Showing 15001 words to 18000 words out of 155717 words
Chapter 6 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
ta gama sanin kaso 80 daga cikin dukiyar Alhaji naki ne duk da ba raba gado akayi ba ansan idan aka raba dole za acire kason yaran ki maza har ukku da suka rasu kuma ga tumilin takaban ki ma dayawa ne sai nida Nasuru Wanda baifi kaso 20 ba aci da zamu samu tabbas bazaki gane waye yake sonki da gaskiya ba to bawai bana son ki aure wani bane a a Fanna ina gudu kawo wani b'arakan ne ayanda gidan nan ya ginu da son juna da kwanciyar hankali da zumunci ba zamu so bare ya shigo ba shiyasa muka zauna muka yanke shawaran zamu nemi alfarma a wajen ki duk da muyi da yaran agobe zamu tunkare ki amma naga yana da kyau nafara jin ta bakin ki nida yaran nan mun yanke shawaran zaki auri daya daga cikin su dan gujewa wannan matsalolin da zamu iya shiga idan kika auri bare".
da sauri mommy ta d'ago kai tana kallon hajja
hajja taci gaba "amma idan hakan bai miki ba abar zancen".
cikin karyewar muryar mommy tace'' Hajja kamar yanda bani da kowa sai ku haka bani da wani zafin da zan bijirewa shawaran ki ni ina daukar kine a matsayi uwa mahaifiya umarnin kawai zaki bani ba shawara ba".
Hajja rungume mommy tayi tasa kuka tana sa mata albarka
tace'' kuma Abdulmajid ne fara nuna ra'ayin hakan cikin kwana kin nan yayi mugun takurani akan na fada miki tunda yaga alh Yahaya yazo da batun yana son ki ya gigice abinda na fuskanta Abdulmajid yana sonki sosai son da banajin ko marigayi yana miki shi
kuma Abdulraham ma da muka gaya masa yayi murna da abin sosai".
dasafe bayan an gama breakfast hajja tace'' tana sonyin magana dasu a main parlour bayan yara sun tafi makaranta Hajja ta umarci Abu da yabude taro da addua cikin shikima tayi musu bayanin abinda yake faruwa da kuma amincewar Fanna
da sauri mommy ta d'aga kai ta kalli Mama sai taga murmushi take ita tafara cewa "Alhamdulillah Hajja hakan shine dai-dai dama muma baza muji dadi ba idan a kace yau mommy ta fita acikin mu insha Allah zanci gaba da daukan mommy amatsayin tana yar uwata kamar da Allah yabamu zaman lafiya".?
Ameen sukace dukkan su suna murmushi Hajja tace'' ai Aisha dama nasan bakida matsala balle Fanna Allah yamuku albarka kuma zan kafa na tsare muku daga kuba k'ari.'
ta k'arashe maganan cikin raha
Ummu tayi saurin cewa "Yawwa hajiyarmu mun gode Allah yabar manake".
Hajja tace'' bar saurin godiya kema sai yayi biyun eshe".
tak'arashe maganan tana ged'a kai
duk murmushin sukayi banda mommy data sunkuyar da kai
bayan mazan sun fita Hajja mata tashi ta haura sama dan gabatar da walha Ummu ma tace " bara naje zanyi bak'i ta tashi takoma part din daga mommy sai Mama awajen ganin yanda mommy ta kasa sakewa ne yasa Mama ta mek'e ta koma inda take kamo hannan ta tayi cikin sanyi murya
tace'' mommy dan Allah kar kisa wani abu aranki inde tani ce ba damuwa ni tunkafi Abdulmajid ya aureni ya gaya min cewa bashi da ra ayin zama da mace daya saboda yana son yara dayawa dan dun kafin nashigo nasan ba ni daya bace
kuma dadin da dawa ma a haifuwar bari aka ciremin mahaifa dan
haka kullum cikin baza idon wacece abokiyar zamana nake ta ina zata fito ya halinta yake kullum sai nayi addua Allah yakawomin wanda zamu hada kai kuma gashi Allah ya amsamin nasan ki nasan wacece ke insha Allah zaman mu zai burgr kowa ki Allah yasa nan da shekara ki kawowa Kamal k'anne ukku".
shiru mommy tayi dan bata san me zata ce mata ba ita gaba daya kunyar ta takeji
Dr Hafsat da mommy ne cikin office din mommy Dr Hafsa tace'' wllh ni hjy Fanna banga wani abin damuwa ba Hajja tayi gaskiya dan duk wanda zaice zai aureki dukiyar ki kawai yakeso kiga de cikin mene manki Alhaji Lawan dan uwa na ne
uwa daya uba daya amma bisa amana Abdulmajid shi yafi can canta gashi alk'ali malami masani bazai cuceki ba kuma kinsan halinsa".
Numfasawa mommy tayi tace'' ummm ni kawai abin yana dauremin kai mutuwar mijina ko shakara 2 ba ayi ba amma awani damu sai nayi aure kuma wllh ina mutukar jin nauyin hjy Aisha duk data nuna abin bai dameta ba amma ai kishi kishi...
da gatar da ita Dr tayi dacewa ''a a Maman Nasir karki sa wannan aranki kisa aranki bautan Allah zakijeyi ba jin nauyin wata ba".
cikin sati biyu aka daura auren Dr Fanna da Abdulmajid namiji ba kunya aranan a part dinta ya kwana
da safe tana zaune gaban mirror tana gyara durin d'an kwalinta ya fito daga wanka towel daure a k'ugunsa yana jifan ta da murmushi tacikin mudubin gaban tane taji ya fadi da ake cewa Abdulmajid da Abdulsamad suna kama ba tagani ba sai yau ta sake tabbatarwa komai nasu irin daya hatta yanayin yanda yake tafiyar da mace kamar a makaranta daya suka koyo ban banci kawai Abdulsamad yafi Abdulmajid haske k'adan
tana cikin wannan tunanin taji ya dafa kafadunta da hannayen sa ya daura kansa awuyar ta ruwan jikin sa yana diga jikinta yana cigaba da yimata murmushi
yace " dan me akayi mudubi?."
bata bashi amsa ba saboda wani irin mamaki da tambayar ya bata idan marigayi ne amsa take bashi da dan ya hasaka sirri fukka shikuma sai yace amma yafi kyau ga masu hasken fata irin ku saboda kinga kekika haska mudubi bashi ya haska kiba,,
jinya ciji gefin kunne ta ne ya dawo da ita daga cikin dogon tunanin ta yace Doctor mubudi ma yafi son masu hasken fata irinku kiga kekika haska mirrorn bashi ya haska kiba ".
ya k'arashe maganan yana kashe mata ido
murmushi tayi tace'' ummmm abin yana bani mamaki ne yawancin kalaman ku irin daya".
mek'er da ita yayi tsaye yakai hancinsa dai-dai nata ahankali yake tifo da kalaman acikin mak'ok'oron sa yace my heart ai ba kalamai ba hatta zuciyar mu iri daya dan munyi tarayya da juna dashi azuciya akan abu daya aranan da nafara ganin ki aranan nakamu da soyyyar ki ina shirin gaya miki naci karo da wasiyar Halima naki auri dan uwa na aranan ba k'aramin tashin hankali na shiga ba dak'er da temakon Allah na jure na daukeki amatsayin matar dan uwa na Fatima ban dauki son ki dawasa ba dan Allah ki bani matsugun ni ko ya yake na miki alk'awarin zan shafe Abdulsamad acikin zuciyar ki nin kinga kin tunoshi to wajen addua ne amma bawani abu na rayuwa ba, Fatima I love you all my heart very very gashi kin bani farin cikin a dare daya kin kaini duniyar da ban san ana zuwa ba Fatima Ina miki sonda ban san iyakan saba".
zaunar dashi tayi tana masa murmushi tace'' nagode sosai".
ta dauko Mai tafara shafa masa aranan de ba dasu akayi breakfast ba har angama watsewa a falon Hajja suka shiga ba itaba shima yaji kunya musamman na uwar gidan sa Aisha
Nasir kam sai akwana na biyu yasan gidan nasu ya sauya tsaye yake abakin kofar mommy knocking yake sosai dan amma shiru Agrif yashawo saman yace Nasara zamuyi letty fa Nasir da gaba daya ransa yagama baci yace "dalla jeka ni sai na gaida mommy jiya mafa ban gaidata ba...
bude kofar akayi mommy ce daga ita sai rigan bacci zai shiga ciki ta fito ta kama hannusa suka fito ta rufe kofar kallon tuhuma yamata yace "mommy bazamu shiga d'akin ba gaidaki fa zanyi".
murmushi tayi tace'' son mu gaisa anan karkuyi letty'.
Yasake cewa "mommy da asuba naga daddy yashiga d'akin ki kuma jiya ma da naje gaida daddy kamal yacemin daddy a part dinmu ya kwana me daddy yakeyi a d'akin ki?".
tambayar ya daure mata kai dama shi take gujewa rasa mezata ce masa tayi ta sauk'e ajiyar zuciya
tace'' kasan tunda muka dena kwana tare nake jin tsoron d'aki na kaga kaima Agrif ya dowo d'akin ka shine nima daddy ya dawo d'ak ina kuma ma ba kullum zaina kwana anan ba wataran part din su wataran nan". kallon ban gamsu ba yake mata yawani hade fuska
amma baice komai ba yajuya zaibi bayan Agri
Mommy tace'' my dear ko ba kason kwanan daddy din anan ne".
juyawa yayi yana kallonta kai tsaye cikin maganan sa na isa tace " eh mommy ai shi namiji ne me yasa zai zo d'aki ki ai malamin islamiyar mu yace ba kyau namiji da mace suna kwana a dadi daya inba mijin gidan bane".
wani irin faduwa gaban mommy yayi tana mamakin malaman yanzu yanda suke fayya cewa yara komai tun basu kai matakin hakan ba yanzu d'an shekara tara har ya isa sanin komai amma afili kuma
tace'' kai my Son daddy ma ai mijin gidan nan neko".
shima cikin mamaki ya kalleta yace" a a shi daddy mijin Mama ne kemuma Abba na ne mijin ki nide gaskiya Daddy ya dena shigowa d'akin ki".
dafa kan sa mommy tayi tace'' oooo Nasir zaka ku makara idan kadawo sai muyi zancen kaji".
cikin fushi yafice ko gaisuwar bai mata ba
to haka mommy tayi ta shan tambaya a wajen Nasir cikin ikon Allah auren daddy da mommy bai cike wata 3 ba ciki ya bayyana ajikin ta alokacin Ummu ma tana daciki zaikai watani 4 tare sukayi goyon ciki har Allah ya sauk'i Ummu lafiya awannan karon macce ta haifa ayanzu yaran Ummu sun cike 4 Agrif Aiban Abbati sai wannan jaririyar me sunan Mama akasa wato kishiyar mommy Aisha anaki kiranta Humairah Hajja da kowa na gidan yanzu sai Humairah awajen takwaran ta Mama take wuni sai idan zata sha nono akawota wajen Ummu
bayan wata 2 itama mommy Allah yasauk'e ta lafiya kyakkyawar yarinya mekama dasu daddy su Agrif bak'a bata biyo mommy da Nasir ba
Nasir yana dawowa a makaranta zai wuce sama sai Dr Hafsa
tace'' Nasara kogani kafi mutum Nasara me wuyar badan ci baka ga jaririya ba kayi k'anwa "Mami nagani".
atunanin sa Humairah ce dan haka ya yamutsa fuska yace "nagan ta mezan mata".?
Dr Hafsat tayi dariya tace'' shikenan zan tafi da ita gida zan bawa Ayman dama matar sace namasa kamu".?
bai sake magana ba ya hakura sama sai Agrif ne yagane mommy ce ta haifu dan haka jefar da school bag din sa yayi yatafi da gudu
ai yana arba da yarinyar yasa wani irin ihu yana cewa "woow mommy haifa mata ita kikayi mommy kiga tafi Humairah kyau sosai kyakkyawa ce mamin Ayman bani ita".
ya k'arashe maganan yana zama akan kujeran yana washe baki Nasara da bai k'arasa hayewa ba yaji yakasa tafiya yajuyo yana kallon inda suke ahankali ya sauko yasa hannu yaja tawel din da aka nade yarinya sai da yamata kallon kamar na second 9 ya yamutsa fuska ya koma baya yana kallon mommy da take kurban tea itama shi take kallo yace mommy meyasa baki haifi fara kamar mu ba kika hafi wannan bak'ar ai wannan k'azama ce nide wllh bana son ta kuma kar a haura da ita saman mu".
ya k'arashe maganan yana yarfa hannun sa daya taba tawel din alanman yana tsantsanin hannu sa
Hajja ta meka masa zagi da hannu
tace'' kai ungo naka".
kallon raini ya mata yace " a a rik'e abin ki."
cikin matsifa Hajja
tace'' kai har ka isa kace kana k'amar bak'i uwar ka Halima bak'a uban ka Abdulsamad baki kaimu kaf dan ginmu ma bak'ak'e ne waye kaga fari kaima wayasani ko a hasbitin aka canjo ka da kanin b'akin halin ka baka gado mu ba idan an haura da ita saman ka kasheta".
shima cikin matsifar da dama sun saba shida Hajja yanuna mommy da yatsa yace kinga uwata farace tas niban san wata Halima ba... mommy ta ajiye cup din hannu ta
tace'' my Son jeka ka cire uniform din ka''.
wani dogon tsaki Nasir yaja yafara hayewa
Hajja tace'' Fanna kinga irinta ko ke kika b'ata yaronnan gashi yanzu y'ar da kika Haifa ma yace ba yaso kuma kinsan tunda ya furta baya so baya sonne nifa halin yaron nan tsoron yake bani bak'in halinsa fa k'aruwa yake" .
Mommy tace Hajja Nasir yarone zai dena".
Hajja tace''d'an shekara goman ne yaro"?.
shiru mommy tayi
Dr Hafsat tace'' gaskiya Dr Fanna ki duba al amarin yaron nan ki ajiye son da kike masa ki fara fashim tar dashi abu mekyau da barar kyau dai-dai da ba dai'dai ba ya kamata da rashinsa ba wata uwa wanda bata son d'anta saide hakan take dannewa da nusar dashi hanya......
Nasir da har yakusa hayewa yaji kalaman mamin Ayman sun gama bak'anta masa rai afusace ya juyo cikin rashin kunya yace "ke kije kinunawa Ayman dai-dai mana aishima jakin ajine kuma kullma sai yayi Letty kiji da kanki malama."
ya k'are maganan tareda jan uban tsak'i ya haye cikin sauri
Hajja tace'' kunji ko yaron nan wata rana dukan mu zayyi harke me daure masa gindin tunda gashi yafara da zagin aminiyar ki".
mommy tace'' Hajja zagi kuma ai amagana Nasir ba kalman zagi martani kawai ya mayarwa Mamin Ayman''
Mommy ta kalli Dr Hafsa tace'' amma dan Allah Dr Hafsat kiyi hakuri haka Nasir yake bayason a shiga harkan sa kuma inda Nasir zai shekara da mutum wllh baya shiga har kansa sai yashiga nasa".
cikin mamaki Dr hafsa take kallon mommy tarasa wacce iri yace ita itade tasan wannan ba tarbiyya bace mekyu amma afili tace
'' to Allah ya shiryeshi Amin mommy tace'' tana mek'ewa tayi sama
Hajja tana nunata da baki tace'' ta tafi lallashi
Mommy kai tsaye d'aki Nasir ta wuce a tsaye a tsakiyar d'aki ya dafa kai ahankali ta k'arasa inda yake ta zaga tasa hannu tacire hannusa akan ta girgiza ai tace'' am sorry kan ka ko ciwo amma meyasa kake da daukar zafi da wuri ka din ga hakuri kuma zakabawa Mami ku hakuri".
"me nayi mata zan bata hakuri ai ita ta zageni har tana cewa a dai'dai tani".
"kayi mana cewa fa kayi bakason k'anwar ka saboda bak'ace kuma mummuna".
"mommy nide ba k'anwata bace kuma wllh bazan taba sonta ba na tsaneta".
cikin damuwa tace''
''Meyasa katsaneta naga kai kake ta cewa kafison na Haifa maka y'amace kasa mata suna *NASRIM*".
cikin fusata yace
"Eh amma yanzu bana sonta Mommy kinsan fa duk yanda nake son abu idan wani ya rigani ina hakura meyasa Agrif zai rigani daukan ta har yana cewa tana da kyau ni yakamata na riga kowa ganin ta".?
numfarawa tayi tace'' amma kaima kasan farin jini irin na jarirai nida na haifeta ma har yanzu ban dauketa agaban mutane zakace bakason k'anwar ka".?
cikin k'osawa da maganan yace
"Mommy ki dena cewa k'anwata niba k'anwata bace k'anwar Kamal ce tunda y'ar gidan daddy ce ni kannena sun rasu yaran Abba na ".
wani irin nauyi maganan nasa ya mata lalle Nasir yazuce duk yanda take tunani gashi da azabeben kishi ta jima da sanin yana kishi da Daddy".
Murmushi tayi afili
tace " ok ni ina son ta kuma sunan maman ka Halima ce zamu kirata NASRIM kamar yanda kace da farko".
"Wllh mommy ko da sunana Nasuru aka k'irata ba zan sota ba tunda aka rigani cewa tana da kyau".
"Ok am sorry my Son kayi wanka kaci abinci ka kwanta kan zai dena ciwon".
gyada mata kai kawai yayi har tajuya zata fita
yace" mommy anjima zanje aski kuma zanje gidan su Ma'aruf abokina".
"Ok amma kar kace zakaje kai daya Ya'u drive yakai ka yadawo dakai kuma ban yarda kace basa yabar ka acan ba".
"Ok thanks my mommy."
a parlour ta samu Dr Hafsa Hajja ta fita su Mama ma sun fita dr tace'' mommy Nasir zan tafi sai tomorrow insha Allah".
mommy tace'' ok nagode sosai Allah yabar zumunci Dr kuma ina k'ara baki hakuri akan lefin Nasir ".
murmushi Dr tayi tace''ba komai Dr Fanna kece ma za abawa hakuri dama yawanci marayu haka suke shiyasa rik'on su yake da Lada amma dan Allah ki dage ki kula da tarbiyar sa kisani amana ne ahannun ki".
nisawa mommy tayi tace''hakane zan kula amma kisan me wllh bani kad'ai na batashi ba har da Hajja dan yanzu dani nafara masa magana yafusata shi haka fashewa da kuka zatayi tana cewa ai maraya ne ko tanemi cewa bana son sa wllh Hajja wata iriyace da ba agane ina ta dosa kuma Wllh ayanzu aduniya ba Wanda Hajja take so kamar Nasuru ko yaran nata bata so Kai ko shi marigayi bata masa sonda takeyiwa Nasir duk wannan fad'an da tayi na burgane wllh inda zakiyi awa daya agidan nan da zakiga yanda zata shigo tana basa hakuri kamar zata masa sujjada shiko bawani wanda ya rena kamar ita'..
Dr Hafsat tace''gaskiya naga alama bata mintuna 30 ba ta ambace shima keda ita bansan Wanda yafi wani son Nasir ba".
Haka aka sha sunan Nasrim duk da bawani shagani akayi ba dan Hajja ta hana wai acewar ta rabon tane ya kashe mata d'a dama ance rabon y'amace kisa yake dan haka ko daukar ta batason yi kamar sauran jikokinta
haka Nasir da gaskensa yake nunawa Nasrim k'iyayya musamman dayaji FURRUCIN Hajja na cewa ai adalili ta Abban sa yamutu ko ganin ta bayasan yi ko shiga yayi yaganta a hannu mommy to sai de yafita idan taga haka ita zata ajiye Nasrim ta fito wajen sa tun mommy tana daukan abin a k'uruciyar har abin yafara bata tsoron da akwai randa ta samesa.....
*To masoya mu hadu a page 4 insha Allah nagode*
*Taku BJ*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCINA NE*
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCINA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*Page 4*
NASIR ta samu ya toshe mata hanci sai famar wutsilniya take a k'afa da hannu
cikin sauri