inda da gaske ne me yasa ba mu taba ji su Mama suna fada ba ko Hajja a yawan surutunta za muji tayi koda subutar baki ne ta fada dama fa masu aiki munafukai ne duk da Nasara me bak'in haline banajin zayyi haka".?
Nasrim tace'' ita Hajja sona take da za muji a bakin ta su Ummu kuma kin san ba fad'a za suyi ba ni na yarda da abin da inna Harira take fada tun daga ranan da aka haifeni suke boyeni saboda baya son gani na har yabar k'asan uwar da ta haife ni dalilin sa ta watsar da ni yanzu waye zai ce mommy ni ta Haifa ba shi ba wllh bani da abin k'i sama da shi, kuma sai munyi shari'a agaban Allah da zaku ce k'arya ne duk da bawani cikekken sani nayi wa fuskans aba nasan cike take da k'ina Agrif fa ko waya baya iyayi dani a gabansa.
Humairah ta ce
"To Allah de ya kyauta mu de muna fatan Allah Ya kawo k'arshe abin".
Nasrim ta ce
'' ba Ameen ba wllh kamar yanda ban san farkon k'iyayyar ba bana son naga k'arshenta ni da shi har abadan"
Daga nan ba su ƙara cewa komai ba ta yi wa motar key suka ka wuce gida.

*******

Daga shi sai wani dan guntun boxer yana kwance a bakin ruwan swimming pool a kan wani dan gadon k'afe wasu siraran kyawawan yan matan India ne suke masa tausa idonsa akan Agrif da ya kama dimaucewa a kan rubuta kalaman soyayya jikin wasu flour murmushinsa wanda ba ya sakin sa sai yatuno da mugunta ya yi, sannan ya yi wa 'yan'matan alama da su ba sa waje
mik'ewa y ayi zaune ya sa hannu ya janye floor din da Agrif ya dafe a k'irji Agrif buɗe lumsassun idonsa yayi a kansa ya ce
"Why"?
Murmushi yayi yace "wai bro me kake shirin yi ne".?
Shi ma murmushi yayi yana mek'a hannun alaman ya bashi abinsa amma Nasara ya hana sai Agrif ya ce
"Abin da nake shirin yi ko na gaya maka ba ganewa za kayi ba tunda baka san sa ba. Ina shirya kallaman da zan gaya wa Nasrim ne na burgeta na kuma saurin dilmiyar da zuciyarta ka san Nasrim ba jigari-jigarin macce ba ce".

A hankali Nasara ya sakar masa fulawar ya koma ya kwata dariya Agrif ya yi ya ce
"Ai dama nace ba za ka gane ba, da dai harkan business ne dai kum...."
Sauran maganan ya tsayewa Agrif ganin wani irin hawaye da yake bullulawa a idon Nasir wanda tun suna yara bai taba gani hawayensa ba sai a mutuwar Abba, akwai ranan da ya karye a ball amma murmushi ma ya yi a maimakon kuka. Da ya ga Agrif yana masa kuka da sauri ya k'arasa inda yake ya kama hannunsa cikin firgici yake tambayar sa me ya faru, cikin wani irin sheshek'ar kuka Nasir ya fara bayani
"Haruna ban san yanda za ka d'auki al'amarina ba amma al'amarin yana da girma da rikitarwa Agrif a ranan wanka an ce ba a ɓoye cibi, wllh na fika son Halima tun kafin ta zo duniya dan Allah dan'uwa ka min alfarman bar min ita".
wani irin zabura Agrif yayi ya mek'e tsaye
"What! wllh NASURUDDEEN k'arya kake ba sonta kake ba ka sha fada ka tsane ta mai sonta ma ba ka so, ka sha bani shawaran na rabu da ita wllh Salo kawai kake son canzawa wani manufa kake da shi a kanta ba So ba.....

Shi ma mik'ewar ya yi yace "Agrif tunda nake da kai na taba maka k'arya".?
Agrif ya ce
"A a amma na san yanda k'iyayyar Nasrim ya ginu a cikin jininka za ka iyayin komai dan ka cutar da ita".

Nasir cikin laushin murya ya ce
"Shi ke nan dama na san ba wanda zai yarda da ni sai kai, dan kafi kowa sani na ka san ni bana furta abin da ba zanyi ba amma tunda kai ba ka yardani ba abar zancen ma na san ko mommy ta sani amma ka sani wllh bazan rayuba in ban aure ta ba, amma na bar maka inde ba za ka iya sadaukar min ita ba gobe tare za mu tafi kamin alfarman neman gafaranta na cutar da ita shiyasa Allah ya jarrabeni da sonta".?
haka de yayi ta yiwa Agrif kalamai kamar gaske har ya yarda zai sadaukar masa da soyayyar ta amma da sharadi
da sauri yace "meye sharadi wllh ko na mutum ne zanyi".
Agrif yace" Nasrim tana mugun k'in ka dan haka idan har ka shawo kanto na bar maka ita har abadan idan kuma kuma ta k'i to ba dole".
Murmushi Nasara yayi yace thanks brother amma kafin nan sai kamin wata alfarman wanda shi ne na k'ashe so nake acikin yaran gidan kace kana son wata ka ga zata ji zafi ta ce ka ci amanar ta daga nan ni zan fara kafa nawa fadan aguntq."
Agrif yace " ai gidan mu babu wasu y'an mata sai Zahra da Izza ita Zahra ta Ayman ce sai wannan Izza ni kuma gaskiya bana ra'ayin ta farinta bai min ba kamar zafiyan nake ganin ta".

Nasir yace " yawwa ita zaka so zaure kazo Nasrim zata fi jin haushi ta yi saurin karb'an ta yi na dan tarama abin da kayi mata ka auri aminiyarta ka ga ita ma za ga ce zata rama ta aure ni".

Agrif yace "okay zanyi tunani akai".
ya d'auki tar kacen sa yayi gaba

wani irin murmushi irin Nasir yayi yana binsa da kallo sai kuma ya murtuke fuska afili yace ni Nasuru na AURI wannan yarinya kamar yanda bana son ta bana son wani nawa ya rab'e ta zan baka mamaki Agrif yarinyar nan sai ta zama abin kwatance a duniya ta yanda ko kare ba zai shinshina ta ba balle mutum sai na tarwatsa rayuwar ta tunda na rasa ubana a kanta. Ya yi murmushi yana tuno kukan da yayi a fili ya sake cewa ashe zan iya shirin Film
to Allah ya kyauta Nasuru

Kano

"Izzatu kin sani a gaba sai kuka kike me yake faruwa kukan ki yana ta damin hankali".

Cikin kuka tace'' Baba nika bar ni a cikin dibin masoyana na fitar da wani a waje kai ka kafe sai yan cikin gidan nan Wllh bani a gabansu ba samarin ba har y'an mata Humairah Kamal yana son ita ma Zahra nan y'ar karere Ayman dan gidan Dr hafsa k'awar mommy yake son ta NASRIM Agrif ne yake sonta ni kenan ba Wanda zai soni na gaya maka kabarni na zaba a cikin masu sona idan kudi ne ai Khaleed ko Shamsu duk masu kudi ne dama fa tun ina yarinya Hajja ta ce ita ajikokin ta bawanda zai aure ni tsintacciyar magi ce Agrif ya zaunar da yan uwan sa ba bu irin wulak'ancin da basu min ba bazan manta wannan ba ni na hak'ura

wani irin dariya Baban nata yasaka yace tsincciyar magi ko zafuga herrin tsuntattun magina wllh sai na tarwasa farin cikin wannan gidan idan kikaga baki auri daya daga cikin suba to ni sunanan ba BOKA Cuna ba
kwantar da han kalinki ai dama shi Nasurun nake hari shiyasa na b'ata lokaci amma jiya naduba nagani cikin Agrif da Aiban wanin su akwai aure a tsakanin ku nayi nayi na gane waye amma na rasa samoda jininsu daya amma tabbas akwai mijin ki a ciki

Cikin tsoro Izza ta ce
" Baba dama kai boka ne"?

Dariya ya sake yi yace ai dalilin da yasa aka koreni daga k'auyenmu kenan da na yi wa limamin garinmu asiri shi ne asirinna yatonu aka kore ni a hanyar mu ta zuwa aka haife ki, ana haifan ki na hasko taurarunki na ga zaki yi arzik'i ta hanyan auren me kudi muna shiga Nigeria na sake gaskata dubana da naga masu kudi sun fi son kyawawan mata shi ne na fara bin gidajen masu kudi ina musu gadi dan wata rana ki AURI me gida ko yaron gida ba korata ake ba amma idan na hango gidan da yafi wanda nake ciki kudi sai na gudu anan nasan yanda zanyi na koma aneman gidajen masu kudin na gano cewa nan yafi kowa ne gida kudi a birnin Kano ko nace Nigeria ma baki daya shi ne na zo nan da mahaifiyar ki kuma da gan-gan na bata guba ta mutu dan na san idan ina tare da gawa za a temakeni shine na zauna da gawa a farkon shiga layin nan duk wanda ya zo ya ganni da gawan yanin magan bana kulashi har sai da na tabbatar da motan numbar gidan 3'brother ne na yi magana kin ga idan zan kashe masoyya ta Farada akan cikar buri na to ba abinda bazan iya yi ba Izza kinu na min kedin jini nace kiyi zamba cikin aminci dama masu iya magana sun ce cin amana yana biyo bayan yar da" .

cikin wani irin murya tace Baba me yasa............


*To masoya an kusa kutsawa cikin labarin dan har yanzu da saura kusani FURRUCI NA NE RIKICIN BABBAN GIDA NE*

*To RIKICIN ta ina zai bullo Nasrim za ta yarda da auren Nasara meye manufar Nasara akan Nasrim kubini asannu*

BJ
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURRUCI NA NE*

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

*page 5*


*ASSALAMUALAIKUM*
*FATAN AL'KAIRI GAREKU MABIYA* *WANNAN LABARIN da farko de naji dadi da yanda kuka karbi labarin hannu biyu biyu ina godiya sosai Allah yabar kaun*

*SAN NAN INA SANAR DAKU FURUCIN NA NE BA KULLUM ZAMU NA POSTING BA YAU IDAN AKAYI TO GOBE ZA A HUTA INA FATAN HAKAN YAYI MUN GODE DA COMMENT*
🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻

"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki.....
"ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin hankali abin bazai miki kyau ba dan ni zan iyayin komai akan cikar burina na kashe Faida ma balle ke zaki kawo min maganar banza yanzu kinga wani abin da ya Dan ganci bokan ci ne atare dani na dena aikin ki kad'ai zan cigaba dayi shima idan burin mu yacika kika auri daya daga ahalin gidan nan zan bari na tuba meye Allah baya yafewa nide nasan zai yafemin".
shiru tayi can ta nisa tace'' to shikenan Baba ance idan zaka sha giya shata dubu ni megaba dayan nake so Nasuru din".
dariya yayi yace"shegiya Naira ba babba ba yaro ni kai na naso haka naso ace Nasara kika mallaka amma sam taurari sun nuna ba al'kairi taurarin ku basu hadu ba ba aure a tsakanin ku da Nasara shine na hakura amma ina lefin Aiban ko Agrif din'."
tace'' amma Baba nafison Agrif din dan shine akusa da Nasara kaga yafi sauran sanin sirrin komai na dukiyar ".
murmushi yayi yace"yanda kike so haka za ayi wa gareni inba keba".

************
Nasrim tun asuba ta tashi da farko ta fara da gyaran parlour da bedroom na Agrif tana tsaye akan ma'aikatan duk abin da ba suyi dai-dai ba tace su kyara ko tayi da kanta dama ita tafi gane tayi abu da kanta dan tana da tsananin tsafta duk k'okarin mutum sai ta k'ureshi dan koya aka mata wanki ko shara to sai tasake sai da taga komai ya koma yanda take so ko ina sai tashin k'amshi yake mommy ce ta sauk'o da shirinta na fita aiki murmushi tayi tace'' haba ashe sarkin tsaftan nan ce a part din nan shiyasa nake jiyo k'amshi tun acikin bedroom tana maganan tana sauk'owa a steps
sai data k'araso Nasrim ta durkusa har k'asa tace''
"Mommy barka da fitowa an tashi lafaya?.
"Alhamdulillah okay na tuno ashe fa yau me tsadan ne zai zo shiyasa aka ganki anan".
murmushi tayi ta sunkuyar da kai dan kwata kwata ba sabo irin na uwa da y'a a tsakanin su
"ammm yawwa Nasrim dan Allah idan Hajja ta tashi kice mata ina da aiki sosai a office ne yasa ban jira breakfast ba sai nadawo".?
Nasrim hannu tasa ta karbi jakan hannun mommy ta fara binta a baya har wajen mota sai da drive yaja ita kuma ta koma part din su direct kicin ta wuce nan ma tadawa ma'aikatan hankali tayi yan kamin wancan beremin wannan ko tarin kirki basayi yanzu zata balbane su da fad'a Humairah ce ta shigo tana cewa "ummmm Wllh k'amshin girkin nan ya hanani bacci. zaro ido tayi dai-dai lokacin da ta k'arasa shigowa tace 'kai wai duk wannan abun na tarban mutum daya ne gaskiya Ya Agrif yafi kowa gata ummmm har ma da abinda bayaci kinsan bayacin chicken".
Nasrim tace'' zaici wannan gashe ne kuma ba surutu ba kunun gyada yana hannun ki ni zan hada masa shurba".
Humairah tace'' to amma kinsan bana aikin banza ko shurban nan sai na masa sha iya sha".

Nasrim tabe baki tayi tace''ai wllh baki isaba sai yaci kowa zai ci guntun sa".
dariya Humairah tayi tace'' wannan ne baki isa ba".
Nasrim bata kulata ba tajuya tana kallon yanda Fanta take gasa *garabiya* tace aunty Fanta ai ya gasu dan Allah zaga baya kiduba min ndalayin nan ko ya tuk'u kar sumin shirme Zainab kema fita ki dubanin Umar sun gama *denderun* nan".
Zainab tace''
ranki yadade Nasrim ai saide a kawo miki kigani dan nasan ba zaki gamsu da amsar da zan baki ba".
tayi saurin bin bayan Fanta suka fice
Zahra da take shigowa tace'' yau de ko shehun Barno za a sauk'e iya girkin da za ayi na bare bari kenan".
Haumaira tace'' wllh kuwa ai ni yanzu ma zuwa zanyi nayi brush nazo naci miyar *daddawwo* gashi nan yasha busheshen kifi dama najima ban ciba tun wata rana da mommy tayi mana".
Zahra tace''ni kam wannan miyar baya burgeni d'aci ne dashi idan akwai wannan miyar *manumbi* din nan da ake sa agushi da wake shi zanci".
Nasrim tace'' duk kugama maitar ku ba me baku sai yaci yarage".

karfe Sha biyun rana jirkin su Agrif zai sauk'a amma tun sha daya Nasrim ta azalzali Bala drive ya hada mata kan direbobi da bodyguard su tafi airport kada ya sauk'a yayi jira ta higa ta fesa wanka tabdi aiki awajen make-up aka bata lokaci
kalliyar ta single ba wani hayani ya amma tayi kyau sosai Nasrim wankan tarwad'a ce wato kalan chocolate Allah ya bata baiwar kyan fata gashi ya hadu da hutu ko macce k'arya take tayiwa Nasrim kallo daya bata sake ba ko Izza da take fara sol farin buzayen asali ba takai Nasrim d'aukan hankali ba haka fuskan ta tako ina acike yake ba wani tayani muni ko kumatu shi bayyi fadi ba shi bayyi siriri ba haka hancin ta ba siriri bane can amma amek'e yake san bal haka jajayen leben ta wanda yake a tsuke ya samu kyakkyawan zama kamar ita ta zana
abinda yafi zaukan hankalin mutane fiye da komai atare da Nasrim idon ta duk da basu fiye girma ba amma farare ne sol me d'auke da dogayen gashi a sama da k'asar su gashi ta iya sarrafa ido sosai yanda take k'adasu da juyasu idan tana magana zaka zaci tsabar yan gane da iyayi nan ko halittar tace a haka tun tana yarinya kullum da safe Mama sai ta tofa mata La'ahwaula a idon ta Nasrim tana da zanen nen gashin gira siriri wanda inba wanda ya santa ba zaice concealer take zanawan dan bawani karkata a setti yake sai kwanceccen sajen ta wanda yazo mata har kunne ta tana da cikar gashi da tsawo
bai war Nasrim na jan hankalin mutane bai tsaya anan ba Nasrim macce ce ta sama da k'asa heeps din ta awani irin mulmule yake ga tozo ko ya take tafiya sai sun motsa shiyasa Mama take yawan cewa tasa shijab duk da de tozon sa a cikin shijab ba yana fitowa gata bata fiyye son sa shijab ba ita manya kaya ma takurata suke kullum suna cikin fada da Mama akan sa k'ananun kaya
boops dinta acike suke dayake bata da jiki sosai girman su yake fitowa har takurata yake mutane suna neman k'arin heeps da boops ita tana neman rage sa so dayawa tana cewa Mama ita a nemo mata maganin rage girman heeps da boops musamman idan anyi bak'i maza Mama tana kula da yanda idon su yake kan Nasrim koda yaushe ahankali take tafiya wai Dan kar su motsa amma sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login