Showing 54001 words to 57000 words out of 155717 words

Chapter 19 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

634

K'iran sallah sai kuma yamasa shud'uba yajuya ya mek'awa Humairah ahankal yafurta "sunan sa ABDULSAMAD amma za adinga kiransa da KHAFLAN".
sai yasake daukan me binsa shima yamasa kamar yanda yayiwa wancen ya mek'awa zahra yace " sunan sa ABDULRAHAMAN za adinga kiransa FAYYDAN
sai k'aramin shima yamasa kamar yanda yayiwa yan uwan sa yace " shi kuma ABDULSAMAD za adinga kiransa KHALDUM".
yayi kiss din yaro tareda fita dashi gaba daya a d'akin
wani uban ashe Nasrim tamaka tana dirowa a gadon Nasir da bai k'arasa ficewa ba yana jinta juyowa yayi ya mata kallon Ido cikin ido Wanda bata san ya zata fassara Shiba ya k'arasa ficewa yana murmushi

"Kan uba wannan wane salon renin hankalin ne shiwa meye hadin sa da yarana kai harda wani yimusu hud'uba dan iko har da fad'an sunan da za akirasu dashi wllh kayi kad'an tayi hanyar fita zata bisa Zahra ce ta rik'ota tace'' Ina zaki".?
"ki barni Zar d'ana zan karbo".
kafin Zahra tabata amsa Hajja tashigo da kwanon kunun kanwa da ludayi ahannu
tace'' ke kuma fa ko mutanen na kine sukaji k'arnin jini suka tashi kike wani fincike fincike".
Humairah ce tayi mata bayani tana dariya
Hajja tace'' ooyo aikin banza dan kinsamu ma Nasuru yanuna kulawan sa akan yaran ki kike wani falli kinga yanuna kulawa akan dan gidan Humairah da Kamal ne ko kinga ya taba d'aukan yan biyun Izza kema kinci darajan shak'uwa su da Haruna ne".
Nasrim muzurai ta bara da ido ta zauna a bak'in gadon tana gunguni
Hajja tace'' gashi kunnun kanwane saboda ya warkar miki da gun kwanciyar yaran da wankin ciki idan kinga dama kisha".
"ni kam gaskiya ba kunnun da zansha ai nasha maganin".
Hajja zatayi magana me aikin mommy Zahira tashigo ta zube a k'asa tace'' ranki shi dade Halima yallabai Nasara yace zan kai masa Khafulan da Fayydan".
Hajja tace''suwaye kuma hakan".
Zahira tace'' ban sani ba haka de yace".
dariya Izza tayi tace'' Hajja jaririn na ne mana".
Hajja tace'' gaskiya sunan yayi d'adi".
sai da Hajja ta dage Sosai Nasrim tabari Zahira tafita da yaran
Nasir yana zaune da Khafulan aciya a parloun mommy Zahira tashigo da yaran ahannu mek'ewa Nasir yayi tsaye cikin tsawa yace "ke baki da hankali ba zaki nemi wani yataya kiba zaki cukuy kuyamin yara kaman kayan wanki kika...
Mommy ce tamek'e ta karbi yaran daya bayan daya ta kwantar akan kujera tace'' Zahira jeki abinki". Jiki
na rawa tabar wajen . mommy ta kalleshi tana mamakin yanda ya damu dasu tace''sorry Abban su Khafulan."
murmushi yayi yace "mommy sunan yayi kyau dani daga yau kidena kirana da son sai Abban KHALDUM".
Mommy tace'' eh mana gashi nafara ai ka girma kazama Baba Allah de yanuna min naka yaran".
tsugunnawa yayi yana janye showel din da ya rufe fukan Fayydan yace "mommy bakiyi mamakin yanda jariran nan sukayi kama dani ba".
Mommy ta dauki Khafulan tana sake kallon sa sosai ta numfasa tace'' ai kowa mamakin yakeyi saide idan akayi la a'kari da uwar da uban duk ka jinin ka ne ba abin mamakin bane su biyo ka a na samun haka Sosai kai wani mafa kwata-kwata basu had'a dangi ba amma sai kaga suna fisgen kama".
"ajiyar zuciya Nasir ya sauk'e
yace" mommy ban taba son wani abu a duniya kamar wadan nan yaran ba mommy ina son kizama sheda na basu rabin kasona acikin dukiya ta sannan idan Allah yasa na mutu ban haifi wasu yaran ba na basu duk a bin dana mallaka a dukiya".
zaro ido mommy tayi tana kallon sa tace'' Nasir baka iya hausa ba cewa zakayi idan na mutu ban haifu ba amma idan kace idan na mutu ban haifu wasu yaran ba tamkar kana nufin kai ka haifi wadan nan kenan kuma gaskiya kyautar tayi yawa kade duba wani abu ka musu kyau tan dashi amma rabin dukiyar kafa zai iya zama wani abun da ban a gidan nan kaga Abdulsamad yaron Kamal shine babban amma banajin ko daukan sa ka tabayi ga yaran Aiban suma yan biyu baka taba d'aukan suba sai wadan nan zaka sa adinga ganin kamar kana nuna ban banci ne saboda su wadan nan jikoki na ne baza suyi duba da shak'uwar da yake tsakanin ka da Agrif ba saide ace dan ni kayi kaga ba dad'i dama Hajja tayi mugun sa Ido akan abinda Allah ya bani duk da ban rage su da komai ba kuma ban zag'e akai na nuna musu nawa nawane ba yanzu idan taji an bawa yaran Nasrim wannan babban kyauta zatayi magana". daure fuska yayi yace
"Mommy nide na basu kuma kar ta fasa tayi maganan naji".
Mommy tace'' ah ah son ai ba agaban ka zatayi ba".
kawar da zancen yayi da cewa "mommy yanzu wane Madara ya kamata afara daurasu kinga Faydan yunwa yake ji".?
yayi magana yana nuna mata dan yatsar sa da Fayydan din ya raruma zai kai baki
" ai Abban Khafulan nonon uwa shiyafi dacewa akan komai awajen jariri amma tunda sunyi yawa balalle ya ishe su ba NAN yaka mata a hada musu dashi".

*****************
a ban garen su Nasrim kuma

shigowa Agrif yasa su Izza dasuke da faman lallashin Nasrim ficewa a d'akin a hankali ya k'arasa yazuba guiwowin sa a k'asa sunkuyar da kan sa yayi itama batayi magana ba amma tayi mugun cin kunu rasa yanda zayyi yatun kare yayi can ya numfasa yace " hakuri juriya sune mataki na farko na nasaran komai a rayu musamman akan soyayya nasrin zan baki hakuri akaro na ukku wanda in Sha Allah shine na k'ashe wanda kuma ina sa sammanin yafiyar ki saboda girman SOYAYYA ta a zuciyar ki".
me makon ta bashi amsa sai kawai ta mek'e tsaye kamar zata shiga bathroom tafara wak'a cikin zazzak'ar muryar ta tace'' _ashe Wanda kayar da dashi wataran zai cutar da kai k'ashi nide rayuwa nake Sam Sam bani da jida kai kaicon wannan rayuwar Wanda ka so shi zai ba dakai shin dawa zaka yarda ne_
sauk'e numfashi yayi
shima yana mek'ewa kamo hannu ta yayi yace "Halima da kanki kawai zaki yarda ba mutane duniyar yanzu ba koni bance kiyarda dani ba dama kawai na keson kibani Nasrim jiya yawuce yanzu ma zay wuce wllh Nasrim aiki ne aka hadani dashi kuma aka d'au reni da umarni uwa wanda yazame min dole nayi amma bana jin akwai fitar nufashina da zai iya fitowa cikin k'oshin lafiya ba tare da tunanin ki ba ni na yarda da kaina bayyi dan na cutar dake ba"..
zama takoma tayi tana kallon sa tace'' Agrif ni bana fushi da kai tunda naganu matsala mu
kasan meye matsalan mu ne".?
girgiza kai yayi yace " nasan Wanda na sani amma ballene nasan wanda kika sani ba sai kin sanar Dani".
ajiyar zuciya ta sauk'e tace'' Nasir ne kuma saboda ni ya K'ara maka yawan aiki saboda baya son muji dad'in rayuwar mu meyasa dacan bai k'arama ba sai yanzu amma kai ka kasa yarda kullum k'okarin kareshi kake".
g'ada kai yayi yace" good naji dadin yanda kika gano manu farsa abin da baka sani ba shi zai cutar dakai wanda kasani kana da al'hakin shayo kan matsalan Nasrim a sharawa ta a halin yanzu idan muna son mu kasance dare dole sai mun hak'ura da karatun ki duk inda zanje muje atare".
"a a a ya Agrif ba zancen ajiye karatu na saboda shima yana daya daga cikin burina".
"to Nasrim so dayawa idan aka hada buri biyu to basa cika gaba daya sai an kashe wani araya wani amma ni zabin ki shine nawa".

"gaskiya na zabi karatu Yaya sabo burina ne tun ina yarinya nazama lawyer saboda na nemi hakkin cutar dani da wancan azzalumin yayi wajen ciremin yatsa sai dana girma na k'ara wayo nasan cewa alokacin da yamin hakan bai kai minzalin da za ayi Shari'a dashi ba amma duk da haka banji bana son zama lawyer ba saboda burin daddy na ne".

"Ok to Nasrim ni zan zame miki dukkan garkuwa wajen ganin cikar burin ki dan haka nidake zamuyi hakurin bin rayuwa yanda yazo mana dan haka meye matsalan ki game dani ayanzu bayan wannan"?.
"Yaya Agrif babban matsala ta shine bari da kayi wannan dan rai nin hankalin yake yanda yaso kana sane da cewa shi ya karbi haifuwa ta bayan ba muharramina bane sannan yazo yashigo min har d'aki batare da neman izzini ko sallama ba dan iko har yasawa yaran mu suna da bada umarnin sunan da zamu kirasu dashi cikin iko da isa".
murmushi yayi yana jawota jikin sa yayi hugging dinta Sosai atare suka saki ajiyar zuciya har sunaji bugun numfashin junan su
ahankali ya dan janyeta suna facing din juna yace " dan yakarbi haihuwa ba matsala bane wani can daban ma inde likita ne zai iya karban hafuwa musamman da matan suka kasa
zab'an suna kuma bawani matsala dan yanuna kulawa ga yaran mu kuma koda nine ita abinda zanyi kenan na maida suban su daddy tunda magadan sune".
shikenan amma sunayin da yabada akirasu dashi ne bazan Kira ba".
murmushi yayi yana shafa fuskan ta yace " wannan kikon kine na uwa my beautiful wife ke wallahi haifuwar ma wani k'ayatacciyar kyau ya karamiki anya bazamu koma part din muba".
ya k'arashe maganan yana Shirin setting din bakin su
salatin Hajja ne ya dawo dasu hayyacin su tana tafa hannu tace " nashiga ukku ni lami ke Aisha zoki ganonin meye haka Ummu da Mama da suke parlourn da sauri suka shigo gaban su yana faduwa atare sukace lfy Hajja
"Ina ko lafiya ku gano min mejogon yau yau dinnan yakama yake tandewa saura kiris komai ya baru nazo kai Allah ya bawa wannan yarinyar Halima jaraba ko dan jinin inya murai ce ni maryama yau naga jaraba"
Ummu hararan Agrif da har yanzu hanun sa yake cikin na Nasrim tayi tace''Hajja ga me lefin nan ai shine ya tako yazo tashi kafice kar nasake ganin k'afanka anan". ta k'arashe maganan tana nuna masa hannan fita

fadin irin shidiman da Nasir yayi wa yaran nan b'ata lokaci ne a part din Mama yamusu d'aki namusamman haka a part din mommy da na Ummu dana su Nasrim ya musu wanda duk in da aka kai su suna da komai da za abuk'ata kudin kam yakashe kamar bayaso Nasrim tun tana fasifar yanda Nasuru yake nuna iko akan yaran har tazuba Ido ganin abin yafi karfin ta bikin suna ko center aka kama na musamman aka Sha shagali duk da dagashi Nasir din har Agrif din sun koma bakin aiki su akayi sunan

*******************
A yau Nasrim zatayi arbanin kuma ayau Agrif ya sauk'a a k'asan da sanyi safiya dama tunkafin yazo yasa sarkin gida an gyara gidan ta ko ina ya sha finti hatta kayan furniture an canza gashi dama wannan aikin da yakeyi manya kudin ne suke shiga hannun sa saide shi mutum ne mai facaka idon sa idon kudi sai ya b'atar ga kyauta shiyasa Baba yakubu yake cemasa nd'ororo
Nasrim kam yaran ta sun warware Masha Allah dasu kamar ba yan ukku ba ga wayo sai faman rawan kan tarewa part din su take a daren ranan aka rakata da Sabin yan aikin ta wanda zasu tayata kula da su Khafulan Shatu da Adama
bayan fitan su Izza Nasrim yayi sallama dasu Adama ta barmusu yaran da duk abinda zasu buk'ata dan dama tare suke kwana dasu
Bedroom din su na sama tanufa wanka ta fesa tafito bayan tayi shafa'i da wuturi ta zauna a bak'in mudubi mai kawai ta shafa ta nufi wodrop wani English wears mekyau da kama jikin tasa ta dauki turarenta tana fesawa taji an murda handle din kofar tacikin mirror suka hada Ido gira ta d'aga masa tana jifan sa da murmushi ajiye ledan hannun sa yayi ya k'araso inda take ta baya yazoro hannayen sa yayi hugging dinta cikin tsokana
yace " kai wannan amarya tawa da rawan kai take keda yakamata nasame ki a zaune a saman gado a lulube da liffaya na tsayi baki kamar ko wane ango kawai sai nasameki ahaka".
"au haka ma kace to kafita sai nayi".
"No no ni ai hakan yafi min ma alamace na baza aban wahala ba".
murmushi tayi tace'' Abban KHALDUM kaje kagan su kuwa".?
shiru yayi can yace " zanfi son ki kirani da Abban Amreesh".
"Amresh wacece kuma haka".
murmushi yayi yace
"wanda nake sa ran ayau zan ajiye anan"

yayi maganan yana shafa maranta

"cikin mamaki tace'' sure baka son na kiraka da Abban KHALDUM ko Khafulan".
cikin dan daure fuska yace " because nafison akirani da sunan inkiyar Baban yarinyar mace kinsan ina mutuwar son y'ay'a mata".
ita ma hade fuska tayi tace'' amma ai kowane mutum da sunan first born din sa ake masa inkiya kuma su Allah Ta'ala ya bamu".
cikin rashin damuwa yace
"Ni kuma second born na zab'a sorry zanje na dubasu amma yanzu nafi buk'atar mamar su".
ya k'arashe maganan yana cusa harshen sa cikin kunne ta ahankali ya fara kunce igigoyin rigan ta still harshen sa cikin kunne ta dai dai sanda yagama kunce igigoyin rigan yayi k'asa gaba daya dama ba Bren ajikin ta atake lafiyayun books din ta suka bayyana hannu sane yafara rawa ahankali ya d'aga hannun zai Kai kan books din
Ringing din wayan sane ya dawo dashi cikin hayyacin sa dan janye ta yayi yazoro wayan Nasara yagani b'aro b'aro ajiki cikin sarkewar murya yace " sorry my wife two minutes".
yafita da wayar sai da yaje har parlourn k'asa ya dauka
"NASARA ko gani kafi mutum NASARA me wuyar badanci goshin jirgi me wuyar karau ya akayi".?

Dariya Nasir yasake yi daga ban garen sa yace " bakomai angon bazauwara me y'ay'a ukku inason katuna da wannan kafin kashiga daga ciki".
Agrif ma dariyar yayi yace "hakan ma nagode ai guntun gatarin ka yafi sari ka bani auren bazauwara ai sunnan ne kuma bakaji hausawa suna cewa dumaso kafi sabo dad'i ba
Musamman ni danayi dace da macce kamar Nasrim auren me dad'i arayuwa da mosoyi me dad'i dan duk wanda bayyi shiba rayu bata masa dad'i ba kuma yana gaf da tabewa kasan me NASURUDDEEN wllh da na kasance cikin d'akin aure daga ni sai Nasrim jinayi duk wani damuwa ta tafi jinayi kamar danni aka halicci duniya jinayi kamar in........
cikin wani irin tsawa Nasir yace "dakata Agrif yanzu kasani baka san ya gobe take ba musamman me gurba taccen rayuwa irin ka wllh ka dauwa kanka kara da kiyashi".
dariya Agrif yayi yace "sorry NASURUDDEEN ai da Karan da kiyashin na cefar su na gama k'onasu tuni rahama ne Allah Ta'ala ya nuna maka mak'iyin ka wawanci ne ka kasa kare kanka daga sharrin sa katuna wannan to na dauki matakan kariya".

shima Nasir dariya yayi yace "wanne mataki ka dauka hanyan NASURUDDEEN yana da yawa wllh ba Wanda ya isa ya nuna zai ja dani..........
Agrif haurawa sama yayi ba tare da ya kashe wayan ba yafara kwallawa Nasrim Kira
"Hony kina kina zakara yayi Kara bani Rena mafara rik'e son mu a task'i ra rik'e dan babban gida ni bana jan aji soyayyar k'unci ni nazama megida agareki kiyi mini shimfid'a guntafi kuma ta iya sam batayin Shariya randa duk tayi dariya zuciya kauna ta tad'a".
da karfi ya sake cwa
SO YAKORI HAYANI......
yanda Nasir zai ji da kyu

wani irin jifa Nasir yayi da waya yabuga kansa ajikin bango da sauri ya rarumi kwalban giyan da yake gaban sa ya doka a kansa atake kwalban ayi rugurugu a kan sa jini yafara fitowa ya rufe fuskan sa gaba daya baya ganin gaban sa hakan yasa yafara dake kwalaban da suke fashe awajen suna nutse masa a k'afa k'aran da yayi ni yasa Aliyu da yake parlourn shigowa da sauri
"What!!!!
yace alokacin da yaga yanda Nasir ya maida kaman nin sa
"meye haka Sir me yafaru da kai "?.
Nasir girgiza kan sa yayi yana fatsar da jinin da rafure masa fuska aiko
jinin da yake cikin gashin sai da yab'a ta jikin Aliyu Nasir hannu yasa ya goge jinin fuskan sa cikin muryar Wanda yafita a hayyacin sa yace " ya cucuce ni kashe sa zanyi wllh mutuwa zayyi zayyi mutuwar wahala wannan *FURUCI NA NE*




lodinng

*To masoya muje zuwa rikicin babban gida za mu kasance a pg 12*


*Bj Dan bada shawara ko tambayar ko cin gyara*
08062383027

*Ina k'ara godiya sosai da comment din ku Allah yabar kauna*


[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
( _rikicin babban gida_)





*NA*





*BATUL ADAM JATTKO*



*Kai Masha Allah da masu comment* 🤝



*12*

*ban samu nayi editing ba kuyi hakuri idan k'unci garo da typing errors saboda Ina cikin wani uzzu'a*

"Nine ajalin sa kashe shi zanyi".
da sauri Aliyu ya karasa inda yake ya kamashi ya kwantar akan bed da sauri ya k'ira motan asbiti ba ad'au lokacin ba likitocin suka samu nasaran cire fasassun kwalban da yaka tare a ciki k'afer nasa sai aka amasa alluran bacci d'inkin daya aka masa a kan sa
bacci yake sosai Aliyu yana kusa dashi a zaune wayan Nasir ne da yake hannun Aliyu yafara Ringing cikin hanzari ya dauka ganin mommy ce
"Abban Khaldum kana lafiya kuwa jiya ban jika dasafe ma haka bayan kuma mun......... cikin ladabi Aliyu ya katseta da cewa "mommy sorry Aliyu ne"
"Aliyu ina shi Nasara".?
"amm andan samu matsala ne bai da lafiya bacci yake".
"What me yake damun sa yana ina a ina yake tun yaushe ba shida lafiya meya sameshi".
"Sorry Mom muna hospital amma yana baccin bawani abin damuwa".
cikin tsawa tace "Aliyu abinda ya same sa nake son kasanar dani".
"amm dama mommy kwalban ya fasawa kansa yana ambaton sunan A'A wai sai ya kashe sa amma de ina ganin family issue shiyasa ban bincika ba".
"Subbahanallah me yafaru to tsakan sa da Baban gidan har haka me zafi to sosai ne Nasir din yaji ciwo ne Dan Allah ya yake".?
cikin matsanacin damuwa taketa jero masa ambayar
"Mommy kar ki damu jikin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login