Showing 18001 words to 21000 words out of 155717 words

Chapter 7 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

627

mommy ta k'arasa gurin ta ce "ya haka? Son kashe k'anwar taka za ka yi?".
mik'ewa ya yi ba alaman tsoro ko firgici idonsa cikin nata ya ce ''Mommy so nake na kashe ta kowa ya huta tunda dalilinta Abbana ya rasu".
Mommy ƙarasowa ta yi inda yake ta kama hannunsa ta zaunar da shi bakin gadon, ai ko da sauri ya mik'e yana yamusa fuska ya ce "Mommy ba na son ki sake zaunar da ni a kan bed din nan tunda kika kwatar da yarinyar a kai".

Mommy ba ta ce komai ba ta zaunar da shi a kan jujeran 2setter ta kira Harira me aikinta ta ce tafita da Nasrim bayan ta dauketa sun fita, da kusan mintuna 3 tana kallon sa ta nisa ta ce
''Nasir ka yarda da ƙaddara ba Nasrim ba ce ta kashe Abba, Allahn da ya halicce shi shi ya dauk'e shi dan bawai dan zuwan Nasrim kaɗai ba ne ka ga kafin Nasrim akwai k'addaran aure da ya shiga tsakanina da daddynku ba dan Allah ya sauk'e Abbanku ba da babu yanda za a yi hakan ta faru Nasrim yarinya ce ita, ba ta ma san kanta ba yanzu dan Allah ko ba ka dauki Nasrim a masayin k'anwa ba kar ka cutar da ita sabo da".
"Mommy meyasa ba kyason na cuceta".?
tace''saboda ina sonta".
"Mommy ni kindena sona".
"haba my Son ya zan dena sonka wallahi ko da irin Nasrim goma na haifa ba su isa na musu rabin son da nake maka ba".
"To mommy ba na son ki sake furta kina son ta ni kawai za ki ci gaba da so".

Dariya ta yi ta kai masa kiss a kumatu ta san abin nasa har da kishi da kuma ƙuruciya
"In sha Allah ba zan sake cewa ina son ta ba, kai zan ci gaba da cewa I love you my beautiful son."
murmushi yayi wanda ya lotsa duk kumatunsa
Ya ce" I love you too my sweet mom".
"Thanks my dear Son kayi alk'awarin ba za ka cutar da Nasrim ba ko".
Ya ce "E, amma ni ma ina da sharuɗɗa: Na farko ya zamana duk lokacin da zan shigo gaida ki kar na gan ta, kin san lokacin tashina tun kafin na zo ki kira masu aiki ki basu kar na shiko na ganta,
Na biyu idan an san ina gidan a daina barin ta a main parlour ko hanyan da zan gan ta in dai ban ganta ba ba zan cuce ta ba, ba na son ganinta".

Shiru mommy ta yi ganin da ta yi kamar kalamansa sun yi tsauri, amma dai farincikinsa shi ne kwanciyar hankalita dan ba ta son ganin sa cikin damuwa.
Sai ta fara magana cikin sanyi murya
tana cewa "In sha Allah zan kiyaye in dai hakan zai sanya ka farinciki dan alk'awarin da na daukarwa mahaifiyarka kenan za ka rayu cikin farinciki in sha Allah".
"Mafaifiya ta kuma?

Mommy ta ce'' Eh Nasir".
Daga nan ta kwashe komai ta fada masa ba ita ta haife shi ba, ta cigaba da cewa
"Ka k'addaran aure na da Abdulsamad shi yakashe ma haifiyar ka Halima saboda rabon yara uku da suka rasu kamar yanda k'addaran auren daddy ya kashe Abba duk da dama ina da niyar gaya maka ba ni na haife ka ba, ko dan ka yi wa mahaifiyarka Halima addu'a saboda ba ta da kowa sai kai ɗin nan, amma ba yanzu na yi niyar gaya maka ba sai ka kai ko da shekara 20 ne kafin ka sani yau de na gaya maka ko wacece Haliman da kullum nake cewa ka mata addua amma yanayin halinka ya sa na gaya maka yanzu daga yau ka yi wa Halima addua a matsayin mahaifiyarka ita da Abban ka".
Cikin mamaki yake binta da kallon
sai da ta gama ya ce
"Mommy idan ke ba mommy na ba ce me ya sa muke kama sosai dake? ko shi ya sa Hajja kullum take cewa ban gado halin Halima da Abba ba, ita ce hotonta a main parlourn mu da na Hajja ko?"
Ya jero mata duk waɗannan tambayoyin a jere

"Nasir ni kaina ina mamakin kaminmu da kai sai dai ina tunanin tabbas ba za mu rasa dangantaka da Halima ba, shiyasa kullum addua ta Allah Ya ba wa Baban Halima Baba Nasuru lafiya shi zai warware mana komai dan nima ka ga ban san dangin ubana ba, ba zayyi yuwu a ce komai namu iri daya da kai ba musamman idan anyi duba da zanen barebari da yake fuskana irin sane a fuskan Baba Nasuru".

"Mommy Allah yaji kan Mama kuma na ji ina son Baba Nasuru".

"Ameen my Son nima na so Halima ita ma ta soni kuma ban san me yasa nake son Baba Nasuru ba duk da har yanzu ba wani magana yake sosai ba".

Haka dai suka cigaba da hira kamar ta samu wani babba.

Daddy da yake tsaye ta window tun fakon shigowar Nasir yana kallon duk abin da yafaru ya jij-jiga kai ya bar wajen mommy ta ce
"Son zan shiga wanka ka san yau zan fara fita wajen aikitun haifuwar Nasrim".

"Ok Mom zan je wajen Hajja kuma zan yi hadda anjima".

"Allah ya timaki d'ana".

Mommy ta gama shirinta tsaf daddy ya shigo kallon sa tayi tace''Ranka ya dade yau ba shari'a ne ban ga kana shiri ba"?
"Ai week ɗin nan ma gabadaya ba ni da wani aiki amma an jima zan fita office".
k'arasowa ta yi inda yake ta ce
"Amma kamar kana cikin damuwa ko".

" E, amma damuwar tawa ba ta da wani amfani a wajenki".
Cikin mamaki ta ce
'' Because of what"?
kallon ta ya yi tare da juya fuskarsa wani gefen yana cewa
"Saboda ba damuwar Nasir ba ne Dr! Na ga duk abin da kuka yi da shi yanzu har Nasir abin ya kai ya yi yinkurin kashe min yarinya baki dauki abun a bakin komai ba".
Cikin k'osawa mommy ta ce
"Amma alk'ali ai ka ga na yi masa magana ko".

Cikin b'acin rai ya ce
"wane magana kika masa idan ke idonki ya rufe da son Nasir ni nawa a bude yake, ko baki fashimci akwai barazana a FURRUCINsa ba? Cewa fa ya yi duk sanda zai ganki kar ya ganki da ita kuma kar ya ganta a babban falo ko hanyar da zai wuce kar a bi da ita wai hakan ne k'adai zai sa ya kasa cutar da ita, ya kafa miki sharud'a kika amsa kin karba kin yi daidai kenan? ko wannan ba damuwa ba ce a gabana fa aka furta 'yar'uwar y'ata tana cikin wani hali Dr har ga Allah ina son NASURUDDEEN din amma FURRUCINSA ya yi ts'auri a kan Nasrim, ba zan iya kwatanta miki yanda nake jin NASRIM a zuciyata ba, ko Kamal shi ne babba ba na jin sa kamar ita ba zan iya jurewa ba idan wani abu ya same ta".

"To dan Allah alk'ali ka yi hakuri ai yaro ne zai dena".
Shiru ya yi yana sauk'e a jiyar zuciya yace" Allah Ya sa, Ya shirya shi. A dawo lafiya".
Cikin shagwaba ta ce
"Haba Abban Nasrim yau ba rakiya"?
Jinjina kai ya yi yana jan bargo yace I love you my wife sai kin dawo".
taku ta fara a hankali da niyar ta k'arasa inda yake ta yi masa kissing

Cikin wata irin murya ya ce "Allah kika kuskure kika k'araso nan bake ba tafiyar nan dan zan b'ata shiri".
Cak ta tsaya tana masa shagwaba
yinkurin tashi ya yi da gudu tayi hanyar fita si ya ce "Da ki tsaya mana ki ga illar tsokana". Sai da ta kai kofa ha hura masa kiss din a hannu ta yi saurin fita dan tasan in ya kamata bakyau.


********


Bayan kwana biyu haka mommy ta zaunar da Maimunatu da Harira tana ce da su
"kuna ji na ko? Nasir ba ya son ganin k'ananan yara jarirai dan haka nake son ku dinga boye Nasrim idan kun gan shi kar ku yarda ya ganta a tak'aice dai ni ma ba na son ku bari ya gan ta, sannan ina neman alfarmarku wannan ya zama sirri tsakanina da ku ka da ku bari wasu su gane ko da Hajja ce".

Maimunatu tace'' in sha Allah ba mai ji wannan maganar"
Ita ma Harira haka ta faɗa wa mommy.

Mommy ta ce
"Yawwa na gode da yanda kuke kiyaye dukkan dokokina ina jin dadin zama da ku sannan ke Maimunatu iyayen Garba sunje garin ku an gama komai sai saka ranan aure kuma na ji dadin yanda suka ce ba sai kin je ba sun bar komai a hannuna su za su zo nan ayi shiyasa na sa a muku gini a nan kusa da part dina ta baya in sha Allah kafin lokacin za a gama ginin".

Cikin kunya myaimunatu ta yi godiya
haka maaikatan nan sukaci gaba da ɓoye Nasrim duk ko yaran da aka samu akasi Agrif ya nace ya dauketa ya ganta to duka da minsini de sai ta sha su a wajen Nasir, Agrif ko ya ce bai yarda ba dan batuwa da Agrif a kanta dan shi duk abin da Nasir yake masa ba ya damunsa amma muddin ya taba masa Nasrim to za suyi fada a ranan ko abinci ba za su ci tare ba, zai ce yayi jagolgolo ta k'azamar yarinya sosai Agrif yake son Nasrim ita ma Nasrim tunda tayi wayo take son sa, amma ba ta son ko da ganin Nasir tana ganin sa za ta sa kuka kaman za ta shide yau ba Harira ta barta a main parlour ta tafi hado mata madaran ta, ta rarrafa ta fito compound shi kuma Nasir yana zaune ya juya bayansa da litafi a hannunsa dan karatu yake tuk'uru sun kusa zana jarabawan fita daga primary ya ji an rike masa k'afa yana juyowa yayi arba da ita bai gane taba dayake baya tsayawa ya kalli fuskanta sosai murmushi yasakar mata ita ko tana d'agawa ta kalleshi ai k'o ta fashe da wani irin kuka da sauri yasa hannu ya dauketa yana cewa am sorry beautiful baby girl". yana kallon ta yana shafa kwantaccen suman kanta yana murmushi ya sake cewa komai naki me kyau ne baby".
ita ko sai wani irin kuka take tana neman sauk'a ajikin sa,
Agrif da yake baya shima yana nasa karatun ya ji kukan Nasrim yayi yawa ya juya da niyar ya shiga parlour ya ganta a hannan wanda bai taba zato ba
Nasir yace ''Agrif kaga wata beautiful baby girls gashinta mai kyau komai nata me kyau dan Allah yar wacece mommy tayi bak'uwa ne"?

Wani irin dariya Agrif yasa yana tafa hannu ya ce "Ashe ka san mai kyau ce ashe za ka dauke ta, ba kai ka ce ko hanyar da ta bi ka gani ba zaka sake bi ba? Ashe duk k'arya ne''.
Ya k'arashe maganan yana cigaba da dariya, sai alokacin Nasir ya tuno da wacece a hankali ya sake ta ta yi kasa da sauri Agrif ya yi niyar ɗaukota amma ina! Har ta yi k'asa tif kafin Agrif ya sunkuya ya d'agota har Nasir ya sa kafarsa ya take yatsunta biyu yana wani irin murzawa da takalminsa sawun ciki Agrif yayi-yayi ya d'aga kafar ya kasa ga Nasrim kukan ma ta daina tsabar azaba sai wani irin d'aga ido sama take kamar za ta sume, shiko Nasir sai da yaji k'aran k'ashin alaman yatsun sun karye ya d'aga k'afar a lokacin Harira ta fito wani irin kuka Harira tasa tayi kan Nasrim ta d'agota har tasuma shiko Agrif neman abin da zai bugawa Nasir ya illata shi kawai yake nema jiyake ko bindiga ya samu zai iya harbin sa wani gilas da a kacire a window Hajja ya hango zaran gilas din yayi da wani irin gudu yayi kan Nasir da yajuya baya yana ta fitar da numfashi Baba Yakubu da sauran masu aiki da gudu sukayi kansu amma kafin su k'araso Agrif yasamu nasaran bugawa Nasir a kai
sai de Allah bai sa yai Koda k'ozani ba dan gilas din ba me saurin bashewa bane saide yadanji ciwo juyowa yayi yana kallon Agrif din yace"ni ka bugawa wannan dan wannan banzar ko".
"Eh na buga kuma Wllh bai isaba sai na sake rama mata kuma Nasrim ba banza bace gaka babban banza". yasake yin kansa za k'arfi yanda idan ya buga masa ko bai faahe ba zai illata shi dak'er aka shiga tsakanin su
shiko Nasir ji yayi ya dake tsanan Nasrim dan ba a taba zagin sa haka ba sai yau a kanta har buga masa gilas din ma bai masa zafima irin zagin da Agrif din yake masa yafi masa ciwo da sauri ya sake zaran Nasrim ahannu Harira zai bugata daidai lokacin motar daddy tayi parking daddy bai jira an bude ba yayi sauri ya fito da sauri yayi saurin k'arasawa inda suke Kabiru yana kokarin karban Nasrim a hannun Nasir amma ya hana wani irin mari daddy ya dauke shi dashi zai sake k'aramasa yaji an rike hannu sa yana juyowa yaga Hajja ce cikin b'acin rai,
Ta ce'' Abdulmajid kashe min shi za ka yi a kan wannan yar taka wadda dalilinta na rasa ubansa, tun daga yanzu Nasir zai fara fuskantan maraici akan y'arka za ka dake sa? Yaushe Abdulsamad ya mutu da har za ka fara manta shi waye ka rufe ido har kana dukar masa tilon jininsa ".?
Ta k'arashe maganan tana sakin kuka
Daddy ma cikin b'acin rai Hajja ba ta taɓa ganin sa da shi ba ya ce
"Haba! Hajja ba ki ga laifin da yayi ba inda ya jefar ta fa?"
Kafin Hajja ta yi magana Nasir ya ce
" Dan bani da ABBA ba me rama ni shi ne za ka dake ni akan y'arka kuma wllh sai na rama a kanta kashe ta zan yi wllh sai na kashe ta".?
Hajja ta ce "A'a daina wannan FURUCIN, zo mu je na duba ko ka ji ciwo Allah zai saka maka, ai maraici ba siya ka yi ba marici yana kan d'an kowa maraici ba hauka ba ne soyyayata kaɗai ta ishe ka, ni ina son ka kai da ya Abdulsamad ya bar min, kai nake gani a madadinsa ba zan yarda a cutar min kai ba a kan wata banza ba".
Ta idasa maganar haɗe da jan shi suka yi gaba.

Mommy da take tsaye ranta idan ya yi dubu ya ɓaci cikin b'acin rai ta ce
" Yanzu Alk'ali abin har ya kai haka har ta kai ka d'aga hannun ka daura akan Nasir da sunan duka kuma a gaban maaikatansa za ka k'ask'antamin shi ?".
shi ma Abba cikin nasa b'acin ran ya ce "Na daka Dr Fanna ko kin fini iko a kansa ne kina ganin kamar kin fi kowa iko a kansa ko, Dr Fanna na fa gaji da irin wannan halin! Ke wacce irin uwa ce? Idan Nasir amana Halima da Abdulsamad suka bar miki ita Nasrim amana ce kai tsaye daga wajen Allah kina shi Ya ba ki kuma amana Ya ba ki kika rik'e amanan wani bawa amma kin banzatar da amanan Allah Sam.... ".

Dakatar da shi mommy ta yi da cewa "ka gaji da irin wannan halin nawa kace ko ? Na ji ka gaji za ka iya daukar matakin da ka ga za ka iya amma inde akan Nasir ne Wllh baka isa ka ce min ba ni da iko a kansa ba ko ka fi ni iko da shi ba".
har zayyi magana yaga yanda yatsan Nasrim ya kunbura sai yanzu yakula da ashe daya yasan ma rawa yake alaman ya karye cikin wani irin razana yace "Dr Fanna ya karyata fa".
"E, na gani ya karyata naka ka sani ai, yanzu ka san halin da shi Nasir yake ciki".
Cikin sanyin murya daddy ya ce "Dr ki zo mu je a kai ta asbiti ba lokacin wannan maganan ki duba halin da y'ar nan take ciki."
Ya k'arashe maganan yana karban Nasrim a hannun Harira
"kai me zai hana ka kaita".
tana gama fadan haka tayi part din Hajja
wani irin hawaye ne ya surtowa daddy yana na kallon Nasrim da sai yanzu ya gane a sume take ga yatsa yana rawa. Ya rasa ma ya zai yi Habu drive ya ce "Alhaji mu je asbitin" Shiga yayi motar kafin driver ya ja yana cewa Baba Yakubu dan Allah
"Yakubu ka cewa Aisha ta same ni a asbiti yanzu".


********

Mommy tana cikin lallashi ta ce'' my Son ka ji mata ciwo fa sosai amma na san Abu ma sai ya yi maka fad'an dan haka idan ya tambaye ka ka ce kai ba ka sani ba ka taka kar kace wa Abunku da gan-gan ka karya ta ka ji".
cikin dafe kansa da yake jin yana masa ciwon ya ce
"No Mom ba zanyi k'arya ba ina sane na taka ta ai dama na ce kar na sake ganin ta kuma dan raini har fa kamani tayi wllh na zaci watace har daukan ta fa na yi Allah ba zanyi k'arya ba da gangan na taka ta shi ma Abun haka zan ce masa".
Mommy tace'' wannan ba k'arya bane kare kai ne nasan Abu zai maka fada ko ya dake ka kamar yanda daddy ya yi".
Cikin kawar da maganan yace mommy kaina ciwo yake min Agrif ya buga min glass Dad ya mare ni''.
"Ok sorry my son mu je hospital ko".
ya ce "Na mommy ba sai mun je ba ki ban magani kawai".
Mommy tace''ok ka sha sai ka kwanta ni kuma zanje na dubo Nasrim an tafi da ita asbiti"?
turo baki yayi yace " wllh mommy ba za ki ba ai a kanta aka dake ni".
" OK my Son ba za ni ba".
Hajja da take sauk'owa daga steps ta tabe baki tace'' au dan ita yar gata ce har asbiti aka kaita daga dan takawar ummmm gata ni Lami yar Habubakar amana yayi k'aranci har agabana Abdulmajid zai nuna bambanci ga d'an Abdulsamad dan Adam kenan mai manta alkairi".
Ummu da take kallon karfin halin su ta kasa jurewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login