Showing 57001 words to 60000 words out of 155717 words
Chapter 20 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
sauki kawai yana cikin damuwa ne yasa aka masa alluran bacci".
"Shikenan Aliyu nagode amma dan Allah ka kula min dashi kafin gobe in Sha Allah ina hanya".
ta kashe wayan tana dialing wayan sarkin gida
Bala sarkin gida yana daukan wayan yace "ranki shi dade mommy Allah ya kara miki yawan rai".
"Yawwa Bala kasamu password d'ina dan Allah ka shiyamin tafiya Dubai yanzu idan ba jirgin a yiwa Aiban magana yaturo min jet".
"Ok ma'am za ama samu dan yanzu Ado yake cemin zai tafi amma sai 4 na yammma jirgin zai tashi insha Allah nan da mintuna 40 zan shirya komai ki shiga cikin masu tafiyar ."
"shikenan nagode sarkin gida".
Agrif kwance cikin bathtub idon sa alumshi yarasa me zai fassara abin da yake ji farin ciki ko bak'in ciki ashe dama haka jinsin mata yake da sanya nutsuwa a jinki bai taba sanin haka saduwa yake ba sai jiya da ya kasance a cikin wata duniya ashe da duk shime yake da yake kwatan ta abin aransa ashe duk ba haka bane ahankali yake shafa maran sa da yake jin yayi masa wani sakayau shi kansa ji yake kamar an rage masa yawan nauyin jikin sa ahankali yafurta Al'hamdulilih Ala kulli halin
ALLAH mun gode maka daka alakta mana jinsin Mata suka zama ababen nutsuwar mu
sai idan ya tuna da FURUCIN Nasir na cewa _ni na kwashe romon farko duk Wanda zaka samu to bazai kai ko rabinnawa ba_
dafe kansa yayi yana ci gaba da tariyo kalaman Nasir na ranan kaman yanzu yake gaya masa
inda yake cewa
_sai de ina maka albishir da matar ka komai yayi zam zam bawai kyan fuska da sura kadai Allah ya bata ba tana da sirrin boye Wanda yafi na zashiri in ganci_
wani irin k'ara yasa tare da dunk'ule hannu sa yadaki bathtub
tabbas bai San meye kishi ba sai yanzu inde zai cigaba da nuno wannan abin aransa to zai iya zama ajalin sa
Afili ya furta Nasir ka cuceni ka gina zuciya ta da tabon da bazai taba gogewa ba ka b'ata duniya ta Nasir
Dak'er yasamu ya lallashi kansa yatashi ya d'aura towels ya d'auki na goge jiki ya yafito yana goge jikin sa ahankali yake kinsawa yana kokarin mantawa da damuwar yana janyo farin cikin har yagama yana murmushi ya k'arasa bakin gadon ya zauna yana murmushi yaja blanket din ahankali har yanzu bacci take daga kansa yayi yana kallon agogon da yake lik'e ajikin bangon 11 pm lokaci ya tafi ya kama ta ace taje taga halinda yaran ta suka kwana ga kuma baccin gajiya da takeyi Wanda idan yayi duba da yanda ta ai'katu bai ci ta tashi yanzu ba amma ya ya iya dole ya tasheta azuciyar sa yace Allah ya isa Nasir
hannun sa ya d'aga ya d'aura a goshinta ahankali yadinga shafawa har ta fara bude Ido cikin muryar bacci Sosai tace'' Abban Khaldum bacci".
hannun ta ya matsa da daya hannun sa dayan kuma yana cigaba da shafa goshin ta yace "sorry mamyn Khaldum kar mu shiga hakkin su Khafulan kinga zasu buk'aci abincin su kinga yaciga taf shima yana buk'atan arageshi yayi maganan yana cusa hannun sa cikin rigan nata wani irin Nishi mai tsuma jiki ta sakar masa asan da taji tattausan hannun sa cikin rigan nata atake yagigice amma tunowa da yaran yasa yayi control din kansa ya mek'e yace" kiyi wanka ina jiran ki a parloun".
yafita
Idon ta ta bude tana murmushi tana tone lips dinta na k'asa tafara birgima tana cewa "wayyo rayuwa aure dad'i ya Allah kasa Haruna ya zauna dani daya b'ata fuska tayi tana turo baki afili tace'' kajini da wani wawan dan iskan tunani da dawa zamu zauna ai ni dan ni aka hallici Agrif dani kadai zai zauna
Mek'ewa tayi tanayin hanyan bathroom din sai da ta tashi ta gane cewa ashe Agrif ya mata d'anye aiki ahankali ta fara takawa
ta b'ata lokaci Sosai wajen tsala make-up wanda tasan zata murgesa dama tasan Agrif dan son gayu ne
cikin nusuwa riga da siket tasaka nawani swwiss atumfa yagama zama ajikin ta sosai pink color ne bak'in takali files tasa bata daura dan kwali ba taja rolling da wani yaluluyin mayafin ta bak'i shima ta daura agogon ta na golden tsake juyawa tayi taga gomai yayi ido daya ta kannewa kanta tareda jujjuyawa afili tace na yarda ni me kyau ce anya banfi IZZA kyau ba ummmm aikuma tafini fari kai hakama nagode Allah kowai yayi yanda nakeso a jikina tace tare da fara kwada takun dafiyar da zatayi a gaban Agrif ta canza tafi yafi kala 7 sannan tajuya tafita tana sakin murmushi ganin yana parlou a zaune da jarida ahannu yasa bata san sanda ta canza tafiyar da bata masan ta iya ba a haka take taka steps din duk jikinta yana wani rawan daukan hankali k'amshin turaren tane ya sanar masa zuwanta tundaga k'afanta yafara kallon ta ahankali yake Jan kansa har ya sauk'e a fuskan ta mek'ewa yayi Yana cewa "Masha Allah matar dan gata".
murmushi tayi tace'' sannu da hutawa mijin y'ar gata".
shama takawa yayi ya k'arasa inda take yana cewa
"ban san dame zan kwatan taki ba wajen iya ado ke kenan komai naki ado ne komai kikayi mekyu ne farin ciki da kika bani inde zaki cigaba da bani to tabbas idan nak'ira kaina da dan gatan mazan duni banyi kuskure ba Nasrim kece duniya ta da gaskiya kin can_can ci akiraki NASRIN MINALLAHI WA FUTUHAN KARIBA kinci sunan ki NASARA ce daga Allah NASRIN me kwamshin da sa nutsuwa gaskiya mommy ta zaba miki sunan da yadace dake".
turo baki tayi tace'' nide wllh sunan bai min ba tunda mommy ta gaya min wancen bayahuden ne ya zab'amin sunan tun ina ciki".
shiru Agrif yayi yana tunuwa tabbas Nasir ne ya zabi sunan tun kafin a haifi Nasrim sai kawai yaji ya tsani sunan kuma yayiwa kansa alk'awarin bazai k'ara k'iranta dashi ba
murmushi yayi yana d'an janyewa ajikin ta yace"ok my honey tunda bakyaso daga yau nadena K'iran ki dashi halimatus Sadiya me hali dubu Halima ai mar taban kice".
murmushi tayi tana sakar masa kiss akumata tace'' su Khafulan".
gyad'a mata Kai yayi tare da kama hannun ta suka shiga d'aki masu renon yaran Fayyat ne kawai yake baccin Khafulan yana hannun Adama Khaldum kuma Shatu da sallama suka shiga duk zubewa sukayi suna gashesu cikin mutunci suka amsa Nasrim tayi inda Fayyat yake acikin gadon sa
tace " Allah sarki Alhaji Abu na baccin yake ko me hakuri ba irin Khafulan ba masifaffe". ta k'arashe maganan tana sakar masa kiss goshin sa
Agrif ma ya k'arasa yana cewa "ai Abban kike cewa masifaffe to wllh kulldin ki kar Hajja tajiki yanzu tamiki sharrin kin zagi original din
shima ya k'arashe maganan yana shafa kan Fayyat din ahankali dan karyatashi
Nasrim ta kalli Fayyat na dan tsawon lokaci ta d'aga kai tana kallon Agrif sai taga shima yaron yake kallon "Yaya kana kallon kyau ko Allah jaririn nan kamar mommy ce ta haifesu".
Agrif da yalula zangon tunani ya sake ajiyar zuciya shi tausayin yaran nan yake yana tsoron kar ace wata rana asiri ya tonu ya zasuyi insha Allah yayiwa kansa alk'awarin boye wannan sirrin har tsawon rayuwar sa zasu amsa sunan sa tunda dama shari'a tabashi hujjojin Nasir bai isa ya kamsar da kotun musulumci har abashi yaran ba yara nasane tunda da auren sa akanta tasamu cikin ajiyar zuciya ya sauk'e
Afili kuma yace " Eh mana sun fiyo kyan mommy".
yajuya ya karbi Khafulan ita kuma ta karbi Khaldum suka fita zuwa part din Hajja
suna shawo kwana sukaci karo da Baba yakubu " kai Kai Kai Haruna kafin k'asan randa yawan wanka Haruna kan d'aki bade hannu daya ba Haruna ng'ororo anbaka kabawa yaran baya me kyauta adad'a na fadan NASARA 3 A full duniyar Allah mijin nasiriya y'ar Mama me tafiyar k'asaita Baban masu gida baban 3 full".
murmushi Agrif yayi yace" Alhaji Yakubu ka kawo mutum 5 wanda kake son suje aikin hajji sannan katara duk kan ma ai'katan gidan nan idan a yan uwan su ko abokan arzik'in su Wanda yake buk'ata to a samu sarkin gida".
ya k'arashe maganan yana sake rungume Khafulan yayi gaba baba yakubu yace "allahu akkar wanna irin kyautan three brother kenan kyautan Alhaji Abdulsamad kenan aduk sanda yake cikin farin ciki kai Allah yajik'an maza"
"Ameen Baba yakubu nima a yau ina cikin farin ciki ne"
washe baki baba yakubu yayi yace "ai da ganin kama anga kwanciyar hankalin Ya Rabbi ka dauwamar Haruna cikin moment din da yake a yanzu".
"Amin."
Agrif yace
sai da suka kusa shiga cikin parlourn Hajja Nasrim tace''da gaske Yaya kana cikin farin ciki?.
"Okay dan ban baki giv dinki na first night ba baki sheda ina cikin farin ciki ba kenan zuba ido zakiyi kallo".
dungure masa k'eya tayi cikin shagwaba tace'' Allah kai ko tayi saurin shigewa
a dai_dai lokacin da mommy take waya hankalin tashe alokacin suka shigo duk hankalin su yatashi dajin halin da nasir yake ciki amma banda Nasrim sai ma dad'i da taji ya gama ratsa zuciyar ta amma ta danne saboda rigiman Hajja
Hajja kuka ta fara Sosai tana cewa "na shiga ukku idan akace yaron nan yamutu shikenan babu Abdulsamad ba labarin sa wasu da banne zasu jinye dukiyar sa gaba daya bashida me tunawa dashi niko dama kwana nawa yaragemin wayyo Allah NASURUDDEEN kar ka tafi ka barni".
akayi_akayi Hajja kin zama tayi dole da ita aka shirya zuwa Dubai da Abu da mommy da Ummu aka tafi daddy yana da Shari'a gobe dan haka yace suyi gaba zai bisu idan ya Free
*Dubai*
kuka Sosai mommy takeyi ganin yanda Nasir yakoma hannun ta yakamo cikin sanyi murya yace" mommy ki de min kuka nagaya miki ba abinda yake damuna ".
" ban yarda ba Nasir baka k'arya tun kana yaro iya gaskiya kake fada amma yanzu al'amarin ka yafara bane tsoro dubi yanda kamayar da kanka mashayin dole mashayi fa bai san me yake ba shida mahaukaci daya ne komai naka yakoma baya bakada abinci sai giya kaga yanzu dagani sai kai gayamin koma meye yake damunka ada de amatsayin uwa nake a gunka yanzu ko bansan ya nake ba tunda har baza ka gayamin damuwa ka ba saboda bani na haife .............
da sauri yasa hannu ya toshe mata baki yace'' mommy Dan Allah kar ki kawo wannan zance najima Ina gaya miki ni ina mantawa da bakece kika haifen ba mommy adduar ki kawai nake buk'ata amma wllh mommy bazan iya gaya kowa meyake damuna ba sai de namiki alk'awarin daga yau zan dena damuwa zan cire abin araina duk da ni mutum ne da Allah ya halinta idan inason Abu to da zuciya ta da gan-gan jikina......
sai kuma yayi shiru
can yace "mommy namiki alk'awarin nadena shan komai
*******************
bayan kwana 2
Al'hamdulillah Nasir ya samu sauk'i Sosai ayau su Hajja suke Shirin komawa kuma kamar yanda yayiwa mommy alk'awari ya cire komai aransa har giya yamata alk'awarin bazai k'ara shaba
Nigeria
Agrif sai da yadauki hutun sati ukku cif yana shan amarci yayi Shirin tafiya
bayan watanni 10
Nasrim tana da tsohon ciki su Khafulan ta yaye su tun suna wata 5 dan dama bawani samun nono suke a kai a kai ba tunda tana zuwa school
Izza tasake haifuwa wannan Karan ma maccen ta Haifa
Adama tana mopin a bedroom din Nasrim taji wayan Nasrim yana ta Ring da sauri da dauko tayi parlourn dashi tana mek'awa Nasrim
"ranki shi dade ana kira".
dak'er Nasrim tasa hannun ta k'arba tana matse lebe
Daga can ban garen Agrif yace "honey yajikin kin fa tadamin hankali sarki gida yace kink'i aje hospital"
tana cije lip tace
"wllh mommy ce ta hana wai komai normal lokaci ne bayyi ba ni yanzu jikin Fayyat ne ma yafi damu na wllh bashida lafiya gashi ance wai jini za'a k'ara masa kuma wancen bayahuden yace kar a sake a sa sama jinin sai dawa gashi na ya Kamal dana daddy dana Abu duk baizo daya danasa ba".
"Sorry my wife kar ki zamu insha Allah nima ganinan zuwa yanzu haka Ina saudia yanzu jirjin mu zai tashi Allah zai baku lafiya kinji".
"Yaya Agrif shikenan ba Wanda ya isa ya hana dan iskan can abinda yayi ni ya ikon sa baya tashi sai akan yarana wllh".
"Am sorry kin ga jirji zai tashi zan kashe wayan I love you with all my heart".
kafin ta bashi amsa har ya kashe
Kusan atare Agrif da Nasara suka sauk'a kowanne su direct asbiti yawuce mommy tace a ibi jinin Agrif aka kwada bayyi dai dai ba cikin idon Allah ana kwada na Nasir yayi dai dai aka iba aka sawa Fayyat Nasrim kam alokacin ta kanta takeyi ba ita ta haihu ba sai 4 na asuba tasamu y'ar ta macce Masha Allah da ita
tun kafin amata wanka kowa ya ganta sai yace ita masu Khafulan ta biyo sak ba suda ban banci
duk a falon Mama ake
bayan an yiwa jaririn wanka Hajja ta dauketa tace'' ikon Allah kugano min yarinyar nan har wannan bak'in tabon na cikin tafin k'afan Nasuru bata bari ba kuma itama a k'afar hagu dai_dai inda na Nasir din yake Allah mai iko dubi yanda take juya idon kamar shi asanda aka fito dashi a tiyata".
Abu yace " nide bana gane kamannin jariri amma wannan kam tana tunumin sanda Nasir yake jaririn Sosai amma fa Nasir dina yafi wannan me kwalelen kan kyau".
dariya akayi
mommy tace'' kai Abu kode kana ciki dama Ummu ta sha miya kayi sabon zubi".
"Daddy yace "Ah ah wannan tawace saide idan Muwadda ko Ummdatu ko wannan k'anwar tasu yama sunan".
Mama tace'' y'ar bak'a sai sadaka".
yace "Yawwa to ka had'a harda y'ar bak'a nabaka sadaka"
Ummu tace'' ito takwara ta de zataci al'barkacin sunanan na bata d'aki amma banda wannan me idon a tsakar ka". ta k'arashe maganan tana nuna Ummdatu da take hannun Mama
Izza ce tashigo da sallama da waya ahannu tace'' umman Khafulan ga Abban Muwadda zai miki sannu".
ta k'arashe maganan tana mek'awa Nasrim wayar murmushi tayi tana cewa
"Ya Aiban agogon sarkin aiki".
dariya Aiban yayi yace
"ai kinfini aiki shekara biyu kin ajiye yara 4 aike za a k'ira agogon sarkin aiki".
Nasrim hararan wayan tayi kaman yana gaban ta tace'' yamuke daku kuma ai 3 kukayi ko".
yace "ai mu auren mu yacika shekara 3 kuma ai keda kika dashi dare daya kika handamo 3 ".
"towai kuma ba kun handamo 2 ba barka zakamin ko sa ido?".
"yes giwar mata munyi godiya duk da wannan Karan daya tak kikayi bayan kin cimana abincin kusan shekara".
k'wafa tayi bata masa magana ba
dariya yayi yace" my dear sister nima na dauki hutu gobe zanzo Ina nan za ayi sunna Ina brother A'A".
Nasrim daga kanta tayi ta kalli inda Agrif yake gaban tane yafadi daganin yanayin sa sai wani gumi yake fitar wa gaba daya yanayin sa ya canza".
kafin tayi magana har ya mek'e yafita dafa kansa dayake jin kaman zai rabe gida biyu yayi yana zaune a bedroom din Nasir yana jiyar fitowar sa a bathroom dan yaji
motsin shower Nasir yana fitowa yaga Agrif ahaka kallo daya yamasa yajuya yayi inda wodrop din sa yake wani riga yaciro fari me yankekken hannun yasaka ya dauk'o wandon Marrom iya gwaiwa yasake yana brush din kansa ya sake kallon Agrif ta cikin mirrorn yace" kana lafiya kuwa".?
Agrif cikin muryar sa da yake wani irin k'amewa wanda duk wanda yaji sai ya tausaya masa yace" Muhammad meyasa y'ata tayi kama da kai".?
ajiye brush din yayi yana d'agowa inda Agrif yake yana jifan sa da murmushi ya dafa kafadan sa yace " wannan wacce iri tambaya ne meye abun damuwa dan y'a tayi kama da uban ta".
"Nasir meyasa baza ka dauki makami ka k'ashe ni ba ka huta bana tunanin zanji dacin mutuwa fiyeda da abinda nake ji yanzu ni musulumi ne ubangijina bai yarjemin na k'ashe kaina bazan iya ba amma dan Allah Nasir ko sawa kayi akasheni banga amfanin rayuwata ba kab'ata min duniya ta yanda bazan taba jin dadi ba".
murmushi Nasir yayi yace' tun daga yanzu ai nazaci zaka jure ko kazaci barazana ne ai kai shirya d'aukan wanda yafi haka ma tunda kasan ni me fad'a ne nacika bana taba fad'an abu bayyi ba ina amfanin da DAMA TA akan lokaci nafada maka k'addaran Nasrim ba me kyau bane ka gauraya da ita to ni ba da bakami san kashe ku ba da azaban bak'in ciki rayuwa zaku mutu ina son kajira ranan sunan wannan jaririn kaga abinda zai faru amma kafin wannan ga zabi idan kana son lafiya to baka makara ba zaka iya sakin Nasrim kafin satin sunan inba haka ba akwai gagarumin matsala wllh wllh wllh akwai babban rikicin a three brother?".
shiru yayi yana sauraron Agrif kozai fadi wani abun amma Agrif yakasa magana
can
Nasir yayi murmushi yace'idan ba kada abin cewa ni zanje nayiwa y'ata hud'uba
sunan ta Zainab wato Mama jummai k'anwar Hajja ta Dardum".
Yana gama fadan haka yajuya yafita Agrif jiyayi ko harshen sa bazai iya d'agawa ba
kamar yanda Agrif ya barsu ahaka ya samesu dan yau breakfast ma anan bangaren Maman Hajja tace ashiya musu cikin takunsa na Izza da nutsuwa yashigo
"daddy Abu Mama Ummu kuntashi lafiya".?
a tare su kace morning my Son
daddy yace sannu zumunci Nasir ya kakejin jikin naka jiya an ibi jinin ka".
"ba komai Dad ni lafiya ma yak'ara min inaga ma yanzu duk wata zanje a din ga iba wllh jina nake lafiya sosai".
ya k'arashe maganan idon sa akan jaririn da take hannun Hajja
numfasawa yayi yace' Mama amma y'ar ki fa ta iya haifuwa wannan baby girls din itace ontop a kaf three A full". ya k'arashe maganan yana mek'a hannun alaman a basa Hajja mek'a masa tayi tana tura bakin bai gaida taba amma bata isa ta furta ba
bayan yamata K'iran sallah da salatin annabin ya mata hud'uba