Showing 123001 words to 126000 words out of 155717 words

Chapter 42 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

663

ƴarsa da sauri zai bani amma kai mutum ne marar zulama mai nuna so tsakani da ALLAH bazan iya barin daman nan ta wuceni ba daman mallakan zuri'ar ka ba Sadiya ba ko Zurfa'u ka bani zanyi renan ta tazama matata wataran".

dariya Malam yayi yace " to ga Zurfa'u din amma Sadiya da ka bada dama kunsa santa da three brother da ina ga ka bada ita ga jinin ka Adamu Abdulrahaman sun zu tambaya nace kai ne mai bada ita amma yaron ya matsa dayawa sosai".

cikin sarƙewar murya Nasir yace "Abbaty kuna son kuci *RIBA BIYU* a kaina kenan mai na muku ne idon ku baya sauƙa a ko ina sai akan zabina,

girgiza kan sa yayi yace" awannan karan ba wanda zai ci riba a kaina bazan rasa DAMATA a karo na biyu ba".
ya girgiza kai
tareda juyawa ya shiga mota Scurity din sa suka rufa masa baya Direbobin suka jasu

Umma ta kalli Malam tace haba Malam ka tausayawa yaron nan tunda ya nuna yana son Sadiyan kabasa".

"ni bazan basa Sadiya ba mun gama magana da ahalin sa suna da wani buri nasu akan sa idan nayi AMFANI DA DAMAR da nake dashi a wajen Nasir na dage na bashi ƴata nayi son kai kuma na musu shi shigi kuma zuciyar Nasir ba Sadiya ta yake so ba ayan da suka min bayani na gamsu nima ina son haɗa zuri'a da NASIR amma ina da dalilin na na saurin kaɓan tayin
da sukamin na Adamu".


Nasir bayan ya koma gida da sauri ya cire sut din jikin sa yayi jifa dashi yasake cire Fece glass din sa yayi cilli dashi ya jefa kansa kan kujewa ya rumshe ido yace " me yasa me yasa basa son na samu farin ciki sun san tsawon shekaru nawa ina neman yarinyar da zan mata koda rabi rabin son da nakeyiwa N&N Agrif yarabani da NaNa kai zaka rabani da wanda nake gani zan iya maneji da ita a wannan karan zan cire rauyin baki na ja ra ayin Sadiya Ladan Abbaty zaka tamka kuskure"
tunowa yayi da maganan Malam Ladan na cemasa ya auri Nasrim
murmushi yayi yace ni nagama da ita tun adaren da nasan Agrif ya kusan ceta bazan iya auran bazawara ba ni nasani da soyayyar NASRIM zan mutu dashi zan koma ga ALLAH amma bazan iya sex da wanda nasan wani yayi ba ai ma wannan ƙazan tane bazanyi tarayya da wani ba no yace yana murmushi ya sake cewa amma de zanyi garkuwa da ita zan aure ta badan nayi tarayya da ita ba Nasrim kinyi gan gancin bawa wani kan ki bayan nayi wanning naki

bayan sauƙan su malam ya ƙira malam yana nuna masa serious shi ba maganan wasa yabashi Sadiya amma malam ya kafe akan ya gama nagana dasu Alhaji Abdulmajid
jin zuciya ya hassaloshi zai iya ciwa malam mutumci yasa yayi saurin kashe wayan yana hura hanci amma yayi wa kansa Alƙawarin bazai bari wannan ta wuce shiba tunawa yayi da ZUHURAN Maiduguri wanda ashe ƴar uwar sa cema arashi sani girgiza kansa yayi yace no bata da abubuwan da zan iya rayuwa da ita zan auri Nasirm da Sadiya zan maida Nasrim hoto zanyi ta kallon ta idan ta tadamin sha'awana sai na sauke akan Sadiya Nasirm zanyi amfani dake ne kawai saboda ba maccen da nake tunawa sha'awata ta motsa idan bakeba idan kika motsamin sha'awa ta ina da Sadiya wanda wani bai ganta ba murmushi yayi yana ayyana yanda zai dinga yiwa Nasrim tsirara ta motsa shi ya sauƙe akan Sadiya dariya yayi yace *RIBA BIYU* ya sake yiwa kansa murmushi ya kaɗa hannunsa biyu ya meƙe ido a lumshe yana dafa setin zuciyar ya shige bedroom


**********************

Nasir ma yau yayi shiren kaiwa Ta soro ziyara a gidan Alhaji Isiya dake nan America dan tafi wata a ƙasan tazo ta kanas saboda shi amma yana busy yasha kira da ƙwarafin ta yaude ya daure zai leka dan yahana tazo gidan sa

Nasir yana saka kansa cikin falon Alhaji Isiya cak ya meƙye alaman girmamawa haka Ma'ruf da ƙanin sa Shui'bu ma cak suka meƙe Alhaji zai zube a gaban Nasir ya dafa kafaɗan sa

yace "haba Sir".
suka zauna still de cikin girmamawan Alhaji ya gaidashe suka zauna M'aruf da Shu'ibu zubewa sukayi suna masa sannu da zuwa Alhaji ya kalli ƙaramin yaron da yake zaune yace kai Mujashid jeka ka kira Hajja ga Maddibon tanan yazo".

Mujashid da sauri ya haura sama dakin da Hajjan take tana zaune a kan sallaya yace " sai kifito kiyi welcome din sa gashi yazo".
yajuya zai fita
tace "kai Amodu magana kayi ban hanaka hadamin magana da kalman da bazan gane ba kaje kayiwa Baban gida ko Fatime".
cikin daure fuska bai juyo ba yace baƙon da kika damu mutane a kan sane yazo yana mains parlour na ƙasa......

ai tun kafi Muja ya ƙarasa Hajja ta meƙe tafito tana cawa Maddibo na kamar ta kifa take taka steps din tana cewa "dama sai da nacewa Isiya bana son sama amma ya nace wai yafi rashin hayaniya yo ni a gayan hayaniya nayi zaman soron fada ma
gashi yamin asaran fara ganin Moddibo dani zan fara ganin ka kai ɗin ɗan baiwa mai cin RIBA BIYU ne".
~sunan wani littafin JATTKO~ *RIBA BIYA*

Nasir ɗaga kai yayi yana murmushi yace "Hajiyar mu sauƙo a hankali yau ina gidan nan har sai kin ce kin gaji".

"ni Amina Ta soro zan gaji da ganin Ɗan baiwa ɗan da uwar sa ta haifeshi da Bismillah kai ba bismilla ba harda li'ilafi tayi ta haifoka".
ta karashe maganan tana zama aƙasan kilishin da aka shinfiɗa dominta sauƙowa shima yayi yana cigaba da murmushi yace "barka da yamma Hajiyar mu ya zaman jirana"?.

"haba Moddibo kabani wahala sosai fa yau satina biyar kenan anan ƙasan nake ta zaman jiranka wllh wai ganin kama wahala ne dashi kai kuma shikenan dagayin kudi sai ka gujemu duk dama ashe kai din ɗane ga dr fanna tiri buroda amma kaje kake mana gadi ranan da aka gano kayi gadi a gidana har da ƴan sanda akaje meman ka ku kuma kun taho nan kaji tambayoyi sai kace nice nace su koraka duniya ko jiya sun zo wai idan kazo na ƙirasu kai Mahadi du bomin number din Hajiya Mariyama tiri boroda".

ta karashe maganan tana meƙawa wanda taƙira da Mahadi wayan
Nasir yayi saurin cewa "Ah Ah Hajiya kibari shiyasa fa naƙi zuwa miki tun farko kina da yawan magana ni kuma bana son mutum mai yawan magana dan Allah basai kin gaya musu nazo ba".
Hajja Ta soro galala tayi tana kallon Nasir tace "kana nufin bakason su san kana nan shikenan na fari bawan da zan gayawa amma dan Allah Maddibo kana yawan zuwa ko idan ni naje kana cewa folisawan ka su na barina ina ganin ka dan Allah kar ka gujeni saboda kayi kudi".
ta ƙarashe maganan kamar zata saki kuka tana kamo hannun Nasir tana hadawa da nata ta danƙe
Nasir ya sauke numfashi yace" Hajja bazan gujeki ba kawai bana son ne ki fadawa family dina inda nake amma ni bana daga cikin mutanen da suke daukan akwai bam bamci tsakanin mai kudi da talaka ni kawai idan zanyi mu'amullah da mutum ina duba halayen sa ne idan naga ya can canci nayi mu'amullah dashi zanyi ko mai kudi ko talaka asali ma ni duk duniya bayan Mommy na da Agrif da Ayman da Aliyu ba wanda muka shaƙu dashi kamar Baba Yakubu mai gadin gidan mune ina son sa sosai ina zama cikin ma aikatan gidan mu Hajja ni tun kafin na ganki da Baba Jafaru ya bani labarin ki naji ina sonki halayan ki irin daya dana Hajja kakata abin sona a she zaki zame min matakin Nasara a rayuwa ta Hajiya bazan taba mantawa dake ba kin shiga jerin mutanen da bazan taba mantawa dasu ba a rayuwa".

sosai Hajja da Nasir da sauran mutanen gidan suke cin fira anan yaci abincin dare Nasir yana kula da Farida da Yusura da suke ta faman yimasa karairaya amma yanuna kamar bai gani ba shi yarasa me yasa yanzu mata suka rainashi in da dane wadan nan matan ko kudi aka masu akace su masa kallo ukku baza suyi ba wani irin kunu yaci ya koma Nasir din sa na ai nishi ya meƙe tsaye yana ajiye (cek) akaman Alhaji da Hajja yace "ba yawa Hajja kinsan yanzu ina tsaka da aikin kudi ne wllh amma insha Allah kudi sun kusa zuwa yanda ko wanka zakiyi dasu".

ya ƙarashe maganan yana juyawa
Alhaji yana ganin cak din ya wani zaro ido yace "meye haka wannan me zanyi dasu Ah ah dan Allah kabarsu kai da kake da bashin akan ka".
murmushi yayi yace "Alhaji ai an biya bashi tun a wancan kuɗin naso na fitar muku Allah yakawo wannan cigaban da in sha Allah duk zai amfane mu kusa Albarka kawai".

Ta soro tace "ai Albarka kullum cikinta kake ko baka bamu kuɗin kaba ma cigaba da Isiya yasamu ta dalilin ka awajen aikin su kaɗai ya isa abin Alfahari Allah yamaka jagora ya kare gaban ka da bayan ka".

Ma'aruf yace "hakane Sir Daddy ya taka matsayin da bamu taba tsammani ba ta dalilin ka muna godiya sosai mu kanmu a dalilin ka mun haɗu da mutanen da bamu taba tsammanin haduwa dasu ba".
haka de sukayi ta godiya
har gaban mota suka rako sa Yusura ta zo ta leƙa kanta ta window cikin karairara tace "yallabai zan samu Alfarman number ka tunda kazama yayana ".
ɗagowa yayi ya watsa mata wani birkicecen kallon da bata san sanda taja da baya ba shima bai sake kallon inda su Ta soro suke ba ya zige glass din sa driver ya ja


*Nigeria Three brother house*

Abu ya kalli Hajja da take kuka wiwi ita shikenan ya tabbata bazata sake ganin Nasir ba ido da ido sai de ta hangoshi a tv ni da jikana jikan ma ɗan wajen Abdulsamad ni Maryama".
yace" haba Hajja bakiji abinda Ayman yace ba sun dauki duk wani mataki sun shigar da three brother a meeting din da za ayi a wannan watan wanda Dr Fannan zataje kuma nasan In sha Allah zai saurareta duk wannan abin ai bai basu tabayin gaba da gaba dashi bane".
"wannne irin gaba da gaba yayi gaba da gaba da kai yanuna bai san kaba yayi gaba da gaba da Abdulmajid ya nuna bai san saba yayi da Aliyu shima yace bai san saba haka Ayman Abbaty kam ma sawa yayi aka wulaƙantashi ashe haka daukaka yake Nasir ya gujemu saboda abin duniya".

Mommy tace "Hajja Nasir ba saboda abin duniya ya gujemu ba saide wani dalilin nasa na daban da abin duniya zai ruɗ Nasri da bai bar abinda yake mallakin sa yatafi ya rayu cikin ƙasƙanci ba kawai de dawani dalili amma insha Allah ko bamu hadu awajen meeting ba Mlm Ladan ya min Alƙawarin ganin sa komai rintsi".

***************
bayan wana biyu

"Abbaty ya haka baka fita bane me yasa kake son wasa da aiki ne da kamar ka fara abin kirki yanzu kuma gashi ka koma shagoɓaɓɓen Abbatyn ka na da can".
ɗago da idon sa da yarine yayi jajir yayi
yace " Mommy dan Allah ki temaka min rayuwa ta tana cikin matsala Baba Ladan ya nace wai dole sai Ya Nasir ya yarda shi zai bani auren ta Nasir bazai taba bani auren Sadiya ba naga tsanata a fuskan Nasir sosai ranan da muka hadu kuma da na bincika wai shima son Sadiya yake taya zai bani ita Mommy duk duniya bayan Nasrim ban taɓa son macce kamar Sadiya ba Sadiya tana da duk abin da nake so ajikin macce nayiwa su Daddy biyya da sukace na haƙura da Nasrim amma bana jin zan iya hakura da SADIYA Mommy ina jin son Sadiya ne ajalina ina tausayawa Ummu na ta rasa Aiban ta rasa Agrif nima zata rasani".
cikin ɓacin rai Mommy tace "baka tausayawa Ummun taka da kana tausaya mata baka jefa kan ka cikin wannan haliba dame Sadiya tafi Zuhuran maiduguri nace kaje ka nemi auren ta kaƙi".
"Mommy kin manta itafa Zuhura babban abokina Shamsu ne yake neman ta kuma dalilina suka hadu bai kamata na zame nace ina son taba kumama Mommy kiyi hakuri ziciyata Sadiya kawai take so".

"to cigaba daso ko kuma ka kwana a office din".

ta ƙarashe maganan tana ficewa kwantar da kansa Abbaty yayi yana lumshe ido

america

Nasir zaune a ƙayataccen office din nashi sai juya takardan da secretary sa yabashi yake meyasa tun randa aka kawo takardan bai duba yagani ba da yasan yanda yayi yacire ~three brother~ azaman amma gashi yanzu ya makara saboda yanzun nan za ayi zaman meetingn din ɗaga kansa yayi ya kalli agogo lokaci yayi yanzu haka shi kadai ake jira gashi shi kuma shine jaroran taron dole sai yaje za afara ba halin canzawa ta kowacce ƙafa dade ba ashiga bane da sai canza amma yanzu ai kin gama ya gama a fili yace "Allah yasa ma Mommy bace".

kallo daya ya yiwa inda take yaji gaban sa yayi wani irin faduwa ganin shi take kallo sun kuyar da kan sa yayi cikin hanzarin sa yake takawa har zuwa inda aka tanada domin sa cikin kwarewa yafara zayyano jawabai game da kasuwancin ƙasa da ƙasa da yanda za a gyara mu'amullah da cigaban kasuwancin ƙasa da ƙasa na duniya ya nisa gyada kai kawai ƴan kasuwan suke wanda cikin su turawa da larabawa da chanis sunfi yawa
kansa a ƙasa har ya gama tafi sosai suke masa tare da jijinawa baiwa da basiran NASURUDIN
bayan an tashi Nasir bai tsaya gaisawa da mutanen da suke tason su gaisa ba hanyar zamewa ma yake nema amma ta ko ina mutane ne suke tun karoshi da sauri ya juya inda scuritys dinsa suke ya musu alama da kada su bari mutane su zo kusa dashi juyawan da zayyi jiyayi hannun sa ya hade da tattaurar hannun da bazai taba man tawa dashi ba
sake ƙasa yayi da kansa
ƙafanta yazubawa ido jikin sa yana rawa sosai da sauri ya dakatar da wani scurity din sa dayayi kan Mommy ga dan gadan da hannu amma bai ɗago kai ba
Mommy tasa hannu ta ɗago haɓar sa ta seta Fece din sa da nata da sauri yayi ƙasa da idon sa bai bari sun haɗa ido ba cikin ɓacin rai ta ja hannun sa ta fara tafiya dashi da sauri wani bodyguard din sa ya sake yun ƙurin zai shiga gaban su a hankali Nasir ya girgiza masa kai yana masa alama da yabari su wuce kuma kar yayi gigin bin su yawanci mutatan cikin mamaki suke binsu da kallon duk da wasu dayawa sun san MOMMYN sace direct motan ta ta wuce dashi jefashi tayi a back seat ta rufe ta zaga ta shiga gefin nasa da sauri driver shima ya faɗa yaja bodyguard din Mommyn suka rufa musu baya gidan mommyn suka nufa basuyi wani tafiya mai nisaba yacusa hancin motan wani ƙayataccen gida fitowa tayi ganin bashi da niyar fitowa yasa ta zaga ta bude masa a taƙaice
tace "zaka iya fitowa ko".

sake ƙasa da kai yayi ya zura ƙafar sa daya yasake zuro ɗayan sai kuma yafito da gan ganjikin gaba daya Momny kama hannun sa tayi suka nufi falon sai da suka je tsakiyar Parlour ta saki hannun sa ta kalleshi sama da ƙasa
tace "ba shakka komai yayi maka dai-dai dolle ka manta da wacece Fanna Nasir ni zan dinga turawa ana baka baki ana roƙon ka dan ina so na ganka za ka dinga wulaƙan tani Nasir har kayi kudin da zaka min haka?".

cikin rawar murya yace "Mommy ki gafir ceni inason bin umarnin kine Mommy bayan umarnin Allah bana wanda ya can canci nabi umarnin sa sai ke Mommy zuciya ta ta a zabtu da rashin ganin ki Mommy idan natuna kalaman ki akaina sai naji duk na tsani kaina Mommy nayi sanadiyar jefaki cikin ɓacin rai Mommy amma Mommy bayin kaina bane SO ne na yarda SO masifa ne na yarda dan Allah Mommy ki ya femin ban gujeki dan kaina ba saidan umarnin ki kince bakya son ganina nikuma duk abinda bakya so bana fatan yinsa Mommy na azabtu Mommy dan Allah ki bani umarnin ɗaga kaina koda kallo daya ne namiki Mommy idona yana son ganin ki gan gan jikina ya azabtu dan Allah Mommy na kalleki koda shine abu na ƙarshe da zanyi aduniya ninason ganin ki Mommy ko duniya na mallaka bai kai rabin farin cikin kiba ba abinda zan mallaka aduniya wanda zai..........


bai ƙarasa ba tajashi ta mannasa da jikin ta ta saki kuka sosai cikin kuka
tace "Nasir me yasa me yasa me yasa kayiwa ƴar uwar ka haka Nasir ka jefa rayuwar NASRIM a garari me yasa bakayi duba da Nasrim jini na bace".

a hankali ya zame ya zube a gabanta
"yace Mommy so ne nayar da so masifa ne Mommy Son Nasrim shi yake sarrafa rayuwata Mommy tun tana ciki na sha gaya miki macce zaki haifa kuma ni zaki haifawa kuma idan kika haifeta ni zan fara daukan ta sai kawai na ganta a hannun Agrif mai makon naji haushin Agrif sai naji haushin Nasrim
Mommy a duk sanda nayi yunƙurin zan nuna ni nake son Nasrim sai AGRIF yayi min wani abin haushin da zanji sai kawai na huce akan Nasrim da farko Mommy wllh ƙuruciya ce daga baya kuma borin kunya ne ban gayawa kowa ina son Nasrim ba amma ina gayawa Allah nasha zuwa hajji da umara ina DAWAFI a ɗakin Allah dan na samu NaNa ta cikin sauƙi har aka saka ranan auren su da Agrif Mommy nasha yiwa Nasrim kyauta ba tare da sanin taba nasha turamata kalaman soyayya Mommy ki bani dama akwai abubuwan da zai gaskanta wannan abin da nake gaya miki Mommy ki yarda dani nasha bawa Nasirm kyauta cikin shikima ba tare da kowa ya gane ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login