Showing 66001 words to 69000 words out of 155717 words
Chapter 23 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
a yanzu jina nake nida gawa daya ne ni Agrif zai tozar ta".
ta k'arashe maganan tana daukan wayan ta cikin sauri da samo hoton Izza dana Agrif ta hada ta kansale da Jan rubutu ❌ sannan ta rubuta *RI JF* ta daura a status din ta tayi murmushi ta haura sama Humairah tace'' dan Allah Nasrim kar kiyi abinda zaki janyo mana nadaman a family".
bata mata magana ba ta k'arasa hawa steps
da sauri Humairah ta fito taje tayi Ummu bayanin abinda ya faru Ummu murmushi tayi tace " bawani abinda zan iya yi amma anjima zanje na mata nasiha Nasrim akwai taurin kai".
Humairah tace'' gaskiya Ummu wllh ba amata adalcin ba bawara yaje waje yasamo ba da ya auri Izza data gama sanin sirrin ta wllh kishin yanzu ba irin daya bane danasu Mama da mommy kuma Ummu wllh seriously ba wani batun sai anjima ki tashi muje yanzu ki mata nasiha ni wllh in yakama ma araba auren ta hakura ta barwa Izza din in yaso Allah ya bata wani da wannan munanan FUFUCIN da takeyi".
mek'ewa Ummu tayi tace'' to tashi mu tafi
"haba Nasrim kamar ba me ilmi ba to meye kishin da zaki ta da hankalin ki kituna fa kece tamu ba wani gata da ni'iman da Allah bai miki ba dan ya jarrrabe ki da kishiya sai kiyi butulci".
"Ummu ki gane kishiyar fa na cin Amana ne nifa naga Izza da Baban ta da gawa agaba ruwan sama yana dukan su nasa daddy ya dauko su duk wani mataki da Izza ta taka da sa hannun na da temakona amma tarasa wanda zata ci amana sai ni".
Ummu dafa kafadan Nasrim tayi tace'' Nasrim ki dauka amatsayin k'addara ba cin Amana ba zakiga riba Insha Allah kiyi misali da zaman hjy Aisha da Dr Fanna mana Wllh muna zaune agidan nan duk kan mu muna zaune tsakanin Dr Fanna da Aisha sunfi kusanci har Ina ganin kamar ni sun wareni ko da Abdulsamad ya rasu Hajja tace'' daya daga cikin mazajen mune zai auri Dr Fanna wllh nazaci nawa mijin za a bawa saboda yanda Dr da Aisha suke k'awance amma sai Allah yasa Abdulmajid ne mijin kuma alak'an Dr da Aisha k'aruwa yayi bai ragu ba wani abun ma sai suyi su binne ban sani ba kinga ba fa basu da kishi bane sun danne abun a rai ne kawai dan shi kishi ta yanda ka daukeshi haka zai zo maka kiyi hakuri ba abinda Izza zata rage ki dashi kuma nasan Insha Allah nima zan sa Ido akan zaman ku Baban gida zai kwantan ta adalci a tsakanin k.........
cikin b'acin rai Nasrim tace'' shikenan Ummu nagode".
Ummu bata gamsu da yanda Nasrim ta amsa abin ba gashi kuma gaban ta dare ne komai zai iya faruwa dan haka sai
tace'' ko za muje ki kwana a part dina gobe sai kizo".
murmushi Nasrim tayi tace'' lah Ummu ba komai ba abinda zai faru insha Allah".
"Ummu tace'' Yawwa Nasirisiya ta Allah yamiki al'barka."
bayan fitan Ummu Nasrim kicin ta shiga kwalin wuk'a ta dauko sai da ta zabi adda wanda yafi kaifin da tsini ta dauka ta zaga baya ta fara gogawa ajikin wani dutse ahankali take gogawa Khafulan da yake sama yana cire uniform din islamiya ya hango mamyn tasu a baya yace "kai bro gata can tana wasa adda ko Abbamu zata kashe muguwa ce".
Fayyat ya lek'a yana kallon ta yajuyo ya kalli Khafulan yace " mamy kake cewa muguwa Allah idan nagirma sai nasa an daure ka kullum kanayi wa mamy rashin mutumci".
"Eh nayi din karama mata mana ai itama batason Papa na bayahude take ce masa".
Fayyat yace "to tafada din".
shima Khafulan yace
"To nima na fada din daga nan suka kama kokuwa Allah yatemaki Fayyat shima yana da k'arfi dan haka dai dai suke karawa Khaldum ne dama bawan Allah ba ruwan sa
A office ko Agrif sallahn azahar ne kawai ya tashe sa bayan ya dawo daga sallan ya d'auki wayan sa ainda ya ajiye tun zuwan sa bai ma tsaya duba yawan Miss call da message din ba yasan Nasrim baza ta kirashi ba sai wannan na cacceciyar Izza tsaki yayi yana kashe wayar gaba daya batare da duba cikin saba ya maida ya ajiye sai asannan yafara aikin sa shine har sha biyun dare tukun ya tattara tarkacen sa yarufe office din ya fito yasamu drive komai akasalance yakeyi Allah Allah yake idan yaje gida yasamu Nasrim tayi bacci
Nasrim ko tasake hawa dam duk atunanin ta Agrif yana wajen Izza dan Izzan ta sake daura wani sabon status da yake nuni da suna tare har tana ikirarin tare zasu kana a hospital din
Yana bude kofar falo yace
"Inna'lillahi Halima bakiyi bacci ba".?
"banyi ba sai na aiwatar da abinda nake son na aikata".
"Halima kin gane nima a cikin damuwar nake wllh bansan wani mafita ba da nasani da nayi nima inda akwai hanyar da za ayi nagujewa auren da nayi amma kemeye naki shawaran".
Murmushi tayi tace''
Ummmm huuuu maza kenan har Kai kana da bak'in magana ka taba kaiwa bayan magaruba a waje amma yau saboda masoyiyar ka tana asbiti shine kaje kasata agaba kuna daura status na cin zarafina wllh bani kuka tozar taba kanku".
"Status kuma wani irin status".
kallon sama da k'asa ta masa tayi dariya ta shige ciki shi kuma ya jefa kan sa kujera there'siter lumshe ido yayi yana "Lahaulawalakkuwata'lillah'billah" .
bayyi auni ba kawai yaji an yankeshi a hannu a firgice ya mek'e kafin ya Ankara ta sake yankan sa ahannu
"Halima Halima Halima."!!!!!!
ganin zata masa illa yasa ya yi kanta gadan gadan
Tana nunashi da wuk'an tana ja dabaya tace'' inde dole sai kayi auren nan to zan kasheka inyaso a fanshi ranka da nawa".
"Halima ki saurara ni wllh bani da niyar auren nan zan miki bayani".
ni wllh bawani bayanin da zaka min ba kace ko Rana da wata zasu dena haske sai ita ba".?
"yaushe na fad'a mezanyi da wata Izza da har zan furta wannan akanta".
"a bayyane kafada yanda duk duniya zasuji shine dan kazo gabana......
gani da gaske take yada Agrif yin waje da gudu itama biyo sa tayi amma Allah ya temake sa yafice yarufo kofan ta waje yasa annu a al'jihun sa yana zaro wayan ya kira Kamal a take Kamal yafito a nasa part din yana tambayar sa lafiya
Agrif nuna masa annun sa dayake jini yayi yace " kaga hannu na Nasrim ce tamin haka tana ciki wai sai ta kasheni".
Nasrim ta ciki sai dukan kofar take
Kamal ya numfasa yace " Agrif duk lefin kane ai ba ka kyauta ba ko zaka fara d'okin Izza kabari tazama matar ka mana amma wllh nima banji dad'i abinda ka aikata ba".
"me na aikata Kamal wani d'oki na nunawa Izza yarinyar da ko kirana ta bana dauka".
Kamal yace "status din da kayi da ita ba doki bane".
cikin mamaki da rashin sani Agrif yace " ban gane status ba" ?.
yace yana duba wayan sa yace karo da status din da bashi ya d'aura ba kuma a wayan sa "what!? meye haka Kamal wllh bansan dashi ba ni bani na daura ba wllh ni bani da wani hoton Izza a wayata meyake faduwa".
Kamal yace"ban gane ba ta yaya wani zai d'auki wayan ka ya d'aura maka status".
cikin gigicewa Agrif yace
"Wallashi Kamal ka yarda dani ba tare muke da kai ba yau kaga ma nayi amfani da waya
" a silent fa na sata".
Kamal yace" ai shine nima abin yaban mamaki ina zuwa nasamu Humairah tana kuka ita take gayamin ga abinda yafaru wllh ban yarda ba Saida ta nuna min na yarda".
"Kamal me nayiwa mutane suke son ganin bayana da matata".
ganin yanda jini yake fita Sosai a hannu Agrif Kamal yace muje hospital
bayan su dawo daga asbitin
nasrim ta gama buge bugen ta wullar da wuk'an gefi tana maida numfashi dak'er Kamal ya shawo kan Nasrim tayarda ta shiga bedroom din ta Kamal yaraka yana kwantar mata da hankali tashiga wanka Yana zauna tafito sanye da rigan baccin har sai da yaga ta kwanta yaja blanket ya rufeta yafita
shima Agrif din Kamal dinne ya rakashi bedroom din sa
Kamal yace"shikenan Haruna ta hakura har ta kwata ma kaima kayi kwanciyar ka amma dan Allah idan da matsalan kayi saurin kirana dan FURUCI Nasrim Yana bani tsoro
************************
" da a suba Nasrim tana farkawa taji gaban ta Yana wani irin faduwa sai kuma ta kejin buga kofa kamar ana kuka kuma kamar kukan yaran ta da ta gudu tayi d'akin nasu tana bude kofar taci karo da Fayyat da Khaldum a kwance cikin jini an musu yankan rabo sai bige bigen kofar batdroom din d'aki a ke jitayi komai ya tsaya mata ahankali tayi kofar ban dakin tace'' waye aciki !"?
"mamy Dan Allah kar
ki kasheni na dena miki rashin kunyar wllh dan Allah kin kashe Fayyat da Khaldum !!!
"Khafulan bani na k'ashe suba dan Allah ka bude kaga yamin da kaske fa sun musu waye ya kashe su".
"Mamy kece kece da wuk'an da kika wasa d'azu kika kashe su bazan bude nima ki kashe niba".
Nasrim da gudu taju ya ta fita dakin Agrif nan ma me zata gani shima gaba daya an gama cakeshi da wuk'a juyawa tayi da gudu ikon Allah ne kawai ya kai ta part din su Kamal tana cewa ya Kamal sun mutu da gaske ne!!! dan Allah ya Kamal me yake faruwa Kamal da yake zaune a parlou da carbi hannu agaban sa tazube summemiya
a gigice yace " suwaye suka mutu jin k'aran Kamal yasa Humairah fitowa da sauri Kamal yace " yau me zamu gani Nasrim kashe San kikayi da kugu Humairah da Kamal suka fita direct bedroom din Agrif Kamal yayi kanin halin da yake yasa ya fasa wani gigitaccen k'ara yayi waje da gudu haka Humairah ma
Mai ai'kin Humairah ne suka sanar wa mutanen gidan
dan Humairah wuk'a ta dauko tana ta faman sumbatun itama sai ta kashe Nasrim tunda takashe mata Dan uwa itako Nasrim asume ma take bata masan me take ba duk masu ai'kin Humairah suke rike Humairah
gaba daya gida ya rikice
tun ba asan mutuwar su Fayyat ba mommy ce ta gano basu awajen tashi tayi ta shiga dakin fitowa tayi tana nuna d'akin da yatsa tana cewa
"ku shiga nan kuga".
Khafulan sai da yaji muryar su Abbaty ya bude kofar yana cewa" wllh mamy ce mamyn muce ta kashe su
kafin kace me har yan sanda sunzo Nasrim da take cikin wani hali suka dauka zasu saka amota mommy ta rik'e ta gem tana kuka "wllh ba Nasrim bace wannan wani mak'ircin ne aka kulla mana wllh Nasrim baza a iya kashe mijin ta da yaran ta ba" .
Hajja tace'' idan ba ita ba waye ba gashi Khafulan ya fada ba kuma jiya agaban kowa tace sai ta kashe daya acikin ukku tace rigiman duniya dame rai akeyi ".
cikin kuka me tsanani mommy tace "abin ya hau kan *FURRUCI TA NE*
Khafulan yace "wllh mommy itace da wannan kayan na jikin ta ta shigo ni ina batdroom zanfito na ganta tana kashe su har na mata video kashi nan ma dama papa yace duk abin da zatayi na mata video ".
yan sanda ne suka karbi wayan hannun Khafulan suka hada Nasrim suka fita da ita mommy tana kuka tace'' na sani duk mak'irci ne wallahi wallahi inde Ina raye kuma kudi suna magani a duniya Nasrim ko furzin ba zatayi ba ........
*Tofa masoya sai kunyi hakuri fa dama sunan litafin rikicin babban gida nasan pg yau zai ba k'anta ranku kamar yanda nima yau dag'er nake typing amma ya muka iya wannan shine jigon labarin*
*Dan Allah kuyi hakuri rashin yawan typing dalilin wani uzzu'a nagode sosai da comment din ku Allah yabar kauna*
Bj
S&R kayan Mata
Assalamu Alaikum shin Kuna da labarin S and R kayan mata, Kaya masu inganci da sauki daga sokoto Sai angwada akan San na kwarai, Muna da Gumba, Gumbar Aya, Gumbar nonon rakumi, Gumba aya, kwakwa da dabino, Gumbar mallaka, akwai kaska, ko kurma ne, Issasar mace, tsimin maqale mata, tsimin ridi, tsimin dabino, Dahuwar kaza, Dahuwar tantabaru 'yanshila da sauransu, Muna aika Kaya a duk inda mutum yake. Distance is not a barrier.
Wallahi duk macen da bata gyara kanta tana tare da ganin bacin rai gun mijinta, Hajiya ki cire komai kike ji ki gyara kanki, gyara shine mace, gyara gaskiya ne, mudai mun gyara Kuma mun gani. Akwai da yawa matan da kullum zakaji basu da matsala Sai ta miji da ya shiga ya kawo some ko 2 minutes basayi🙈🙈hajiya wallahi hada rashin gyara na Kara haddasa wannan matsalar ki Sayi Kaya kiyi amfani dasu ke da kanki Zaki bada labari .
07014149410 S and R kayan Mata Sai na jiku.
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*15*
Mommy bin motan take tana rusa kukan ita akwawo mata y'arta walahi Nasrim tafi k'arfin shiga motan Police tana binsu har kusan babban get tana faduwa tana tashi Barira da mainunau masu ai'kin ta ne suka rik'eta suna ta kuka mainunau tace ''dan Allah mommy kar ki bisu a haka ki bar Adamu yakai ki a mota Allah yana ji yana gani da k'er suke rike ta Allah sarki mommy sai sunbatu take tayi tayi da hausa tayi da turanci tayi da barbarci tayi da asalin yarenta na ibo Barira ce tafito da waya ta kira Dr Hafsa ta mata baya yanda zata iya
Har ambulances na asbitin yazo tafiya da gawar wakin dan ayi musu gwaji daga mutane gidan har ma'aikatan gidan bame ko bakin kuka gaba daya an hargitse suna gani aka dauki su Khafulan da Agrif aka fita dasu itako Ummu jitake ba awannan duniyar take ba gaba daya kwakwalwar ta takasa daukan abin
Hajja tace'' inna'lillahi wannan wacece iriyar musifa Allah ya tsaukar a gidan nan bana zaton ko a tashin duniya zamu shiga cikin irin wannan yanayin Abdulmajid me ka haifa mana irin zuciyar kafurai ko ashe kwara da Allah yakashe yara ukku maza da wannan dangin kafuran ta Haifa ashe ba al'kairi bane da sun rayu ba gashi k'anwar su mace ma tayi haka da suna nan da duk sun kashe mu
me yasa baki kashe iya yaran ki ba dan kirage mana mugun iri kika kashe Haruna da baiji ba bai gani ba nifa dama wllh ba wani gamsuwa nayi da wannan Fanna din ba kawai dan naga Abdulsamad yana sonta ne nabari ya shigo mana da ita cikin zuri'a mu...........
Kamal yace " Hajja ki dena fadan haka baki da wani hujjan da zaki daurawa Nasrim al'hakin kisan nan Nasrim bazata taba iya kisan kai ba musamman yaran ta idan ta kashe Agrif saboda kishi to yaran ta fa?".
"haba Baba na rashin Ima'ni mana bakasan marar Ima'ni kansa ma sai ya kashe ai irin kafurai ce ba bakaji abin da ita kafuran uwar ta tace ba wai ko duk dukiyar da ta tara zai k'are yarta Ko person bazatayi ba ni kuma na dau alk'awarin tare za a jera gawan su a kabari daya ita dasu Haruna ....
jin rin wannan kalaman na Hajja yasa Barira da maimuna suka janye mommy da bata ma cikin hankalin ta zuwa compound dinta suna ta tofa mata duk adduar da tazo bakin su har dr Hafsa tazo ita dawata k'anwar ta da yarinyar ta Amira k'awar su Nasrim ce matar Aliyu abokin Nasir
Allah mai iko dubi yanda cikin k'an'k'anin lokacin wannan ahalin sun koma kamar basu taba farin ciki a duniya ba tun ba afi 30 minutes da yin abin har abu yazaga duniya abun ka da gidan da dama ansan sa a duniya duk wani kafa na labaru da social
Media da duk wani kafafun yada labarai ba idda zance bai jeba duk inda kashiga a Media to hotunan su da bayanan sune duk da haka wai Kamal yasa masu gadi sun hana kowane yan jarida ahigowa yan uwa ma idan ba najikin 3A full bane sosai to ba kowa ne yake samu yashigo ba
*Dubai*
Aliyu ne yafara gani a
fece book cikin dabara yakira gida aka tabbatar masa da gaskiya ne cikin dabara ya kwace wayoyn Nasir ya kashe wayayoyin
ya samesa akwance zama yayi abakin gadon yace "yade my friend yanzu ba lokacin kwanciyar ka bane yau duk na ganka wani iri very slowly kode aikin ne".
juyi Nasir yayi yana yamutsa fuska yace " gabana yana faduwa kuma kasan me misani 1 pm naga kiran Khafulan ba adadi atunanin na sunyi abinda suka sabane shida Fayyat amma da na kwanta nake ta mafarkin yaran abin ba dadi kuma kasan wayan su games ne ba waya bane basu kai rike waya ba nasa anyi setting na yanda nida A A. kawai wayan zata iya k'ira da nayi mafarkin nayi da K'iran number A'A baya picking Khafulan kuma ba daman na kirashi saide shi ya kira na kira Kamal mommy da Abu da daddy duk bawanda yayi picking".
Aliyu yace'' inaga basu tashi bane amma ai kaima yanzu zakaje 9j din nagama shirya mana kaya har wayoyinka na kashe nabawa P'A danmu samu
mu shiryar dawuri jet na jiran mu tashi mutafi".
"Nigeria kuma kasan me kake cewa Ali".
Aliyu yace'' Eh zanyi surprise din Ameera ne yanzu muka gama waya da ita take cewa wai ni Inata maka bauta amma da zannemi alfarman lokaci daya baza ka iya min ba sai nace meye alfarman sai tace tana son ganina yanzu idan na isa kuma tana da matsayi shine ni kuma naci mata alwashin bani