Showing 30001 words to 33000 words out of 155717 words

Chapter 11 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

632

ta yayi mugun hawa lokaci daya haka me yasame ta da girma haka".?
cikin kuka suka ce basu sani ba
haka aka wuce da ita hospital
********************
a hankali ta bude idon ta da take jin ya mata nauyi idon ta ne ya sauk'a akan nasa yana rike da hannuta wanda ake mata k'ren ruwa dashi shima idon sa akan ta juyawa tayi tana kallon sauran mutane mommy Mama Ummu da Abu da daddy
Daddy yayi saurin cewa "daughter daughter ya kika ji jikin naki me yake damun ki meye damuwar ki me kike so".?
Murmushi tayi tare da tura lips dinta na k'asa cin bakin ta ta matsa a hankali tace
"Daddy kawai dama jinayi kaina yana min ciwo amma yanzu banajin komai dan Allah mutafi gida".
Mama tace'' damana fada bawani abin da yake damun Nasrim to meye ma zai dameta kawai fa rashin bacci ne ni nasan kwananan tana ta faman shirye shiyen zuwan Agrif bata zama sam itace wankin kai da kitso kunshi shekaran jiya fa da kanta ta tafi kasuwa wai baza a mata yanda take so ba gashi agarin burgr Agrif y'ata zata sawa kanta ciwo".
dariya sukayi amma banda Agrif da mommy ita mommy daya ke likita ce tabbas tasan da akwai abin da yake damun ta
Nasrim kallon hannu Agrif dayake cikin nata tayi a hankalin ta zame hannun ta tasa daya hannuta ta finciko drip din yafice kafin wani ya yunkura yace wani abu har ta sauko Abu yace" subahanallah ya haka Halima?".
"Abu bana son hospital din mutafi gida".
Daddy da Abu za suyi magana mommy ta dakatar dasu da cewa "a a Abu mu tafin kawai bawani abu zan kula da ita ko agidan ne".
part din mommy aka wuce da ita har cikin bedroom din ta da misalin Sha daya na dare bayan kowa ya watse mommy ta zauna abakin gadon tana kallon Nasrim da tayi sanyi sosai tace'' what is it you're doing Nasrim
kau da kanta Nasrim tayi cikin sanyi murya tace"
everything happens to meye ma bai faru dani bane mommy amma ke ba uwar data dace tasan damuwar y'arta bace".?
"Why zaki fadamin haka Nasrim me kika nema kika rasa a wajena".
Mommy so so na rasa soyayyar ki mommy kin fison wani daban bani ba tun ina jaririya kika yakice ni ajikin ki kika nisan ceni ban jima da sanin wai kece kika haifeni da cikin ki ba azatona Wanda kike so shi kika haifa nikuma Mama ce uwa ta to mommy nasamu labarin yanda keda da'n ki kuka azaftar dani ina tuna wani lokaci da yazo kikace kar na sake shiga part dinki har sai ya tafi idan gaisuwa ne namiki idan mun hadu wajen cin abinci a parlourn Hajja tun daga lokacin na dena zuwa part dinku sai de idan na ganki na gaisheki kin taba damuwa da wannan wani lokacin zamuyi kawana 3 bamu hadu ba musamman san da muke secondary kafin kutashi mun tafi idan mun dawo kungama cin abincin dare kowa yakoma part din sa kwanaki nawa nakeyi bangan kiba so bawani shak'uwa da yake tsakanin mu wanda zaki ji damuwata ba
bakya sona Agrif ne yakare rayuwata daga sherrin da'nki kuma yanzu gashi shima Agrif na rasa shi shikenan".
"Nasrim please finish ba dogo magana na tambaye kiba because ban taba ganinki cin wannan yanayin ba Nasrim ba uwar da zataki y'ar data haifa ina da nawa manufar na janyewa a jikin ki but bazan iya jurewa ganin ki haka ba mek'e damun ki Nasrim hankali na a tashe yake akan ciwon da naga yana barazanan samun ki Nasrim zuciyar ki cefa ta kusa bugawa wanda tsananin nisan kwana ne yake sa mutum ya tashi tabbas wani abu ne yafaru dake me girma Nasrim bani da kowa sai ke da Nasir a kullum burina Allah ya hadamin kan ku kuso junan ku shine buri na kuma ni nasan duk dare gari zai waye wata rana shida kansa zai furta yana son ki dan shima bashi da wanda yafiki a rayuwa Nasrim ki gaya min damuwar ki?.".
ta k'arashe maganan cikin kuka me tsanani tare da rungume Nasrim din tasa ta ajikin ta sosai
Nasrim ajiyar zuciya ta sauk'e jinta ajikin mommy taji wani sanyi aranta wanda sai yanzu taji hawayen data kasa fito dashi tun dazu ya fara fitowa da k'arfi

cikin kuka tace'' mommy ya Agrif yace bani yake soba Izza yake so mommy idan yasan bani yake soba meyasa ya zalinci zuciya ta ya dasa mata son sa b.....
awani irin zabure mommy tayi tare da mek'ewa tsaye tace''me !?
Izza a a wllh ko kaffara bazan yiba ke yake so ya gayamin wannan tun ranan da aka haifeki kuma ko kwana nan maya gayamin ke yake so bari na kirashi".?
tayi maganan tana daukan wayan ta dayake kan bedside da sauri Nasrim tada katar da ita
"Mommy ya riga ya furta Izza yake so kuma yace har cikin zuciyar sa har yana cewa _shi baki dan aike ne abin da yake cikin zuciya yake furtawa_
wllh mommy na hakura dashi ko yanzu yace ni yake so bazan so shi ba ni ina da kishi bazan auri wanda ya furta yana son wata ba ki min addua Allah yabani wanda zan so shi fiye da shi kuma wanda bazai min kishiya ba".
Mommy tace'' gaskiya ni ban yarda da wai baya son ki ba saide da abinda ya can za masa ra ayi".
Nasrim tace''mommy kyan ta yagani".?
"tsak'i mommy tayi tace'' Izzar banda farin fata me ta isa ta nuna miki ke abu nawa kika fita idan ana maganar kyau ta isa ta tunkaro inda kike ma dade abin da ya sauya Agrif amma ba wai kyanta ba kuma har yanzu Agrif yana miki tsananin son".
ta k'arashe maganan tana danna wayar ta da nunawa Nasrim wani pic din ta ire iren wanda Agrif yake daurawa a status din sa da kalaman soyayyar da yake daurawa Nasrim duk da tun ranan daya d'aura ta gani amma jitayi yanzu ma tana son sake karanta kalman da yarubuta kamar haka
_ME RIGUNA DUBU HALIMA AI KWALLIYAR KICE ME HALI DABU HALIMA AI MARTA BAR KI CE

sai wani da yasa
BURIN HARUNA HALIMA ARA NA KE DAYA CE A ZUCIYA KIRIK'E KI AJIJ DADI WUYA NA D'AU ANIYA_

sai wani wanda ya rubuta
_i na son ki na yaba da halin ki k'yan jiki da suran ki_

Sai na gaba wanda yarubuta
_masoyiyya ta nada kyau kuma bataji da kai hakan ne yasa ake mini barka sonki ya cikin jikina buri na dare da rana_
dade sauran su dama mommy yana daurawa dake dauka ta adana a wayan ta dan tanan take samun pic din Nasrim ajiyar zuciya Nasrim ta sauke tace "mommy ya cutar dani da kalaman da suka fi wannan ma". Mommy tace
"dan de kince ko yabar Izza bazaki soshi bane da sai nayi yan da nayi kika sameshi amma tunda kikace na miki addua in Sha Allah zan miki Allah yasa hakan shi yafi alkairi kuma nafi damuwa da kicire komai aranki ko agidan nan kar ki nunawa kowa komai kibi abin ta yanda yazo miki kuma ki samu Izza ki gaya mata kamar yanda yace kinji".
"to mommy amma a yanzu ba sai gobe ba zan kira Izzar na sanar mata".
da wani irin k'arfin gwuiwa ta mek'e tafita
a parlour n Hajja ta samu Izza kamar yanda ta zata tana aikin nata wato kallo
kama hannun ta tayi suka tafi k'aramin falon Hajja cikin dauriya da nusuwa ta mata bayani
komai amma tayi mamakin ganin farin ciki a face din Izza kuma ba musu ta amsa tayin soyayyar Agrif bayan tasan yanda Nasrim take son sa
a wannan daren de Nasrim bata wani samu baccin kirki ba
*****************
Washe garin tashi tayi cikin walwala dan tasa niyar danne abin sosai a ranta a hankali take takawa duk inda ta gif ta ma'aikata suna mata sannu cikin murmushin take amsawa
Part din su ta nufa kusan cin karo sukayi da Zahra da Humairah su zasu sauk'o ita zata hau kama hannu su tayi sukayi saman a k'aramin falon saman suka zauna cikin nusuwa ta musu bayanin sak'on Agrif
Humairah tayi tsalle ta dire tace ina wllh bazai yuwuba da Ummu zanje na hadashi...
hannun ta Nasrim ta kamo tana murmushi tace'' a a Hummee Ya Agrif duk yamin bayani kuma na gama gamsuwa dasu dama can nice nake ganin kamar son aure yake min ashe son yan uwan taka ne Itama Izzar tun jiyan wajen karfe Sha biyun dare na k'irata muka zauna na mata bayani kuma ta gama gamsuwa".
Zahra tace'' ta amince fa kika ce bayan tasan shine zabin ki bazata iya sadaukar miki shiba."
Humairah tace'' ai ni shiya sa dama can Izza ba wani burgeni take ba wllh fuskar salihai kawai take yabawa a zuci ba haka bane in ban da munafuka sarai tasan yanda kike son ya Agrif mutum ko awa daya yayi dake ai zai san matsayin sa awajen ki balle ita da muke Kwana mu tashi tare" .
Murmushi tayi cikin rashin damuwa tace "Please come down duk Wannan ya wuce nawa ne za ayi soyayya kamar acinye juna amma daga k'arshe ba za'a auri juna ba balle nida bai taba cewa yana min son aure ba".
Zahra tace'' shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkairi amma wllh ko duk jikina kunne ne ban yarda Ya Agrif bake yake so ba kawai de ya canza ra'ayi ne jiya zuwa yau".
cikin slow voice's tace ''haka mommy ma tace amma ku tayani addua Allah yabani k'arfin dan gana".
Humairah share hawanen idon ta tayi tace'' amma meyasa baki fada masa kefa shi keke soba wllh da zai soki meyasa baki bankad'a surruka kin temaki Yaya na ba Nasrim wllh yayi babban rashin ko nace asara."
ta k'arashe maganan cikin tsananin kuka na abin yana damun ta
muryar Izza suka ji akan su tace
"Ah ashe ku dama anan kuke tun dazu ana ta neman ku meeting parloun Hajja".?
Zarha da Humairah ne kawai suka d'aga kai suka kalli Izza da taci wani gayu na musamman cikin wani riga da sket na less Blu mezanen ja bata daura dan kwalin ba tayi rolling da yellow wani yaluluyin mayafi sai zabga k'amshin take
Nasrim data goge hawayen ta afak'aice ta tago tana murmushin tace'' meeting lafiya kuwa?".
Izza g'aga kafadun ta tayi alaman bata sani ba tayi gaba
mutane gidan zube a parlourn Hajja iyayen sune asaman kujera Hajja ma a hakimce akan kilishinta na iko sai yaran da suke k'asa
gyaran murya tayi tana kallon Abu tace'' Abdulrahaman ka bude mana da addua bayan ya bude ne Hajja ta nisa tace'' dalilin taraku anan Haruna ne yazo min dawani batu da ban gane ba wai yana neman izinin auren Izzatu bayan mu duk a daukan mu da Halima yake soyayya wanda nima shedace kullum ina bude status din sa hotunan Halima da kalman soyayya amma jiya da daddare har da kukan sa wai shi ba soyayyar aure yake mata ba abin ya bani mamaki shine na tara ku anan Haruna maimaita abin da kace min a gaban iyayen ka".
tsunkuyar da kai yayi cikin swoly voice dinsa yace Hajja " nifa ban taba cewa kowa ina son Nasrim da aure ba abin da nasani tun Nasrim tana jaririya nake mutuk'ar son ta amma bawai yana nufin aure ba ina ganinta tamkar Humairah ne wato muharramata ". mommy " tace shi kenan Agrif kowa ya fashimceka ita Nasrim din ma munyi da ita tace ba soyayya a tsakanin ku".?
Ummu tace'' Agrif kai ne me cewa ba son Nasrim ka keba".?
ta fadi maganan cikin b'acin rai sosai dan abin ya girgiza ta ta gama sa rai da surukar ta da Nasrim
Daddy ma abin ya bashi mamaki amma sai ya danne yace "shike nan Agrif ai bawani matsala Izzatu y'ar gida ce a cikin gidan nan ta tashin munsan halinta dana Baban ta insha Allah ayau zan yiwa Baban ta maganan saranan auren ku dan mu burin mu kenan kufito da mata kuyi aure ayanda kuke rike man yan kudi ya ka mata ace kuna da iyali hankalin mu zaifi kwanciya Masha Allah Allah yamuku albarka".
shiko Abu tsabar ta k'aici bayyi magana ba
Hajja tace'' to nima de sai de nace Allah yasan ya Alkhairi dan ada nace bazan yarda abawa jikokina marar asali ba amma ganin yanda Izza take da hankali da biyayya har tafi su Halima hankali da yimin biyayya idan nace ban yarda ba Allah bazai barni ba dan abinda Izza take min Allah yabata mai yimata nide anawa bangaren ba wani damuwa ta kalli Humairah da Nasrim da zahra tace tofa kuma kufidda naku dan duk tare za a hada har Kamal da Aiban da Abbaty da wancen bayahuden mu huta duk kun isa aure ".
haka de aka tashi ran da yawa daga cikin su ba dadi musamman daddy dan kiran Nasrim yayi har d'aki yake tambayar ta ko sun samu tsabani ne da Agrif yasa ya canza ra'ayi tace "a a Dad dama ba yanda kuke zato bane".
******************
bayan kwana biyu

sosai abin yake damun su Humairah yanda Izza take wani zak'ewa akan Agrif ko halin da Nasrim take ciki bata gani dan kowa yasan ta canza daga me yawan fara'a takoma me sanyi me shiru shru ko makarantan ta kasa zuwa
haka shima Agrif duk da yanda Izza take shige masa kokarin kulata da cusata a zuciyar sa kawai yake shi yanzu babban damuwar sama yasamu yasa Nasrim a idon sa yana son bata hakuri amma ita kuma ta toshe duk wani hanyar da tasan zai ganta ga Humairah da zahra yaga kamar fushi suma suke masa dan idan yace su kira ta cewa suke bacci take gashi bata daukan wayan sa akwai maganan da yake son gaya mata sai de yarasa hanya amma yanzu yacewa Izza idan ta shiga ta turo masa ita

Nasrim kallon su Humairah da suke ta damun kansu akan Izza tayi cikin sanyin murya tace'' "Hummee dan Allah meye lefin Izza ne ita fa ba ita tafara cewa tana son saba yaka mata ku sassauta mata dan Allah".
tabe baki Hummee tayi taci gaba da danne dannen wayan ta
Zahra tace'' shikenan Nasy ai dama ba gane wa zakiyi ba nifa yanda take nuna zak'ewa ne yake bani mamaki kamar dama haka take so yanzu haka fa ta cab'a wanka ta fita wajen sa".
Hummee ta danna wani uban Asher wanda ya razana Nasrim da Zahra suka juya suna kallon ta da sauri ta mek'awa zahra wayan hannuta tana cewa lalle wannan Izza butulu ce har mu zata zauna tana daurawa habaici a status".
ta k'arashe maganan tana mek'awa Zahra wayan ta Zahra ta k'arba tana gani hoton Izza ne da Agrif sunyi kyu sosai tayi rubutun ajikin hoton zahra ta fara karantawa a fili kamar haka _yanda Allah yaso ramarin sa yabar damun ku yanda duk yatsara shi ba mai iya juya fa_
sai wani na ita daya tayi kyau sosai wanda tasa
_SA'A YAFI GATA_
atare suka sauk'e numfashi Humairah mek'ewa tayi tsaye tana cigaba da dura aher

*to masoya muje zuwa shin da gaske sa'ar zaifi gatan kamar yanda Izza tace me Agrif yake shirin gayawa Nasrim ina labarin Nasara namu*


*B JATTKO*


[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURRUCI NA NE*
( *rikicin babban gida*)



*BATUL ADAM JATTKO*

*rikicin babban gida*

6

Humairah sai sake maimaita SA'A YAFI GATA take tace wato tana nufin Nasrim y'ar gata ita me sa'a
ko Wllh sai ta san tayi da y'an halak ba marassa asali butulu ba shikuma ya Agrif kin barshi kenan bari na har abadan Allah zai baki wanda yafishi in Sha Allah zakiga ri ban hakuri".
Izza da zata shigo d'akin K'iran Nasrim taji duk abin da suke fada komawa baya tayi ta tsaya a dan korodo tana murmushi tana danna wayan ta tana ne man hoton Agrif tasamu Wanda yayi kyau sosai ta daura sabon a status dinta ta rubuta
_samun irin ka zayyi wahala Dan ba a b'ari akwashe d'uka_

sai wani da tasake rubuta
_sai Dana tace na_
_zab'oka aduniya Kai ne gayya mazaje kubi baya babu rinka na duba duk nahiya_

gashi dama duk ta rufe manyan gidan kafin ta d'aura status ta yanda ba zasu ga status din taba sai su Humairahn da tayi domin su kuma gashi sak'on yaje inda take bukata tayi murmushi a san data ga alaman an bude sabon status din a wayar Humairah
dan dama basu fita a status din ba tana tsaye sai da taji Zahra tace'' to ai gawani ma".
bayan sungani Nasrim ta dafe k'irjinta
tace ''lalle Izza bata san zafin so ba bata san rad'adin rabuwa da masoyi ba da baza tamin haka ba saide tamin addua duk da gaskiyar ta ba a b'ari akwashe duka hakan bazai hana tamin addua mafi alkairi agun Allah ba tunda Allah yayi duniya da fad'i kuma gaskiyar ta samun irin ya Agrif akwai wahala wacce ta samu dole takira kanta me sa'a kun man ta nida irin rawan kan da nake akan sa azatona Sona yake ai ni abinda nayi ya wuce nata amma yanzu duk wannan abinda yake faruwa bai kamata ba bana son mu samu matsala da Izza dan halinta na kirki da Kamala dan kuskure daya bai kamata kuna mata wannan fassaran ba
ba danni ta daura duk wannan kalaman ajikin hotunan ba giyar so ne kawai ni nasan waye ya Agrif yafara rud'atane da soyayyar sa mezafi amma kar kuyi zaton dani tayi hakan zargine bai kamata ba muyi kokarin dawo da Izza cikin rayuwar mu kamar da muzauna lafiya kada iyayen mu Susa wani abu aran su".
Humairah tace'' haba Nasy ke baki fashimci zafin kalaman ta ba ko? whll habaicine ki duba wannan wanda ta saka na k'arshe nan mana".
ta k'arashe maganan tana mek'awa Nasrim wayan Nasrim ta k'arba ta karanta afili
_yanda Allah yaso lamarin sa yabar da mun ku yan da duk ya tsara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login