Showing 105001 words to 108000 words out of 155717 words
Chapter 36 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
Insha Allah Nasir zaizo na yarda da uzurin Babanki na cewa yafi son idan Nasir ya bayyana sai ya dauke ku yakaiwa danginsa yace halima ta rasu amma ga ɗanta gakuma ke Fatima kinga yabada uzurin lefi yayiwa ƴan uwan sa ya gudu amma idan suka ganku gaba daya zasu yafe masa suce rabon kune ya fitar dashi kin manta yace yana da mata da yara acan maidugurin dan haka ki ƙwantar da hankalinki kinga ke yar dangice ma".
Mommy tace " shikenan Hajja".
Hajja tace "yanzu Fanna abinda nake so dake ya kamata a tara family meeting a sanar wa Nasrim gaskiyar lamari kin ga yanzu taware tafara harka da jama'a kinsan abin duniya baya buya zataji a gefe
da taji awani waje kwara taji awajen mu".
Mommy tace
"dan Allah Hajja abari idan shi Nasir din yazo sai sabar da ita amma har yanzu Nasrim bata gama gomawa normal ba".
Nasrim akan gado ta zube tana kuka sosai taji wayan ta yana ta ƙara share hawayen ta tayi taga baƙon numbar ne amma a tunanin ta wata mata da cese dinta yake hannunta ce dan batayi saving no din nata ba
cikin tsarƙewar murya na alaman ta gaji da kuka ta dauka tayi sallama
daga daya bangare aka amsa sallaman matar tace "Halima 3AFULL ko ".
"yes".
Nasrim tace badan ta gane me maganan ba
"ok Halima ni kuma Rafi'at Yakubu mrs barrister Fu'at Jiji dan Allah zan iya ganin ki a yanzu dan Allah ."
cikin sakin murmushi kamar agaban ta tace ayya ba damuwa sister ina kikeson mu hadu zaki zo gidan mu ko ni kikeson nazo".
ajiyar zuciya Rafi'at ta sauƙe tace " kinsan mu matan aure ba kasafe mukafiye samun daman fita ba zamu iya haduwa a gidana".
murmushi Nasrim tayi bata dauki maganan ta dawata manufa ba dan ita bata da saurin farssara abu
tace Ok zanzo ai nasan gida naje rannan akan wani cese da nake son sako barrister aciki sai Allah banyi samu haduba baƙanan amma insha Allah gani dan zuwa".
fitowa tayi sanye da doguwar riga dankwalin rigan ne akata iya kafadun ta kawai yarufe kasan cewar rigan bubu ne maroon colour yazauna sosai a fatar ta key din motan tane da wayan ta sai jakan hannu sauri take zata shiga mota ta hango Izza da Humaira suna ɗaga mata gannu shiga motan tayi ta zauna tana jiran isowar su suma zuna zuwa izza ta shoga front seat Humaira ta zauna a back seat
murmushi Nasrim tayi tace kun tuna baya kenan dan Allah mudawo da moment dinmu irin na da".
Izza tace har kin tunomin da wayyo Allah ƙuruciyar mu daɗi muyi wanka tare muyi komai tare".
wani irin dariya Haumaira tasaka tace " wanka tare wai ashe da wata idan ta zage wllh sai mutum yafita da gudu".
Izza ma dariya tayi tace "wllh kuwa su kwaila an bada mamaki".
daure fuska Nasrim tayi tace "i dade yanzu ba shegiyar data fini wani abu ai mahaƙurci mawataci da kuke cemin kwailan yanzu ai nayi shidan ku wllh".
dariya Humaira ta sakeyi tace "mai rakacaniya kenan".
itama Nasrim dariya tayi tace "har kin tunomin Zahra zanda Zahar ta fara fito da nono Izza ce ta fara gani ta gaya min na fasa ihu ina cewa mundena wanka da ita tunda tazama karuwa".
dariya sukayi suna turo ƙuruciyar su har Nasrim tayi parking a cikin gidan barrister jijjji
a babban parloun suka tadda matar gidan da bazata wuce sa'ar suba cikin mutumci ta Ƙarɓe su
can ta nisa tace "kada na shagalar daku dalilin kirana fa shine HALIMA meye tsakanin ki da mijina jiya yake gayamin wasu magan ganu a kanki wanda banajin zan yarda dashi".
shiru Nasrim tayi batace komai ba
Izza tace " Halima da mijin ki wa yafi can canta kiyiwa wannan tambayar".
cikin wani irin tsawa Rafi'at tace dakata malama bada ke nake ba da MAGE nake mai kwanciyar daukan rai ko nace macijiya wanda bata da ramin kanta tun farko Agrif ma ai saurayin ƙawar tane tayi ƙwanta ƙwanta da tagaji dashi saboda tana son auren kwarton ta wanda suka saba harka ta kashe Agrif din waye baisan irin ƙazamin rayuwar da ake agidan ba da auren ki kika hanawa mijin auren ki kanki kike bawa ƙwarto har kuka haifi yara 3 wanda ba ko tantama NASIR ne uban su bayan asirin yatonu ya gudu ya barki shine ni za lik........
HUMAIRA tayi wani irin tsalle ta cafo wuyan RAFI'AT
*MU KASANCE A 25 DAN ALLAH NAGODE SOSAI*
*BJ*
*FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
*25*
da sauri Nasrim tashiga tsakanin su tana jan Humaira daƙer tarabasu tace izza kaita mota Izza gaban Rafi,'at tazo tana murmushi tace " mrs Fu'ad kinyi kokari kuma acikin gidan ki keke mu munsan doko dan mu muke kafata ba afada da mutum acikin gidan sa duk abinda yameka kai katako amma idan a wani wajen ne baki isa ki daga ido ki kallemu bama ke idan a three brother ne wllh saide ki tsinci brain din ki a wajen kanki ai duk maccen da tayarda da kanta bata fada akan namiji"
"kut ni Rafi'ta Yakubu ƴar sarki jikar sarki wata take gaya magana haka garin nawaye dan uban mutum kuɗin ku din banza me da kuɗin naku inba rigima da rikici ba waye bai san har kisa kukeyi akan kuɗin ba ".
Nasrim jan Izza tayi tana dafa kafaɗan Rafi'at
idon ta cin nata tace " my sis kiyi hakuri dan Nasir ya haifi ɗan Agrif duk daya ne kede kiji da kan ki kuma ki gargaɗi mijinki muddin yaci gaba da ruɗani da kalaman sa masu rikitarwa to ina gaf da shiga rayuwar ku kuma idan kika sake nashiga cikin rayuwar ku to sunan ki sorry".
ta ƙaraahen maganan tareda jan hannun izza da humairah suka fice
har auka ƙarasa ficewa a parlour suna jin zage zagen Rafi'at
Nasrim tana cikin tuƙi ganin yanda duk moment din izza da humaira ya janza ahankali ta gangara gefen titi tayi parking ta juya ta kalli Humaira sannan ta sauƙe idon ta akan Izza tace meye haka sister dan Allah karku bari abinda Rafi'a tayi ya dameku dama yanda su khafulan sukayi kama da Nasir dole nawaje wanda baisan cikeken halaƙar muba ya zargi wani abu ko kunsan nima ada ina mugun mamakin yanda suka dauko komai nasa amma yanzu da aka gano momy da mahaifiyar Nasir ciki daya suka fito sai na dena mamaki kinga yarana mommy suka biyo dan de suma mazane shine ake ganin kamar tasu da nasir din kuma nima ai farine kawai ban dauko na mommy ba amma ai hancinmu da idon mu iri daya ne so meye abin damuwa zargine kuma Allah yasani".
tacikin mirror Humairah da Izza suka hada ido suka sauƙe atare izza tace "badamuwa tayi mugun cin zarafin mune taƙiraki har gida".
Nasrim tace "ba damuwa ta tada motan dan ta kauda nunanin su tace ". gobe thursday za ayi fulani's day na Rashida ku zaɓa mana ɗaya wanda zamuje a cikin Pattyn din tun bazamu iya zuwa duka ba" .
da sauri Humaira tace ".bride bath".
Izza tace " shegiya ƴar bidi'a to sister day zamuje ko Allah zaisa musamu ana walima".
Nasrim ta gyaɗa kai tafarayin rawa tana cewa "sai bidi'a sai bidi'a".
harsuka ƙarasa gida Nasrim tana cikin nishaɗi su Izza suna biyeta amma awani ɓangaren suba matuƙar tausaya mata ranan da gaskya zatayi halinta
Nasir awani anguwa da akayi sallan isha'i yaci gaba da zama acikin masallacin kama da misalin 11 wani mutum yashigo yace " ah waye kuma a masallaci har iyanzu lokacin rufe masallaci yayi kuma sai 4 na asuba idan ALLAH yakai ranmu".
Nasir ya ɗaga kai yana kallon mutumin da shi ba tsoho ba shiba yaro ba babba de haka ƙaton kwaɗo a hannu sa
yace "Babba karufeni
ni baƙone bani da wajen kwana".
mutumin cikin nazartan yanayin Nasir can yace "ayya ai bazai yuwu ba ƙa idane rufe masallaci amma kai baƙo daga ina".?
ahiru Nasir yayi yanayin saya canza
mutumin yace "shikenan ko zaka iya bina akwai shagon da yarana samari suke kwana a jikin gidana dan daganin ka bakayi kama da wanda zaka cutar da wani ba zaka iya bina".
ba musu Nasir ya maƙe yabi bayan mutumin har yakashi fanka da ƙwan suka fita yarufe, gidan nasa bani sa da masallacin
suna ƙarasawa bakin shagon mutumin yace " Hamza Ali Ibrashim Umar...
atare matasan samarin guda hudu suka fito cikin ladabi suka zube suna cewa gamu Baba
"yawwa ga baƙo nan kumasa shinfida kunga yafiku ku girmamashi".
daganan ya dafa ƙafadan Nasir yace "sai da safe ko".
gyada kawai yayi yabi samarin cikin shagon da taciki babba ne harda bathroom aciki
washe gari da safe aka kawowa nasir breakfast kokko da danwake da ruwa fure water 2 yaji dadin yanda yaran suke girmanashi
bude kwanon samiran yayi yaga danwake duk da bai san ma meye bane cokali ya dauka yana juyawa dan yasa aransa zai koyawa kansa cin kowane irin abinci yana son ya manta da rayuwar da yayi abaya bayan ya gama juyawa ya yakai bacin sa yana rintse ido yafara tauna ai baisan sanda yayi saurin dawowa dashi ba atake yafara wani irin shaƙuwa yana shaƙuwa yana firfita bakin sa dayake ji kamar an hura masa wuta aciki fito da harshen sa yayi yana girgiza kai
Umar yace " subbahanallashi Yaya ya haka yaji ne?
yayi maganan ya ɓula masa ruwan da sauri ya karɓa ya kafa kai yafara sha duk ya kwankwaɗe amma ko second ruwan bayyi acikin saba yadawo dashi
cikin gigicewa su Hamza suke tambayan sa bashida lafiya ne saida yadan samu nutsuwa ya kalli jikin sa duk yaɓaci da aman ruwa
yace "dan Allah ko zan samu nayi wanka.."
da sauri Ali yace " bari na ebo maka ruwa".
ya ƙarashe mafanan yana lekawa banɗakin ya dauko bokatin yafita Nasir ko dayayi wankan kayan mai gidan aka bashi yasa dan na yaran bazai masa ba darana shinkafa da wake akayi iya magi aha saka masa yadan ci balefi
bayan wata 2
Nasir kam sosai yasaba da mutanen gidan har cikin gida yake ahiga malam Ladan yayi mugun yarda dashi sosai,
Nasir kam zai iya cewa yana rayuwa cikin farin ciki amma yana tausayi yanayin talaucin rayuwar da sukeyi sosai
Malam ladan yana da mata biyu da yara 17 maza da mata malam ladan bashida wani sana'a sai na facin mashin a kofar gidan sa yaran sa wasu suna tayashi irin sana'ar sa wasu kuma suna zuwa kasuwa dan koyon wasu sana'o in,
sosai nasir yake jin daɗin rayuwar gidan musamman yaran yanda suke girmamashi yaya yaya abu ɗaya ne Nasir yakasa sabawa dashi shan ruwa ko fure water ba ya iya sha yayi yayi ya koyawa kansa saboda yana ganin wahalan da malam yake sha wajen saya masa ruwan roba na roban ma ba kowanne yake iya sha ba
Hamza yace
"Umma wllh wannan Ya AHAMED ɗinnan tausayi sa kawai nakeji gashi shiru shiru".
Umma da take tuƙin tuwo tace haka Umar ma yace amma sadiya tace tsoron sa takeji ko jiya da kuna kasuwa nace ta kai masa abincin sa wllh sai waje tafita tasamo yara suka kai masa".
Sadiya da take gefi tace " Allah Umma yafiye kallon mutane ga shegen tambaya ranan fa wai yake tambaya na wanne makaranta nake zuwa ina da saurayi ko ina ruwansa ni wllh kaman ninsa ma tsoro yake bani ga shegen shishigi".
ta karaahe maganan tana shigewa ɗakin su anan ta tarar Mamar ta
Mamar ta kalleta tace "wai ke meyasa bakida kunya ne wai Ahamed ba yayanki bane".
turo baki tayi tana cire shijabin islamiyar ta
da sauri ni kaina jattko naja da baya wow yarinya tacika maccen da dole Nasir ya shige ma dan duk wani abinda Nasrim takeji dashi to yariyar tana dashi saide muce masha Allah dan tsaya tsara kyan Sadiya ɓata lokacine
malam da Nasir suna zaune malam yana facin wani babur wani mutum yayi musu sallama malam yana ganin sa cikin rawan jiki yace "Alhaji da kanka sannu da zuwa mushiga daga zaure ko".
ya karashe maganan yana meƙewa tsaye
mutumin wanda malam yaƙira da Alhaji yawani haɗe
Fuska
yace "Ladan ba wannan ne yakawoni ba zaure kuma ai ko bakace na ahiga ba idan ina da ra ayi zan ahiga nida gidana Ladan ina maka uzuri ne saboda kanada ƙima a idon mutanen anguwa amma duk bakaga haka ba to nace maka nasa gidana akasuwa kuma dillalai sunce baza su shiga gidan matan aure ba nabaka nan da awa 2 ku kwashe duk abinda kukasan nakune kufita idan ƴan anguwan su matsu dakai saka wani yabaka nasa gidan nide gidana na sai dawane".
atake moment din Ladan ya canza cikin roƙo yace "Ahaji kasan ina da iyali dan Allah ka ƙaramin lokaci koda zuwa satine dan Allah".
"wllh bawani lokaci da zan iya badawa".
Nasir da yake tsaye cikin ɓacin rai
yace " haka ake tada mutum agida ba wani bada notice kuma haka ake saka gida akasuwa ba tare da anyiwa wanda yake ciki magaba ba ko yanada ikon tsaya,
aƙa ida idan mutum ya tashi saida gida sai yayiwa maƙota magana ida da mai so mai s kuma maƙoci bawai najiki kaɗai ba a a sai ka irga gida 40 a dukan gefe hudu na jikin gidan sannan kafita a hakkin maƙoci
ANNABI da yazauna yana karantawa sahabban sa hakkin maƙoci akan maƙocin sai da sahabbai sukaji kamar daga karshe Annabi zaice idan ka mutu maƙocin kane zai gajeka sabo kakkin maƙoci,
balle wanda yake cikin gidan baka masa magana ba kasa gida akasuwa kana ga baka shiga hakkin saba".
mutumin yace "ba hadisi nazo jiba gidana nazo na kwata awajen wanda yake ganin kamar gidan yasama nasa sama da shekara 30 tun auren fari kuma da kake maganan nayiwa makota magana akwai wanda zai iya sayan gidan nan ne cikin su kasan nawa nake son ayiwa gidan kuɗi ne".
numfawa Nasir yayi yace "maganan hakki nake gaya maka ba batun zasu iya ko baza su iyaba kuma nawane gidan naka" ?
Alhaji yace miliye 2 nakeso amin kudin sa lakasan".
Nasir ya kalli zoben hannnu sa nadana wanda aka zana (NN) jiki girgiza kai yayi afili yace bashiba
yaciro na hannnun sa na hadu
yace "gashi ka saida ka dauki kuɗin ka kakawo wa Baba ragowar kuɗin".
mutumin dariya ya kece dashi yace " nizaka renawa hankali zobe nanne zai biya kudin gidana".
nasir yace "muje kasuwar da ake saida gol idan ansaya abaka "
ko da sukaje mesayan gol gigicewa yayi da yaga farin gol irin wanda ake musu tallan su samo ko waya daya ne gram za atsaya miliyoyin kudi saida ya dauki hoton sa yatura a companyn three brother na Dubai sukace konawa ne yasaya su zasu bashi kudin
ya kalli nasir yace na saya 3 million".
kallon sa nasir yayi ido cikin ido yace " idan baka bukatan saya ka bamu muyi gaba kawai".
da sauri mutumin yace "shikenan zan saya 5 million".
Nasir kallon sayi yana girgiza kai wai zoben sa ake yiwa wannan tayin wulaƙancin zoɓen da yayi 50 million ake tayawa 5 tota yaya Nigeria zatayi albarka,
amma kawai dan bayason jayayya
yace "shikenan kawo".
godiya mutumin yayi tayi atake yaba
suna komawa anguwar mai anguwa yatara mutane shedu gida yazama na mlm Ladan
murna awajen mlm Ladan da iyalen gidan sa ba acewa komai abin da basu taɓa tsammani ba
Nasir yafito da dan kayansa cikin jakan keda
yazube agaban malam da matan sa da yaran sa da suke ta murna
yace " malam nagode sosai da karamcin ku bazan taba mantawa da kuba nakoyi abubuwa dayawa daga gidan nan wanda kuɗi bazai tsayesu ba Baba ga ragowar kuɗin kaja *jari*
ni yau zanyi gaba Allah yasaka muku da alkairi".
cikin sauri Umma da Mama sukace kamar yaya Ahamed ina zaka."?
" Umma bazan iya rayuwa a gidan da akasaya akuɗin wannan zoɓen bane daganan ya kwashe tarishin rayuwar sa yagaya musu amma bai ce shi daga 3Afull ya fito ba
da zaifita daga yaran har iyayen kuka suke sosai
matsawa yayi kusa da sadiya cikin sanyin murya yace " my HALIMA yau de shi'shigi zai tafi amma kisa aranki zan zo".
cikin kuka yaran suke cewa dan Allah yaya ka dawo mu bamason gidan kai mukeso dan Allah kar ka tafi shima Malam yameƙe yace " inde gidane mun hakura Ahamed daw..........
*******************
cikin murmushi Nasrim da tayi parking tace " au kana nan kenan ranka shi dade
".
ta ƙarahe maganan tana dauko jakar t abayan mota tareda juyowa tana kallon kyakkyawan saurayin da yake azaune
a saman motan durƙowa yayi yana murmushi
yace " ke kuma baki so hakan bako tunda naga alaman guduna kike ko".
ba haka bane
Habib kawai de ban zaci zan zon dawuri ba sorry".
"bawani sorry da zaki cemin Halima tun yaushe nake bin bayanki kike wani wulaƙantani to koke ƴar golce na hakura dake ki auri tsohon korton naki da kije jira yazo banda ba so makaho me zanyi dake ina dan gidan shugaban ƙasa banyi auren fariba na tsaya ina kulaki banza karuwa dake to dama i..........
"Habib ni kake kira da karuwa".
" au har dan nace miki karuwa kike jin haushi dan ban kiraki da asalin sunan naki ba kefa galefin zina gana cin amanan aure gana haifuwan yara shegu gana kisan kai soboda kada yaran su girma susan gaskiya kika kashe su saboda kina nason ko mawa wajen kortonki kika kashe mijin ki da hadin bakin ki kortona ki shi ya gudu da asiri yatonu k............
"da kata Habib wllh ni ban taba aikata *zina* ba asali ma ba abin dana tsana irin aikata zina amma kaine mutum na hudu da sukamin wannan gorin bazan dauka ba yanzu zan nemi hakkina na ƙazafin zina a wajen ka ba ɗan hugaban ƙasa ba ko ɗan majalisan ɗinkin duniya ne kai b".
cikin tsawa shima Habib yace "dalla malama ki rufawa mutane baki waye bai