Showing 84001 words to 87000 words out of 155717 words

Chapter 29 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

652

tasa waya agaba tana ta rusa kuka itama Humairah rungume Ummu tayi ta fara
Kuka Ummu tace'' Humairah bazan iya ba bazan iya ba ankaini bango ya isa daga yanzu zan nuna nima uwace kuma Haruna yana da gata kamar kowane da agun uwa da baifi da ba mutuwar Agrif ko shekara bayyi ba har Nasrim da take gidan kaso ta ware tana daura hotunan su da waka ba shakka wata ranan sakin ta za ayi ta zo ta zauna to ko yanzu meye yayi saura tana gidan prison amma tana da duk wani Freedoms na rayuwa da ganin Nasrim acikin walwalan ta take tunda har tasamu danan daura hotuna".
Humairah tace
"Ummu kiyi hakuri ai ya Nasir yana bayan mu shiyayi duk wani ciku cikun daukaka k'ara kuma wannan abinda tayi ta sake tabo kowa ma duk wani wanda baya koyon bayan ta to zai fito yayi magana muna tare da ya Nasir Kamal ne yake tare dasu ni wllh sai na bar masa gidan sama akan fansan dan uwana kuma ni har shi Kamal din zan shigar k'ara duk wani bayanan da yan sanda suka nema duk yasani kin fada yayi dan kar a kashe masa k'anwar sa tes din da ya Agrif ya turamasa na yazo yaceceshi Nasrim zata kashesa ai gogewa yayi sai a wayan ya Agrif din aka gani".
"Humairah Abu kune yake cewa nayi hakuri shima Abbaty bawani abinda yakeyi Yana bayan Dr Fanna gaskiya yanzu bazan iya ba Nasrim ta cutar dani ta kashe min d'an da yafi yimin biyayya me farin jini ta kashe yaran sa amma anbarta nata rayuwa kamar kowa".

Humairah tace'' Ummu dama hukuncin da aka yankewa Nasrim bayyi dai dai da lefinta ba hukuncin rataya yakamata ayanke mata kawai shima daddy kanin y'ar sa ce bayyi adalci ba wllh wllh sai an kashe Nasrim idan ta haifu".


Nasir ya shiryawa Mommy zuwa umara yayi Wanda zatayi wata ukku acan kuma idan tazo agida zata sauk'a ranan da mommyn tazo aranan Nasrim ta cika sati da haifuwar dan ta namiji me kama da Agrif sak amma shi farine Abu yazo duba yaron an masa hud'uba da Haruna
a ranan sunan aranan Madam Timona ta shirya wani Dan party akayi sa'a kuma aranan ne birthday din Nasrim ita Nasrim duk wannan bai da meta ba bata ma tuno yau ne birthday din taba tana tsaka da kuka su Maryama suka zowai sai tafito waje haka firsunoni yan uwanda suka jata ta fito abin mamaki Mp takani suna ta raye raye girgiza kai tayi ta dafe kai zata koma wata ta jata tsakiyar filin alallai wai sai tayi rawa murmushin da yafi kuka ciwo tayi tad'an ged'a kai a laman tayi rawa murmushi tayi tafice acikin filin d'akin ta koma direct tana rusa uban ihu kuka ko zataji sanyi suko sai rawan su suke suna na nata Haruna happy birthday Halima happy birthday tana jin iface ifacen su da raye raye da suke

ashe duk wannan party da Timona ta shirya dan ta sake daurawa a media ne murnan haifuwa dakuma birthday party Nasrim takeyi a cikin gidan prison abu yasake jakulewa masu zagin Nasrim suka Kara azama tsine mata

Ko Ina kale k'a a media bayanan Nasrim zakaji k'arya da gaskiya

aranan Mommy ta dawo Nasir bai koma ba komai na three brother ya tsaya cak hatta aiki

Mommy jikin a hanyaye ta sake kallon Nasir tace'' to wai ya akayi ta samu wayan ta kuma meya hada gidan prison da kayan kid'a meyasa Nasrim batayi tunanin abinda zai biyo baya ba take haka ko mutuwar Allah mijin ta yayi ai bazatayi haka ba mutuwar sa ko shekara bayyi ba Nasrim ta janyo mana hau da abin fad'a duniya da a gidan nan ."
Nasir yace'' Mommy wannan shi ya tabbatar da Nasrim me lefice kamar yanda kowa yake fada dan haka karma kiji wani abu idan an yakke mata kukuncin kisa".
kuka mommy ta fashe dashi Nasir fe cewa yayi mommy taci gaba da rera kukan ta

Kamal ne yashigo yana yadin ga zuga Mommy akan Nasir baya kaunan Nasrim tare da hujjoji masu k'arfi numfasawa tayi tace'' nasani Kamal baya sonta nun tana yarinya amma meyasa har yanzu bazai can zaba".
"Mommy saboda yayi alk'awarin bazai taba barin Nasrim taji dadi a duniya ba ko kinsan Nasir ya kulle Dr Hafsa saboda tana zuwa visiting wajen Nasrim watan Dr Hafsa hudu a kule kamar yanda ke kike a kulle bakiga kina can ba mezuwa ba haka Nasrim ma da nake zuwa wllh yahana zuwan kuma idan lawyer bai samu daman ganin Nasrim ba lalle muyi Na sara ba zamu iya samun babban matsala Mommy ki ajiye son Nasir a gefe ki k'waci yaruwar y'arki wllh Nasir baya son Nasrim kema kudin ki yake so daga zaran ya samu zai gujeki duk take taken sa wllh dukiyar yake yiwa k......
Mommy mek'ewa tsaye tayi cikin sauri tace'' Kamal koma baya me kake cewa Nasir yasa an kulle Dr Hafsa saboda mu shiyasa yaki yakawo min wayata tunjiya da nazo nake bin bayan sa ya bani waya ta na kirata yaki kuma ya hanani fita ashe shi Sherri da ya kulla kenan me Dr Hafsa ta masa".?
Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Kamal ya d'aura da cewa
"Mommy abinda nake son kigane kenan duk akan kudi yake yi".

"kudi fa kace Kamal iya na kudin yake komai yana gunsa harrta company shikafa yanzu Yana wajen Nasir".
Murmushi cin nasara yayi a fakaice
yasake cewa mommy wllh kinyi kuskure mommyn akwai wani abu da na nake son na bayyana amma sai anje gaban Hajja an Kira family meeting anan zaki gane Nasir k'in gaskiya yake miki keda y'arki".
"Kamal ka kayamin tun anan meye ne dan Allah ".

"Mommy zai iya daga miki hankali sai mun hadu a main parlour
Sai da safe Kamal yasa aka tara kowa Nasara ne Yanuna bazai iya zuwa ba mommy da kanta tazo ta sameshi tace taron nawane sai katashi kazo".
tana gama fadan haka tafice cikin mamaki yake bin bayan ta da kallo to meyasa mu Mommy
a haka ya tashi ya bita daga shi sai riyan bacci yana tsaki ya yi sallama daddy ne ya amsa yasamu gu a twositer ya zauna Kamal tashi yayi tsaye yayi addua bude taro ya fara bayani kamar haka
Daddy kai da Abu nasan abin da zan bayyana ayanzu zai muku ciwo tunda ya shafe ku shine ma dalilin da yasa nayi shekaru 7 Ina boye abin saide cigaba da boyeshin zai iya zama matsala zuwa gaba musamman yanzu da ake neman mafi akan wannan abubuwan da suke faruwa amma dan Allah kuyi hakuri".
ya k'arashe maganan yana zuwa gaban tv memory ya fitar yasaka acikin DVD ya kunna tv take Nasir da Agrif suka bayyana danna stop yayi yasake yace wa "daddy wannan video ne na daukeshi aranan da Hajja tak'ira Agrif akan yazo Nasrim tana da ciki ai su biyu suka zo idan baku manta ba suna zuwa direct a gerdeng suka tsaya nima Ina cikin akusa dasu bayan bishiyar kwaiba daganan ya danna pl duk tattaunawar da Agrif da Nasir sukayi wanda yanuna k'arara yara na Nasir ne gashi a filli ya bayyana har gargadin da Nasir yakeyi wa Agrif na idan bai saki Nasrim ba rayuwar baza ta tabayin musu kyu ba
kowai gashi ashi a bayyane

wannan shiya tabbatar wa iyayen yara na Nasir ne

Hajja ce tabara kwallah Kara tana ihun kuka suma su daddy kukan suka fara haka Humairah Mama Ummu hatatta Izza yau abin ya girgiza ta sai kuka tayi ita duk masifan da take tsammanin zai balle batayi zaton zayin haka ba daddy da Abu suma kukan suke suna maimai allahuma gafurni'walhamni
gaba daya dasu da yaran kuka suke ba me lallashin wani
cikin kuka Ummu tace'' Nasir Allah ya isa tsakani na dakai da Nasrim da ita uwar munafukan Dr Fanna ashe kwara da gaskiya ta bayyana na dena yiwa shegun yara kuka haba dama da alaman tabbaya yanda sukayi kaman nan kaman ma har ya b'aci ni nasa wannan araina tun randa FAYYT ba shida lafiya jinin kowa bai masa ba sai na Nasir za a saya a saka yace kar a sawa d'an sa jinin saidawa gashinan zuwa aranan yazo kuma nasa jinin ne yayi mun dauka duk a zumunci yakeyiwa ashe yaran sane
Allah yajin k'an Haruna ya mutu da bak'in ciki mafi girma wllh ita ma Zainab din tashi ce banzan karbeta amasayin jika ba harshi wannan jaririn duk da ban ganshi fili ba a hoto fari ne bazan k'ar ba ba bajinin Haruna acikin su balle Zainab da itama kama daya sukeyi sak ai shegiyar ce....

Mommy cikin Wani irin zafi ta dashi ta shak'e Nasir iya k'arfin ta dace da gaske ne nace da gaske ne Nasir Allah yagani ni da al'kairi na soka nace da gaskene ban yarda da wannan video ba gayamin gaskiya duniya abin tsorone za a iya hadashi amma ka fadamin da bakin ka.....
ta k'arashe maganan tana sakin sa zubewa Nasir yayi agaban iyayen nasa yace'' Mommy sharrin shedan ne da k'addaran ALLAH ya rubuta dama rayuwar su Khafulan a haka zai zo amma Aiban Zainab da wannan jaririn wllh yaran Haruna ne ni sodaya tak habin yafaru ku yada dani kumin duk hukuncin da yayi dai-dai dani".
"girgiza kai mommy tayi tace'' Nasuru kafi shedan iya hada tuggu kuma Nasir Allah ya isa ba wani hukuncin da zamu yanke nida kai sai agaban Allah".
Hajja tace''towai Abdulmajid Abdulrahaman ku ba abinda zakuce ne bazaku dauki madoki ku fasa kan shege ba wannan ba jinin Abdulsamad bane tabbas an can zasa Dr Fanna sai muyi Shari'a dake wannan wani shegen d'anki kika Haifa yazo dai-dai lokacin da Halima zata haifu kika dauke namu kika sako naki kuma kika samu nasaran shiga cikin gidan kika reneshi ni dama najima ina tunanin ya akayi yaron nan yake kama dake ashe dan ki ne ban yarda ba sai kin nemo min jikana na asali wannan ba jikana bane wllh Shari'a zamuyi da gan_gan kika kashe Halima bawani wasiya da tabada na ki auri mijinta yama za ayi hakan ta faru kawai dan kin karbi haifuwar ta dan yayi kama dake sosai ni dama Ina zargin wani abun yau ayanda kuke kama dashi wllh ban karbi Nasir ba kamar yanda Amina tace bata karbi Zainab da wannan jaririn da akasawa sunan Haruna ba cikin kuka ta k'arashe maganan zan iya cewa tun da family nan suke basu taba shiga cikin tashin hankali irin wannan ba dan atake Abu ya yanke jiki ya fadi daddy da Abbaty sukayi kansa amma Ina da alaman ya gamu da paralysis cikin sauri daddy da Abbaty ne suka dauke sa zuwa asbiti mommy taci gaba da newa nazama makafuwa dama Dr Hafsa ta gayamin kaine kaine naki yarda yanzu Kashi kayi abinda hankali bazai taba kawoshi ba Nasir na tsaneka ina son ka dawo min da dukiya ta ko sadaka nayi dashi yanzu nake son kadawo min da komai nawa Nasir yanzu zan bar gidan nan bana son ganin ka tsakani na da kai sai alashira.....
da sauri Nasir yace'' Mommy kuskure daya nayi zan nemi yafiyar Nasrim Agrif ya yafenin mommy kibabi dama na gyara kuskure na dan Allah Mommy ki dena FURUCIN na bazaki yafemin ba yayi tsanani akaina mommy cewa fa kikayi KIN TSANE ni mommy ke nasani bane da kowa ke kar kimin haka ki naji Hajja tace'' bata karb'eni a jikan ta ba dan gidan Abdulmajid ba ke bai kamata kimin haka ba ki yarda kedin kece uwata kamar yanda ta fad'a ke nasami mommy mommy ke nasani mommy".

cikin wani irin tashin hankali Mommy tace'' ban taba tsanan wani Abu aduni sama dakai ba Nasir bana son ganin ka zan karbi kakkina ko agaban Shari'a ne".
da sauri Nasir ya fice duk wani file da yasan Yana hannun sa yakwaso da sauri harda woyoyin sa da laptop din sa ya dire agaban momny yace'' Mommy inde abin duniya ne ni na barmiki su halak dinki ne mommyn ban taba tsammanin makiyan mu zasuyi nasara akan mu ba nayi zaton mune zamuyi nasara mommy makiya sunyi Nasara akan mu mommyn akwai abinda ake kullawa acikin gidan nan kar ki zauna acikin dan ba aikin mutum daya bane mak'ircin gidan nan mommyn kuma nasan keda NASRIM!!!!!! ne zaku fi fad'awa ciki amma Isha Allah daga wannan bazasu cutar daku ba zan dauki mataki mommy zan tafi kamar yanda kika buk'ata amma nasan zaki nemeni Mommy kwana kusa zaki ne meni
zan tafi hatta takadduna na makaranta ba zan dauka saboda agidan nan na samesu zan nemi komai da gumina Mommy Allah wadaran abin duniya da zai shiga tsakanin mu Mommy iya kayan jiki na zan fita dashi Naira biyar din gidan nan bazan dauka ba haka ga komai na bar muku zan nemi halak dina yasa hannu acikin ajihun wandon sa yafitar da dukka al'jihun waje alaman bazai fita da komai ba ya juya sai da yakusa fita yajuya yace Mommy dan Allah kije wajen Baba Nasuru kice masa zaki he Lagos kiji abinda zai ce miki yana gama fadan haka yafice da sauri mommy tana kwallah masa K'iran kazo ka zauki shegen yaron ka wazaka barwa su".
juyowa yayi ya mata murmushi ya fice

masu gadi da ma'aikatan gidan suna mamakin ganin yanda Nasir yafita a k'afa suna daga masa hannu sai da yaje fita daga babban get yajuyo yayiwa gidan kallon k'arshe ya fara takawa cikin sauri

Mommy da sauri ta k'arasa part din Baba Nasuru cikin sauri tace'' Baba Nasuru ni zanje Lagos".
azabure ya tashi yace'' Lagos Lagos ki kaini zoki ki kai ni wajen Emaka zan karbo y'ata ZANNA FANNA Emaka muguwa ce a a Sherri akamin ta yarda zata sa y'ata ZANNA FANNA ta tashi arniya dan Allah ki kaini ai kece Halima ko FANNA yan biyun HALIMA ce zan je Lagos na karbo yarinyata maiduguri zamuje FANNA EMAKA FANNA EMAKA

wani irin runguma Mommy tayiwa Baba Nasuru cikin kuka tace'' BABANA.............

*wai ya batun su Abu a hospital ne*

*To masoya muje zuwa rikicin babban gida yanzu aka fara fa da gaske ne Hajja bata yarda Nasir jikanta bane ya Ummu za ta dauki Zainab da jaririn Nasrim mu hade cikin pg 19 insha Allah*



*Bj*
[4/8, 1:48 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
_rikicin babban gida_








*NA*





*BATUL ADAM JATTKO*
*SOSAI NAKE YABAWA DA* *COMMENT NAKU*
*JATTKO GROUP 1*
*JATTKO GROUP 2*
*BATUL BATUL JATTKO GROUP*
*FURUCINA NE 1 2 3 4*
*KANUWA 1 2 3*
*SOSAI KUKE SANI FARIN CIKI ALLAH YABAR KAUNA MASOYA BAZAKU LISSAFU BA*
*SAI NACE KOMAI WUYA DAKU BALLE NO WUYA INSHA ALLAH MUNA TARE OVER AND OVER*




*Allah ya albarkaci rayuwar nawa three brother din* *BABAITU*
*KURU*
*MUNNA*


*19*







" sake d'agowa tayi tana janyewa a jikin sa ta kama hannunwan sa duk biyu tace idan na kai ka Lagos kasan inda Emaka take zaka iya kai ni gidan ta?.

cikin rashin fashinta yace'' sai gobe zamuje gidan Emaka Lagos ah ah zanje zanje".
cin son tasake tabbatarwa tace'' a Pasta yake gidan Emaka din ko".

"Eh eh a layi na ukku ne gidan me number 43 d'akin mu number 6 ne eh eh anan take y'ata Fanna zan karbo".
kuka mommy tacika dayi tace'' BABANA nice Fanna nice Baba".
"to to Fanna ce to Halima zamu karbo".
sai
yazubawa Mommy Ido tare da girgiza ai yace " ai Halima bak'ace kece Fanna Halima dani take maka Fanna tabiyu dogon hancina sai tabiyu b
farin Emaka ai Fanna kece kinsan Halima ansace ta ahanyan Lagos muje mu karbota Fanna ce to to kina sallah ko Emaka bata saki kafirci ba ko"?.

girgiza kai mommy tayi tace'' insha Allah Baba zaka warke zaka dawo tunanin ka gaba daya kama hannun sa mommy tayi suka fita zuwa part din ta bayan tashigar dashi d'aki na musamman ta samu adamu tace" dan Allah Adamu asake kulamin da Baba Nasuru".
Adamu yace'' ai ranki shi dade jikin sa yafara samun sauk'i ada yanda nasan Babban Nasuru bashi da yawan magana amma yanzu gashi yana magana sosai kuma yana cewa shi dan maiduguri ne".

Mommy neman wayan ta
ta shigayi dak'er ta samu hannun ta na rawa take neman number doctor din da yake kula da Baba Nasuru
suna gaisuwa ta daura da tambayar sa
"ammm doctor dama jikin Baba Nasuru ne yanzu yafara magana saide yana yawan suraitar barkatai kuma gashi bai zama normal ba har yanzu".
Doctor yace "Madam ai sauk'in kenan kin san da baya iya maganan sosai yanzu kuma ya samu daman magan sai yazama kamar irin yaron da yafara koyon magana kinsan yadinga surutai kenan amma shawaran da zan bada kudin ga yawan tuna masa abubuwan da ya sani ada da rayuwar da yayi a baya musamman abinda yafi so da Wanda yafi k'i sosai hakan zai dinga motsa brain din shi ko adinga gaishi guraren da yake yawan zuwa da shima zai temaka wajen dawo da tunanin sa adinga yawan yi masa abin yake so da Wanda bayaso hakan zaisa brain din motsawa".
Ok Dr nagode amma idan kasamu lokaci dan Allah kasamu lokaci kazo kasake dubashi sosai".
"Ok madam".

tana gashe wayan
Kamal yana shigowa da dukkan file din da Nasir ya ajiye a main parlour na Hajja yace'' Mommy ga wannan ki adana ai ba abinda zakiyi wasa dashi bane wannan fa shine shedan mallakan duk company na 3AFUL".
Mommy zama tayi tana cewa " Kamal ina maccen ya zan ajiye abu irin wannan kai ya kamata karik'e awajen ka tunda dama ai na Nasrim ne kai kuma kai ne shak'ik'in Nasrim ka rik'e a wajen ka kafin muga abinda Allah zanyi amma shi wancan azzalumin da yabar mana nashi yatafi ka d'auki nashin ka bawa Abu ko daddy su suka san yanda zasuyi dashi nide nawa na Nasrim ne da yaran ta kuma kaine mafi can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login