Showing 75001 words to 78000 words out of 155717 words

Chapter 26 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

647

yau basu zo mun gaisa ba".
"Wllh mommy nima yau ban gansu ba da safe ance Ya Abbaty yafita dasu yanzu kuma inaga sun wuce islamiya ne".
gyad'a kai mommy tayi tare da cewa
"Ok madallah."
shiru mommy tayi ita ma Izza haka can Izza tace "mommy dan Allah kiyi hakuri akan abin da yafaru wllh naso ni nazama lawyer me kare Nasrim y'ar uwa ta wanda tamin dukkan halaci arayuwa to abinne wllh yafi karfina anbiyo ta inda a kafi k'arfina ne bayan da zanyi amma dan Allah mom......
"Please Izza wacece y'ar uwar ta ki ai Nasrim ban santa da wata y'ar uwa mafi kusa ba sai Humairah kuma Al'hamdulillah Humairah ma lawyer ce amma bata ce zatayi ba wanda ya dauke ki yasan zaki iyane kare Nasrim kuma dan bakiyi me yene Nasrim uban da ya haifeta ne ya yanke mata hukuncin balle ke da bama kece babban lawyer ba temakawa kikayi so bana son k'ananun magan ganu mu barwa Allah ikon sa zaki iya tafiya nagod........
Mommy bata k'arasa zancen ba Zaliha me aikin Hajja ta shigo arikice cikin in nina tace'' mommy mommy Hajja zata mutu".
Mommy tace'' meya sameta tana cin abinci kawai sai tace cikin yana ciwo bakin ta kumfa yafara fitowa yanzu ma asbiti za akai ta".
Izza tace" wayyo Hajja gatana nashiga ukku....
tayi maganan tana ficewa da gudu
Mommy ma tabi bayan ta kafin su k'arasa har Kamal da Ummu sun shiga motar mommy taja
Izza ta hau nata motan ko mayafi babu ta fita a guje arikice mommy da Mama Adamu driven mommy ya dauke su
Asbiti
duk suyin cuku cuku a kan Hajja har Nasir da Abu da daddy
Daddy ya numfasa yace " kamar yanda Dr yamana bayani Hajja guba taci to a gida an bincika wanda yasa a bata a bincin kuma an gani ta hanyar CV tv muje gidan munafiki ya bayyana ita kuma Hajja Allah yabata lafiya Al'hamdulillah Allah ya yafiyar mu cikin wannan duhu da muka shiga asiri ya tonu mujede gidan tukun".
Mommy zubewa tayi a k'asa tana sujjidan shuran cikin kuka tace'' Alhamdulillah Allah na gode maka da kafitar mu a duhu Nasrim zata yiwa mijin takaba a gida".

suna zuwa gida motocin yan sanda ne har guda 2 mommy tana fitowa daga mota Abu ya nuna ta inspector ya nunawa mommy I'd card yace Hajiya arrest
Mommy juyowa tayi cikin mamaki tace''me nayi ".
Abu tace'' kece kika saka me aikin ki Barira ta sawa Hajja guba".
ya k'arashe maganan yana nuna Barira da take bayan Hilux din yan sanda kuka Barira ta saka tace'' mommy dan Allah kizo ki ce su barni wllh ba lefina bane kece kika sani dama sai da nace Ina tsoro kikace zaki koreni idan banyi ba gashin an gamani kar akaini Police station Ina tsoro mommy".
wani irin kullewa kan mommy yayi ta taka a hankali har bakin motan inda Barira take tace'' Barira ni nabaki guba kika zubawa Hajja ni".
Barira tana jan majina tace'' eh jiya da muka je chemist anan kika karbo shima me chemist din gashi nan acikin motan".
ta k'arashe maganan tana nuna mata Friday Wanda yake aiki a pharmacy din mommy
Mommy sai alokacin ta kula da Friday yace "madam dama poison din da kika saka na miki order su a Chaina da sunan zaki wada wani chemist ashe mutane zaki bawa wata daya da yawuce kin karbi biyu sai jiya kika karbi daya kin cuceni nikam".
Mommy tace'' wai ni me nayiwa mutane."?!!!!!!???

Abu yace "me kikayiwa kanki de haba Fanna me kike so nan duniya baki samo ba idan dukiya ne keda talauci har abadan amma kika jefa kanki cikin wannan halin gashi yanzu idan ba a yanke miki hukuncin kisa ba to zaki k'are rayuwar ki a pirson ".
Murmushi me ciwo mommy tayi tace'' shi kenan na daukawa kaina asaki Nasrim tunda nice me lefi duk abin da ake zargina dashi nayi Nasrim kuma a sake ta".

Nasir yace "hakan bazai yuwu ba ita Nasrim rai har ukku ta kashe ke kuma ansame ki da safaran kwayoyin poison sannan kin sawa yara jikokin ki daya yamutu daya ta tahi yanzu kuma yau kin sawa uwar mijin ki wanda ta na nan rai ahannun Allah ke lefinki da ban lefin y'ar daban".
cikin mamaki mommy ta daka har inda Nasir yake
tace'' kai ma ka yarda nice nayi duk wannan kulleleniyar ko Nasir".
Mommy ai ance ke kika cewa Hajja zata ga aikin tubebbiya so FURUCIN ki ne."
girgiza kai mommy tayi tace'' TABBAS NASURUDDEEN WANNAN *FURUCINA NE* amma ka yarda zan aikata hakan".

tabe baki yayi ya d'aga kafadun sa
yace" me zai hana na yarda nasan abinda yake jikin zuciyar ki ne ai *ZUCIYAR MUTUM BIRNIN SA* ".
ya k'arashe maganan yana juyawa ita kuma mommy police suka kamata suka shiga da ita
cikin motan
cikin kuka maimunatu me aikin mommy ta dauki waya ta kira Dr Hafsa tana gaya masa wannan sabon labarin

Mommy acikin cell ta kalli Barira tace'' Barira dan Allah ki dubi zaman da mukayi dake tun baki kai budurwa ba har Allah yayi na hadaki da drive na kukayi aure na dauki duk wani d'awai niyar ku da dangin ku da mijin ki da ranan ku na zauna daku bisa Amana ki dubi da rajan wannan ki gayamin Wanda yasaki wannan aikin ni wllh zan sa afitar dake kuma bazan gayawa kowa bani kawai rayuwar nasrim nake son kubutarwa kinga Nasrim y'ar kice kema".
dariya Barira tayi tace'' mommy dawayo zaki min to dan kin min aure ina zauna a k'ar k'ashin ki sai me ba wahala nake miki ba wahalan da nakeyi dake kin isa kiyiwa kan kine ko kudin ki zai miki to Wanda yasani aikin kudin da zai bani yanke talaucine nima yanzu gashin kaina zanje naci na dauki ma aikata masu yimin shidima duk iko da isan da kikayi min da wahalan da na sha akansu zan sauke maganan zaki sa asake ni malama kiyi ta kanki ni yanzu za azo ayi belling dina".
tana rufe bakin ta kafin mommy tashi magana akace Barira Adamu tazo aka bude mata har zata fita tajuya tace " ammm Mommy zandan bude akwain gol din ki zan Dan zab'i wanda suka min kinsan na zama Hajjjaju."
ta k'arashe maganan tana d'agawa mommy kafada tare da canza tafiya irin kita tama zama Hajiyar tafice police din yaja kofar yasake kullewa
dafe kanta mommy tayi tace BARIRA aminceciya ta ke duniya
bajimawa aka zo akace Mommy tazo ahankali tamek'e tabi yar sanda
Dr Hafsa tagani a zaune a falon station din tazuba uban takumi mommy dafa Dr Hafsa tayi firgir ta juyo mek'ewa tayi tsaye tace'' Fanna kece acikin wannan halin waini meyake faruwa ne meyasa duk wannan abubuwan suke faruwa dake Dr Fanna ke macece me son ibada me yawan kyauta mewancan tausayi me yasa why why Fanna"?.
zama mommy tayi tace'' Hafsa sai yanzu na gane duk akan me duk wannan abubuwan suke furuwa dani Dr Hafsa nayi kuskure babban duk wannan abunda yake samuna na gama nazarin hakkin mama Emaka ne mama ta tana Sona tasha wahala akaina Mama har faskaren itace dayi tayi tuyan kosai tayi dako akai na duk dan tabani ingan taccen rayuwa duk wanda ya batamin rai Ina yarinya Mama sai inda k'arfin ta ya k'are tasha fada da mutane a kaina ta nuna min gata da son da ban taba ganin wata uwar ta nunawa y'arta ba amma lokacin daya na gudu na barta akan soyayya da kuma ra ayin zama musulma burina duk ka yacika narayu cikin in'ima wanda harda masu aiki na ma motar da suka ga dama suke hawa a duniya gaba daya ahalin yanzu idan banzo na 8 a masu kudi ba to bazan haura na 10 ba amma nabar mahaifiyata da danginta cikin talauci yanzu idan mama emeka taji nice Dr Fanna 3brother zata yafemin nayi kuskure babban a da tsoron masifan mama emeka ne ya hanali zuwa amma yanzu ai ba abinda zata iyamin meyasa banje na sauk'e hakkin ta dayake kaina amatsayin y'a ba duk da airniyace tana da hakkin akaina Allah bazai barni ba Ina son ganin Mama na duniya ta shagalar dani na manta uwar ta haifeni sai yau na tuna da ita ina buk'atan adduar Mama Dr Hafsa mama ta kawai nake son gani tabbas hakkinta ne yafara bibiyata nasan ta rayu cikin kunci adalilin rashina ".

Dr Hafsa ta numfasa tace'' hakane amma yanzu mu fuskanci halinda kike cikin idan kika fita zamuje wajen Mama zata yafe mana maimunatu tamin bayani a rar rabe naje nasamu nasir amma yana gaya min wasu magan ganu da ban gansu dasu ba meyake faruwa".
Mommy cikin kuka tayiwa Dr Hafsa bayani
Numfasawa Dr Hafsa tayi tace'' kinsan wanake zargi yanzu kuma NASIR nake zargi doctor".
girgiza kai mommy tayi tace'' Nasir bazai taba min haka ba duk da bai goyi bayana ba nasan mutumne da yake bayan gaskiya akoda yaushi azaton sa Ina da lefine shiyasa bai shiga cikin lamarina ba amma nasan watarana zai kuka da kansa idan abin yabiyo ta kansa".
cikin b'acin rai Dr Hafsa tace'' Fanna ki ajiye duk wani yarda da ki kayiwa Nasir ki bude Idon ki idan ba haka ba wllh haka zai gama dake dama so dayawa abinda kake son tashi Allah zai jarrabeka ni danaji FURUCIN Nasir akan ki tabbas na zar geshi".
Mommy hannun Dr Hafsa takama tace'' Dr kidena zaigin Nasir akan me Nasir zai min haka".

Dr Hafsa tace'' akan dukiya mana ba kin dauki dukiyar ki gaba daya kin dank'a masa ma yayi nutso aciki yaji dad'i yana tunanin yazama nasa saboda baki da yaro namiji sai kuma ga Nasrim ta haifi maza kinga dukiya wata rana zai zama na Nasrim ne da yaran ta shiyasa ya kashe mijin ta da yaran ta kuma ya d'aura al'hakin kisan akan ita Nasrim yanzu haka kimga wannan *sammaci* ne na daukaka k'ara wai bai yarda da hukuncin da aka yankewa Nasrim na zama agidan yari ba sai de a yanke mata hukuncin kisa
kuma gashi kema ance kotu za aturaki kinga dukiya yazama nasa yanda yahau kan dukiyar nan ba Wanda ya isa ya k'owace".
Girgiza kai mommy tayi tace'' Ah Ah Ah Hafsa Kar ki rabamin hankali karki da samin wani abu azuciya akan Nasir Nasir Amana ne awajena kuma Nasir bazai taba min haka ba duk Wanda ya shirya wannan to da niyar yarabamu da Nasir yayi dama kuma wllh kowaye ba zanyi nasara Allah yana ji yana gani".
tsaki dr Hafsa tayi ta tashi zata tafi mommy ta rik'ota tace'' Hafsa ya Nasrim kin je wajen ta kuwa".?
cikin b'acin rai Dr Hafsa tace'' eh anji ma zan koma akwai lawyer da yace na rakashi Nasrim akwai taurin kai irin naki har yanzu taki bada hadin Kai tayi bayani yanda lawyer zasuyi aiki akan sa saboda cese babban ne a high court anan za ayi Shari'a amma yanzu kafin nan zanyi cuku cukun beliln din ki dan idan kina nan aikin bazai tafi yanda yakamata ba duk dama Ayman da Ramadan da Kamal suna bakin k'okarin su k.....
Police din da yake tsaye akan sune ya ce Hajiya lokaci yayi haka de mommy ta dashi Dr Hafsa kuma tawuce office din D P O

Difio yace Hajiya cese din doctor Fanna babban ne bazamu iya bada belling din ta ba yanzu haka ma cuku cukun turata kotu muke idan kotu ta bada beliln to Al'hamdulillah".

haka Dr Hafsa ta hakura ta karasa gida tana zuwa gida abakin get ta tadda motan yan sanda da kuma wasu motancin 3 A FULL har anbude mata get zata shiga wani police ya dakadar da ita dacewa ita suke jira sunyi arrested dinta cikin mamaki tace'' menayi motan da yake tsakiyan motocin 3Afull ya nuna mata fitowa tayi ta karasa wajen motan ahankali Nasir ya bude kofar yafito da k'afar sa daya wajen Ido cikin ido ya kalli Dr Hafsa
yace "Mom yakike"?.
"Lafiya Nasir meyake faruwa ne".
Numfasawa yayi tareda kunna mata recorder din muryar ta acikin wayan sa inda take cewa Nasir take zargi ya mek'a mata sai da tagama ji ta mek'a masa

tace "kenan a yan sandan ne aka samu wani muna fikin ya tura maka tattaunawar mu ko."

murmushi yayi yace " ba munafiki bane akan aikin sa yake".
"Dr Hafsa tace'' shikenan yanzu yakake son ayi"?
"Mom baki ji police yace za atafi dake ba Ina neman hakkin na ne akan kazafi da kika min dan k'azafin kisan kai ba k'aramin cese bane".
Dr Hafsa tace'' Nasir kai ba mutum bane butulu azzalumin maci Amana ban taba ganin azzalumin irin kaba Dr Fanna kayiwa haka matar da har yanzu bata yarda kaine kake kulla mata duk wannan abun ba yanzu gashi ni da nake k'ok'arin akan naga tafidda ta nima kajefani cikin wani hali to wa zai tsayewa Fanna bata da kowa".
cikin sauri ya k'atse ta
"Ah Ah Ah Mom kika jefa kanki de Sharri na miki baki fada ba to Nasara baya yafiya kuma ba a sabawa umarnin sa."
ya k'arashe maganan zai ja kofar motan yarufe Amira da take cikin gida tafito da gudu tace'' haba Ya Nasir Mom cefa idan bakaji nauyin ta haifi irinka ba ai zakaji nauyin ya Ayman ko Ya Aliyu".
wani kallon kekuma awa Nasir ya mata
yace "ta shiga cese din kidan mune cese din gidan mu kuma hatta mommy ban ragawa ba balle ita cese din gidan mu family issue ne idan bare ya shiga bazai masa dad'i ba dan haka cikin ku duk Wanda yace zai shiga to zai gama rayuwar sa agidan prison
bayan haka Ina kuma Wornig din ku duk Wanda yayi gan gancin zuwa acikin ku da sunan zanyi belling din Dr Hafsa to shima zai gama rayuwar, sa a prison
Yana gama fadan haka yaja kofar yarufe direba yaja
Kuka Amira ta fashe dashi tana gani akayi cusa momn ta amota aka tafi


*Ummmm wannan rikicin na gidan manya ne Dr Hafsa kin kain ki sai Allah yafiddaki*

*Tofa masoya muje zuwa ko ya Izza da Humaira zasu kasance ko ya ya Nasrim take a* furzin
BATUL

*ban taba kuka acikin labarin na iran na yauba idon har dishi dishi yake dak'er nayi typing wllh pg yau yaman tausayi Sosai mommy tana cikin wani halin mutanen duniya akan dukiyar ba abinda bazasu iya ba wani lokacin kai talakan kafime kudin kwanciyar hankalin*





*BJ*
*08062383027*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
_rikicin babban gida_






*NA*





*BATUL ADAM JATTKO*




*masoya Ina godiya sosai da comment din ku Allah yabar kauna* 🤝




17


*Prison*

"kai kai kai ke dan uban ki haka ake surfen marara kiga ko dusa bai faraba shine kika bari kika zauna dan uban ki bayin kine zasu miki surfen da za a dafa abincin abaki".
ta k'arashe maganan tana d'aga kulkin hannun ta zata dokawa Nasrim da sauri Nasrim ta mek'e
tace'' ma'am dan Allah kiyi hakuri wllh hannuna ciwo yakeyi tayi maganan tana nuna mata tafukan hannun ta da yaduru ruwa sabar rike Tab'arya ".
"ke ki fa kiyayeni baki sanni bako ina miki sassauci nefa akan ke bak'uwa ce amma naga ke zumace sai da wuto dan haka kiyi surfennan tas yafita gacan wankin barguna na mokofta na na nazo dashi kezaki wanke tsaf Nasrim sake zubewa tayi a gaban shrgegiyar matan da tasha stocking cikin uniform na ma'aikatan gidan prison "Dan Allah dan Allah ma'am bani da lafiya Wllh".
kallon ta matar tayi tace'' rashin lafiya kike ke ba rain ma gaba daya kika dauka ba dan Allah ya d'aura miki dan rashin lafiya zaki damu mutane ke ko ba kece Halima 3Afull ba wanda labarin ki yacike duniya oganniyar marassa Ima'ni ashe gado kikayi gashe can uwar ki ma taso kashe kakar ku uwar mijin ta
ta hanya saka mata poisonin acikin abinci wai dan bata goyi bayan ku ba kai ni da zuma naji a cikin a daidata a nacewa ma tsohuwar ta mutu kinga gada kikayi awajen uwarki kisa saboda kuna da kudi".
"Paison mommy Hajja ta mutu to ina mommy me aka mata ita kulleta akai .?
tana magana cikin sauri kamar zata janyo amsan abakin matar
tabe baki matar tayi tace'' ai an kulle shegiya ashe anguluce da kan zabo kullum ita kenan a gidajen radio rerere da baki tana tallata aikin al'kairin da takeyi kowa kaji Dr Fanna three brother kamar ita dayace me kudi a duniya ashe de wai kudin nata bata hanyan halak ta Tara ba haba ai dama wannan dukiya da ayar tambaya akansa shi kansa Abdulsamad din fa cikin dama cikin shekaru kadan yayi kudin da duk duniya aka Sansa dukiya kullu zakaji anyi kaza an gina ismiya agu kaza an ankaiwa marayun jaha kaza tallafin gashi daga k'arshe hau ai ya gama fadawa kan ki da uwar taki yanz..........
katse ta Nasrim tayi dacewa "Dan Allah yanzu ina mommy tana ina".
tana can cell mana tana ta kanta daga k'arshe nan za a kawota ku hade ku cigaba da girban abinda kuka shuka".
wani irin azabeben Kara Nasrim tasaka ta zube a wajen summemiya
asbitin cikin prison din aka kaita doctor din ita ma ma'aikaciyar gidan prison din ce
tace'' haba madam Timona nafa gaya miki yarinyar nan ki bita a sannu tana da k'aramin ciki sannan bata ma cikin nutsuwar ta gaba daya ni wllh duk da tana da lefi tausayin Haliman nan take bani badan komai ba sai yanda magan ganun ta ya baza duniya ko Ina ita kamar ita tafara kisa kowa da abinda yake fada bayan kisan nan ko yau anyishi amma dayake ba sanannu bane shiru kakeji kai shahara da kudi masifa ne Allah mun gode maka da kamar a haka".
Madam Timona tace'' ke Safiyya ni wllh baruwana dawani kudin ta ko cikin ta duk abinda sauran sukeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login