Showing 90001 words to 93000 words out of 155717 words

Chapter 31 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

643

taga yayi part Mommy shine ta tsaya taga fitowar sa

dak'er daddy da masu gadi suka kwaci Kamal ko hannu baya iya d'agawa dan yadoku Sosai
Baba Nasuru cikin huci yafara cewa " kubani shi wllh kashe sa zanyi kashe sa zanyi marara amfani wawa mugu makashi zai kasheni yazo ya kasheni filo ya dan namin zai kasheni ni zai k'ashe ni zai k'ashe kubari na k'ashe sa nace mugune amma soko ko k'arfi bashida shi kubani shi".
Hajja tace'' to kisa kuma Kamal me Baba Nasuru yama kabiyo shi har d'akin da yake zaka kashesa kakan Nasuru nefa Amanan Abdulsamad nefa ikon Allah ni mariya Haruna ya tafi yabarni awani irin duniya..
sai ta fashe da kuma
Kamal cikin shak'iwar muryar yace'' ah ah nashigo ne fa zanyi masa mu kwan lafiya tunda mommy tace Baban tane naji ina son girmamashi shine nasamu yayi bacci kuma naga ya sauk'a akan fito zan gyara masa shine kawai ya hau kaina me wannan tsohon zai min da har zan nemi kashe sa".

aiko Hajja ta dena kukan tana Jan majina tace'' Babana ban da abinka ana irin wannan ganganci da mahaukacin ne yanzu fa da yakashe ka yakashe banza ba a Shari'a da mahaukacin
to tsaya tsaya ma meyaha naka kwanciya har karfe daya darabi kana yawo gidan mutane yo idan ba munafiki wayake yawon dare ko de gadin mu kake saboda tsaro ganin kashe kashen da ake agidan ran mutum ba abakin komai yake ba agidan yan ukku".

Mommy tamatsa kusa da Kamal sosai tace'' sorry my son amma de ba abin da yake damun ka ko".
"Eh mommy Ina lafiya".
"Ok dan Allah kayi hakuri Allah yakiyaye gaba
dama yanzu doctor din sa yakirani yake cemin wai gobe za afita dashi abin yaban mamaki dazu mukayi waya yace ba komai amma yanzu wai za afita dashi nace zan nemi me kai shi yace ah ah shi zai kula dashi jirgin asuba zasubi".
Mama tace'' mommy amma bai dace abawa doctor kawa yatafi da Shiba sai kace marar gata wacce k'asane za akai shi ma ".?
Mommy tace'' wllh ban sani ba".
Hajja tace'' to de Allah yabashi lafiya ya fada mana inda danginsa suke musan asalin Halima ita wancan k'edarar ta Lagos kuma yau she zakuje mata ai ni wannan abin kunyar har Ina ni Maryama ce da hada jini da k'edaraye Haruna ka hadani da aiki".
Ta k'arashe maganan tana ficewa tare ta toshe baki tana rufe hamman da takeyi

Daddy yace'' Dr Fanna muma a goben zamu wuce da Abdulrahaman JIDDA zamu tafi da Aisha da Abbaty yayi magana yanayin gaba Mama tace'' gaskiya alk'ali ba inda zani y'artawa tana cikin wannan hali ankusa zaman kotu na bari na tafi Ina ai bazai yuwu ba".
Daddy zuyowa yayi Yana kallon ta yace'' ba jimawa zamuyi ba bai fi 2 days ba zamu zo saboda cese din".
Mama da daddy suka fita ita ma
Humairah ta kama hannun Kamal tana cewa " kai me yakawo ka ai da kashe kan yayi da ya kashe banza za afake da mahaukaci dangin makasa kawai Allah sai ya isar mana jinin ya Haruna bazai tafi abanza ba sai an kashe Nasrim ko ajikin gol aka sassak'o ta".

Kamal yace"Humairah na gaya miki gaskiya zamu iya samun matsala idan kika cigaba da fadin wannan kalaman naki shifa Shari'a sabanin hankaline wai Nasrim da kikafi kowa sanin ta kike gayawa irin wannan Magan ganun".
Har suka fita mommy ta sauk'e ajiyar zuciya ta kama hannun Baba Nasuru ta kwantar da shi taja blanket ta rufesa ta tofa addua a kowacce kusurruwa na d'aki tafita Taja masa kofan
A parlou ta zauna tayi tagumi tana tuno irin matsin rayuwar da suke cikin duk tunanin da tayi yana tsayawa ne akan Nasir ya aikata duk wannan ta asan dan ya tsani Nasrim tunda har zai iya mata fyade ranan auren ta a daren tana farko kuma ya hana mijin sake kusan tar ta to meye ma bazai yi ba tunda dukiyar ta yake hari
girgiza kai tayi afili tace'' why why Muhammad Nasir me zakayi da abin duniya kaidin d'anane jinina d'aya nake daukar ka da Nasrim meyasa kayi kisan kai me nayi maka".
cikin kuka da yazame mata abinci da sha duk Wanda yasan mommy ada a yanzu idan yagan ta dole ya tausaya mata gaba daya a birkice take tama rasa meyake damun ta dafe k'irjin ta dayake mata matsanancin ciwo tayi tana fadin inna'lillahi

atare suka fito daga wankan nasa kayan tafara daukowa ta bashi yafara sawa ita kuma ta juya tana kallon cikin wodrop din da alaman akwai abinda take dubawa har yagama saka kayan ya k'arasa mirror Yana shafa Mai har ya gama yajuya yace "ai kin kasa zaban wanda zaki sane kome dare yayi bacci nakeji".
juyowa Humairah tayi tace'' kasan me my money wllh sleeping dress dina wanda ya Agrif ya kawo mana nida Izza da Nasrim a zuwan sa na k'arshe shi nake ta nema ban gani ba Wanda de Nasrim ta kashe su ajikin ta".
cikin basarwa Kamal yace'' ok kina da irin sa kenan kema ".
"wane irin tambaya ne wanna Kamal da akwai wani kaya da Nasrim take dashi ni banida shi naga idan kaine katashi sayo mana tare kake sayowa haka ya Agrif tun muna yara kata ba ganin an ban ban tamu da wani Abu ne? ".
"haka amma ai kaman sleeping dress in naga wanda yamin ai ina iya sayo miki musamman idan na kunya ne sosai ko".
Humairah tace'' Eh amma ina dashi nawan naraa shi".

kai my heart kisa wani mana dolene sai shi
ko kuma ya b'ata awayen wanki ne dan nima Ina neman wasu kayan Ina rasawa".
ajiyar zuciya Humairah ta sauk'e tace'' ah ah bana tunanin haka dan gaskiya ni ban taba sa shiba ma Kai ban fitar shi a ledan saba ma gaskiya balle yashiga kayan wanki
sannan akwai wani shijabi na marroon color wanda shima de irin me nikaf din wanda shima dashi Nasrim tayi kisan gaskiya ina son sa mommy ce takawo mana a saudia bana ganin sa shima kuma nasa sade amma ban ma sa acikin kayan wanki ba bazan manta randa na sakashi ba zamu Kai kayan sa rana na ya Abbaty na fara sa shi ina zuwa anan na rataya kuma kasan washe garin ranan Wednesday abin ya faru sai takalmin da yake k'afan Nasrim a video din da tayi kisan bazan manta ba Nasrim tayi kyauta da nata ko sakawa batayi ba tabawa Nabila ina na Izza kuma bak'i ne namu yellow to abin yana daure min kai".
Kamal k'an k'an ta Ido yayi yana kallon Humairah yace" to me hakan yake nufi kenan".?

Humairah ta sake jefa idon ta cikin nasa tace'' meko kawai de neman kayan nake daga shijab din har takalmin da rigan ban ganshi ba".
tsaki yaja yace "yanzu Humairah har kedin ce kike neman kayan da yayi kusan shekara kituna ko kin bawa wani de dan mutur su Agrif mafa wata shida kin manta ne dare yayi bacci nake ji idan kuma baki da niyar kwanciya sai da safe yayi magana yana hayewa kan bed din yaja wutan gefin sa ya kashe yaja blanket yana sake jan tsaki
gyad'a kai Hummee tayi ta dauki wani rigan bacci tasa ta haye gadon


Da asuba doctor yazo yatafi da Baba Nasuru shima daddy shida Abbaty suka tafi asbiti dan wucewa da Abu India

" Kamal kana nufin kayan sun bata kuma da jinin ajikin sa ya akayi hakan ta faru dama tun ranan ba nace kafita da kayan a gidan ba wannan abin fa ba karamin abu bane idan kayi wasa wllh zamu iya kwana ciki fa yanzu dama daga takalmin har rigan da shijab din da safan hannu da nabaka ka fita dasu aranan a cikin daki kaje ka ajiyesu inna'lillahi Kamal ka b'ata komai".
Kamal dafa kan sa yayi yana feso da iska me hucin zafi ta cikin bakin sa yace'' wllh Mama ban samu dama ba aranan kinsan yanda gidan nan ya hargitse shine naje na daga katifa nasaka a k'asan bed shine na manta gaba daya yanzu kuma na duba ban gan shiba".
Zama Mama tayi ta dafe kanta tace'' shikenan dama binciken da Humairah take yawan yi maka akan sane tasani Humairah tasan komai amatsayin ta na cikekkiyar lawyer wannan kayan kadai ya isa hujji awajenta Kamal yanzu ya za ayi gashi saura 6 days ayi zaman kotun ".
azabure ya tashi yace'' Mama yau Humairah zata mutu baza ta kwana da rai ba".
zai fita Mama ta kamo hannun sa
cikin tashin hankali tace'' Kamal kar kaje ka sake tafka kuskure bamu sani ba ko Humairah ta sanar wa wani kaga idan ka kasheta kamar ka kashe macijine ba ayanke kan ba dan haka yanzu abin yi dauke Humairah za musa ayi akaita wani gu abata azaba ta fadi wanda ta fad'awa sai musan abin yi amma bayan ta fad'a mana sai mukashe ta
ga mata dayawa agari kazabi zabin ranka ba wanan matar cushe ba".
shiru yayi ya gamsu da abin Mama tace'' masa
Mama tace'' Kamal har yanzu ka kasa gane inda Barira take ko wllh bamu kadai bane muke ai ki acikin gidan nan tunda kaga bamu muka saka abawa Hajja paison ba mahaukaciyar tsohuwar nan bata gabana yanzu abar ta tun da tana mana aiki ai ita take k'ara hura wutan Shari'a Nasrim kaga ai tana mana temako yanzu ga wannan shege doctor din Baban Nasuru yafita dashi kuma wai yaki fadan k'asan ma da zai kai
nifa yanzu abin duk ya dagole min".
Kamal zanyi magana yaji shigowar message cikin wayan sa
yana gani azabure ya mek'e tsaye yace'' what!!!!!!!!!?
A take wani irin gumi yafara karyo masa Karatun ma yakasa
Mama ce ta k'arba ta fara karantawa kamar haka
_slm ya abin kauna na dan Allah Ina neman izinin tafiya amatsayin ka na mijina amma fa ba zaka san inda zan jeba kasan duniya abin tsoro ne Ina gama sai ranan Wednesday zan zo da misalin 11 na safe mu hadu high court I love with all my heart by_

Mama tace'' shikenan Kamal komai ya tsaya asirin mu zai tonu".
" Ah ah Mama hakan bazai taba faruwa ba basu da wani hujjan daura mana ba agan mu Ido da Ido ba yanzu fa nabar Humairah a part din mu Ina zuwa".
Yayi magana yana shirin ficewa Mama tace'' ah ah Habubakar dawo bazaka samu Humairah ba mu samu mafita yanzu ni na yarda zan dauki duk wannan al'hakin kisan da sharrin a kaina kai karayu a hukunta ni".

"Ah ah Mama kwara mu gudu zan kwashe duk kudin mommy na account nata dana Nasir ya shihemu rayuwa zamu gudu k'asar maggep Ina da account ancan kuma da gida da takardan shedan zama a k'asar na har abadan idan muka je zamu shafa assets a fuskan mu kinga daga nan musa a canza mana fuska muyi zaman mu cikin kwanciyar hankalin shi kuma Abdul mu barwa daddy zai dinga tunowa dani".
Mama tace'' good hakan yayi ".
ka ahiya mana tafiyar kawai amma kasa duk company da yake waje akasuwa mu saida dan mu k'ara guzuri".


Nasir tun fitar sa a gida yake yawo idan yagaji ya huta idan lokacin sallah yayi yasamu masallaci yayi har dare a masallaci cin da yayi sallah isha'a anan ya kwana washe gari ma haka ya dinga yawo sa arsa daya shi bame daura hotuna bane a media bai fiye tsayawa yayi fira da yan jarida ba hakan yasa ba wanda yagane shi dan wani ne
saide mutane suna yawan kallon shi har Yana tsarguwa nan ko tsaban kyan shin da hutun suke gani dan Nasir irin farin igbo din nanne me tar kamar balerabe
sai gashi awani anguwar da kamar ba akano yake ba anguwar masu k'aramin k'arfine sosai ishir ruwa ya addabe sa yunwa kam yaji ya cinye shi yana cikin haka yaga wata yarinya tana buga tuk'a tuk'a ruwa Yana fitowa ahankali ya karasa inda take ya mata alama da zai Sha ruwan atunanin sa zaifi wannan ruwan na buta daya ke alwala
dashi wani irin rugawa da gudu yarinyar tayi tabar ruwan da bokatin awajen karasawa yayi yasa hannu biyu cikin bokatin ya ibi ruwan ya kai bakin sa ruwan ya na taba harshen sa yayi wani irin dawo da ruwan har yana zuwa masa ta hanci d'an d'anon bakin sa bai taba bashi abu marar dad'i irin wannan ba zubawa ruwan ido yayi azuciya sa yace toko magani ne wannan baruwa bane
cigaba da tafiya yafara har magaruba yayi tsayawa tsallah yayi har akayi isha'a Qu'rani ya dauka yana karatu har yafara jin garin shiru yunwa sosai ya bara addabar kwara ruwa awajen alwala ya rintse Ido yadan gurba amma shima Yana shiga cikin sa ya amo dadi kaman misalin 9 pm yaji anata hayani ya sai kuma yaji ana cewa wllh layin nan yayi nan yayi sai kuma yaji ance gawani mutum a masallaci sai suka shigo suna cewa shine shene wllh shine daga nan kawai yaji an shiga dukan sa ta ko ina tun yana fashimtar me ake har ya suma
bude idon sa yayi yasamu a gadon asbiti yan sanda akansa ahanhali yamutsa hannu sa da da yake ji kamar ba ajikin sa ba wani k'ara yasa tabbas hannu a karye yake haka k'afar sa daya doctor din ne ya k'araso yace "sorry kabar motsa hannu za ka iya samun matsala kwanan ka biyu anan duka aka maka awani anguwa dalilin kayiwa wata rayanya y'ar shekara 12 fyade kuma kafin wannan ancirewa wata yarinyar Ido daya yarinyar da a ka cirewa Ido tana nan hospital din mun kawota ta guka ta bada tabbacin Kaine ka cire mata ido San nan da yammacin randa kayi fyaden ka Kai wa wata yarinya Maryam hari abakin famfo Allah bayyi ba ta gudu ta barma bokatin itama Maryam tazo ta bada shedan Kai ka Kai Mata wannan harin dan gaka muna son jin sunan ka da inda zamu samu family ka".

"cikin dak'iya yace bani da family ayanke min duk hukuncin da yadace dani.............




*To masoya Ina Humairah taje*

*Mosoyi kuyi hakuri wllh yau ba samu daman yayin typing me yawa ba*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*


```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*





*21*





*NASIR*

Police din yace'' ok kama amsa lefin ka kenan".?

gyada kansa yayi alaman eh
"Ok family kafa Ina zamu same su".
ajiyar zuciya ya sauk'e ahankali yana son ya shafa idon sa da yakeji kamar ba a jikin sa yake ba baya gani dashi sake gwale daya idon yayi Yana kallon doctor din da police din yace''
I don't have any family ".
Palice din yace''please da ganin ka Kai ba k'aramin mutum bane daga yanda jikin ka ya nuna kaidin wani ne kafada mana family din ka suzo wllh ko cell baza kaje ba za akashe cese din anan iya ka Wanda kacirewa Ido su karbi diyan idon su suma na raipping masu k'aramin k'arfine dan wani abu zamu basu arufe cese din dan bakayi kala da cell ba
Kuma idan ka sake report din yaje station to tabbas oga zai turaku court kuma kasan abin da zai biyo baya".
cikin k'osawa da maganan ya ya mutsa fuska tare da cizon lips yaja daya idon ya rude daya kuma a kumbure sosai
police ganin de Nasir bashida niyar magana yayi shiru


*Prison*


ayau Barrister Zahra ta samu daman ganin Nasrim

Nasrim tace
"Zahra nace miki bana buk'atan komai hukuncin kisa shi nake jira idan aka barni a duniyar amfanin me zanyi d'adin mai zanji zan rayu cikin bak'i cikin da k'unci bugu da gari cikin zargi tunda tabbas wasu idan sun yarda banyi ba wasu bazasu yarda ba so mutuwa tafiye min sauki".

Zahra tace'' please Nasy tare muka tashi dake nasan abinda zaki aikata da Wanda bazakiyi ba Nasrim baki kashe Agrif dasu Khaldum ba amma kinason daukawa kanki al'hakin kisan yanzu kinyiwa Agrif adalci kenan duk wani son da kike i'kirarin kina yiwa Haruna wllh ya tashi a banza inde baki tsaya kin gano waya kashe shi ba kinci amanan shi'
jajircewa wajen gano waye yayi wannan aikin shine zai sa Agrif yaji dad'i yayi alfari dake Nasrim ki bamu dama mu gano waye yayi aikinnan
nima sai jiya na tsaya na k'arewa video din kallon a tsinake ba ke bace Wanda yayi kisan bai kai ki tsawon ba yafiki jiki muna da huja da dalilai da zaki kubuta ki bamu dama bawai dan ki cigaba da rayuwa kadai ba a a dan ki gano waye mak'iyin ki ko kinsan Mommy tana cikin matsala Sosai gidan fa kowa yana zargin dan uwan sa kinga kece zaki warware ta hanyan bamu labarin abin da yafaru ko kinsan Mommy da Nasir sun rabu kaca kace ba shiri ya ajiye komai ya tafi"
daganan ha kwashe komai ta fad'a mata amma Banda na yaran na Nasir ne
da daura da kinga kece zaki temaki gidan nan Nasrim bani da dangan taka daku amma acikin gidan three brother na tashi naga kaina Allah yagani bani da wasu dangin da yawuceku kowa yana cikin damuwa Nasrim kece kadai zaki fitar mu aduhun da muke ciki please Halima".

numfashi Nasrim tayi tace'' amma mommy da bata zargi d'an taba Nasir yana son Agrif musamman su Fayyat bazai kashe su ba duk da bamu so da shak'uwa tsakani na dashi bazan iya zargin sa da haka ba sai idan ko a ma'aikatan gidan wani yake son ganin bayan mu".

Zahra tace'' yauwa to Nasrim hadin kan ki shi zai fitar mu cikin wannan ko kadan ki bamu wani haske".

ajiyar zuciya Nasrim ta sauk'e tace'' Zahra ko banyi ba nayi ne FURUCINA NE tabbas nayi FURUCIN sai na kashe shi amma wllh adare Haruna ya sameni da wuk'an da na masa barazana a hannun sa yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login